Showing 69001 words to 72000 words out of 82431 words

Chapter 24 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

207

shi ya yi alkwarin bazai kara yarda a rika juyasa ba.
Karfin Hali kenan baka da ko asi sai bakin rai da isa,tab zan ko ga yadda wannnan zaman zai kasance.
Sai dai na roki Allah kafin hakan ya faru Allah ya bani mafita.





*Janafty*
*KNKB2018*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Magana fa taki ta kare,Saboda Yaya Ishaq yayi rantsuwan Zainab bazata zauna a ko'ina ba sai gidan nan tare da mu,kuma bazai amince Mahaifinta ya kama mata gida ba.
Kowa yayi mishi mgana ammh bai ji ba,daman yana da Taurin kai wani Lokaci sannan rashin aikin nan nasa yasa zafin zuciyarsa ta karu,Mama gajiya tayi da mai mgana ta kyalesa har da kaninta Dake yamai ta had'a shi ko zai ji mganarsa ammh yace matsayarsa kenan.
Ni tunda nayi mai mgana yace nan din zata zauna ban kara masa mgana ba,na cigaba da Harkokin gabana. Ammh ganin ya dage da gaske yake yi yasa naji kamar nima in kai k'aransa wajen Abba ko Yaya Abdul'Ahad da kan kirani shima duk bayan kwana Biyu yaji lafiyata,Sai kuma na fasa saboda kai kara ba Halina ba ne sannan bayyana sirrin aurena ba Halina ba ne shima,ammh mganar gaskiya Yaya Ishaq zai tauyemin hakkina,Kuma gani yayi ya saba shiyasa yake so ya gwamatsa mu acikin wannan gidan.
Ni ban ma jin kaina nafi jin yarana Saboda komai daman nake yi saboda su ne, an saba tauyemin hakki na Hakura saboda su daman.
Sai nafara tunanin in Zainab ta dawo gidan nan a ina zai sauketa..?
Dakinsa dai falle d'aya ne,Sai bayi rayuwar mace bazai yu yu acikin wannan Dakin ba,bansani ba ko Dakin yara zai sauketa ko kuma ni yake so ya fitar dani daga dakin ya sakata ban yi dai mgana ba na zura ido ina ganin ikon Allah.
Ban sani ba ko sun yi ta ja'in ja da Zainab din ne,kan mganar sai kuma Kwana Hud'u da fara mganar sai ga Mahaifinta Dr.Lawal ya diro gidan Dakin Mama ya sauka sannan,sun jima suna mgana da Mama domin da kan shi yace shi Ishaq din ya basu waje zai yi mgana da Mama, daman wajenta yazo sai ya koma Daki yana cika yana batsewa ina tsakar gida ni dai ina Harkokina ban bi ta kansa ba. sai bayan awa D'aya da wani abu Mama ta leko ta kirasa,ya shiga shima ba jimawa sai ga shi ya fito ya kirani Lokacin kuma na gama Dafa zobo ne, sai na bar ma Anum ta kular min da shi kafin na fita na koma Dak'i na sanya Hijabi nayi sallama Dakin Mama na shiga.
Mama da Dr.Lawal ke zaune kan kujera shi kan shi Uban gayyar yana zaune a kasa nima sai nabi ayarinsa na zauna a kasa dagachan bakin kofar cikin Ladabi na kara gaisheshi, sai naga ya amsa cikin kulawa ba kamar sauran Lokutan da in na gaisheshi yake amsani a wulakance ba.
Mama ce ta kalleni tana fadin"Kan mganar Dawowar Zainab nan ne. Yazo mun yi mgana yace a kira ki  Saboda mganar ta shafeki"
Tana rufe baki yayi gyaram murya ya cigaba da fadin"Ai itama y'ta ce Hajiya. Engr Usman karaye mutumin kwarai ne mun yi zumunci sosai da shi Lokacin muna masters a Buk bayan mun gama shi sai bai cigaba ba,ni kuma sai na tafi nayi Phd dina,nayi mamaki da ya ce min ke y'a kike a wajensa"
Kaina na kasa ban yi mgana ba sai yanzu nasan wato Dalili kenan da ya fara sakemin Tunda yasan Abba, kai wannan rayuwar sai Allah wa ka sani waya sanka ne. ya manta nan ya taba cewa zai batar dani har da Dangina akan yarsa ammh yanzu ko kunya ya zauna yana fadin nima yarsa ce'
Ina jinsa sama sama yana cigaba da bayaninsa Ishaq yake yi ma fad'a akan ya nemesa yazo ammh yaki zuwa.
