Showing 57001 words to 60000 words out of 82431 words
yaya mariya da su Nana Fatima sun zo tarban Amarya muka Rumgume juna muna murnan ganin juna, sanye nake da Less din da Hajiya ta dinkamin na yinin ta nayi kyau duk da ban yi kwalliya ba,Da anan za'ayi walima sai aka sauya akace Ndc za'a koma gidan Abba achan za'ayi,gabadaya muka tattara muka koma chan,Hafsah sai wajen walima na ganta ita da Nana khadija sun ji kaya iri daya kamar yan biyu su Anum kuma an saje cikin su Falaq sai dai naji ana fadin Umma haka su Ahmd sun ci gayu suma suna ta wasan su cikin yara sa'aninsu.
Su Yaya ishaq da mazajen su Yaya Asiya Abba ya hanasu tafiya suna nan tare da shi,Sai bayan isha'i aka tashi Daga walima,aka kuma fara shirin Tafiya Dinner ni dai ina ganin in da ake bikin yan gayu,sai ga shi duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.
Sai ga shi su Anty Binta da Mama ne a rab'e mu kuma mune amara kirjin biki.
*Janafty*
*KNKB2015*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Kuma daidai gwargwado ba'a wulakantasu ba,an kula da su sosai duk abunda suke so shi suke yi,ba mai hanasu.
Balle kuma ga Badariya da sune manyan kawaye,Raliya ta mata komai na kayan fitan biki,kawancen su ba irin na sauran kawaye ba ne hatta duka ankunan biki duk Hajiya ta siya ma Badariya,Sai dai kunya ce da nauyi yasa suka koma gefe suna kallon abunda ke gudana.
Sanda muka zo naga Abba muka gaisa shima wajen Ammi yazo suna mgana,Baya gidan suna Hotel inda bakin sa suka sauka har da su Yaya Ishaq suna chan suma,Abba sai da yayi min tsiyan ido na kenan..?
Ina dariya nace"Abba kanwata na tsaya nayi ma rakiya"
Ammi tace"kuma matar yayanki ba"
Mukayi dariya gabadaya Ammi bata manta ba sai da tamin mganar Turaranta nace nazo mata da shi sannan tace na fita ko ba soso da Sabulu, abunda na lura da shi Ammi macece wayayyiya mai son kamshi da gayu,domin yar gayu ce ta Bugawa a jarida in ba an fad'a maka ba,baka isa kace itace mahaifiyar Yaya Abdul'Ahad ba,Tana ta shiga tana fita ko a jikinta damu da yaranta duka D'aya ta Daukemu.
Da ita da kawayenta da yan'uwanta suma suna ta shirin zuwa Dinner din Shashen Ammi aka sauke Amarya da Tawaganta,mu kuma shashen Abba gida ne ba ni da gida ba wajen Haduwa da kayan more rayuwa,babban gida mai shashina ba adadi harta Yaya Abdul'Ahad yana da shashensa a gidan.
Da zai iya zama da matarsa basu takura juna da su Ammi ba,nan su Nana khadija suka zauna da Kawayensu,dasu Hafsah da aka zama yan matan kd,su Goggo kuma suna Shashen Inno ita da su Baba Ati suna nasu sha'anin.
