Showing 12001 words to 15000 words out of 82431 words

Chapter 5 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

188

bushashiyar Zogala da rama sai gyada mai bawo da Mai gishiri da ta kawo ma yara Tsaraba Dadi ya cikani sai cewa nake yi"Allah ya saka da alheri Goggo na zama yar gatan ki"
Goggo tace"Daman ke yar gata na ne tuni zaman ki ne kawai bai yuyu a Hannuna ba"
Nasan haka domin duk wata kauna Goggo ta nuna mana barin ma ni,Su Hafsah tuni sun ja gyad'a gefe suna ci ita da Amir na balla musu Harara ina warce ledan Lokaci d'aya ina fadin"Wannan na sauran yara na ne yan makaranta"
Amir yace"Umma wannan yayi musu yawa fa..?
Na bude ledan ina gani sai naga da yawa sai na debo a hannu na zube a gabansu na boye sauran ina fadin"yara kun ci rabon ku"
Goggo na mana Dariya naji Dadin wannan zuwan na goggo muka yini muna Hira,Hafsah tayi abincin rana bayan ta gama nace ta dibar mama da Badariya da taje kai mata sai tace sai yanzu aka ga daman bata abincin..?
Ita dai Hafsah bata tanka ta ba sai da ta Dawo daki take gayamin Ban ce komai ba Goggo tace"Sai kin kara Hakuri daman fa'iza yanzu Saudatu zatayi ta tsiro da abubuwa saboda ta kuntata miki, to kada ki biye mata Har a gobe uwa take gareki"
Kai na jinjina ina fadin"Goggo ni ban da Lokacin wannan kina ganin bama zaune nake ba"
Goggo tace"Ba shakka Sana'a ai mganin Damuwa ne da sha'anin Duniya,"
Sai da muka yi sallar la'asar sannan Goggo ta yi shirin tafiya daman da La'asar Ya Isa yace zai dawo shima daga ma'aikatar su ta nepa dake Dutsemah ne aka turo su meeting babban Headquater su na katsina da ya gayama Goggo tace zata Biyosa.
Aiko sai ga shi hudu da wani abu sai faman hon yake yi ma Goggo tunda yaki shigowa na zuba ma Goggo kunin Aya da zobo mai yawa shima Yaya isa na bashi na shi Goggo sai fada take yi tana fadin"bai yi yawa ba Fa'iza? kada mu karya fa jarin"
Ina Dariya nace"Cikin Riba ne fa Goggo"
Sai ta karba tana fadin"To Allah ya yi albarka Allah ya sanya miki nasibi da karama acikin Kasuwancin ki da sana'arki"
Na dinga amsa mata da Ameen na rakata Dakin Mama tayi mata sallama ni da Hafsah da Amir har kofar gida muka rakasu Yaya isa ya zaro dubu biyu ya bani naki karba sai ya harareni yana fadin"Kyauta na baki ni ba kudin zobo ba ne"
Jin haka yasa nayi dariya na karb'a ina masa Godiya Hafsah na ganin haka tace"Yaya isa kada ka manta yar makaranta marainiyar Allah"
Dagowa yayi yana fadin"Data zaki saka ko..?
Da Sauri tace"Eh Yaya ai muna Browsing sosai"
Sai ya yi dariya ya zaro dubu ya bata yace a saka data ayi ta browsing ta karba tana godiya sai kuma ya bama Amir dari biyar yana fadin"Kai baka fara zuwa makarantar ba ne..?
Da Sauri nace"Bai fara ba sai zangon karatu na biyu Yaya isa"
Sai ya jinjina kai har Goggo ta shiga mota sai ta leko ta window tana fadin"Kinga na manta Maman isuhu tazo da kanta ta kawo min goro da mintin biki Isuhunta zai yi aure tace kada a yada zumunci don Allah"
Fatan alheri nayi kafin nace"Da wahala zuwa na Goggo kinga ga Mama ina fita sai kiji ance ban kyauta ba"
Goggo tace"Hakane ki yi zaman ki ni da mariya sai mu leka"
Da haka muka yi sallama suka tafi muna Daga musu hannu sannan muka koma cikin gida,Danwake nayi mana da Daddare Hafsah kuma sai ta hada kunin Aya zobo ma bamu yi na yammah ba nagaji nace ta bari da Safe yan sari ma basu samu ba duk a gida ya kare.
