Showing 72001 words to 75000 words out of 82431 words
Dakin yara tana karatu sun kusa fara Jarabawa Ni da Anum me muke kwance ita har tayi barci ni kuma ina faman sake sake a daran nan na yanke ma kaina abunda zai fissheni bayan na roki Allah kada ya barni ni kad'ai ya yi min jagoranci.
Da Safe wasai na tashi,Duka aikin gidana ni nayi abuna. Abun kari kawai Hafsah tamin,Sai aya data wanke ta mikamin nika kafin ta fita,ni kuma sai ta barni da Dafa zobo,Ganin yadda nayi ne ko da Safe saboda a gaban yara ne muka gaisa na Sakar mai Fuska suna watsewa na had'e raina gim ko fara'ata bai gani ba.
Mama ta aiko Anum ta kirani ina zuwa na durkusa na kara gaisheta ta amsa cikin kallona Lokaci d'aya tana fadin"Ishaq ya same ni da wata mgana. Wai zaki koma Dakin yara Zainab zata zauna a dakin ki nace kin amince ne yace eh! shine nace sai na tambayeki"
Kai tsaye nace"Eh Mama yau zan fara ma Tattara kayana. yaran kuma duk inda ya ijiyesu daidai ne a wajena"
Sai ta muskuta tana fad'in"yaran ba matsala ga daki nan su zo mu zauna damam xaman kada'ici ya isheni kece bana so mu kara yi miki wani rashin adalci kamar yadda muka yi miki a baya,Shiyasa nace sai naji ta bakin ki,ki fad'amin in hakan bai miki ba to bai isa ba"
Sai nayi mirmishi takaici kafin nace"Bakomai Mama na amince ni daman ba mazauniya ba ce.Dakin daman ai jingina ne, Zainab ce ke da wajen zama na har abada"
Nasan bata gane kan mganata ba, sai dai nauyin baki yasa ta kasa min mgana har na fice,ina komawa Daki bayan mun gama hada zobo mun zuzzuba agoruna Anum ta jera a Frezee,kunin Aya ne zan had'a shi jira nake nepa su kawo wuta.
Anum na bar ma sharan Falo da gyaran kitchen, ni kuma na shiga Dakina na fara had'a kayana a waje daya duk abunda nasan nawane na Daukosa babban ghana d'aya gareni itama sakon kayan sallar yara aka kawo aciki daga kaduna kuma tamin kad'an sai na kira Hafsah nace in ta shiga kasuwa ta siyomin manya guda biyu
Kafin dare wardrope dina kaf ba kayana aciki Hafsah ta siyomin manyan ghana guda biyu sun isheni na dura komai nawa,aciki akwai wasu kayan da ko di'nka su ban yi ba. na Ishaq ne ban kara dinka kayan da ya siyamin ba,tun bayan auransa da zainab hatta kayan da Anty Binta ta bani na Fad'an kishiya suna nan suma na Had'a masa kayansa waje daya.
Gadajen yara daman duk ya b'abb'alle,sai nayi tunanin na basu na Dakina da wardrope din ya ishe su saka kayan su,nasu kuma a gyara ma Anum tunda ita macece ni ba zama zan yi ba,so kayan basu da amfani a wajena.
Da dadadre suna falo da shi yana musu karatu,na fito ina kallon Amir kafin nace"Amir ku fara had'a kayanku waje daya,ka taya kannen ka su had'a nasu .Anum na fara had'a miki naki kema kije ki karisa in kun gama"
Da mamaki suke kallona ammh sai na juya zuwa kitchen ina ji suna tambayanta Umma ina zamu..?
Sai na bar mishi ya basu amsa sai kuma ya kasa ina kitchen din ya Biyoni yana fadin"Fa'iza bafa yanzu ba ne naga kina ce ma yara su had'a kayansu'
Ina juya tumatur din da Hafsah ta Dora Tafashensa akan wuta nace"Eh gwara su fara had'awan tun yanzu kada sai lokacin yayi kuma basu samu sararin had'awa ba. gwara tun yanzu kowa yasan matsayinsa"
Na fad'a ina kokarin rab'asa na bar kitchen din sai ya bake hanyar yana fadin"Fa'iza.."
Kai Tsaye na kallesa ina fadin"Na'am Ishaq"
Sai mamaki ya hansa mgana,Girata na Daga ina fadin"Bani hanya na wuce"
Ba musu ya matsamin na fice ina jin wani irin Tukuki acikin kaina Amir ne ya taso yana fadin"Umma ina ZAMU KOMA..?Ko zamu yi tafiya ne.?
