Showing 45001 words to 48000 words out of 82431 words
yadda yayi tsammani ba?
Duk wad'anan tunanin suka taimaka wajen da dakushe murnanta a fili har Yaya Isa yayi sallama kofar falon Goggo Ya shige Hafsah tabi bayansa nice karshen shiga falon, sannan sallamata ma a saman bakina ta makale idanuwana suka fara wurgawa cikin falon ina neman bakon fuska naga Goggo da megidanta,Sai Baba Ati da wasu Tsofaffi maza daga gidan su Tamadina ne,Sai wata Dattijuwa mai natsuwa da Haiba zaune kan kujera cikin shigar alfarma kallo d'aya zaka yi mata kasan ta samu dukkan gatan duniyan da suka Boye shekarunta.
Gefenta a kasa wajen kafafunta wani kamilin megidanci ne baki sai dai bakinsa ya hade da hutu da jin dad'i da Fatarsa ta sauya,yana Sanye da Shadda Mai ruwan kasa har da babban Riga tana maiko kansa da Hula zanna na mutanen maiduguri,yana duke ne ammh ina iya ganin yadda yake saka karamin farin kyale yana Tsane ruwan Hawayensa,Yaya mariya na gabansa itama a duke kamar kukan take yi, Dattijuwan nan ta rike mata hannu alamun lallashi.
Daga sama naji murya Goggo tana fadin"Alhamdulillah ga Fa'iza nan da Hafsatu nan sun iso.."
Kamar an zabure sa haka ya mike cikin Haibarsa da muryansa da ta dakeni yace"Ku matso nan ya'ya na ku matso naji dumin ku..Ku zo ga Abban ku"
Yake fad'a cikin nuna tsananin murnansa sai alokacin na kara kallonsa ba shakka jini ba karya ba ne ina ganin kama ta jini Tsakaninsa da Tamadina Hafsat ne ta nufesa zata duka ta gaishesa sai kawai ya Rumgumeta,hawayensa na zuba ni kuma ya miko min hannu sai na sulale kasa a gabansa idanuwana sun ciko da kwalla,Dattijuwan nan ta kallemu ta kara kallon mu musamman ma ni sai kawai ta fashe da kuka tana fadin"Allahu akbar daga ganin wannan na shaida jinin Lauratu ne"
Sai kawai ta rikice tana rusa kuka Goggo ta matso tana fadin"Haba Hajiya zuwaira ashe kukan naki bazai isa hakan nan ba..?.
Cikin kukan take fadin"Dole nayi kuka, Dole na koka na yi sanadiyar da na yanke ganawa Tsakanin yan'uwan juna.?kaico na.."
Tafad'a cikin wani yanayi da sauri ya tareta da fadin"Inno ni ne kika yi ma wannan laifin kuma nace na yafe miki ba shikenan ba..? Ni dai naji ciwon rashin ganawa da yar'uwata guda d'aya da nake da shi,Ammh nayi murna daya kasance ta barmun zuru'an da bazan jima ina kuka ba, in na kallesa zan tuna yar'uwata ta bar min su ne domin kada in na zo nayi kukan rashinta"
Gabad'aya kalamansa sai suka sakani rauni bansan Lokacin da na fashe da kuka ba ganin haka yasa sai Hafsah ta d'auka Yaya mariya ma daman mun sameta tana kukan ta ne.Wacce aka kira da Inno ta sauko kasa tana neman Durkusa mana cikin kuka tace"Ku yi hakuri ku yafe min ya'yan nan na zalunce ku na yanke ganawa tsakanin mahaifyarku da dan'uwanta"
Da Sauri ya saki Hafsa bayan ya zaunar da ita ya karisa gareta ya rikota ya maida ta saman kujera yana fadin"Inno ki daina wannan kukan don girman Allah"
Sai ta ji mganarsa ta koma tayi shuru tana sharan kwallah kasa ya zauna a gabanta yana kallonmu d'aya bayan d'aya kamar yadda muke kallonsa. Lokaci da'ya yana Dauke Hawayensa da Farin hanky din dake hannunsa.
Cikin Kayattaciyar Muryansa ya dago yana kallon su Goggo kafin yace"Cikin su wacece tafi kama da yar'uwata..?
Har Baba ati da goggo suna had'a bakin wajen fad'in"Gata nan a gabanka Fa'iza kamar Tamadina ta tsaga kara yadda ka ganta haka mahaifiyarta take. sai dai ita bambamcin Tamadina bebiya ce ita kuma Fa'iza jinta ne yake da rauni"
Kawai sai ya kuramin ido Lokaci d'aya yana fadin"Naji dadi da akwai fuskar da zan rika ganin yar'uwata a ciki, baku da Hoton yar'uwata ku nuna min ya'yana..?.
