Showing 18001 words to 21000 words out of 82431 words
akanta"
Daga haka na juya nayi ficewata Mama ta rakani da fadin"babu abunda ta iya yanzu sai rashin kunya har shi ta raina"
ni dai bansan ya suka kare ba ina wanke wanke abun na dawomin ni kaina ina mamakin yadda bakina ya bude wani Lokacin na yarda ba shawara ko nuniya ke saka mace tayi baki a gidan mijinta ba Wuya ce mutanen duniya ke chanzata,batare da tama sani ba kamar yadda yake faruwa dani domin ban taba kawowa ma kaina zan iya maida ma Yaya Ishaq mgana ba ko shi ko Anty Binta ba sai ga shi shakkar da nake ji da yanzu wlh bana gani,wani abun ma ina raga musu ne saboda wasu Dalilai.
Tunda Mama ta raina kokarina ni ko a raina nace sai na bata mamaki na tsame hannuna a kula da shi ai daman ba hakki na ba ne, ita da bai jingine auranta ba,yafi zama Dolenta ta kula da shi nifa daman taimako ne da Darajan ya'ya sai ta wani Fanni in na Duba zumumci.
Sai ana mangariba na gama wanke wanken nan sai lokacin Hafsah da Badariya suka dawo,Amir da su musty sun bi babansu zuwa masallaci daya fara rarrafa d'azu,sannu da gida suka yi min kowacce ta shige inda tafi wayau.
Ina komawa Daki daman na Dafa ruwan zafi nayi wanka,Hafsah kuma nace in tayi sallah taci abinci taje makotan mu ta Dauko min ninkan Ayan da dazu yaron gidan ya shigo Siyan zobo na bashi sai ta amsamun na shige Dakina nayi wanka nayi sallah na zauna ina azkar,ina ga sai da sukayi sallar isha'i suka dawo shi Uban Gayyar Dakin Mama ya shige yaran kuma suka dawo Daki Hafsah da ta dawo dauko nikan na saka ta raba sauran abinci nace ta diba ta kai Dakin Mama da yawa Saboda Zainab sauran su ci su da yara.
Akace Namiji ya iya munafunci nidai tunda na shiga ban fito ba Hafsah na bari da hada kunin Aya,Ashe da ya gama zamansa Dakin Mama tare da Zainab suka dawo Dakinsa sai suka bar Fadil wajen Mama bakinta washe,Adakin nasa ta kwana ni ban sani ba ko da na tashi da asuba ban lekasa ba ina ma yara shirin tafiya makaranta,muna falo da ni da yaran suna cin abinci sai gata ta fito tana mika sanye da rigar barci Riga da wando masu taushi gashinta kanta ya bazu wata hula ce ta saka ana ganin kanta,sau daya na kalleta ban kara ba ita ta fara gaisheni na amsa ta cikin Sakin Fuska har ga Allah ban ji Haushi ba, to me zai dameni ai ba yau aka fara ba an dade ana haka.
Abun karin ma na aika Dakin Mama basu ci ba Zainab ta basu kudi suka siyi kayan tea Badariya tazo kitchen dina ta soya musu kwai, ni ina Dakina Hafsah ke fadamin nace saji da shi dai.
Sai da chan rana na shiga na Duba sa yana kwance sun yi kaca kaca da Dakin,daga nesa na tsaya na gaishe shi da jiki ya amsa sai naga yana karemin kallo sai na Tsargu da Sauri na kalli kaina Riga da sikat ne a jikina Atamfar ni na siyeta da kudina na Dinkata sai dai dinkin yayi min Cif a jikina ganin yadda ya kuramin ido ne yasa kawai na juya zan fice da Sauri ya yunkura ya mike yana kiran sunana na Juyo ammh ban karisa gabansa sai yace"Fa'iza kariso mana bana jin dadin yadda kike maida Dakina kamar bakon ki"
Sai kalamansa suka bani mamaki kai tsaye nace"ai bakon ne a wajena.."
