Showing 3001 words to 6000 words out of 82431 words

Chapter 2 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

185

isa..?
Ya kalleni cikin Tausayawa kafin yace"Ba mganar aiki Fa'iza ya samu ma ya fito lafiya"
Su mama sai kuka Daman a gidan ne ake maida zencen,Agidan muka kwana Dagani har yara saboda ana saka ran dawowar Yaya ishaq acikin Satin.
Haka ko akayi hukumar tazo ta Duba Gidajen da Yace kada a saka gidan Mama,Mama ta saka kuka miye amfanin gidan in bashi a Had'a dashi,Sannan akwai tsabar kudi a wajenta na sana'arta miliyan uku Anty Binta ma ta saka miliyan Biyu,suka tura ta asusun bankin Ishaq,Saboda kudin su rage nauyi.
muna ji muna gani Hukumar ta kwace gidan da muke ciki da gidan Mama da filin da ya siya acikin gari chan ma Abuja ta karbi wanda zainab ke ciki da motar hawansa, sannan sun bamu Notice Wata daya mu tashi Saboda wajen ya zama mallakin Gwamnati
Lalle mun ga tashin Hankali mai suna tashin hankali,Wannan labarin sai dai mun Dauki Dangana tunda zasu sake sa,Bai amsa laifinsa ba ya riga ya rantse bai da hannu akan lamarin, zasu sake sa ammh ba su kyalesa ba in bukatar wani Binciken ya shigo zasu kara nemansa,Shima da taimakon manya acikin lamarin mijin Hajiyar dala da Kanin Hajiya dake hukumar tare da Mutanen Mahaifin Zainab Dr.Lawal bako.
Mama ta tsine ma duk wanda ya saka Danta cikin bala'i tayi mugayen addu'o'i akan sa,Ta ce tunda ya jefa Rayuwar d'anta cikin bala'i shima bazai ga rayuwa mai kyau ba.
Watan Yaya Ishaq biyu a Hannun Hukuma suka sakesa,Daga Abuja tare da Dr.Lawal da Zainab da yara, sai su Yaya Isa da su Jamal suka iso da shi katsina ko da suka iso karfe goman Dare ne an so ya kwana sai gobe yace Zai je yaga Mama yasan tana cikin Damuwa.
duk da Dare ne, gida cike yake da masu dakon dawowarsa.
Mama na jin Dirin motarsu ta Fice da gudu ita ta bude masa Mota ya fito Allahu akbar Duk wannan fafan da kyau da nasabar ta Yaya ishaq ta tafi cikin wata Biyu.
ya rame ya fita Hayyacinsa sai sumar kai da kasumba ta rufe masa fuska, yayi duku duku kamar ba d'an kwalisa Ishaq Kabir Karofi ba.






*03/07/2023*
*Janafty*
*KNKB2002*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon. a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Mama ta rikesa cikin Fitan Hayyaci,da Dimaucewa ta furta"Ishaq.."
Ashe zan sake ganin ka..?
Sai ta rushe da kukan da ta Dade tana yin sa ammh na yau na Dabam ne, cike yake da tsantsan farinciki sannan hade da fargaba da fidda tsammani.
Rumgumeta ya yi shima cikin wata murya mai cike da laushi da sanyi yace"Mama.."
