Showing 54001 words to 57000 words out of 82431 words
ya tattaro wayar baban nashi ya had'ata ya miko min yana Fadin"Umma ga wayar Daada"
Sai na saka Hannu na karba ban kallesa ba nace ya had'a kan kannensa su shiga Daki,Anum sai da yayi mata jan ido ta tafi ta tsaya tana Kura ido da Daukan komai sai anjuma kaji tana maimaitawa.
Sai da suka shige ne na kallesa Mama ta Dake sai faman bashi Hakuri take yi,tana ya kwantar da Hankalinsa shi kuma yana kara rantsuwar Wlh matukar Zainab ta yarda Mahaifinta yasa aka cire cikin nan auran su ya kare.
Kai Tsaye nace"Saboda me zaka ce zaka Saketa..?
Sai duka suka dago suna kallona, ni ko na gyara tsayuwa a raina nace yau ce ranar maida martani Mama ce tace"Haba Fa'iza ai suma abun nasu ba su saka Tunani aciki ba"
Kai Tsaye nace"Zainab ce fa Mama. Zainab matar so yar Dangi,yar gata masu kudi da nasaba"
Sai ta kasa mgana ta Tsaya tana kallo na,Shi ma haka sai ko na kara fadin"Eh ai Zainab ce mai kyau ce ba Mummuna ba, sannan yar asali mai ilimin zamani yar gata yar masu kudi yar dangi mai cikakken gata,matar nuna wa duniya,wacce zata haifa maka ya'ya farare masu kyau ba irin ya'yan Fa'iza ba,matar da kuka zabeta sama da kowa matar da kuka fifita ta fiye da kowa matar da kuke so da kauna. Meyasa saboda wannan matsalan kace zaka saketa ke kuma Mama baki Tsawarta masa ba..?
Na karishe fad'a ina tsareta da ido kunya ya kamata sai ta kasa mgana shiko Tsawa ya dakamin bai so na kara mgana na warware komai ban kulasa ba na cigaba da fadin"Ita fa ka zaba sama da ni. Ka fifita ta sama da ni,Ka fifita zuru'arta sama da tawa zuru'ar, sannan ka fifita ya'yanta sama da nawa ya'yan,to ta ina kake Tunanin zaka hanata abunda take so.?ai tun farko a haka ka ganta, kuma ka ji ka gani kana sonta.."
Cikin hargagi yace"Ya isheki Fa'iza..Ya isheki haka nace"
Ya karishe fad'a kamar zai Dakeni sai nayi baya na tsorata kada yakaimun duka,Cikin wata murya yace"Ki bari Fa'iza ba kyau irin haka. don Allah ki bari kada ki kara Tunzarani"
Sai da na tabbatar da nayi baya sannan nace"To ka daina mganar Sakin nan bai dace ba gaskiya, ai ku ba yara ba ne, kun fara tara kyakyawan zuru'a a tsakanin ku"
Sai kawai ya Dafe kansa ya koma kasa ya zauna Dirshan yana kara Dafe kansa,Mama na gefe jikinta yayi sanyi da kunya yasa ta kasa mgana,ni ko sai naji zuciyata wasai ko banza na gasa musu mgana sannan na maida musu martani.
Yana girgiza kansa yake fadin"Nayi Nadama Fa'iza nayi nadama ba tun yau ba.wannan auran bai amfaneni da komai ba sai bacin rai da Nasani,ban bi Turban Annabi ba wajen auran nan sai Allah ya barni da zabina,ya bani mace tagari ban gode masaa ba,na rika Hange hange ina ganin na wuce da ajin Fa'iza,Sai ga shi na bi auran kyau da nasaba da ilimi daga karshe hakan bai amfaneni da komai ba.."
Da Sauri nace"Ya amfaneka mana Zainab na sonka sannan kuma ta fara tara maka irin zuru'ar daka ke so"
Idanuwansa Jajir ya d'ago yana kallona kafin yace"Bata so na, in da tana so na,da bata fifita ta mganar mahaifinta akan nawa ba. Tana ganin tana da kyau alfarma tamin data aureni,Tana ganin tana da ilimin da Taimakona tayi ta aure ni,tana ganin tana da Gatan da ban isa da ita ba. kaico na da nabi Rudin duniya da Rudin Shed'an,ga shi yanzu ina Nadama Shiyasa duk wanda bai bi Turban Annabi ba, tun a duniya zai Tabe Annabi ya fad'ama mu auri mai addini domin itace mafi kyawun cikin su"
Dagani Har Mama ba wacce tayi mgana ita kunya da Sanyi ni kuma na shiga wani yanayi mara Dadi a lokacin.