Ban kallesa ba nace"Ku yi abunda nace Amir kaji"
Sai ya amsamin da Toh ammh sai jikinsu duka yayi sanyi,nan na barsu na shige Dakina ina Sauke numfashi,Adaran na saka Hafsah ta taimaka musu suka had'a kayansu itama ban bata ikon mgana ba sai dai ta tambayi yaran Anum tace"Umma bata ce mana komai ba"
Sai itama bata kara mgana ba, ammh ta kara tsorata da ganin na kara had'a kayana a karo na biyu wannan karon bata san kuma me zai iya Dakatar dani ba.
Lalle kana naka Allah na nashi Washegarin jumma'a da Safe Ishaq ya samu wayar Dr.Lawal inda yake sanar da shi an gano saka hannun nan ba nasa ba ne, kwaikwayo ne na wani abikin aikin su.Mr James mutumin osun State ne Daga office din sa sai na Ishaq,da shi aka had'a baki aka kwaikwayi saka hannu Ishaq Daga office dinsa aka fitar da wad'anan kudaden,yanzu Mr james din ya tafi gida chan Osun,abu d'aya ya rage bangaran Cibiyar Bincike ta EFCC ita zata ba da umarnin a kamo James ya fad'i gaskiya sannan ta wanke shi Daga zargi.
Da murna ya fito yana fad'a mana,ni da Mama da muke tsakar gida ita tana shan iska ni kuma ina Dafa zobo,sai na manta da abunda ke tsakanina da shi na mike ina fadin"Alhandulillah. Ka kira Abba kira Abba ka fadamasa"
Mama ko sai da tayi sujuda tana godema Allah sai kuka shi ko Jiki na rawa yace"Shima Daddyn haka yace na kira Abba..yayi ta kiransa bai same sa ba'
Kiransa yayi sau biyu bai Dauka ba nima na Ruga daki na Dauko wayata na kirasa bai Dauka ba.
Sai na Kira Ammi bayan mun gaisa na tambayi Abba tace ya tafi Office ina fad'ama Ishaq yace"kila ya shiga meeting ne. mu basa Lokaci"
Anum na gefe tace"Daada me ya faru..?
Cikin farinciki ya dagata sama yana Fadin"An gano gaskiya Anum.angano bani da hannu a satar kudin ma'aikanmu"Sai itama ta washe baki tana fadin"Congratulation Daada"
Sai da yagama juyi da ita sannan ya sauketa yana kallona Lokaci da'ya yana Fadin"Fa'iza kinga abun Allah ko..?
Sai na jinjina kai ina fadin"Allah yasa karshen wahalan kenan"Mama ta amsa da ameen ta mike tana fadin bari ta kira Binta Yaya ishaq ya hanata da fadin"ki bari mu yi mgana da Abba tukunnah"
Da sauri nace"Eh Mama gwara labarin ya kamallah Tukunnah"Sai ta gyada kai yini mukayi Duba waya ko Abba zai kira sai Dare ya kira Yaya Ishaq,kafin shi yayi masa mganar ya fara yi masa. yace sun yi mgana da Dr.Lawal yanzu nan ya kira Engr sun yi mgana shima ya ce Mr ABDULGHAFFAR ABDULBASIT BABATUNDE ya dawo Office satin daya gabata,zuwa gobe ko jibi ya sauraresa"
Nima Abban ya kirani yayi min bayanin komai ya karishe da fadin"Last friday ai muna Abuja da ni da Maman Nana mun je duba Hajiya Kudirat olamide,itace kakar Engr sun dawo gida bayan an yi mata Dashen koda,da mukaje mun samu Engr din a gida sai na kara tunasar da shi mganar aiko yana masa mganar yace a tuna masa in ya shiga office sai fara Duba Case din,balle da Engr ya fad'a masa Ishaq Inlow ne a waje na,ya tabbatar min da ba matsala mu jira cewarsa kawai"
Da wannan labarin mai Dad'i muka kwana sai dai na Tsananta addu'a na Allah ya kawo mafita da karshen al'amarin.
Har yara na saka suka yi ta addu'an Allah ya kawo ma Daada mafita shima nace yayi ta addu'a da ikon Allah sai an wanke sa daga wannan zargin.