Mama ce ta karb'esa ta basa Hakuri da Fadin"Ayi hakuri Alhaji ni kaina bansan meke damunsa ba kwanakin nan"
Mirmishi yayi kafin yace"Rashin aiki ne Hajiya kuma ina nan ina masa kokari. yanzu haka kwamitin Binciken da na kafa ya fara nisa kuma da yakinin insha Allahu za'a samu mafita"
Mama ta amsa da karfin Gwiwan Allah yasa a dace da mafita na Alheri,suka amsa da Ameen nima sai na amsa acikin raina Yaya Ishaq kansa na kasa bai ko Dago ba,Sai da shi da kansa ya kira sunansa sannan ya Dago yana amsawa,Cikin mirmishi Dr.Laawal yace"haka ake yi sai kayi fushi da Baban ka.?ni har Abada a D'a na Dauke ka. Kaunar da nake yi maka yasa na baka auran yata mafi soyuwa gareni. Wlh tallahi ba domin kai ba ne bazan taba yarda Zainab ta baro inda ta saba rayuwa zuwa wani wajen ba,Sai dai tana sonka sannan ta shirya ta zauna dakai,ammh sai nace ga Sharad'ina zan nema mata gida inda zata zauna domin bisa adalci ban ga wajen da zata zauna anan ba,Kuma ga Dawainiyar yara achan duk na Dauke ma kasu gata nayi maka sai kuma naga baka gani ba,kana Tunanin ina maka iko ne da matarka,Sannan nace zan nema mata aiki a nan garin,da aikinta ka sameta baka kuma da ikon da zaka hanata. Ammh sai naji kace baka yarda ba,Sai dai ta zauna anan tare da ku kai kanka kayi ma kanka Adalci,Ta yaya zaku zauna awannan gidan kalli fa gidan ga yara ga ku haba sai kace akuyoyi zaka saka ba Mutane ba..?
Ya fad'a cikin zolaya da yanayin mganarsa zaka san sulhu yake nema Saboda yarsa shi kuma nashi Jarabawar kenan,ammh duk wad'anan mganganun bai shiga kunnen Yaya Ishaq ba. yana dagowa sai cewa yayi"Gaskiya ni Daddy bazan amince kace zaka kama ma Zainab wajen zama ba, nan din zai ishemu muma aciki muke zaune me ya ci mu..?Fa'iza nan take zaune da su Amir kuma akwai ishasshen wajen da zata zauna bazata Takura ba, idan ma har zan raba musu gida sai dai in ni na kama Hayar da kudina ko na siya gidan. ammh alfarman ne Daddy bana so, ba domin kuma na raina kokarin ka a kaina ba,a'a wlh nagode sosai bisa Dawaniyar ka gareni"
Ya karishe fad'a cikin Ladabi Dukkanmu shuru muka yi ni sai satar kallonsa nake yi ina ganin mamakinsa mutum ka Dage baka da ko asi lalle zan ga yadda za'ayi wannam zaman.
Mama ranta ya baci ta taso mai tana fadin"Kai dai ka cika Taurin kai meyasa baka jin mgana ne..?
Kai tsaye yace"Mama ki bar ni kawai akwai abunda nake dubawa ne. Indai tana so na to zata iya zama dani a duk inda rayuwa ta kaini. kamar yadda Fa'iza ke zaune dani"
Ya fada yana kallona sai na kauda kai nace ji wannan zai jazamin bakinjini Daman sunan Abba ne ya wankeni,To yana ambaton sunana tsakani ga Allah,Shi ko Dr.Laawal jinjina kai yayi kafin yace"To duk naji zencen ka, nuna min in da in Zainab d'in ta Dawo zata  zauna..?
Kai Tsaye yace"ko ta zauna ad'aki na akwai Tiolet aciki. ko kuma dakin yara sai su koma Dakin Mama tunda Badar na kano duk inda ta zaba duk D'aya ne"
Baki na bude galala ina kallonsa yako hade rai yasha mur,Mama tace"Wannan wani irin lissafin banza ne..?Kai ya girgiza ma Mama yana fadin"Ba lissafin banza ba ne Mama. Mganar su Fadil kuma Fa'iza zata rika kula da su"
Jar uba bansan haka mutumin nan ya raina ni ba sai yau, wato mganar yara Boyi boyi yar reno zata kula da su kuma bai ji kunya ba,Saboda daman baisan adalci ba kuma bai san yadda ake yi ba,Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda gani nayi ko nayi mgana babu amfani ammh na rantse da Allah in ya fitar min da ya'yana daga bangarena to sai dai mu fita tare da ni da su,domin  bai isa ba.