Aiko Mama tayi ta fad'a wai danwake ne abinci da daddare kamar a gidan yari..?yarda aka kai mata haka Hafsah ta Dauko kulan da safe da zatayi wanke wanke, Badariya bata dawo ba kila gidan Anty Binta ta kwana,haka na cigaba da Hakuri da Mama ammh Allah ke da kullum da Sabon korafin da take tashi da shi sai dai bana biye mata,Yaya Ishaq tunda ya tafi bai kirani ba nima ban damu ba sai dai nasan suna waya da Mama.
Sana'ata na maida hankali bani da wani Hutu sai dare ya tsala wani Lokacin Saboda kada ayyuka su Chudemin karfe uku na Dare nake tashi na Dafa Zobo a tsakar gida tunda na koma amfani da gas na kasa 4kg,Sai na siya babban murhun gawayi ina amfani da shi wajen Dafa zobo,har girki ina yi akai saboda gas din ya rika yi mana auki sosai.
In na tashi ukun nan kafin asuba na Dafa zobon,sai naji da saka ruwan wanka. wani Lokacin Hafsah ke abun karin Safe in zata fita da wuri in kuma tana gida sai nayi in ta tashi sai ta Hada zobon ta kuma share gidan da Dakunan in kuma bata gidan duk ni nake had'awa nayi kunin Aya saboda yana Saurin Lalacewa nafi hadasa da yammah saboda an fi samun Wutar Dare kafin safe yayi sanyi.
Hakan ma bai burge Mama ba, duk yadda nake taka tsantsan sai da ta fito tace min wai warin ganyen zobo na tayar mata da zuciya ni ko sai nace sai dai ko ki yi ta sheka amai bazan daina wannan sana'ar ba,kuma duk kushen mai kushe da Hassada ta Allah ba tashi ba.
Duk yadda nayi sai tace kaza kaza ita dai kada ta ganni cikin ni'imar Allah sai dai na zauna ta rika tusamin Haushi da tozarcinta nan kuwa bata isa ba,yanzu ba irin da ba ne an samu Sauye sauye da dama. daman haka Rayuwa ta gada Kifi na ruwan sanyi sai ya iya juyawa ya gansa ana zafi kamar yadda ya faru da ita.
Na toshe jina da ganina na cigaba da sana'ata ina rufa ma kaina da ya'yana asiri,har da ita kanta Mama muna da kayan abinci ammh bamu da Cefane da Riban sana'ata nake mana komai Dawainiyar yara na makaranta na yau da kullum Badariya ma ina bata na mota har da wata matsalan in ta taso in dai tamin mgana ina da shi zan Dauka na bata.
In da na biye mata na koma na zauna yadda ta matsa Yaya Ishaq ya tafi Abuja da ta gane bata da wayau.Anty Binta take takama da ita itama bata da komai yanzu sai karya da Girman kai da tijara fal cikinta domin ban ga abun arzikin da take kawoma Maman ba,Da farko da Mama tace Ucler ya kamata kayan Tea ta siyan mata da suka kare bata kara siyan ba na Tabbata bayan Yaya ishaq ba mai iyawa da Dawainiyar Mama.
Sai da ya shafe fin sati biyu a cikin na uku ya dawo na zata zan gansa da abun arziki ne niki niki yadda Mama ke fadin sun musu komai babu abunda yazo da shi daga shi sai kayansa kamar ma a kidime yake ba wani kwanciyar hankali sai ramar da ya karayi, ashe wai takardunsa yasa yaje mai da shi ko za'a dace yasaka shi yayi zama ba wani labari mai Dadi gajiya yayi da zaman ya dawo ina Tsakar gida ina shara naji Mama nata mai fad'an meyasa bai jira ba ya Dawo dayake Mama ta iya mgana a sama sama.
Yayi mgana sai dai nashi ne yayi kasa ban ji abunda yace ba, ni dai ba gulma ba na cigaba da aikina,Yadda bai ce min kanzil ba nima ban ce mai ba sai na tambayesa ya ya baro su Farhan..?