*Janafty*
*KNKB2019*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Allah maji rokon bayinsa kwana Biyu Tsakani. ranar Litini da misalin wajen sha biyu na rana ya samu wayar Abba in da yace maza ya taho kano yanzu zai had'u da Abdul'Ahad a Airport din Aminu kano zasu hawo jirgi zuwa nan Abuja.
A na nemansa a Office din Chairman na EFCC,daganan bai yi mai wani karin bayani ba. shiyasa sai ya Rude,ya fito daga daki yana fad'amin cikin wani yanayi kafin ya kara da cewa"Gaba na ta fad'i Fa'iza. Allah yasa ba wata matsalan ce ta sake kunnowa ba"
Cikin son kwantar masa da Hankali nace"Haba ba komai abunda muke fata ne jeka ka fad'a ma Mama,bari na saka maka ruwan wanka ka shirya kada ka b'ata Lokaci"
Bai min gaddama ba ya wuce Dakin Mama ya fad'a mata ni kuma na je na kunna gas na saka mai ruwan wanka Tuna murhun gawayina yana waje girki na d'ora akai,sama sama ruwan yayi zafi na sake mai nice har bayi sai da na kai masa.
Da kuma ya shiga wankan na Lalubo masa kayan da zai saka,yana wankan sai ga yaya Abdul'Ahad ya kirasa ni na d'auka muka yi mgana yace yana kano yana Jiransa, daman ya kawo Raliya ta gaida su Hajiya ne, sai ga kiran Abba so in ya taso ya kirasa yadda zasu hadu a Filin jirgin kawai.
Ko da ya fito wankan mun gama wayar,Sai rawan jiki yake yi ya kasa natsuwa fad'i yake yi"yanzu a chan kano zamu hadu da Abdul'Ahad din?
Kai Tsaye nace"Eh mana yanzu ma ya kira wayarka na d'auka muka yi mgana,yace in ka taso ka kira sa"
Sai ya amsamin da toh fita nayi na basa waje ya shirya nasan ba shi da kudi cikin kudad'en sana'ata na kirgo Dubu Biyar na bashi Saboda nasan in dai suna tare da Abba bazai rasa kudi ba in yaje koda na dawowa ne, har ya shirya cikin shadda fara riga da wando,Sai Hula daya sanya ina shigowa yace"Ba sai na dauki wasu kaya ba ko.?
Kai Tsaye nace"Me zakayi da kaya kuma? in ma kwana ya kama ka kana da Muhalli da wasu iyalan achan ka manta ne"Sai ya sauke ajiyar rai kafin yace"Wlh duk na Rud'e ne Fa'iza"
Ina mika masa kudin Hannuna Lokaci daya ina fadin"Ka kwantar da Hankalinka babu abunda zai faru ai Yaya Abdul'Ahad yace Abba na chan shima in kaji zuciyarka bata natsu ba kayi ta ma Allah kirari da Hailala, yafi ka zauna kana wannan zullumin"
Cikin gamsuwa ya gyad'a min kai kafin ya karbi kudin da nake mikamasa Lokaci d'aya yana fadin"Wannan fa na menene..?
Nasan ya rude ne, kila ya Dauka haka zai tafi ba kudi sai na juya ina fadin"a kasa zaka je kanon.?
Sai ya Dafe kansa yana fadin"Shaa..Fa'iza wlh na manta"ina jinsa yana bin bayana har Tsakar gida Inda Mama ke jiran fitowarsa.
Sallama yayi mana ya tafi mama na sakamai albarka da fatan Allah yasa mu dace. ni kuma mun rabu kan sai ya kirani naji yadda ake ciki.
Mun yi masa fatan sauka lafiya tare da Fatan Allah ya tsaresa ni da mama Anum bata san tafiyarsa ba taje kai min nikan Aya,sai da ta dawo nace tayi ma Daada addu'a ya tafi Abuja.
Tafiyarsa ba Dad'ewa Yaya Abdul'Ahad ya sake kirana na fad'a masa ya kama Hanya sai yace ya yi ta kiransa bai Same shi ba,yana ga network ne, bari ya Saurareshi.
Mu dai ya tafi ya barmu da zullumi,bayan ya isa kanon mun yi waya yace suna Filin jirgi yanzu zasu tashi zuwa Abuja .
Daganan shuru bamu kara jinsa ba,Dagani har Mama muna ta zullumi ni kuma kunya ta saka na kasa kiran Abba ko Yaya Abdul'Ahad kada suga kamar na damesu shiyasa na daure Ammh ko Mama bayan mintina sai ta leko d'akina tana fadin"Fa'iza shuru Ishaq bai kiraki ba ko..?