Shuru yayi yana sauke Numfashi kafin yace"Mahaifinta bai Daukeni a bakin komai ba,gani yake taimakona yayi alfarma ya yi min don ya bani auran yarsa shiyasa yake takani yadda yaga dama har cikin gidan nan ya tako ya ci zarafina na, kasa komai ammh wannan karon wlh bai isa ba. sai na nuna masa na fisa cikakken iko da yar tashi ta zubar da cikin ta gani Sai dai kuma a bi wani Sarkin"
Da haka ya shuru takalmansa yayi waje Mama na kiransa bai ko Juyo ba,Ni dai nace Allah ya kyauta na koma ina cigaba da wanke wanke na, Mama na Tsaye ta kasa gaba ballatana baya har ga Allah ba wai dadi naji ba ammh raina bai baci ba,Gwara su fara gani Tun yanzu ban ga laifin su ba,Irin Rariyan da ya siya ne kuma don tayi zubar ruwa shatata bai kamata yayi korafi ba.
Ina gama aikina na shige Daki abuna,Na fara wata Hidiman yaran kuma karatu na iske su suna yi,Duk da nasan suna jin tashin mganar Baban nasu daga falon,tsakar gida na fito zan Dafa zobo na,Sai naga Mama an kwashi kafafun da sanyin jiki ta koma Daki Ranar sai dare ya shigo gidan ajaran majaran a falo ya fadi kan kujera yana sauke Nunfashi ina mai sannu da zuwa ya amsani a Dake kafin yace na sama mai ruwan wanka.
Sai da ya rarrafa ya shiga Dakinsa na bisa na kai masa wayarsa da ya fasa da tawa ina fad'in"Ga shi matarka nata kira, tana son mgana dakai"
Domin tun bayan La'asar Zainab ke kirana tana tambayansa nace mata ya fita ta Dameni ta kira yafi sau goma Daga gani bata cikin natsuwarta ne.
Yana cire rigan jikinsa ya d'ago yana kallona ina shirin ficewa yace"Dawo ki Dauki wayarki"
A kausashe nako ki dawowa na fice ina jinsa yana fadin"Lalle itama ko zan fasata wlh" a fili na furta"Kana fasamin waya zaka biyani kayana"
Daganan na fita zuwa kitchen sai da ruwan yayi zafi sannan na juye mai na ba ma Amir ya kai mai ban koma Dakin ba, abinci ma Anum ta shigar mai da shi yaran suna falo suna karatu ni kuma ina Daki,Hafsah na gefe na muna mgana sai ga shi ya shigo daga gani yanzu ya fito wanka ga kansa nan na digar da ruwa yana shigowa yace"Hafsah jeki falo wajen yara zan yi mgana da yayarki"
Ba musu ta fice ya kariso gabana yana fadin"Ki ka bama Amir ruwan zafi in ya kona sa fa..?
Sai na kallesa kafin nace"Ba yau ya saba dauka ba, zai iya ne"
Sai ya kuramin ido kafin yace"Ba kyau Fa'iza na horu fa don Allah ki yi hakuri".ganin ya fara sauya mganar yasa na mike na fice,na bar masa Dakin jiki a sanyaye ya koma Dakinsa ya shirya abincin ma afalo ya fito ya ci,Ina gefe sai kallona yake yi ni ko nayi kamar ban gansa ba.
Wayata sai washgari ya aiko Anum da ita, ban ko Duba ko sun yi mgana ba. ammh naga an kirani Hafsah ta Dubamin tace Abba ne da Nana Fatima daman sune rana bata fitowa ta fadi basu kirani sun ji lafiyata ni da yara na ba,Har ga Allah ina kaunar Nana Fatima kamar yadda take kaunata,Sai da na natsa sannan na kirata muka gaisa sai tace measurement din yara da nawa take so na Rubuto mata sai nace ta bari sai Hafsah ta dawo zata turo mata,mun cigaba da mgana duk akan Bikin Yaya Abdul'Ahad ne da Raliya bayan sallah Tana fadamin Nana Fadila ta fitar mana da anko imu imu gabadayanmu,Na lura suna ji da Bikin nan ko don shine na farkon da zasu fara na Namiji, barin ma Ammi kamar Abdul'Ahad ba yaron ta na fari ba,ba ruwanta da kawaici da ita ake shiryawa komai. Abba kuma daman ba mazauni ne ba ne tafiya na yawan kamasa Ammi ce akan komai.