Sai yace min Farhan ya fara zuwa makaranta Fadil kuma gidan su zainab ke kaisa in zata fita aiki Daganan bai kara mgana ba, nima na kama bakina fadan da ba ruwan ka ai Dadin kallo ne da shi.
Sai ranar da yayi kwana Biyu da Dawowa yana zaune afalo ni kuma ina safa da marwa aiki ya had'e min Hafsah da wuri ta shiga makaranta ga aikin zobo ga girki,Amir ne ya taimaka yayi min sharan Dakuna da Tsakar gida,gajiya yayi da ina wucesa ko barayinsa bana kallah yasa ya kirani nazo gefensa na tsaya yana kwance ne ya mike yana fadin"Nagode bisa Dawainiyar da kika yi da yara da su Mama bayan ba na nan"
Sai kawai na wuce ina fadin"Ba damuwa daman kasan kula da yara aikina ne Mama kuma itama kamar uwa take gareni, kada ka godemin domin na yi mata Hidima"
Daga haka na wuce kitchen na Dauki Abunda zandauka nayi waje achan nake girki gas ya kare Hafsah nace taje ayi Refiling bata samu zama ba ne.
Har na fice yana bina da kallo nasan a ransa yana mamakin yadda na sauya ne bakina ya bude fiye da yadda yayi tsammani,Haka muka cigaba da Rayuuwa yau dadi gobe Tsumma,ahakan ma ni nake tallafe da kananun Lalurorin gidan nan ammh Mama bata gani take yi komai nake yi alfarman da suka yi min ne nake rama musu.
Ni ko Don Allah nayi abunda take yi bai Taba Damunaa ba,Ba inda Yaya Ishaq yake zuwa yana gida sai dai in masallaci in ya gaji da barci ya fito falo ya kunna kallo in yagaji ya kwanta,ko ya shiga Shashen Mama,duk yadda baya so damuwa ta samu zama a jikinsa sai da ta samu duk yayi baki ya rame hatta na katin waya gagaransa yake yi,kuma yana da girman kai da Fafa bazai yi tambayata ba ni ko bani da masaniya kananun matsalolin da na gani ne nake mgancen su.
Ana cikin Haka jamal ya yo masa waya Kudin hannunsa ya kare sannan kayan abincin sa ma sun kare Bai fadamin ba sai ya shiga bangaran Mama ya fadamata kai tsaye mama tace"Sai kayi ma matarka mgana nasan bazata rasa ba,gidan nan yini ake shiga da fita saboda sana'arta"
Kai tsaye yace"Mama ni bazan iya taba tambaya Fa'iza kud'i ba"
Mama tayi karamin Tsaki kafin tace"Kiramin ita ni zan gayamata"
Amir ya kwalama ya kira da ya shigo sai yace ya kirani ni kuma ina Falo na Dukufa da littafin, ina ta lissafin kudi so nake wannan karon daga rabin Solon Ganyen zobo na siya Solon buhun ina tattara Riban hannuna sannan Aya ma tiya goma nake so na siya,da yawa da Dabino na ijiye kwakwa kuma tana lalacewa kadan zan siya sanda Amir yazo ya kirani shine a raina so nake nayi kokarin na biyasa masa kudin makaranta ya fara zuwa zamansa ya fara Damuna,so nake na fara ji da Hidimarsa kafin su kuma a fara mganar na su Anum
Ijiye komai nayi na saka Hijabi na tafi Dakin Mama da na shiga a kasa na duka ina gaisheta da lafiya ta amsa kafin ta daga murya tana fadin"Jamal ne yayo waya bai da kudi a hannunsa nasan kina da kudi ki bada ko dubu ashirin ne sai a sakamai ya lallaba"
Sai mamakin Mama ya kamani kamar ita ta tarfamin jarin cikin sanyina nace"Sai dai Dubu goma baza'a samu ashirin ba"
Mama ta saki baki kafin tace"Wlh karya kike yi ba za dai ki bada ba ne, meye amfanin samun naki in dai bazaki taimaki mijinki naki ba"
Ina jinta ban yi mgana ba shi ya katse mganar da cewa na tashi na tafi haka na koma Dakina ina jinjina karfin Halin mama shikenan lissafina ya Sauya daman yan riban da su nake Hidiman yau da kullun kudi fa ana zaran su basa zama,Sai na cire dubu goma na ware kayan da nace zan siyo na ijiye bazai samu ba saboda kudin sun yi gibi,ko da ya dawo dakin bai tada mganar ba sai ni da kaina na dauko kudin na basa ya karba Jikinsa a sanyaye lokaci daya yana fadin"Ki rika Rubutawa Fa'iza zan biya ki kudin ki da zarar na samu aiki in sha Allahu"
Ko kulasa ban yi ba sai dai na dago na kallesa kamar bazan yi mgana ba sai kuma nace"Kai dai baka na lissafe da abunda ka karba ba?ai shikenan."