Muna shashen Abba sai shirin Tafiya ake yi Kaya iri d'aya Suka dink'amana Dukkanmu har da Nana khadija da Hafsah,wani uban su material mai ja da baki,yayi kyau matuka dukkammu dinkin Dogayen riguna suka yi mana,Irin na zamani Fitted,sai head ja,da zamu nada da takalmi ja da Karamar pos har da mai yi mana kwalliya na musamman. yaran kuma daga mata har mazan su shadda Fara aka dinka musu sai akayi amfani da zare ja wajen aiki da kwalliya,Ina kallonsu suna ta shiryawa tuni har an fara yi ma su Nana khadija kwalliya,Da farko kayan naga kamar baza su yi min ba, sai da Nana Fatima ta saka nata ta matsamin nima na sake yin wanka na shirya sai ga shi kayan yayi min cif a jikina kamar an gwadani,na juya na kara juyawa na kalli Nana Fatima ina fadin"Wannan ba irin namu ba ne Nana, sun matseni fa dinkin yanmata ne"
Harara na tayi tana fadin"Ni juya na zage miki zif din riga. Ba wanda yace ga dinkin yanmata da matan aure kaji matar nan"Ina dariya na juya ta zage min,na ja head din ina shirin Daurawa ta Fizge tana fadin"Meye haka.?kai tsaye nace"Daurawa zan yi mana"Da karfi tace"Daurawan ta. Mai kwalliya zata daura miki bayan ta gama miki kwalliya"
Sai na Bude ido Lokaci d'aya ina fadin"Ni za'ayi ma wannan fenten fenten haba Nana mana wannan sai su Hafsah"
Dariya tayi Lokaci d'aya tana fadin"Har su fa'i yau sai sun yi kwalliya"na zata wasa take sai gashi tamin Taron dangi Nana Fadila tace"Muma nan kwalliyar zamu yi fa'i banga abun damuwa ba'
Na marairaice ina fadin"Anty Fadila ban fa taba yi ba, na dauka kwalliya na masu kyau ne da yan gayu"
Sai suka kalleni suna Dariya Nana Fatuma tace"Kaji wani Tunani kuma. kwalliya da gayu na macen data san kanta ne Fa'i,kuma yau ko zaki suma ne sai kin yi kwalliya"
Taruwa suka yi suna ta gayamin amfanin kwalliya ni jinsu kawai nake yi, ko kunshi da gyaran kai da nayi Hajiya ta matsamin da na rakata gyaran kai tace sai an yi min, sannan da mai kunshi tazo tace na zauna ayi min gaskiyan mganan hausawa da suke cewa duk wanda ya gyara zai ga dakyau ni kaina nasan nayi kyau a baya ina Tunanin bakin Fatata bazai saka lalli ya zauna ba sai gashi ya fito ras da shi,Tabbas na yarda ko kana da kyau ka kara da wanka ni kaina da yanzu na samu sauyin rayuwa Fata ta fara gogewa.
Ban gama mamaki ba sai da naga har su Yaya Asiya sun sha kwalliya an buga musu Dauri ita da Yaya mariya na kallesu na kwashe da Dariya ina Fadin"Yaya Asiya wai kema ahaka zaki Dinner din.?
Fari tamin ido tana fadin"Kwarai ma kuwa Fa'i bari ma na kira baban Usaini yace min Abba yace suma sai sunje fa"
Ta wuce tana wani juya jiki gabadayammu muka saka Dariya mamakin yadda ta sauya kawai nake yi Yaya mariya ko sai faman duba madubi take yi na kalleta nace"Yaya mariya mata a gidan Manaja"
Ta juyo tana fadin"fad'i ki kara kuma dagani ba kari"
Kawai sai Nana Fatima ta saki guda suka tafa da Yaya mariya chaa sukamin Dole bayan an gama ma Nana Fadila na zauna nima akayi min kwalliyar zamanin da a baya na Dauka sai a Fuskar mata masu kyau ake yinta,kuma yayi kyau ba irin mu munana kuma bakake ba.
Fuskata naji duk ta Daure,har abun ido aka karamin ina bana so ba na so Nana Fatima tace sai an sakamin,Ina tura baki tayi dariya tana fadin"Sai fa kin zama yar gayu kema Fa'i ga mijin ki na ganshi dan gayu da shi ammh ke baki son gayu"
Yaya Mariya ta tabe baki tana fadin"in dai Fa'iza ne abun haushi yanzu kika fara gani, gabadaya ta maida kanta baya shiyasa har miji ya raina ta ya yi mata kishiya'
Sai Nana Fatima ta Tsaya tana kallona cikin mamaki tace"Fa'i daman kina da abokiyar zama ne shine ban sani ba..?
Sai na kauda zencen da cewa"Kun san fa kari ba kyau a addini"
Yaya mariya tace"Allahu akbar Sayyada"
Da na Dake bana so ne sai Nana Fadila tace kada a sakamin a barmin ido na haka,Sai da aka gama na duba madubi sai naga kamar ba ni ba gabadaya Fasalina ya Sauya na sake kallon kaina na koma na kalle su kafin nace"Wai fuskata ce haka..?
Sai suka kwashemin da Dariya,Nima kaina sai da nayi dariya,ko wajen saka Takalmi an sha Fama dani yayi min Tsini Nana Fadila tace"Ke da ma baki da tsawo fa'i ai na irin ku ne"
Kamar zan yi kuka nace"Ban saba sawa ba. Kuma ban iya tafiya da su ba"Nana Fatima tace"Zaki koya yanzu malama"Haka ta sakamin shi mai igiya,ina tafiya ina neman fad'i Suna min Dariya.