Dr.Lawal dariya yayi kawai. Tsakani ga Allah uzuri ya yi masa talauci ai bone ne,Yana saka zafin rai da tunani masara kyau Mama zata fara fad'a ya Dakaatar da ita da fadin"kyalesa Hajiya na Fahimce sa. Shikenan zata Dawo ammh sai aikin nata ya samu,Ina kan nema mata ne,kai dai ka gyara mata muhallin da kasan bazata Takura ba tunda a inda ka Daukota ba'a Takure ka ganta ba"
Kai Tsaye yace"Daddy gidan iyayena Dabam gidan aure dabam. Ba lalle sai ta samu abunda ta ke samu a gidan su ba,in ina da shi zan yi mata abunda yafi wanda take samu a gidan su, in kuma bani da shi zan kwantata daidai misali"
Kai ya jinjina yana fadin"Gaskiya ne'"
Ni kaina nayi mamakin yadda yau ya yi laushi,ammh ba'a san yadda ransa ke bace ba ne. Saboda Zeey yake komai ta rokesa tana kuka kada ya yi Fad'a da Ishaq she love her Husband kuma ta shirya zama da shi a ko'ina. da ya nuna bai amimce ba, sai dai a raba auran sai Hajiya Halima tayi masa Bore ta tafi Chan rugar adamawa ta kai karansa wajen iyayensu akan zai kashe ma zainab aure,Kiransa suka yi suka yi masa Fad'a sannan da ikirarim Zainab akan in ya kashe mata aure to zata shiga Duniya sai ya rud'e zai iya juran komai ammh ban da Nesa da ya'yansa sannan zai iya rasa farincikinsa akan na ya'yansa ba haka ya Dauka yaron yake ba ya Dauka yadda ya rika Juyasa a farko yanzu ma haka zai juyasa. Sannan bai taba zaton Reshe zai juye da mujiya ba,ya dauka shi ne zai so zeey kamar ransa ya rika binta a daidai wannan Lokacin basu ne zasu rika lallaba shi bashine zai rika Lallabasu sai ga shi komai yana Faruwa ba yadda ya yi zato ba shiyasa yayi kokarin Daidaita Fushinsa.
Sannan yana mamakin kamar Engr Usman da ya sani mara d'aukan reni da Tsage gaskiya shine Diyarsa ke zaune in da bata Daraja,Tun farkon had'uwarsa da Ishaq  yasan Fa'iza bata da wani Daraja a wajen sa.
balle in akayi duba da abubuwan da suka yi ta faruwa,Sai dai yayi tunanin kila ra'ayinsa ne ammh shi kam bazai iya barin yarsa cikin wannan Wahalan ba Allah na gani.
Bai jima ba,suna gama mganar su ya tafi Daman jirgi ya shigo daga Abuja zuwa kano sai ya Dauko tashar Taxi zuwa katsina kuma yana jiransa zai maidasa,ni dai tun a matsayar farko ya sallameni na fito na cigaba da aikina ammh mamakin bawan Allah nan bai fita kaina ba wai yara su koma Dakin mama..?lalle bai taba ganin Haukana ba ne zai gan shi kwananan kuwa karyan Iskanci ma yake yi wlh raina ranar yini yayi a bace,ko fara'a ban yi ba shima kila hakan ya gani sai bai min mgana ba,Sai washegari yaran sun tafi makaranta Anum na tsakar gida tana shara basu fara daukan yan Jss1 ba ne wannan karon da wuri ba shiyasa. ammh komai nata Abba ya riga ya Turomin kudin Sakata kawai za'ayi.
ina D'akina ina had'a kudaden hannuna Hafsah zan kira akwai wasu kudi a hannunta ta biya kasuwa in ta Dawo ta siyomin siga na ya kare.
Kamar Daga sama naga ya fad'omin cikin daki a kaina ya tsaya a gabana kere kere,Sau d'aya na kallesa ban kara ba na cigaba da had'a kudina sai naji ya zauna gefena yana fadin"Fa'iza baki ganni ba ne..?