Daganan sai bai kara mgana ba ya saka takalmi ya fita yaje ya tura ma Jamal kudin,ya dawo Yaya Ishaq na bani mamaki ko irin ya dan fita waje ya zauna bai iya ba yana gida koda yaushe dole damuwa tayi masa yawa,kamar zan yi masa mgana sai wata zuciya ta kwabeni na kama kaina.
Zainab na kiransa ko da yaushe ni ban san Halin da suke ciki ba sai wataranar asabar da Safe na shiga kai masa abun karyawansa naji yana waya ya daga murya sai fada yake yi Cikin kaukkausan murya yake fadin"Zeey na fada miki bazai yuyu nazo abuja na tare ba,bani da aikin yi ba wajen zuwa ke ba zaman gida ba ki fice tun safe ki barni da mai aiki, Fadil ma ki bar mun shi ya Debemin kewa gida kike tafiya da shi gwara na Dawo gida na zauna nan din ma ina da uwa da wata matar da kuma yara"
Ni dai daga haka na sauke abun hannuna na fice yayi nisa a mganarsa bai ma san na shigo ba.
Da na fita acikin raina sai abun ya fadomin sai naga Zainab na da gaskiya abunda ya zabar mata tun farko ne meyasa yanzu zai sauya..?ai yasan da akwai rashi da samu akwai rayuwa akwai mutuwa kuma ya zabi hakan duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa yadda ba wanda ya sani cikin mganar nima nayi kamar ban ji komai ba, na cigaba da Sabgan gabana.
Ina ta buga bugan  yadda zan had'a kudin makarantar Amir saboda su Anum sun kusa hutu sannan ga kudin makarantar Tahfez din su yanzu sun ciresa a kudun makaranta Daban za'a biya hakuri na bada wanchan Team din ba'a biya ba yanzu kuma baamai karban uzurin mu,Shiyasa nake aiki ba rana ba Dare rana na Dafa zobo sai Uku,saboda zafi da nake tunkara da Wahala yasa kaina ya fara ciwo da ganin Jiri ina jin haka nasan jinina ne ta haye sama bana samun Hutu ga amfani da Hutu nasan in ya kwantar dani abubuwa ba zasu tsaya sai naje kemist aka auna ni aka ga jinina ya Hau sai aka bani mganguna,Dalilin haka yasa kwana Biyu nayi baya da Wutar Sai dai Hafsah ta Dafamin kafin tatafi makaranta sai ta barmun na hada,kunin Aya bai da matsala da kaina nake yin ta tadawo da wuri sai ta sake Dafa na yammah ni kadai araina ina fadama kaina Fa'iza bi sannu Sannu zafin nema baya kawo samu.
Allah maji rokon bayinsa domin ban daina rokon mafita daga garesa ba,kawai sai ga kiran Hajiya tana fadamin bikin da ta fadamin na kaduna saura sati biyu,In na samu Lokaci nazo gida na sameta ina jin haka ko ban yi wasa ba,Allah yasa Ranar Hafsah na gida sai na bar mata komai Yaya Ishaq na dakin Mama da na shiga ciki na shiga na gayamai zan fita Hajiyar su Raliya ta kirani kan wani aikin Turaren wuta bai ce komai ba yace a dawo lafiya Mama kuwa sai da ta tofa kallona tayi tana fadin"Da zaki kwashi kafafu ki fita abinci wa kika bari ya dafa ya bamu..?