Bai damu ba sai ya dan kalli D'akin yana fadin''Haba Fa'ita kwana biyu ba'a zo an gyaramin Dakin ba. sannan kuma ga kayana duk sun yi Datti wlh ko na sawa bani da shi"
Na kura masa ido ina Dariyan sunan da ya kirani wai Fa'i ta abunda ban taba ji ba ko acikin mafarki har da wani lankwasa wuya yake yi na yaudara sai kawai nayi Dariya kafin nace"Ai wannan ba Hurumina ba ne Hurumin Matarka ce ka kirata ta gyara dakin sannan ta kwashe kayan naka ta wanke"
Kai tsaye yace"Saboda me sai zeey.?ai ke kika saba yi Fa'iza kada ki bata ladan ki don Allah"
Karfin Halinsa ke bani mamaki cikin gajiya da mganar na juya ina fadin"Ba bata lada ba ne, Itama Hakkin ka na kanta ta kula dakai tunda tazo ta amsheni daman ni taimako nayi ba Hurumina ba ne"
Har zan fice ya kwalamin kira "Fa'iza..'
Sai na juyo ina fadin"Wlh bazan yi ba ka kire Zeey din taka mana, inace ita ma Matarka ce"
Sai kawai ya koma ya zauna yana fadin"Fa'iza yaushe na fara mgana kina min gaddama sannan yaushe na fara mgana kina sa'in sa da ni..?
Kai na tsaye nace"Tun ranar da ka furtamin da kanka ka zabi wata matarka fiye da ni nima tun ranar na zabi rayuwata da ya'yana sama da kai.Komai kaga ina yi maka don Allah da taimakon zumunci ne"
Daga haka na fice na barsa da sanyin jiki Hidmar hada zobo na fara satin nan Hafsah karatun Safe suke yi,Allah yasa tamin shara da Safe wanke wanke kadai nayi sai na share tsakar gidan na wanke ina wajen Zainab ta shige bata fito ba, ni ko dakin ban koma ba Fadil ne ya dinga kuka a Hannun Mama ta kasa lallashinsa sai na shiga na karbesa sai na Fahimci yunwa yake ji ina da Sauran garin kuni nan da nan na dora ruwan zafi daya tafasa na Damamai na Duramai tas ya shanye sai barci,naja zani na goyesa ram a bayana na cigaba da ayyukan gabana Mama daman tagaji da renon ta shige Daki tayi kwanciyarta Tunda baiwarta ta Dauke komai.
Da rana Danwake nayi da salat,aiki duk ya Chudemin Zainab kam da uban gayyar sun shige daki ba mai jin motsin su, Fadil na Dakina yayi barci da ya tashi nayi mai wanka nima nayi ban san fitan ta ba ta koma Dakin Mama tayi wanka ba,sai da ya tashi ya fara rigima na lekata sai na ganta na mika mata shi ina fadin"Ya tashi yana rigima"
Ta karbe tana fadin"Daman tunda naji sa shuru nace yana Hannun ki"
Mirmishi nayi mata na fice,ina komawa Daki na ci karo da shi ya fito Daga kitchen da ya gani sai yayi Turus ni kuma sai nayi kamar bangansa ba zan wuce dakina yace"Dama..dama kuna da ruwan zafi ne..?garin ai ko sanyi zazzabi bai sakeni ba kada na Dawo da shi da wanka da ruwan sanyi"
Da nayi niyyar na yi wucewa ta ne sai wata zuciyar tace ashe ya Dameki..?sai na juya ina"Ka kira Zainab ta saka maka mana"
Sai ya bude ido yana kallona,na ganin na juya yasa yasha gabana yana fadin"Don Allah Fa'iza don Allah nace.Zeey bata shiga kitchen achan komai ma'aaikata ke yi mata"
Rashin kunya ba Halina ba ne yasa na juya na koma kitchen na kunna gas na Doramai ruwan zafin na fice na barsa nan falon inaga da yayi zafi ne ya kashe gas din ya juye,yau alhamis ne da la'asar yara suka dawo makaranta Amir ya taimakeni ya tayani Dura zobon a gorina Anum na shirya mana nayi na Safe har ya kare wannan na yammah ne,Addu'a nake yi Allah ya dawo da Hafsah ta dora girki sai biyar da wani abu ta shigo tana shigowa Amir yace'"Umma ga Antyn Hafsan ta dawo"
Daga ganinta ta gaji ta sauke jaka tana fadin"Da Antyn Hafsah tayi me..?