Sai ya kasa mgana gabad'ayan mu muna kansu,mu kanmu Tausayin ya kamani dole ka tausaya ma uwa indai ta bangaran abunda ta haifa ne. Dakyar Mama ta bari aka shigo da Yaya ishaq gida,ko kan kujeran da ya zauna tana kusa dashi kuka take yi tana Sharb'ewa fadi take yi"Duk wanda ya yi sanadiyar shigar ka wannan Halin Ishaq Allah ya Dai'Daita sa,ya hana sa zaman lafiya a cikin wannan duniyan"
Sai ta kara fashewa da kuka tana cigaba da fad'in"Tsakanin mu da shi Sai Allah ya isa bazamu taba yafe masa ba"
Shi ko yana ta faman lallashinta Fadi yake yi"Ba ga shi na dawo ba Mama? don Allah ki daina wannan kukan hakanan"
Su Goggo kuwa sai sannu Ishaq kawai suke ce masa yana amsawa Hajiyar Dala tace"Sannu Ishaq ka auna arziki Allah ya kyauta gaba"
Cikin yanayin Sanyi jiki yake amsawa Badariya da Anty Binta suka rumgumesa suna koke koke yana mirmishin karfin Hali yace"Kuka dai..?ba ku gani ina lafiya, Daddy ka fad'a musu ba wanda ya Dake ni fa"
Dr.Lawal bako na zaune a gefe ya murmusa kafin yace"Tun muna Abuja nake fadama Jamal haka,ammh bai bar kuka ba kamar wani mace"
Sai aka juya ana kallonsa yana ta sharban Hawaye Ishaq yamika masa hannu yazo kusa da shi Cikin karfin Hali yace"Kun gani ina lafiya basu dake ni ba in baku bar kuka ba,Mama ba zata bari ba"
Ni ko ina gefe daya ban tusa kaina ba Farhan ne a sabe a Hannuna yana ganina ya kirani"Umma.."
Ni kuma na Chabesa da yake har Hutu an taba kawosa wajena kuma indai suna garin to yana wajena sosai yaron ya saba dani.
Sai dai nayi hamdala da godiya acikin raina da ya kubutar da shi Lafiya,duk da an rasa aiki da dukiya sai dai an gode Allah Yaran dake d'akin Badariya basu san abunda ke faruwa ba,suna tare da Halisa,Su na kyalla ido su ka gansa sai suka nufesa suna kiran sunansa "Daada.."
Da sauri duka ya Tare su Anum ce akan gaba sai musty da Ahmad Amir dai a gefensa ya zauna yana fadin"Alhamdulillah Daada ya dawo"
Mirmishi ya saki ya shafa kansa yana fadin"na dawo Baba na"
Anum ta fashe da kuka su Ahmad na tayata Ishaq ya fara lallashinta sai ta tsagaita tana fadin"Daada.."
Sai shesshekan kuka ya tareta sai ya rumgumeta yana fadin"Ina fatan baku yi kuka da baku ga Daada ba ko..?
Anum tace"Bamu yi ba da mun fara Umma zata hanamu sai tace mu yi maka addu'an Allah ya kubutar dakai,mu addu'a muka yi ta maka"
Amir ya karbe da fadin"Umma nata karatun Qur'ani ta d'aga hannu ta na ta maka addu'a Daada nima nayi maka sosai"
Gabada'yan falon sai yayi tsit ana Sauraran yaran Yaya ishaq jikinsa ya karayin sanyi kaunar ya'yansa ya kara kamasa ya kamasu duka ya Rumgume yana Dagowa muna Had'a ido ina shirin na gaisheshi tare da barka da arziki karo na farko a Rayuwata tun da na san Yaya Ishaq da ya taba ambaton sunana cikin Tausasawa.

"Fa'iza.."

Idanuwana a bude na dago ina kallonsa shima ni yake kallo, ba ma shi kadai ba.kaf mutanen dake falon sai kallon su ya dawo kaina,mamaki da al'ajabi basu bar ni na iya amsa mai ba, sai ya kara shayar dani wani gumbar mamaki cikin karin Laushin da yayi ya sake fadin"Nagode..Nagode sosai da baki bari ya'yana sun yi kukan rashi na ba.ko achan in na Tunasu nakan shiga damuwa ammh da zarar na tuna kina nan sai naji sanyi a raina ina da yakinin zaki Kula da su fiye da yadda zan kula da su'"
Ya karishe fada yana kallona da zurmamun idanuwansa da suka zurma Saboda wahala abun mamaki baya karewa har da mirmishi yayi min na Daskare a tsaye na kasa mgana Sabon Ishaq nake gani a gabana ko kuwa dai tsohon ne wanda na sani..?
Ni kaina baki na yayi nauyi,Nauyin da dakyar na iya fuzgo mganar dake bakina sannu da arziki nayi masa, sannan na hada da Allah ya kyauta cikin yanayina nace"Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar Allah kuma yasa a mizani"
Cikin Muryansa mai cike da sanyi da Haiba ya amsa min da fadin"Ameen Fa'iza Ameen Ameen"
Tare da su Goggo suma da suka amsa ni Ni dai tsabar mamakin da nake ci bai sakeni ba naji ana cewa ya kamata a barsa yayi wanka yaci abinci ya huta zuwa gobe da Safe.