Ni dai na kasa mgana Hafsah ce tayi karfin Halin cewa"Yaya Asiya na da shi a wajenta"da alamun karin bayani ya ke kallon mu Yaya mariya ta jinjina kai tana fadin"Itace babbarmu wacce su Goggo suka ce tana kano tana aure"
Sai ya jinjina kai yana fad'in"Rashin sani ne ai kano gida ce a wajena chan na girma nayi karatuna kuma chan nayi aure,kafin chanjin aiki ya Dawo dani nan kaduna,yanzu komai ya kare tunda Allah yasa nazo kuma na ganku nayi alkwarin bazan kara sakacin da zaku rasani ba"
Sai ya fara sharan kwallah ya cigaba da fadin"Yau yau din nan Inno ta fad'amin ina da yar'uwa bayan ta sanar dani inda dangin Babana suke,a gaggauce na taho ko iyalaina ban zo da su ba suna kano ana auran kanin Mai dakina,yaran duka suna chan,ni kaina Tafiya gareni zuwa porthercourt gobe akwai Taron da muke dashi daga wajen aikin mu aka turamu,ammh nace bazan zauna ba sai nazo na ga ahalina ina zuwa kuma sai na samu labarin dangi duk sun kare itama yar'uwan nawa Allah ya yanke ganawa tsakanin mu da ita"
Inno na sharan kwallah tace"Allah ya jikan Hafsatu ina kallon fuskarta ranar da zan bar garin Lokacin bata wuce shekara Biyar ba"
Aka amsa da Ameen Ameen mu dai sai kuka muke yi muna sharban hawaye Shi ma kukan yake tayamu ammh nasa bamai sauti ba ne,yana dai yi yana tsane hawayensa,da farin Hanky din dake Hannunsa..
Baba ati ta gyara zama tana fadin"Zuwaira wani dalili ne yasa tunda kika tafi baki kara waiwayomu ba sai yau.?Sannan wannan yaron baki taba sanar da shi komai game da mahaifinsa da Danginsa ba..?
Inno ta fara kuka kasa kasa tana fadin"Ba laifin Usman duka acikin abun da ya faru kada ku manta na bar garin nan yana da kananun shekarun da bazai iya tuna komai ba!
Duka abunda ya faru laifina ne shiyasa nace ku yafemin"
Hannayenta ya rike cikin Lallashi yana fadin"Inno ashe kukan nan ban ce ya isa haka ba..?
Da jajayen idanuwanta tace" USMAN rashin kuka na ba zai sa laifina yaki bayyana ba,da gaske na zalunceka na tafi dakai na raba ka da Dangin mahaifinka gashi karshen karshen sai da na kawo ka gare su"
Sai ya kasa mgana Saboda bata kiran sunansa sai dai tace mai BABAN Nana kamar yadda matarsa ke kiransa.
Gyara zama tayi tana kara gyara zaman mayafin dake kanta tace"Bani da wani kwakwaran Dalilin aikata abunda na aikata Sai dai nace rashin son da ban yi ma mahaifin Usman ba aka aura min shi,alokacin ina da wanda nake so ammh Mahaifina yayi min Dole,ya aura min shi aka kawo ni wannan garin kada ku manta tun Lokacin da aka kawo ni,ban yi zaman Dad'i da kowa hatta da kakarku da ta haifi mahaifiyarku Lauratu,Sannan ban saki jiki da kowa ba,bani da aiki sai kuka sai zama cikin Damuwa Ko Usman Rabo ne ya rantse tsakanina da mahaifinsa aka same shi,ko da zama ya kare tsakanimu da shi bayan rasuwarsu zuciyata bata Rusuna ba. gani nake yi in na barsa a wajen ku bazaku barsa ya zauna dani ba, shiyasa tunda kuka amince na tafi da shi a raina nakudiri niyyar zan Nisanta shi da abunda ya shafi wannan nahiyar,Tsakaninsa da mahaifiyarku bai fi shekaru uku ba yana gabanta domin neman irin haihuwan yakai mallam ga aurena sai bayan na haifi Usman sannan Lauratu ta Haifi Hafsatu tabbas nasan an haifeta da laluran rashin ji da mgana,Sai dai bamu zauna da lauratu ba,Duk da mun yi zaman kishi na mutanen na wanchan lokacin,Ni ba kishi nayi da ita ba, ni tsanar duk abunda ya shafi mallan nayi shiyasa itama ban yi mu'amala mai kyau da ita ba,Ita kuma tayi kishi dani a matsayin wacce ta auran mata miji duka duka zamana ko shekara goma ban yi ba na bar karofi na koma karaye gidan mahaifina ba jimawa shima ya rasu.sai yayana ya Daukeni zuwa cikin Hukumar Dala ta kano inda yake zaune da iyalansa yana kasuwanci.