Ammi ta shigo tana fad'an ga motoci chan a waje ana ta Daukan mutane goma ta kusa dare yayi sai taga ina tafiya ina Tangad'i salati ta saka Tana fadin"Me zan gani haka Fa'i..?
Ina matse ido nace"Ammi bazan iya tafiya da shi ba don Allah kicesu kyaleni"Ammi tace"To bari kada ki yi kuka ki bata kwalliyan ki.."
Tafiya kuma da takalmi ya zame miki Dole ana mganar gayu fa'i ko ni kalleni Da wanda ma ya fishi"
Tafada tana d'agamin kafarta mamaki ya kamani nata baki ne mai igiya kalan leshin jikinta a bunka ga farar Mace Less din data saka baki ne sai ya haskakata na zata Ammi zata Sassautamin ne,itama fad'a ta kama min tana fadin"Saki jikin ki ki yi tafiya ba zaki fadi ba. In baki koya ba sai yaushe Fa'i? yanzu in Tafiya ta kamamu na shiga Villah haka zaki je kina yi mana?
Suka ko kwashe da Dariya Nana Fatima tace"Sai mu tafi mu barta"Ammi tace"Aa fa da ita zamu rika shiga ko'ina bame barinta a baya"
Dole zata koya yadda baki da Tsawon nan ai irin takalman ki kenan yarinya"Ina ji ina gani suka hanani cirewa Yaya mariya tace"'Fa'iza fa sai a hankali komai na gayu bata iya ba"
Ammi tace"
Zamu ko b'ata da ita.Ko ni da nake sauke ku ina gayu na ina Dalili. Shiyasa ban jita tana tashin kamshi ba,kamata yayi yadda kike sana'ar kayan kamshi da jikin ki da Dakin ki sai sun kama kamshin ki, ammh ba ko d'aya"Sai kunya ta kamani na Sadda kaina kasa ammh ita ko ajikinta ta cigaba da min fad'a tana fadin"Mace sai da gyara Fa'iza muma fa duk burga ce,Adon ne ke cetan mu"Tafad'a tana fari gabadaya muka saka Dariya Nana Fatima tace"Ammi to har kishiya fa'i fa gareta..?
Ammi ta saka salati kafin ta mangare ni tana fadin"Ba fad'an yanzu ba ne zama zamu yi,mu yi mata na musamman wuce muje"
Saboda kada Ammi tayi mgana yasa ban ce komai ba, da naga zamu fita dagamu sai wani karamin mayafi,ance Tuni Yaya Asiya da Nana Fadila sun tasa yara sun yi gaba,Mun fito Falo sai ga ango yasha kamshi sai Nana fatima ta fara kirari yayi Tsaki yana fadin"Ku daman baku tafi ba..?
Tana dariya tace"Tawagan ango zamu bi"Kai tsaye yace"To ku cigaba da jira. Ammi wai ina Abba sai kiran wayarsa nake tana kashe"
Ammi tace"ban san to ina ya tsaya ba. Dazu dai ya kirani yace ga Engr ya sauka daga a kaduna daga Lagos yazo masa murna, bai samu zuwa Daurin aure ba"
Abdul'Ahad yace"Engr din yazo ne Ammi?
Tace"Baka ji me nace ba ne, yazo ammh inaga ya wuce domin Baban Nana yace min Karfe goman daran nan jirgin su zai tashi daga abuja zuwa London zai raka kakarsa ganin Likita"
Kasan tana fama da matsalan koda"Abdul'Ahad sai ya fice yana fadin"Ammi in kin same sa kice ya tabani"
Mu dai waje muka fita motoci sai kad'an tunda duk sun wuce sai Amaryan da tawaganta su kuma angwaye zasu bi,Allah sai ya jeho mana Mijin Anty Laila uncle Junaid yaje ya kaisu Laila ya dawo Nana Fatima ta Dafe mana shi ya kaimu ni da ita da Yaya mariya Ammi agida muka barta tace za'a kawota.
Wani Hadadd'en wajen Event ne mai girma da fad'i goma ta wuce ammh kamar rana chan muka iske su Anty Binta da Mama sun je suma,su Goggo dai na gida sun ce a raba su da zuwa wani shegantaka da Daddare.