Da Hafsah ta dawo na saka ta tura mata har da na takalmaa,Ban san cewa Yaya Ishaq bai yi mgana da Zainab ba, sai da ta kara kirana bayan na Dauka mun gaisa sai ta sakamin kuka na rud'e na zata ma ko wani abun ne ya faru cikin Kid'ima nace"Lafiya Maman Fadil..?.
Cikin kuka tace"Maman Amir ki saka baki Honey ya daina fushi dani wlh ba laifina ba ne. Daddy ne ya matsa kuma ni nace mai bana so tunda Honey baya so kuma ba'a cire cikin ba. wlh nayi ta kiran sa wayarsa a kashe bana samun sa"
Sai shesshekan kukan ta, na fara lallashinta kafin nace"Daman jiya baku yi mgana ba ne da na kai masa wayar ..?
Da Sauri tace"kashewa ya dinga yi Maman Amir yaki ya saurareni ma, Daddy fa har fushi yake yi dani saboda naki amincewa da mganarsa Maman Amir don Allah ki basa hakuri wlh ban cire cikin ba, yana nan kada yace zai sakeni wlh ina son mijina"
Sai ta bani Tausayi cikin sanyi na nace"Kiyi hakuri ki daina kuka in ya Shigo zan mai mgana"
Da haka muka rabu sai mganarta ta Tsayamin arai, tana son mijinta har ga Allah nice shaida,ammh Mahaifinta ne ya riga ya saba da juya al'amarin ya'yansa,Ni kuma na kudiri niyar daidaita Tsakaninsu saboda itace Dahir dinsa,Da ya shigo Dakin Mama ya tsaya,sai da ya jima sannan ya shigo Dakina yara suka mike suna mai Sannu da zuwa Dakinsa ya shige Saboda ina da mgana dashi da kaina na tafi kai masa abinci,yana zaune ya yi Tagumi ammh yana ganina sai ya cire Tagumi,sannu da zuwa nayi masa na sauke mai abincin a gabansa ya jawo yana fadin"Me muka samu ne..?
Ina zama nesa da shi nace"dambun Shinkafa ne da zogale"
Cikin yanayin sa yace"Salon ya shake mu Fa'iza"ina Dariya nace"Tuwo naso nayi ban samu gyad'a ba,sai yara sukace Umma ki yi mana Dambu"
Bai ce komai ba sai da ya tashi ya wanko hannunsa ya fara ci sannan yace"Ko bakomai zamu dora da zobo mai sanyi"
Yafad'a yana kashe min ido sai nayi dariya yana ci muna hira,Sai da ya gama ya kuma dora zobo mai sanyi kamar yadda yace sannan na sako mai mganar Zainab kici kici yayi da Fuska kafin yace"Ina ruwanki da wannan mganar Fa'iza..?
Na rausayar dakai nace"Da ruwana mana ai yar'uwata ce musulma kuma shi ai sulhu alheri ne"
Sai kawai ya mike yana fadin"To ki cire bakin ki a ciki ba ruwanki ahto.."
Sai naga daga taimako kawai sai na tattara kwanukan daya bata na fice ina fadin"Allah ya kyauta"
Da gatse ya amsamin da Ameen sai abun ya bani Dariya a raina nace mata da miji sai Allah sai su shirya ma ban sani ba.
Kuma saboda Zainab din yaki kai wayarsa ya gyara. ya gwammace ya zauna ba waya nidai tunda yace ba ruwana na cire bakina data kara kirana,sai nace mata nayi mgana yace zai kirata in ya gyara wayarsa Da dai taga ba Nemanta zai yi ba an fara azumi Takwas sai gata ta iso,ita kadai ko Farhan bata zo da shi ba, ta yayesa yana gidan su Tace ko Daddy bai son ta taho ba Shari'a har Falon Mama ammh Gogan ka yace shi fa ya gaji kowa yayi ta kansa baiwar Allah sai kuka take yi a raina nace ita kuma nata Jarabawar kenan na soyayya Allah yasa mu dace.