Shi ya rikeni ya rike Usman har ya zama abunda ya zama,A baya shi ba mai arziki ba ne,d'an kasuwa ne mai karamin karfi ammh daga baya ya samu arziki har mun koma cikin garin kano a anguwar mandawari da zama,A hannunsa Usman yayi karatu,tun bayan dawowarmu kano Usman na yawan son ya tuna yar'uwansa da Dangin mahaifinsa,Sai dai ina kokarin shafe Tunanin acikin ransa a hankali a hankali sai abun ya shafe a ransa,Da kuma girma ya kamasai sai dangina suka zame masa komai yaya na shi ya bashi auran Diyarsa Azizatu ya aura a shekarun baya har sun tara zuru'a a tsakanin su,Daga baya Usman ya so ya san wani abu kan Dangin mahaifinsa ni nayi masa iyaka da hakan nayi masa Kaushin muryan cewa in ya kara tambayata garin mahaifinsa ko abunda ya Dangance shi sai na Dagamai Nono, daga Lokacin Bai karamin mganar ba.sai naji dadin haka ammh a raina ina jin ba dadi kamar wani abu mai nauyi ya zauna a kirjina,har ga Allah kiyayyar mallam ce da na sakama raina ta Haifarmin da haka na dad'e ina mafarkai marasa kyau har barci bana samu a Lokacin Dalilin haka yasa na zauna sai nayi Tunanin wannan shine babban laifin dana aikata wanda Allah bazai yafe min ba,nayi mafarki da mallam yana fad'amin na ki had'a kan ya'yansa Allah bazai barni ba.yau da Safe na kira Usman na fad'amai komai a kansa sannan na shaida masa yana da yar'uwa a garin Korafi inda na Haifesa"
Ta karishe fad'a cikin kuka Lokaci daya tana fadin"Ku yafe min ya'yan nan wlh sharrin dokin zuciya"
Ba wanda ya iya mgana sai ajiyar zuciya na mutanen dake falon Mu ko sai kuka muke kamar yanzu akace Tamadina ta rasu,Baba ati ta gyara zama tana fadin"Ashhha.Shiyasa dokin zuciya ba dadi..Yanzu ina amfanin wannan..?lauratu dai da mallam Hashimu sun bar duniya itama Tamadina Allah ya karbi abunsa ba domin wad'anan yaran data bari ba da yau kin jefa d'anki cikin Damuwa saboda bazai ga wani abu daya Danganci yar'uwansa ba"
Goggo tace"Koma dai menene yanzu ya wuce daman chan Allah bai kaddara saduwa tsakaninshi da Tamadina ba,Mu yi hamdala tunda muna da sauran rayuwa.Ga ya'yanta nan data bari shiyasa nace a dauko su su ganka kaima ka gansu Asiya ce kadai bata nan saboda tana nesa"
Yana duke a gabanmu kansa na kasa yana sharan kwallah cikin Raunin murya ya dago yana fadin"Naji dad'i da na iske zuru'ar yar'uwata.ku kalleni nan daga yau ku masu gata ne.Bazaku kara kukan maraici ba"
Yaya mariya ta dago tana sharan kwallah Lokaci d'aya tana fadin"Kawu.."