Kai tsaye nace"In na ganka me zan yi maka..?kai ka shigo min Daki ko Sallama baka min ba"
Sai ya gyara zama yana fadin"To Salamu Alaikun shikenan"
A tsime na amsa masa daganan na bama banza ajiyarsa na lura yana so yayi mgama ya kasa sai kame kame yake yi har da tashi yana leka band'aki da kara Duba Dakin na d'ago ina kallonsa cikin mamaki kafin nace"Hala kayi ajiya ne kake nema.?.
Sai ya fara sosa kai yana fadin"A'a ina duba dakin ne sai yau na Lura yafi Dakin yaran nan girma ashe.."
Sai na yi kasake har kofafin hancina na budewa na shaki iska a kasan makoci na kafin nace"Uhm"
Kai tsaye kuma yace"Shine sai nayi wani Tunani me zai hana ke ki koma Dakin yaran nan ita kuma Zainab sai ta zauna anan tunda yafi girma kinga ita ba rayuwar mu da'ya da ita baa,akwai Danne hakki in na ce ta zauna Dakin yaran nan yayi mata karami kinga Dakinta na Abuja?
Wlh yayi biyun wannan Fa'iza.."
Daman nasan za'a zo wajen mai Hali bazai fasa halinsa ba. meyasa nake Tunanin Ishaq zai iya daidaitani da Zainab.?har abada ta fini a wajensa matsayina bazai taba zamowa d'aya da nata ba,Nagode ma da ya sa Rud'add'en kalamansa basu Rud'eni na sake bashi kaina ba.da yanzu na fi kowa nadama.
Maganar bata D'akina ce ma ta tsaya min arai,na bude baki yafi sau biyar ina rufewa sai kawai na maida Hankalina kan kirga kudin hannuna kama kansa ya yi,sai ya durkusa a gabana Lokaci d'aya yana fadin"Kin gane Fa'iza ki Fahimceni wlh ba da wata munafa nayi wannan mganar ba. Nasan ke zan iya sakaki komai kiyi min sannan zaki zauna dani ko a dakin Bukka ne,ita kuma ba kamar ke ba ce shiyasa kikaji nace haka don Allah kada ki Daukeshi a wani abu"
Ya karishe fad'a yana min uban magiya sai kawai na mike idanuwana ne suka ciko da kwallah me na zama ne.?na tabbata har abada in dai a Rayuwar Ishaq kabir korofi ne ni Fa'iza bazan taba samun daraja ba.
Gaban Wadrope d'ina na tsaya kawai na rasa me zan yi ma saboda takaici,Ina jinsa ya mike yana fadin"Kin ji Fa'iza baki ce komai ba..?
Juyowa nayi bayan na Saita kaina Lokaci d'aya nace"Me kake so nace.?ai ba shawarata kake nema ba Hukunci ka yanke sai kuma ka ke bani Umarni,ba komai kada damu ni daman ban taba had'a kaina da matarka ba nasan tafini Daraja. Zan kwashe kayana kada ka damu ka fad'amata zan bar mata Dakina na har Abada"
Na fada Lokaci daya ina kokarin wucesa na fita Daga dakin kawai sai ya Riko hannuna a fusace na juyo ina kallonsa irin kallon da na sakar mai ne yasa ya sakeni da Sauri a Shake nace"Nace maka zan bar mata dakin nawa har abada daman ai D'ofane nake kada ka damu. Hafsah daman ba zama zatayi ba Abba na nema mata Transfer zata koma kaduna yara kuma ya'yanka ne ko a soro ka zaba musu su zauna bazaka samu matsala da Fa'iza ba"
Ina gama fadin haka na fice daga d'akin domin ji nayi iskar Dakin tamin kad'an,na rasa ina zan shiga sai kawai na shige kitchen na fara safa da marwa Anum ta shigo kawo kwanuka ban ma ji shigowarta ba sai ji nayi tace"Umma lafiya..?Da sauri na goge kwallar da suka kawomin,na juyo ina kirkiro mirmishi kafin nace"Bakomai kin gama wanke wanken.?
Kai ta dagamin kafin tace"Yanzu zan wanke tsakar gidan ko Umma..?