Mama da kanta ta rakasa har dakin Jamal ita da su Anty Binta,Mazan kuma fita suka yi Hotel zasu kama su kwana,Sai alokacin muka gaisa da zainab muna ma juna barka da arzikin Farhan na wajena ya makaleni tana Dariya ta bar min shi ta shige Dakin Mama inda ta saba sauka.
Ni kuma daman ba ni da wannan gatan Dakin Badariya ne wajen saukata nan muka shige ni da yaran,basan ya suka kare ba ni dai daganan bayan na gama shirya yara sun kwanta nima na kwanta,Kafin nayi barci na dade ina tunanin Yaya Ishaq da Sabon Tausasawarsa gareni, wata zuciyar ta ankarar da ni da cewa kada na sakankan ce kada na manta Hukuma ce ta tsare shi na tsawon Lokaci yana cikin firgicin da bazai yin wani abu ba kada hakan ya rud'eki daganan na watsar da wannan Tunanin na kwanta barci,ammh sai da na tashi wajen uku na Dare na Dauro alwala nazo na yi nafilfilun godiya ga Allah.
Washegari da na tashi,na riga na saba da aikin da jikina bazai iya zama haka ba,Hafsat bata nan tana Hostel wajen wata kawarta ta kwana tun jiya,Mun dai yi waya da asuba na fada mata Yaya Ishaq ya dawo sai tace ma ta gani a waya Badar ta saka,Sai da nayi sharan duka Dakunan na gyara nayi abun karyawa sannan na kama yaran nan duka nayi musu wanka, Goggo nata min sannu da kokari Su Anum nata Tambayan Daada Hajiyar Dala tace yana Hutawa ba'a so a damesa.
Sai bayan na natsa na kira Yaya Asiya na gayamata sai da tayi hamdala,ta nuna alamun murnanta ammh Yaya Mariya ko ajikinta cewa kawai tayi Allah ya kyauta da nace ko zata zo ne..?sai tace min zaria zata tafi suna, kanwar mijinta ta haihu ban ja mganar ba, sanin bazata zo din ba Yaya mariya akwai kafiya da riko Daman sau d'aya tazo shima ba wai jaje tazo ba,Goggo ce ta dinga mata fada yasa tazo kuma har tatafi Allah ya kyauta bata iya ce ma Mama ba, Da Yaya Asiya ta mata fad'a bude bakinta sai cewa tayi"wani Jaje kuma Yaya Asiya..?Alhakin Fa'iza ne fa ke bibiyan Ishaq da danginsa"
Bige mata baki Yaya Asiya tayi ta na mata fada sai bata kara mgana ba, kuma tunda tatafi bata Dawo ba.
Chan da rana sai ga su Anty Nasara da mutanen karofi gida ya cika da yan Taya murna kamar Biki kawayen Mama har da yan'uwanta na yamai da suka yi sammakon tasowa da makota ammh Yaya Ishq din na barci har alokacin bai tashi ba, ana ta dai yi ma Mama barka da arziki bakinta Har kunne Hajiyar Dala tun safe ta bi mijinta suka koma Bayan Mama tayi ta Godiya,Kuma duk wanda yazo sai ta nuna Zainab tace ayi mata Godiya mahaifinta ne ya tsaya ma Yaya ishaq har aka sako shi,sannan sai ta zauna ta bada labarin sharri a ka kulla ma Danta,kawayenta na tayata mugayen addu'o'i ga wanda yayi sanadiyar haka.
Ni dai ina gefe ban tusa kaina ba,Da kaina na kira Hajiyar su Raliya na fadamata tace sun yi mgana da kaninta ya fadamata an sakesa tace min zata shigo in ta samu sarari yanzu harkokin sun yi mata yawa ne,muka rabu bayan nayi mata fatan alheri da nasara,Yaya Ishaq bai tashi ba sai yammah ya rama Sallolin dake kansa yaci abinci Lokacim Tuni Goggo da iyalanta sun wuce Karofi sai ga Mama nayi mata godiya Goggo tace bakomai an yi ma zumunci ne.