Yadda yake yi mata ban dauka zai iya kallonta ba, ammh dayake Namiji sunnsa Namiji sai ga shi sun shirya an shiga kurya an yi lamo,Daganan na san sha'anin mata da miji sai Allah Shi da har masifa ya rikamin wai na ce ta tafi nace dayake ni na kawo ta ba,Bata koma ba sai da suka Daidaita da juna kwananta Biyar ta koma Abuja,motar Haya ta shiga abunda bata tayi ba ammh ga shi Namiji ya sakata acikin wani Hali.
Ni daman tunda yace na cire bakina na kama kaina, ko da tazo ta zaunar dani tana gayamin har abunda ma bansani ba iyakata da ita hakuri kawai Domin kamar yadda yace ba ruwana to ba ruwana din.
Mun yi azumi sha biyar Hafsah suka samu Huta,Washegari Yaya Abdul'Ahad yazo wajen Raliya shi ya wuce da ita Tare da Anum da Laila ta matsa sai an zo mata da ita haka kurum Allah ya hada kaunarta da Anum da taji ma dagantarkar dake Tsakani sai tace daman ba haka kawai take kaunar Anum ba ashe jini d'aya muke da mijinta.
Musty har da kuka akan sai ya bi Anum Dakyar Babansa ya Lallashesa akan zamu je da sallah sannan ya Hakura,Azumi nada ashirin da Biyar sakon Abba na kayan sallarmu ya iso karofi aka kai,Yaya Isa ya kawo min nawa har gida duka da ni da yara.
Har da Babansu,kala biyar biyar,harda na Anum data ke chan Da na Hafsah kenan wasu za'a sake dinka musu Yaya mariya haka aka kai mata nata ita da Yaya Asiya,Bakina yaki Rufuwa na kira Abba ina masa godiya sai yace"Ba godiya tsakanimu Fa'iza duk abunda nayi muku ba komai ba ne, ku ya'ya na ne kamar yadda zan yi ma Nana Fadila haka zan yi muku"
Sai na kasa mgana,Saboda farinciki ya gamamin komai ganin ba na Mama aciki sai na saka kudi na siya mata kala uku har da Hijabi da takalmi ta karba Karo na farko da Mama ta taba godemin bayan nayi mata wani abun alheri..
Shi kuma Yaya ishaq da nace ya kira Abba yayi masa godiya sai yace"Ba kin kira shi ba?sai na Dagamai kai cikin basarwa yace"Ya wadatar kin hada da godiyata da naki godiyar"daganan ban kara mai mganar ba,na lura ba duka halinsa ba ne ya sauya wani Lokacin rashin Mutumcinsa na nan bai tafi ba,Wannan karon dai mun yi sallah cikin Farinciki da wadata Jamal ya Dawo gida sallah shima nayi masa kayan sallah har da Hula da takalmi,Badariya a kano tayi sallah Tace Hajiyar Dala ta mata kala Daya nima na tura mata kudi tayi guda Biyu ta kara da shi Saboda yanzu ina samun kudi sosai tunda bana taba kudin sana'ata tunda Abba ya karamin jari abubuwa suka daina Cushemin ga shi muna da kayan abinci sosai,wannan sallar ko Anty Binta bata kawo mana komai ba ganin bana neman komai,Naman salla kuma Abba sa ya saka aka siya aka yanka a karofi aka raba mana Nama,Ni kuma na siya mana kaji,sai bayan na siya ma Hajiya ta aiko mana da shi,Sai dai ma muka rika kyautarwa,Ranar sallah na uku naje Karofi ni da yara muka kwana Daya muka Dawo sai kuma washegari naje Gidan su sa'adatu nima tazomin ranar Sallah na biyu,Daganan na sauka gidan Hajiya ana ta fentin gida saboda Biki bayan salla da Sati Biyu ne.
Hajiya tace wajenta zan zauna kaduna sai za'a tafi da Raliya sai na bisu mu tafi ina Dariya ina fadin"Hajiya su da suke jiran mu tun ana sauran Sati daya..?