Ina Dariya nace'Yaji ina ta cigiyarki ne aiki yayi min yawa ban dora girki ba"
Sai ta ce"Bari naci abinci na dawo hayyacina"Da sauri nace"Yauwa yar albarka mu in mun gama sai mu had'a kwanuka mu yi wanke wanke"
Da Sauri Anum tace"Umma ni zan yi"
Ina dariya nace"Ko baki ce ba tare zamu yi kafin nan gaba ki iya na sakar miki,ammh kafin sai kin share inda muka bata"
Musty yace"Ummi ni zan share"
Nace"To ya'yan Umma yan albarka"
Ahmad na gefe yace"Umma zan wanke miki robobi"
Amir yace"Kadai samu na wasa"
Gabadayanmu muka saka Dariya gabadaya bani da damuwa indai ina ganin Dariyan ya'yana su nafi damuwa da su bangaran su Mama tunda zainab tazo ta bud'e musu bakin aljihu suna cin dadin su yau nama gobe kaza ni dai ya'yana suna daki basu gani ba,ballatana su saka rai ammh fa Fadil na wajena ni nake mai komai har wanka uwar tana nanike wajen miji ana shan soyayyah.
Washegari da Safe bayan yara sun tafi makaranta na fada ma Hafsah yau zobo Sau daya zamu yi,sai kunin Aya shiyasa da Safen bayan yara sun tafi makaranata na samu kujera na kwanta sai barci Hafsah ke dafa zobon awaje basu da shiga makaranta yau,ai naji dadin zaman Hafsah a wajena tana bala'in taimakamin kan sha'anin gida da sana'ata wani lokacin ba domin ita ba,bansan ya zan rika yi da wasu ayyukan ba.
Na fara barci sama sama na rika jin Hayaniya na gyara kwanciyata saboda ban ji hayaniyar ko ta macece ba,Sai da Mama ta shigo har Falona ina kwance kawai naji ta Dakamin duka na Bude idanuwana da suka yi ja Saboda barci sai naga Mama a saman kaina
Tsakani ga Allah ina gajiya saboda aikin Hannu nake yi komai sai na sarrafashi da kaina.
Ina kokarin tashi zaune kawai ta hau ni da fad'a nama kasa gane in ta dosa sai da nace"Lafiya Mama..?
Cikin wani kallo tace min"Bansani ba.Kya ce lafiya mana kina kwance kina barci,shi kuma ga shi chan bai da lafiya shi kika bari da wankin kayansa"
Sai taga na mike kawai zan shige cikin D'akina kai tsaye ta saka hannu ta fizgoni na dawo gabanta tana zare min ido tace"Don ubanki ina mgana kina wucewa,ni sa'arki ce.?
*INGANTACCEN ZANCE*.
*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*
*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.*
*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*08032773332.*
✍️.
*Janafty*
*KNKB2006*
*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*
Ba nufina in yi Mama rashin kunya ba ne, saboda a uwa na Dauketa sai na Sadda kaina kasa ina fadin"Naga fad'an bai shafeni ba ne Mama"
Sai ta saki baki tana kallona lokaci daya tana fadin"Wato bai shafe ki ba? ko ni ki keso na kwashe kayan nasa na wanke mai ishashiya Dangin Jaraba?
Sai na dago kai kamar zan yi mgana sai na fasa na kama Hanya na fita Tsaakar gida yana Zaune kan kujerata ta tsuggunon Tsakar gida, ga kaya a gabansa ya saka Hafsah ta taran masa ruwan famfo Har ga Allah Dariya sai da ta kusa kamani yadda yayi kamar mai ko wankin,Karisa fitowa nayi ina fadin"wanki da kanka ina Zainab din..?