Ya iske Dangin mama da makota da kawayen mama da su Anty Binta,ana ta yi mai barka da arziki,yana amsawa kayan Jamal ya saka riga da wando sai naga yana yawo acikinta ahalin yafi jamal cikan namiji a baya sai dai zama waje d'aya da Tunane tunane yasa duk ya zabge.
Ni aikina shine Saukewa da Dorawa da an yi baki Mama tace a kawo abinci da ance ya kare sai tace ina nake da bazan sake dora wani abu ba? ko meye amfani na.?daman nasan ba ni da amfani shiyasa ban damu ba Zainab kuwa yar gatace tun safe tana ciki tana hutawa tace min Kanta ke ciwo saboda tafiyar Mota Fadil ma ni ta bama shi nayi mai wanka na goyasa duk wanda ya ganni da goyo sai yayi mamakin sanin Tunda Ahmad ya girma ya wuce Goyo,Sai na juya aga Fadil ne,ni renon yara bai dameni ba kafin ma nasan zafin Haihuwa na iya kula da yara ballatana yanzu da na haifa nasan zafin su,Ni nake Dawainiya da yaran manyan da zasu iya cin abinci da kansu suci wadanda baza su iya ba na zaunar da su na basu,Zuwa Dare gidan ya watse sai na jiki jiki bayan sallar isha'i mahaifin Zainab ya iso daga chan inda ya kama yana Hutawa shima a falo aka taru har da ni ina chan gefe  fadil na Hannun kakansa yaran kuma suna jikin Baban su.
Mgana yake akan gobe zai koma Abuja Mama da su Anty Binta suna ta mai godiya ya kada kai yana fadin"Bakomai Ishaq kamar Zeey na Dauke sa shima D'ana ne,Ina so na shaida masa kuma ku zama shaida,Na basu gidana na Abuja su zauna da Zeey Saboda bazata iya zaman wani waje ba in ba Abuja ba,nan ta saba sannan yaran nan sun fara rayuwarsu achan bazau yuyu a sauya musu muhalli ba sannan ta na aiki,Sannan kada ya damu nauyin komai ni zan Dauka kafin ya samu wani aiki zamu iya bakin kokarin mu bazai gagara ba In sha Allahu"
Mama ta hau godiya har da Hawaye shi ko Yaya Ishaq mama ya kallah kafin ya kalli mahaifin zainab yace"Daddy ban ki mganarka ba,ba kuma don na raina kyautatawarka a kaina ba, sai don yanzu ba da ba ne.In a baya aiki ya kaini Abuja yanzu fa..?Ina ganin zamana a Abuja yanzu bamai yuyu ba ne"
Kai tsaye batare da Damuwa ba yace"Why da bazai yuyu ba Ishaq..?ai auran soyayya kuka yi da Zeey, kai ka ganta kace kana sonta itama ta amince dakai na aura mata kai,kuma kai ka zabeta na tabbata zaka bita a duk inda take ballatana ma wannan ba abun damuwa ba ne kada kaji komai aikan ka ya kusa dawowa ko ba wannan ba wani zai samu kaji ko..?
Zai sake mgana Mama ta Dake masa Hannu da kafarta ina lura da su ya Dago yana kallonta yana so yayi mgana ta hanasa har ga Allah sai da naku sa yin Dariya.
Mama ta juya tana fadin'"Kai Alhaji mungode sosai Allah ya bar zumunci shirmen sa kawai yake yi me zai hana ya bita chan in ya zauna anan me zai yi..?mungode sosai Zainab ki tayamu godiya fa"
Tana mirmishi tace"Bakomai Mama"
Niko ina gefe araina nace wai me mata da iyalai ne ake cewa in ya zauna anan me zai yi..?ayi dai mu gani in tusa zata Hura wuta.
Bai wani jima ba yayi ma su mama sallama da cewa gobe zai je kano ya bi jirgi zuwa Abuja.Yaya ishaq da zainab din suka fita rakasa jikokinsa na Hannunsa,ya dade yana Tattaunawa da yarsa kafin ta Dawo cikin gida har ga Allah naso mu koma gida sai naga ko shi kan shi Gogan bai yi mgana ba, kada nazo nayi mgana cibi ya zama kari sai nayi shuru da bakina ammh har ga Allah ina cikin Takura.