Hajiya tace"Aa su mariya su je ammh ke kina gidan nan ai Raliya kanwarki ce, ke zaki mata gyaran jiki da Hadin Turaruka'"Na dauka Hajiya wasa take yi sai da Ammi ta kirani tana fadin"Fa'i shikenan sai Hajiya ta mana Haka.? Ina uwar d'iya ammh ana min fin karfi akan ya'yana".
Nidai dariya na dinga yi ban yi mgana ba ina jin Abba na gefe na fadin"D'anki zata gyara ma Amarya fa Maman Nana"
Sai tace"Kuma fa hakane to na d'aga kafa. ammh da sharad'in a Turaran Amarya za'a dibarmin nayi ma Baban Nana kwalliya da shi"
Abba yace"Shikenan kuwa na uwar miji da matar d'a ba"
Ni dai sai dariya nake yi in ka Biye ma Abba da Ammi sai cikin ka ya Kulle Tuni muka shiga shirin Biki,Biki ne na manyan mutane,Balle Abba wannan ne na farkon da zai aurar da Namiji,an aiko da katinan Daurin aure kayattu Abba yace duka jama'ar Karofi yan'uwa na kusa kusa yana gayyatarsu,Har Hajiyar Dala Yaya Asiya ta gayyata ita da suke ta shirin su ita da yan gidan su Ammi ga Nana Fatima a kusa da ita, tunda har gidan juna sun je ina Dutse ina kano.
Hajiyar Dala taga bikin na irin nasu ne tace zataje har kaduna,sai mamaki take yi yadda Lokaci da'ya Gata ya Lullube rayuwarmu yanzu babu abunda ya'yan gata zasu nuna mana muna.
Nima a barayina na gayyaci su Anty Binta da su Anty mahma,da mama ni daman ina gidan Hajiya kamar yadda ta fad'a,Hajiya tamin dinkunan ankon Biki,Kala hudu har da na Lonching din da zata hada na mata zallah,achan kaduna ma su Nana Fatima sun ce duka kayana sun zama Ready na fitar Biki achan zasu yi Dinner din su gabad'aya.
A na saura sati daya biki Badariya ta Dawo suka fara shirye shiryen saboda gyaran jiki sai suka tare a gidana nan suke kwana,gefe daya kuma ina hadin Turaruka ga zuwa gidan Hajiya ba na ko zaman gida,Abba ya kirani yace na turo yara suzo tunda ni sai ranar Daurin aure,sannan a kaduna za'a Daura auran Raliya gidan kanin babanta Hajiya tace ayi chan yafi sauki kawai,su Goggo duk zasu tafi kaduna ana gobe biki sai na had'a su da yaran suka fara yi min gaba da su Mama su goggo tabi Anty Binta kuma ita da Anty mahma da Halisa direban Anty Binta zai kai su, su Yaya mariya da su Yaya Asiya tuni suna kaduna ana sha'ani da su sai kirana suke yi naji kamar nima nayi tsuntsuwa na ganni achan.
Tun ana gobe biki na tare gidan Hajiya,gidan ba kowa sai Yaya Ishaq da jamal,zasu Daurin aure gobe domin Abba yace yana son ganinsa,mota guda Hajiyar su Raliya ta basu zasu bi tawagan mazan da zasu tafi daga nan katsina. mu ko muna chan muna ji da Lonching,na hadu da manyan mata sosai kawayen Hajiya,Amarya bazatayi walima ba sai ranar Lahadi da yammah bayan an kaita gidanta,Hajiya da ya'yanta ni suka saka kan abinci akwai ma'aikata ammh ni nake nuna musu yadda za'ayi.
Ranar asabar daya daga cikin asabar din karshen mako aka Daura auran Raliya Kasim Saulawa da angonta Abdul'Ahad Usman karaye a garin kaduna a masallaci sultan bello,Ana gama Daurin aure ango da Tawagansa suka nufo katsina inda akayi pinic party dasu da kawayen Amarya adaran Ranar,Washegari sai shirin kai Amarya tun Safe aka shirya Daman tuni an je an yi mata Jere a gidanta acikin garin kaduna zai zauna anguwan Sarki chan yake da gidansa mai kyau.
Amarya su suka fara yin gaba ita da kawayenta da angwaye,mu kuma sai da muka Tsaya muka shirya wasu kaya muka tafi da su,Sai yammah muka isa kaduna,gidan Raliya muka fara sauka chan na iske su