Ko kallo na bai yi ba nima sai na juya ina kallon Mama da ta zata da na fito zan karbesa ne, sai taga akasin haka kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Mama kada kiga laifina ba ga Zainab ba, ai itama matarsa ce. kince tana da Hakki a kansa kamar yadda nake dashi daman kuma kin kirata tazo ta kula dashi tunda kin ce ni ba takansa nake bi ba,Ki kirata tana ciki ta fito ta karb'i kayansa ta wanke shima ai yana daga cikin Hakkokin da kika mgana"
Ina gama fad'in haka na kama Hanyar Dakina Mama ta rakani da kallo cikin mamaki tace"Fa'iza yanzu ni kike fadama wannan mganar..?
Kafin nayi mgana ya katseta da fadin"Don Allah kyaleta Mama tun jiya na roketa ta rantse bazatayi ba"
Sai mama ta shiga tafa Hannu tana salallami ni ko nayi shigewata Dakina na kwanta a gado na,ban san ya suka kare ba sai wajen sha d'aya na Safe na tashi na iske Hafsah ta gama Had'a zobon tana jiran ya huce ni ita ke bani Labarin yadda suka kare Zainab din ta fito tana wani yamutsa fuska tace a kwashe kayan aka kai wanki da guga zata bada kudin wai har tana fadin"Honey sai da nace kayi zaman ka achan ka ki inda kana chan wani kuma wanki ne sai kayi da kanka..?
Dariya ma abun ya bani Hafsah tace"Yaya fa'iza wlh kin burgeni gwara da kika fara nuna ma Mama abunda take yi bata kyautawa"
Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba,ni ba mgana na maida mata ba Abunda ta bukata nayi mata daman na rantse bazan kara yi masa komai ba indai matarsa na nan,ba ni sun raina nawa ba? to yar masu da shi tazo tayi musu su gani.
Ashe mgana bata mutu ba mama ta rika yawo dani wai Ishaq bai da lafiya bani da Tausayi da Imani na barsa zai wanke kayansa da kansa, da Mama tamin mgana nayi mata rashin kunya da Yammah sai ga Anty Binta tare da Anty Mahma har Dakina Anty Binta ta biyoni tana gayamin duk mganar da tazo bakinta cin mutumci sai wanda ta manta,Kamar na sani nace Hafsah ta tafi da Anum da Amir gidan nik'an Aya Ahmad da Musty ne kuma suna Dakin Mama wajen Fadil.
Ko daga kaina ban yi na kalleta ba,sai da naga ta Dage wai in nace zan cigaba da yi ma Mama rashin kunya zamana ne zai kare a inda aka rufamin asiri sai alokacin na Dago ina kallonta kafin nace"To ko a yanzu din ma me ya rage..? Adai yi sha'ani an cuci na kauye"
Bata Fahimci mganata ba ta cigaba da fadin mganarta ta dauka irin da ne har tana kokarin kamamin kunni nako mike nayi baya ina kallonta cikin Hargowa tace"Zaki dake ni ne Tattaciya..?bar ganin kin fara wannan sana'ar ta biyar goma dama bamu san asalin balbela ba ne sai ta gaya ma da ga kasar masar ta fito.."
Na lura suna adawa da samun Cigaba na, a raina ko nace sai dai ku mutu sana'a yanzu na fara shi wlh.
Ganin ta fara isata da mgana ga Musty ya shigo ya tsaya yana kallon mu yasa nace"kiyi hakuri Anty Binta ni fa ba rashin kunya nayi ma mama ba. Cewa tayi ta kira zainab ne saboda tazo ta kula da shi,Tunda ni ba na kula dashi. nayi laifi domin na sakar mata komai tunda gata tazo.? ai acikin kula dashi har da yi masa wankin kayansa.."
Kawai sai ta kalleni bataji kunya ba tace"Lalle kin cika mara kunya Zainab din sa'arki ce ko Matsayin ku da'ya da zaki rika had'a kanki da ita..?