Kai tsaye nace"Hafsah zata dafa ai ba jimawa zan yi ba zan dawo"
Baki ta tabe kafin tace"Wanki na ya taru wannan satin naga baki zo kin kwashe kin wanke ba ko kin gaji ne..?
Yadda tayi mganar kamar wata baiwar ta ko yar aikinta Tunda muka Dawo gidan nan ni nake kwashe kayan Mama in sun yi Datti na wanke mata.
  kuma na zauna na goge mata,ba kayan Mama ba Har na Yaya Ishaq ni nake wanke masa wani lokacin saboda bai saba ba,Sai dai in aiki yayi min yawa sai nace yakai wanki da guga zan ba da kudin.
wannan satin da ban ji dadi ba ne ko na yaran Hafsah ta rage musu nasu ammh ji yadda take min mgana kamar tana biyana.
Kaina na kasa nace"Banjin dadi ne wannan satin ban yi wanki ba, ammh za'a wanke in sha Allahu"
Yaya Ishaq mamaki ya kamasa cikin mamakin yace"Mama bata jin dadi yanzu ko Badar baza ki saka ta wanke miki kayan ki ba..?baki ga ayyuka sun mata yawa ba ne..?
Sai Mama ta fara bala'i tana fadim"Kaga Badar din ne a gidan..?da makaranta zataji ko da aikin gida ba zaune take ballatana kace"
Kai tsaye yace"Ai ba kullum ake makaranta ba Mama ita Hafsah ai karatun take yi kuma bai hanata ta taya yayarta aiki ba."
Mama ta cika tayi fam ta faara fadin"Na lura ai yanzu yarinyar nan tafini Daraja a idon ka saboda tana Dauke maka wasu laluron,har Abada bazan so Dangin jaraba da cin Amana ba'"
Naga cin mutumci zai yi yawa sai na tashi na fice sai yi take yi ban bi ta kanta ba, na dauki pos dina da na siya da kudi aciki nayi tafiya ta, adaidaita na hau har anguwan su Hajiya kusa da jami'ar alkalam.
Nasameta a gida da tana shirin fita ne ma sai gani,sai ta fasa bayan mun gaisa tamin bayanin komai zan had'a Turaren rushi da na Humra sai kwallacha sai zan yi ma Amaryan gyaran jiki,duka zasu bani dubu dari biyu,Naji kudi sai na rude cikin Firgici nace"Hajiya duka nawa..?
Hajiya na dariya tace"Eh kudin aikin ki da ladan ki ba'
Sai na hau mata Godiya sai ta bata rai tana fadin bata so na koma na zauna araina ina Hamdala,Nan take ta bani dubu dari a hannuna sauran tace zata Turamin ta banki ta karishe da fadin"Sati mai shiga amaryan zata zo nan zaki zo ki yi mata ko sai dai ta biyo ki gida..?
Cikin Ladabina nace"Hajiya sai dai gida kinga ga yara sannan ga Mama bazai yuyu na rika Dadewa a waje ba"
Hajiya tace"Eh hakane shiyasa da suka yi mganar girki nace su dauki wata kawai zuwan ki kaduna da wahala"
Na jinjina mata kai sai tace ba Damuwa fita zatayi duk abunda ake ciki sai mun yi waya,tare muka fita da ita bayan ta bani kyautar atamfa da Mayafi,sai turare da lotion mai kyau,tare muka taho Direban ta ya Daukoni sai da suka saukeni a gida sannan ya wuce da ita in da zataje.
Bakina kamar gonar auduga haka na shiga gidan cikin murna naja Hafsah Daki na zayyana mata komai na nuna mata kudin cikin Farinciki tace"yaya Fa'iza Hajiya tana da kirki tana son ki da arziki"
Ina jinjina kudin hannuna nace"Bari Hafsatu Allah dai ya biya ta kawai"
Aranar bamu je kasuwa ba sai washegari mukaje da Hafsah ta tayani na sissiyo abunda zan bukata ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login