Amir na ganina ya taso yazo kusa dani ya kama Hannuna yana fadin"Umma kin yi kyau"
Nayi dariya ina shafa kamshi nace"Kai ma haka Amir dina."
Su Anum suna tare dasu Hafsah da Nana Khadija kowa ya kama bangaran da zai zauna muna sai muka kama Tebur d'aya dukkanmu mu Bakwai har da su Hafsah su Laila suna nasu bangaran,Gabadaya ji nake yi a takure saboda shigar jikina ga uban Takalmi Kallon da su Mama suke min ne yayi min yawa na tashi naje na gaishe su Allah ya taimakeni ban Turgud'e ba.
Anty Binta haka take kallo na kamar na Sauya mata har sai da tayi mgana da cewa"Lalle Fa'iza kece haka..?
To kada dai ki manta kina da aure ba Budurwa bace ke'"
Ban ce mata komai ba, sai ga Nana Fatima tazo tajani muka yi gaba tun ina Dari Dari har dai na saki jikina ina ganin zuwan su Yaya Ishaq shi da Jamal sai mijin Anty mariya,da wasu da ban sani ba,kuma a Tebur din bayan mu suka zauna ina da Tabbacin basu gane ni ba.
Ammi tazo ita da tawaganta daga ita sai Tawagan amare da angwaye.
Matuka wajen ya hadu bazaka ma gane Dare ba ne,an ci an sha an sha rawa sannan an yi nishadi,Badariya ta bada Tarihin Amarya wani daga cikin abokan ango shima ya ba da Tarihin ango.
An kira kannen ango mun fita mun yi liki Daman Ammi ta bamu yan Dubu sabbi muka zubda da su,ana bikin Duniya in da ake yi jama'a haka muke taka kudi,Sannan an bamu fili mun rausaya Nana Fatima in na yi kokarin Sulalewa ta rikoni,ni na samu na yafa mayafin su basu yafa ba a Hannu suka Rike.
Mun koma wajen zaman mu sai igiyan takalmina ya warware na duka in gyara ina Dagowa muka hada ido da Yaya ishaq sai naga ya kauda kai kamar bai gane ni ba,sai na mike na isa gabansa cikin wani irin takun da bansan na iya ba kuma abun mamaki Tsab na saba da tafiya da takalmin kafata ina zuwa gabansa nace"Hy.."
Ina mai kura masa ido na make murya yasa bai yi Saurin Dagoni ba. Jamal baya wajen ya koma chan Teburin gabammu.kauda kai yayi yana wani basarwa zan kara mgana sai ga Amir yazo yana fadin"Umma.."
Yaron nan shi ya Tona min asiri a Firgice ya Dago yana kallona yana kuma kallon Amir kafin yace"Bangane ba..Wata Umman..?
Amir yace"Daada Umma ce fa baka ganeta ba ne..?
Yadda ya saki baki da Hanci yana kallona ne yasa na bushe da Dariya ina Talle ma Amir keya Lokaci daya ina Fadin"ji yaro ya batamin shiri na"
Amir shi kanshi Dariyan yake yi ganin yadda Babansa yayi daga sama har kasa yake kallona,daman shi bai so zuwa ba Abba yace sai sun zo tunda suka zo yake ganin yan mata kenan har su Yaya Asiya bai gane ba, tunda ya Dauka yaran yara mata ne kawai a wajen.
Kirjinsa sai duka yake yi yana kallona Amir da ya ga haka sai ya Sulale ya barmu kujeran gefensa naja na zauna ina fadin"Samari."
Sai kawai ya miko hannu ya kama Hannayena duka Biyun yana Fadin"Fa'iza wai don Allah da gaske ke ce..?
Sai na kara saka Dariya kawai ban tsammani ba sai naji saukan sumba a saman bakina cikin wani yanayi yace"Kin yi kyau Fa'iza ashe ke mai kyau ce ban taba sani ba.."?
Ina shirin bashi amsa naji Tafi a bayana ina juyawa Naga Nana Fatima da Sauri na kwace hannuna ina Hararanta karisowa tayi gabanmu tana Dariya Lokaci d'aya tana fadin"Allah ya kamaki wato kina nan kin zo gwada ma miji kwalliya ammh nan ina fama dake kin ki Tsayawa ayi miki,Ranka ya dade a biya ladan kwalliya domin sai dakyar ta amince akayi mata"
Ba musu ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi ya damka mata,suma Abba ne ya basu yace na liki ne,Tako amshe Abunta tana fadin"To yanzu sai ka mora kallon ka..Fa'i."