Sai na dago ina mirmishi kafin nace'Tabbas ba matsayin mu d'aya ba, nasan wannan tun kafin ya aurota ya raba mana matsayi kuma kuka rabamananwannan matsayin. sannan ni nasan ba sa'ata bace saboda ni marainiya ce ban aje ba sannan ban ba wani ajiya ba, sannan ni ba yar gata bace kuma ba yar boko irinta ba, ni yar gargajiya ce da wahala da komai na ke rayuwata kin ga ni kaina nasan tazaran dake tsakani da ita kamar tazaran sama da kasa ne ku yi hakuri na manta ne ammh daga yau zan kiyaye zan kuma tsaya a iya matsayina"
Sai ta kad'a kai tana fadin"Da kin ma kanki kiyamullaili"
Ta juya ta fita Musty ya rugo da gudu ya rikeni yana fadin"Umma zagin ki take yi..?.
Da sauri nace"A"a hira muke yi Musty"
Yaro da Fahimtar abu sai yace"Umma naga fa fada take miki"
Nasan sa da surutu su Amir na Dawowa zai gaya musu sai nace"Waya fad'a maka..?
Hira muke yi baka gani ba.?
Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma sai na daga sa sama ina juyi da shi sai ya fara bangalan dariya.
Har Anty Mahma sai da suka kitso mata zencen ta shigo Dakina tana fadin"Gaskiya Fa'iza baki kyauta ba,ban san ki da haka ba,Bai kamata bai da lafiya ki barsa da wanki ba. kuma ina ruwanki da Zainab ita da ba mazauniya ba, dubiya tazo yi zata koma inda ta fito ke dai kiyi aikin ladanki kada ki manta duk abunda kika yi na lada agidan mijinki za'a ninka miki ne kin karanta na kuma san kin san haka"
Gani nayi in na tsaya mata bayani ma bata Lokaci sai kawai nace"In sha Allahu baza'a kara ba"
Sai taji dadi ta dafani tana fadin"Yauwa ko ke fa Fa'iza in anjuma ki shiga ki bama Mama Hakuri shima ki basa Hakuri"
Sai na gyad'a mata kai araina ina jinjina al'amarin wannan rayuwar.
Sai ta gyara zama tana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin aya naga fa alaman kin fara samun kasa da wannan sana'ar kin zama big madam"
Sai ta bani dariya na dara ina fadin"Kai Anty mahma da zoyala"
Agabanta Hafsah ta had'a kunin Ayan da zasu tafi na bata harda zobo ta karba tana fadin"Kada mu zama karya Jali fa..?.
Sai nace"Kada ki damu bazaku karya ba"
Sai tamin godiya ta fice zuwa Dakin Mama ina jin tafiyar su ita da Anty Binta Gogan daman dakin Mama ya yini shiyasa Tun safe bamu hadu da Zainab ba sai da Daddare muna falo ina ma yara karatun Hadisi suka shigo ita da shi,Yaran sun riga sun sani in suna karatu ba na barinsu su tashi sai ba su tashi ba Ahmad ne ya mike da gudu ya nufesa sai ya Dagasa sama yana fadin"Kai ma fa ka fara zama Lukuti irin musty"
Saukesa yayi ko sauraran gaurancin da Ahmad ke masa bai yi ba Zainab kuwa kala batace min ba,gani nayi kamar ranta yana bace ne sai nima na kame kaina haka suka shige ko sannu Daga shi har ita ba wanda yace min. nima ban damu ba na cigaba da yi ma yara karatu bayan mun gama nayi musu Tarihi sannan nace su je su kwanta.
Ni da Anum da Hafsah muke kwana adakina Hatta Ahmad na maida shi tare da su Amir da Safiyar asabar suna da Tahfezz karfe Takwas na tafi kaisu da kaina Saboda Amir ya shiga ajin yan Hadda akwai littafan da zai siya sannan ina son naji karin bayani,na jima a makarantan suna ta gayamin kokarin yarana musamman Anum da Amir malamin Qur'anin su Anum yake min godiya lokaci d'aya yana