Ni kuma sai nace mata"Mama in ya kirani ai zan gaya miki. kuma nasan in sha Allahu zai kiramu"
Daganan sai muka koma muka Nad'e hannaye,muna jiran tsammani sai wajen karfe goma sha d'aya saura,ya kirani lokacin yara har sun kwanta Hafsah ce kadai a falo tana karatu,saboda sun fara jarabawa,ni kuma ina dakina sai dai ko da na Dauka bana jinsa har sau biyu,daga baya sai ya kira Wayar mama da ita suka fara mgana kafin ta leko da kanta ta kawo min waya bayan mun gaisa sai kawai ya bige da cemin"Wato Fa'iza ki ji tsoron Gwamnati da kuma in kana da Kafa a Gwamnati. kinsan 24hrs ya yi yawa Efcc ta saka an kamo Mr James tun jiya kuma yayi mgana. Dalilin dayasa ma aka kirani kenan ma"
Cikin son jin ya aka haihu a ragaya nace"To ya kuka yi da su yanzu..?
Cikin Farinciki yace"Ya amsa laifinsa Alhamdulillah an wankeni daga wannan zargin. ashe da wani suka had'a baki,kinsan kana zaune da mutum bakasan ya tsaneka ba ni wlh lafiya nake zaune da kowa,Yanzu haka dai an yi cike ciken Takardu an tura chan ma'aikatanmu,kuma Efcc ta bani Hakuri tare da alkawarin zata maidamin da kudina da ta karb'a sun rike Mr james a hannunsu suna kara Bincikensa. ammh ni nace na yafe masa Har abada"
Cikin jin dadi nace"masha Allah. Alhandulillah gwara daka yafe masa, ammh shi miye riban abunda ya aikata..?
Kai Tsaye yace"Matsayina ya ke so. Kuma ya samu tunda bayan Dakatar dani shi aka d'aura akan kujerata"
Cikin mamaki nace"Ikon Allah daman ai abun duniya fararre ne kararre ga shi yanzu komai ya kare masa"Cikin jimami yace"Wlh kuwa. Muna chan har karfe Takwas na dare da ni da Abba da Daddy da Abdul'Ahad,da wasu cikin ma"aikatan mu, sai shi chairman na Efcc din da Sauran ma'aikatan su da wanda suka ja Ragamar case dina a hannunsu.Wh Fa'iza Abba yayi min kokari ke kinga yadda Chairman din nan ya dinga bama Abba hakuri.?gaskiya mutumin nan yasan karamci kuma ba fa ba Bahaushe ba ne, Fa'iza Bayarbe ne. abunda na Lura dashi Megidan Abba da yake kira Engr na ji da Abba sosai. tsakani ga Allah cikin gaggawa akayi komai aka gama,kuma Engr ma ba shi a wajen,naji Abba yace yana Edo ki tayani godiya Don Allah"
Ajiyar rai na sauke kafin nace"Alhamdulillah Allah ya kara Tsarewa yanzu kana ina ne.?ko kuna tare da su Abba ne..?
Da sauri yace''Ina wajen zainab nan zan kwana zuwa gobe. Abba daganan jirgi ya hau zuwa warri suna da taro gobe Abdul'Ahad kuma ya hau jirgin kano"
kai na tsaye nace"Ba damuwa ai kana gida kayi zaman ka mu nan ba mu da matsala"Shima kai Tsayen yace min"Aa zan dawo ai ba wajenta nazo ba, itama"
Ban tsaya jan mgana ba tunda ba Hurumina ba ne,in ba wajenta yaje ba, me ya hana yabi yo Ya Abdul'Ahad su dawo tare ya tsaya nan zai kwana?shine zai zo yana min wata mganar banza jin nayi masa shuru yasa ya kira sunana sai na amsa sai kuma ya kasa mgana sai kawai ya bige da Fadin"Sai dai na dawon"
Yara ya tambaya nace sun kwanta yaso yajani da mgana nace mai barci nake ji duk nagaji cikin Dariya yace"Ai ina samun wani babban aiki duk zaki daina sana'ar nan ta wahala Fa'iza"
Sai ya bani dariya har sai da na Dara kafin nace"To ai ko ni ce da kaina na samu babban aikin ban ji zan dakatar da wannan sana'ann tawa, domin tamin komai a Rayuwa sai dai na nemi Hanyar ingantata kawai'
Da sauri yace"Eh hakane kam.."ina ji sama sama ana mgana ta gefensa ban Tsaya ji ba na kashe wayata na yi kwanciyata sai dai har ga Allah na tayasa murna sai naji kamar komai dake faruwa Mafitan da na Roki Ubangiji ne ya sama min ne.