Sai na jinjina mata lokaci daya ina fadin"Gama ki tayani zuba zobon nan in ya wuce kada su kawo wuta bamu saka ba"
Sai ta amsamin da toh Umma,Falo na koma shi kuma daidai ya fito ina ganinsa sai na juya na fita wlh bana son ma ganinsa,a kwanakin baya sai naji kamar Burina zai samu Rauni na fara Tunanin sauke kudurina,ammh yanzu na ji na samu karfin gwiwan da zan iya tunkaran komai menene tabbas ina Bukatar Sabuwar rayuwa ina son na shaki iskar yanci nima.
Gabadaya yini yayi son kara min mgana ni kuma ban yarda mun had'u ba,ga shi dai nace na amince ammh kuma Fuskata ba fara'a Da Daddare na kira Abba muka gaisa sai na masa mganar Hafsah cikin barkwancin sa yace"Ina ta kokarin nema mata Transfer Fa'i..Wlh tallahi ko kuma ba domin aure ba,da gabad'aya zan tattaraku a gidana"Sai nayi dariya ina Tambayansa Ammi yace"Tana chan ta na kwalliya kinsanta gayu gayu dai Mamam Nanah taki ta bar ma yara"Da Sauri nace"Abba ta bar ma yara ka kyallo wata yar caras"
Sai ya fara Dariya yana fadin"Fa'i Laala..aiko baku isa ku hanani kara aure ba.ku gama shafa dai jan bakin da hoda sai nayi ehe"
Ni dai sai Dariya nake yi tuni Abba ya mantar dani Damuwar da nake ciki mun jima muna mgana,Sannan muka yi sallama,Mun gama wayar kenan sai ga Kiran Nana Fatima itakam sai da taji yanayina ba Dadi tace"Fa'in mu ya ya ne.?naji ki wata so silent ne"
Sai nayi saurin ce mata kaina ke ciwo sai tace na sha mgani na kwanta da Safe zamu yi mgana da haka muka yi sallama sai kawai na kira Goggo ita har ta Tsorata cikin Tsoron tace"Fa'iza lafiya kuwa.?goma saura na Dare fa"
Ina dariya nace"Lafiya lau Daman na kiraki mu gaisa ne naga kwana biyu kin manta da D'iyarki"Sai goggo tayi dariya kafin tace"Kina raina Fa'i nasan kina lafiya ke da yaranki,hidima tayi miki yawa Fa'iza kinsan sana'ar hannu tana da wahala nasan sai hankali yanzu"Gyada mata kai nayi kamar tana ganina kafin nace"Na saba goggo ba matsala ga Anum kinsan tana gida sannan in Hafsah na gida tana taimakamin,haka ma yaran ma in sun dawo. Amir kinsan san shi sarkin aiki su shara har girkin su taliya ya iya Goggo"Sai goggo taji dad'i har sai da ta bayyana min cikin Murnan ta tace"Masha Allah Dakyau.Dama iyaye su rika tunani irin naki Fa'iza su rika koyama yaransu, aikace aikacen gida tun suna da kananun shekaru, saboda taimakon iyaye da kuma taimakon kansu a duk inda Rayuwa zaata kai su Allah yayi albarka Allah ya shirya miki yaranki,Allah ya Daukaka su alfarman Annabi muhammadu salallahi alaihi wasallam"
sai na samu kaina da Hawaye sun cikamin kwarmin idanuwana, ina amsawa da Ameen Ameen cikin jin dad'in da ya bayyana har a murya ta. kafin nace"Goggo Baba ati tana kaduna abunta..?
Goggo tace"Tana ko chan Fa'iza ta samu hutu,Inno tace bata son ta dawo ta samu abokiyar zama ai ma ginin Abban naki an kusa gamashi kila in ya kammallu ta dawo"
Kai tsaye nace"Kila ta dawon to.nima Hutu nake son nazo miki Goggo
"Dariya tayi ina jin ta Dauka Zolaya ce sai tace"Ina maraba da Fa'iza Allah ya kawo ki lafiya"na amsa mata da Ameem daganan ta tambayeni megidan da Yanayin zaman mu da Mama nace lafiya lau kamar bata gidan.
Goggo tace'"Nima naga duk tayi sanyi.Rayuwa ta gara Saudatu daman na fad'amiki watarana sai tafi ruwa sanyi a wajenki"na jinjina kai ina Tunanin yadda Mama ta zama kamar kankara yanzu,Duniya ce da mutanen cikinta suka maida ita haka.
Bayan munyi sallama da Goggo na jima ban yi barci ba,Hafsah tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login