Sai da muka shafe kwana Hudu a gidan mama yayi mganar komawar mu Gida Mama tace mutane na zuwa Jaje da murna ya zauna,Zainab kuma aranar Direba yazo ya Dauketa ita da ya'yanta ta koma Abuja saboda aiki a gabana a gaban su Mama tace ma Yaya Ishaq yaushe zai zo..?ina kallonsa ya gimtse fuska kafin yace bai sani ba sai ta wuce tana fadin zasu yo mgana ta waya Mama har bakin mota ta rakata kamar zata goyata saboda kauna.
Mu kuwa sai da mukayi kwana Biyar naga zaman dai yaki ya kare na Tattara yara na nace zan koma gida,Sai yace mu tafi shi sai anjuma da Daddare jamal zai rakosa zasu karisawa Tattauna mganar da suka fara da Mama,naji dadi da bai hanani ba sannan itama Maman yan mutumcin na kusa batace komai ba ko da yake mai zugatan bata kusa Anty Binta kenan.
Ina komawa gida duk yayi kura na zage na gyara ko'ina Amir na tayani shida Anum saboda na koya ma yara na aiyukan da basu da wahala saboda gaba,bayan mun gama muka yi sallar la'asar sannan na Dora girki Sa'adatu da Habiba sun shigomin daman sun je har chan gidan Maman sun min barka da arziki da su mukayi ta Hira sai yammah suka tafi,girki daman farar shinkafa ne Amir ke dubamin ya iya hae dafa indomie da, taliya kadan bamai yawa ba,Da miya nayi mana ina da komai na kayan cefane na saboda tunda na fara samun gumina na daina jiran ayi min komai,tsaye nake  a kaina kuma na tsaya akan ya'yana, ko yanzu din ma nace su kimtsa gobe sai makaranta fashin ya isa haka duk da sun koma karatun zango na farko akwai Laluran biyan kudin makaranta ga kuma abubuwa duk sun Chude ni dai na gama lissafina ko zan yini ina aikin sana'ata ne bazan gaji ba,Saboda ina so yarana su samu Ilimi bana fatan su rasa damar su kamar yadda na sara.
Ina da Aiki da yawa na Hada Turaran wuta da Humra,sannan akwai masu Dilka wasu har kudin su sun turomin rashin natsuwa ne yasa ban ce musu komai ba sannan ga yan sarin Zobo da kunin Aya suna jirana,So nake sai hankula sun kwanta na Dawo da sana'ata kafin komai ya daidaita naga kuma inda Rayuwata zata kara Cillamu tunda sun bamu Notice nan da wasu kwanaki zamu tashi ashe da gaske zan tashi daga wannan Muhallin sai dai ba irin wanda na Kudiri niyya ba.
Yaya Ishaq bai dawo ba sai washegari da Daddare muna zaune da yaran suna duba aikin da aka basu a makaranta,Ni kuma ina ta lissafin kudaden mutanen dake kaina acikin wani Littafi inda ban gane ba na Kira Amir ya dubamun suka shigo shi da Jamal,ya rakosa yaran suka mike suna Ihun ga Daada nima mikewa nayi ina musu maraba dukkansu nan falon suka yada Zango na shiga kitchen na kawo musu ruwa muka gaisa da Jamal shima na gaishesa ya amsa hankalinsa na wajen yaran.
Jamal nayi ma mganar abinci yace sun ci abinci a gidan Mama sai dai ko In Yaya ishaq zai ci shi kuma sai yace sai dai zuwa anjuma, jamal bai Dade ba yayi mana sallama shi kuma ya nufi bangaransa yaran suka bisa yanzu har Ahmad ya Daina barci da wuri.
Ni yaran suka bari da tattara musu littafan da suka watsar na kai musu Dakin su na adana musu nima na shige dakina, ina cigaba da lissafin abubuwa bani da wasu kayan Hadin sai na siyo sannan Kudina na Hannun Hafsah nake bama ajiya basa Hannuna.
Ina so na kirata sai na Duburce na rasa ta inda zan latsa na nemo lambarta,Daman sun koyamin ba duka na iya komai a wayar ba,Sai na mike na leka shashen shi na gansu a falo suna da Budirin su na kira Amir sai dai ban ga baban nasu ba,Anum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login