Ina juyowa ta kashe min ido tayi gaba na bita da dariya,kai tsaye nace"Ina ka samu kudin tukwaici..?
Cikin wata murya yace"Abba ya bamu wai na liki ni ai ga babban liki na nan"yafad'a har yana wani lashe baki yar Dariya nayi cikin yangar da wlh bansan na iya ba,kai wani lokacin bakin mutane na taimakawa wajen Dakushe tasirin da muke da shi a Rayuwa, yanzu da na samu masu yabani da Daidaitani da Sauran mata har na fara tunanin to dame suka fini..?
Kiri kiri Yaya Ishaq yaki barina na matsa ko'ina har yana fadan na saka karamin mayafi,rai bace ya kalleni yana fadin"Wato kyale kin da nake yi yasa kika maidani sauna ammh bari mu koma gida zaki shiga hannu"
Ina jin haka na shiga Taitayina,Sai da za'ayi Hotuna Anty Fadila Dakyar tazo ta jani shima sai da tasha korafinsa sai bina yake da kallo barin ma takalmin kafana a ransa bai san sanda ya furta"Jar uba.."
Fa'iza fa ta tashi kan sa ,ya so yayi wauta da farko ballatana da kayan suka kamani,gabadaya Shafe dina ya bayyana kamar ban haifi yaran nan ba Tuni kishi ya kamashi muna Hotunan kamar ya fizgoni ya rumgume haka yake ji bamu muka bar wajen ba sai Dayan Dare Shima ba'a tashi ba nan muka bar Amarya da sauran mutane Yaya Ishaq bai sauke ajiyar rai ba sai da muka tafi ba shi kadai ba duk wanda ya ganni sai yace Fa'iza kin yi kyau barin ma Badariya juyi goma sai tace"Kai matar yayana tafi kowa a wannan bikin"
Bamu san yaushe suka dawo ba sai da Safe su Hafsah sukace sai uku na Dare araina nace lalle kaduna bariki.
A ranar muka raka Raliya dakinta Dangin Hajiya da kawayenta suka wuce bayan sun damka amanarta ga Ammi da su Inno,Mama da Anty Binta a ranar suka tafi bayan Ammi ta hada musu sha tara na arziki tare da Jamal suka Tafi Abba dai ya Tsaida Ishaq yace yana so zai yi mgana da shi. Domin yadda ya samu labarin a bakin Goggo Mijina baya aiki yanzu nice duka hidomomin gida shine yake so ya gansa su Tattauna.
Kuma in dai ba wannan Lokacin ba bai kuma da Sauran hutu in aka gama Bikin.
Hajiyar Dala bata zo ba rasuwa akayi mata, Yayan megidanta ya rasu dole ta Tsaya ammh taso ta zo ta bama idanuwanta abinci,sai dai tagani a waya tunda Badariya nata zuba Hotuna yaran ta na Nuna mata,Hajiyar Dala tayi mutuwar zaune da taga Hotona da Badariya ta saka a kasan Hoton ta saka"Matar yaya na tafi ta kowa. Anty Fa'iza"
An ce har Jamal ya Dauka shima ya saka a Status d'insa, gogan bai da waya bai san wainar da suke toyawa ba,Hajiyar Dala aranta sai da tace kamar an yi min wankin in ji nice na koma wata classis haka a baya tasan ni yarkace yarkace kamar yar Gudun hijira,ammh yanzu kuma taga na zama wata mai aji da Daraja.
Inaga ta wayar Jamal Zainab tagani ta tambaye shi yace ina kaduna muna Biki sai ta kirani tamin Allah ya sanya alheri kai tsaye kuma tace min"Ashe kuna da yan"uwa a kaduna.?ni ko sai nace mata eh na kara da fadin"Kanin Mahaifiyarmu ne mai rasuwa"Sai ta jinjina kai tace"Allah sarki"
ba mu jima muna wayar ba,bayan tambayan yara da gida muka yi sallama.
Zuwa talata kaf gida ya watse hatta Goggo ta koma karofi sai mu