Da Sauri yace"Ba sunana kawu ba. ABBA zaku rik'a kirana kamar yadda y'yana ke kirana.nayi shekaru da nauyin kirji ina tunanin akwai wani abun da ban isa garesa ba acikin wadanan shekarun ba,na samu wadatar Rayuwa da cigaba nayi karatun addini nayi na boko har matakin Masters,na fara aiki da Hukumar wutar lantarki na jahar kano. kafinMakotan su Baffa sanadiyar gidan kakanin megidana shi chairman ne na babban Headquater refinering and petrochemical,Limited Edo state,Sanadinsa na samu aiki a Nageria National petroleum corporation NNPC,na kaduna wato Kaduna Refinaring and petrochemical company,Nayi auri da Diyar Baffa Azizat,mun haifi yara Hudu babban su shine Abdul'Ahad ma'aikaci ne hukumar sadarwa ta layin Mtn,zai yi aure wattani kad'an masu zuwa sai Nana Fadila tana Lagos tana aure sai Nana Fatima tana Dutse tana aure,Sai Nana khadija dake gabanmu yanzu tana aji daya ajami'ar kaduna ina zaune a anguwan NDC kaduna ina da gida da motar hawa sannan Ina da Rufin asirin da na Dauko mahaifiyata Gata nan Inno muna zaune tare da ita da. Bikin ma da ba ta tafi tare da su Maman Nanah ba,Tana faman da matsalan ido,jiya ne ranar zuwanta ganin likita yasa nace ta tsaya in na kaita ajiyan yau sai na wuce kano da ita sai kuma muka wayi gari cikin wannan al'amarin nan take na kira Direba nace mu Dauki Hanyar katsina bazan iya sukuni ba sai nazo naga Ahalina"
Ya karishe fad'a yana kallon mu gabadaya su Goggo suka amsa da Masha Allah.
Cikin yanayinsa yace"Ya'yana ku fadamin a inda kuke aure da adadin yaran ku..?ina mazajen ku..?ko dai yake nima ban zo da iyalaina ba. ammh da zarar na dawo daga Tafiyar da zan yi zamu zo gabad'ayan su ku gansu suma su gan ku"
Cikin yake Yaya mariya ta fara fad'in sunanta da adadin ya'yanta sannan ta fad'i yaya Asiya sai ni muryata a shake nace"Fa'iza ya'yana hud'u Kabir Amir,Saudatu Anum,Musty da Ahmad Ina aure a katsina"
Hafsah kuma karamar mu ce tana wajena shekaran nan ta fara karatu a jami'ar katsina"
Cikin gamsuwa ya gyad'a kai yana kallonta kafin yace"Aa Transfer zan yi mata zata koma kasu su yi karatu tare daa yar'uwanta Nana khadija,bazan bari ku yi nesa dani ba bangaran karatu fa baku gayamin inda kuka tsaya a karatun ku ba..?
Sai na kasa mgana Yaya mariya tace tayi Nce cikin gamsuwa yace"Meyasa baki cigaba ba Mariya..?
Sai ta sunkuyar da kanta sai yayi mirmishi kafin yace"Zaki cigaba insha Allahu ilimi shine mace zan dauki Nauyin karatun ki da komai,su Nana Fatima kowacce sai da ta gama Degree tayi aure Nana Fadila Nurse ce tana aiki da aibitin Gwamnati na garin Lagos"
Ni dai na riga na zama mutum mutum ina jin sunayen wasu ahalin namu da bamu taba sani ba,ni ya kallah kafin yace"Ke fa Fa"iza..?a ina kika tsaya a karatun ki..?.
Sai na kasa bashi amsa kaina na maida kasa kafin nace"Ban yi karatu ba ni"
Cikin mamaki yace"Bangane ba..?
Da Sauri Goggo tace"Fa'iza batayi karatun boko ba sai dai na addini,kasan Lokacin rasuwar mahaifin su mun raba su ne a Tsakanimu ta zauna hannun Kabiru ne kafin rasuwarsa D'ansa ma take aure yanzu Haka mai suna Ishaq"
Kai Tsaye yace"Aa wannan ba Hujja ba ne. Da za'a barta batayi karatu ba,Ai ilimi ginshiki ne ga y'a mace Dole Fa'iza zata koma makaranta domin ta sake inganta rayuwarta"
Cikin rauni nace"ko primary fa ban yi ba,sannan ina da raunin ji"
Cikin yar dariya ya Dafa kaina Lokaci d'aya yana fadin"Kada ki damu girma baya hana neman ilimi lesson Teacher za'a sama miki ya koyar dake kafin ki fara shiga makaranta,Mganar raunin ji kada ki damu makafi ma sun yi karatu kuma sun zama wani abu indai ni ina Raye y'ayan yar'uwata bazasu taggayara ba,na ji takaici da ban sameta a raye taji gajiyan dukiyata ba,ammh bakomai tunda ga ku, kamar wani nauyi ne a wuyana kamar yadda Nauyin su Nana khadija ya rataya a wuyana"
kai tsaye yake mganarsa Kuma babu tsoro ko shakka,Nan ya rika mana Tambayoyi kan Rayuwarmu muna bashi amsa ya tambayemu muna sana'a ko kasuwanci ne muka gayamasa ni na fad'amasa ina zobo da kunin aya ina Turarekan kamshi.