Zuwa washegari mgana ta watsu a Dangi Mutanen karofi dai Hafsah ta Fada musu su jamal kuma duk mama ta kira su ta fad'a musu abunda ke Faruwa. sannan sai ta kara da fadin wlh duk sanadin Kanin mahaifiyar Fa'iza shi ya tsaya har aka wanke Ishaaq,Har daki mama ta biyoni Tana min godiya ta kuma saka na kira Abba ta kwararamai godiya.
Abba yace"Hajiya kada ki damu.Da Fa'iza da Ishaq duk d'aya suke a wajena duk abunda nayi kamar nayi ma Abdul"Ahad ne"sai kimar sa ta karu a idon Mama,sai da yaya Ishaq ya kwana Biyu sannan ya dawo ranar kuma Anty Binta tazo ita da Anty mahma,sun zo yi ma Mama barka da arziki,Shima din yana samun wayoyin yan'uwa da abokan arzuka harda abokan aikinsa da suka Dad'e ma basu yi mgana, suma labarai yakai headquater din su tunda EFCC ta tura Takardan wanke Ishaq din daga dukkan zargi.
Su Goggo duk sun kirani hatta ko da Yaya mariya,ta kirani su Nana Fatima ma duk sun kirani tace Abba yace su kira su yimin barka da arziki,Har da Ammi kuma naji dadi sosai masoyin ka ne Zaka yi rashi ya janjanta maka sannan in kasamu shima ya tayaka Murna,su Amir nata murna domin ce musu yayi da kansa kud'in Daada ya Dawo ya'yan Umma nan suka Biye masa suna ta tsallen Murna.
Allah shi ke ba da samu da rashi kuma shi ke da Daukaka da Nasara shu kuma ke da Fad'uwa da Tashi,kwana Biyar Tsakani da EFCC ta wanke Yaya Ishaq ya samu kiran gaggawa daga Headquater dinsu na Abuja aranar ya tafi sai dai mota yabi,bai kirani ba ina ta neman wayarsa a daran a kashe sai da asuba kawai zainab ta kirani ina Dauka tace"Congratulation to us Maman Amir kinga Kuduran Allah ko..?.
Mamaki ya kamani bansan kan mganar ba,ina shirin tambayanta sai kawai ta zarce da fadin"Jiya da Honey yaje ma'aikantan su upper ce suka basa ta maida shi aiki da matsayi mai girma,sun mai da shi office din su na Lagos zai fara aiki nan da wata D'aya"
Karfaffan ajiyar zuciya na sauke a Fili na furta"Alhamdulillah!
Cikin Farinciki tace"Wlh ai tun jiya nayi ta neman wayarki ni da shi bamu samu ba, yanzu haka ya tafi masallaci ne,shi nace bari na kiraki na fara yi miki albishir"
Ciki jin dadi nace"Masha Allah. Allah ya sanya albarka,ya sa alheri a cikin aikinsa damu gabad'aya"
Ta amsa min da ameen ameen bamu jima,muna mgana ba muka yi sallama,Daganan sai na tashi na shiga Dakin Mama na isketa tana azkar bayan mun gaisa na fada'mata abunda Zainab ta fad'amin Mama ta washe baki tana Hamdala ta daga hannu sama tana yi ma Allah godiya.
Daganan dakin yaran na koma na iske sun idar da salla,Amir da Musty suka hada baki wajen fadin"ina kwana Umma"ina mirmishi na amsa ina fadin"Daada ku ya samu aiki a lagos"Sai suka fara murna har da tsalle Ahmad kenan.
Fita nayi na koma falo sai ga Hafsah ta fito na gayamata, Anum na bayanta ta Daka tsalle tana fadin"Eyyee zamu koma Lagos ehyee.."
Sai tsalle take yi ina kallonta ina mirmishi,sai da gari yayi shaa Yaya Ishaq ya kirani cikin Tsananin murna yace"Fa'iza albishirinki"
Ba da niyyar gwasale shi ba nace"Zainab ta riga ka. Har na shaida ma Mama da yara"Sai naji kamar gwaiwarsa tayi sanyi