Mirmishi yayi cikin jin dadi yace"Good ina son naga mace da ta iya sana'o'iin hannu.Dakyau Fa'iza zamu inganta wannan kasuwan cin naki'
Ban san Lokacin da nayi mirmishi ba,Sai Hira ta tsinke a tsakaninmu shi kuma sai kiransa ake yi a waya ya koma gefe ya sauya harshe zuwa Turanci yana ta mgana mu ko Inno tajamu jikinta tana fadin"Ya'yan nan ban ji kun ce kun yafe min ba..?
Dukkanmu muka ce mun yafe mata tana dariyan jin dadi tace"Nagode. Daga yau kun tashi daga marasa kaka kun koma yan gatan Inno.Daga yau ni kakarku ce Baban Nanah Kuma Uba yake gareku Aziza kuma uwa take gareku su Nana fadila kuma yan'uwan ku ne"
Wani farinciki ya Lullub'eni daman zan ga wannan ranar..?
Ashe mu ma muna da gata bamu sani ba..?Nan Yaya mariya ta kira Yaya Asiya ta fad'amata haka ta dinga Tsallen Murna aka bata Inno suka gaisa Lokacin Abban ya gama wayar aka bashi suka yi mgana mutum ne mai barkwanci da son yan'uwa Yaya Asiya ta kirasa da kawu yace"Sunana Abba.Ya'yana haka suke kira kuma ya'yana ne haka zaku rika kirana.
An ce kina kano ai yan'uwanki da maman ku duk suna kano sun je sha'ani nima daganan ni da Inno kanon zamu je zan sauketa ni kuma zan hau jirgi zuwa Porthercourt,muna da Taro ammh da zarar na dawo zan kawo su dukkansu su gan ku,kuma kuga sauran yan'uwan ku"
Cikin murna Yaya Asiya tace"Na kosa Abba don Allah ku zo da wuri"
Cikin Dariya yace"Kada ki damu ba domin kuna gidan mazajen ku ba, da duka Gidana zan maida ku.ko o a yanzu kowacce da mijinta zata zo da ya'yanta ina son ganin iyalan ku gabad'aya"
D haka suka yi sallama da Yaya Asiya duka duka ko awa uku bamu yi ba tare ba, ammh mun saba da juna ji muke yi kamar in ya tafi bazai dawo ba,kamar bazamu kara ganinsa ba,Sai dai ana ta kiransa jirgin karfe hudu da rabi zai hau a kano shiyasa suka yi shirin Tafiya idanuwan mu ya ciko da kwallah ya rike Hannayen mu yana fadin"Kada ku damu da zarar na Dawo daga tafiyar da nayi zamu zo sai kun gaji da ganinmu kuma zan tafi daku gidana kuje ku yi min sati d'aya na san komai akan ya'yana suma susan komai a kaina"
Bai zo da komai ba Saboda tafiyar Gaggawa ce kud'i ya zube mana da bamu san nawa bane Direba ya kawo su da wata bakar Jeep dankareriya,Su Baba ati ma ya cika su da kudi da Sallaman yana dawowa daga tafiya da shi da iyalansa zai dawo,Inno ma tana ta sallama da alkwarin wannan karon zumunci an fara kenan har Abada,kafin ya tafi ya karb'i lambobin mu har da na Yaya Isa,mune rakiya har bakin mota da zai shiga mota ya dafa kan Hafsah yana fadin"Auta sai na dawo ko.?domin kece auta Nana Khadija zata girme miki,Zamu dawo in sha Allahu bayan Abba har Babban Yaya ma kuna da shi"
Da haka muka yi sallama suna d'aga mana hannu muna daga musu hannu,Cikin gida muka koma ana ta maida zence Goggo ta kallemu tana fadin"Kunga abun Allah ko..?
Allah ya nufa ganawar sai a wannan lokacin ne"
Yaya mariya tace"Naji dadi Goggo naji Dadi yau naga wani ahali daga Ahalin Tamadina murna kamar zata kasheni"
Ta fad'a cikin farinciki Hafsah kuma ta Daka Tsalle tana fadin"Abba yace ni ce auta kuma muna da Big bros muna irin na ya'yan yan gayu"
Ni dai sai faman washe baki nake yi farinciki ya gama cikani Yaya Asiya ta kasa zama sai kira take muna bata labarin abunda ya faru,Murna kamar me tace itama cikin Satin nan tana Tafe su Baba Ati sun koma gida da Tarin alherin Abba garesa muma kudi ne sun fi dubu dari ya zube mana,Goggo ko kwandala bata Dauka ba sai muka raba a tsakanimu,nan mukayi azahar da la'asar saannan muka tafi ni