Showing 36001 words to 39000 words out of 82431 words
waliman ko sati ba'ayi ba Hajiya ta aiko min da Kayan saka ranan Raliya,nayi murna sosai Badariya itama tazo tana fadamin har da na Halisa itama an saka,yar wajen Anty Binta zatayi aure a kano dan'uwan mijin Hajiyar Dala ne,ita kuma Raliya chan wajen bikin Laila suka hadu da shi,Yaron yayar wanda Laila ta aura ne.
Bansan me ya faru ba sai gani kawai nayi Badariya ta had'o kayanta tazo ta Bude dakin Mama ta share ta dawo,kamar bazan mata mgana ba sai naga tana cikin damuwa ranar bayan fitan yara makaranta na bita har Dakin sai na isketa tana kuka.
Na tsorata na zauna gefenta ina tambayanta me akayi mata take kuka..?
Sai ta mike zaune tana cemim"Don Allah Anty Fa'iza aure na waye..?
Kai tsaye nace"Aure na Allah ne Badar me ya faru ne..?
Sai ta sakamin kuka tana fadin"ba na fada miki an saka ranar auran Halisa ba?
Na daga mata kai sai ta cigaba da fadin"Shine shine fa tunda ta samu ssurayin nan take min gani gani har Anty Binta tana gani Halisa na min wulakanci don ina zaune a gidan su,Gori kala kala take min wai bani da Tsayayyen saurayi sai shirme shine fa a Shekaranjiya Salisun da zata aura yazo daman ya sanni don yace ta kirani mu gaisa muna gaisawa muna hira sai zuwa tayi ta cemin wai don Allah na fita tana so ta gana da saurayinta nayi kane kane kamar ina so nayi mata sinacin"
Ta karishe fada cikin kuka cikin wani yanayi nace"Miye sinacin?
Kai tsaye tace"Wai zan kwace mata shi Haba Anty Fa'iza ko Hali na ne ai bazan yi ma Halisa ba,mamanta uwa daya uba d'aya muke da ita ballatana ba Halina ba ne"
Sai na rike hannunta ina fadin"To miye na kuka tunda kinsan ba haka ba ne..?
Sai ta kalleni tana fadin"Na shiga damuwa ne anty Fa'iza na kai minzali nima kawayena duk da muke tare sun yi aure,ga Raliya itama an saka mata rana,ni kuma gaskiya Halisa ta fada bani da wani Tsayayyan Saurayi, sai ka samu kana murna sai ka nemi mutun ka rasa ga halin da yaya yake ciki akallah dai nima na kauce sai wata Lalurar ta Dauke muku Anty Fa'iza"
Sai kawai ta kara saka kuka ni ko na Dage ina ta lallashinta sai da tayi shuru sannan na kalleta ina fadin"Saurareni Badar.shi aure da kike gani na Allah ne,Sannan mutum bai isa yayi ma kansa aure ba. shi kamar zanen kaddara ne irin na mutuwa da haihuwa ne lokacin da Allah yace kun ya fakum ba wanda ya isa ya hana Faruwarsa,kada kice zaki saka damuwa don wance tayi aure wance batayi ba ki dai ki bar ma Allah zabi ki kama kanki ki Tsarkake mu'amalan ki da Allah da Mutane kina Zaune Allah zai kawo miki miji nagari kiyi auranki. kada Surutun mutane ya Dameki ita kuma Halisa ki kyaleta in dai namiji ne ai d'an Babansa ne kina zaman zaman ki sai nuna mata kalan da zata gane tayi kuskure ki kwantar da Hankali Allah na sane da bayinsa masu takawa da Hakuri"
Sai da na Tabbatar da mganata ta shigeta kuma ta aminta da mganganu sannan na fito daga Dakin ni kad'ai a Tsakar gida ina aiki Tausayin Badariya ya cikani kowaani bawa da nashi kabulen Rayuwar in kana gida baka yi aure ba, ace kaki aure shi kuma mijin ba Tukunya ba ne balle ka tantance na gari,sai ga shiga gidan wani auran kaji gwara zaman ka agidan ku ma,ammh duk lalacewar aure yana da Daraja saboda Ibada ce ta Ubangiji.
Nayi alkawarin a duka Khamsin Salawatul di'na zan saka Badariya aciki,domin Allah ya sama mata mafita alokacin ma sai da na daga Hannayena sama nace"Ya Allah ga Baiwar ka nan Badariya ka fi ni sanin Damuwarta a cikin zuciyarta Allah ka kawo mata mafita daga cikin kyawawan mafitan da kake bawa bayin ka Salihai,Allah ka turo mata miji nagari wanda zai share mata hawayenta"
Sannan na shafa a raina ina jin Wani iri,rayuwa kenan kowa da irin tasa kaddaran.
*Janafty*
*KNKB2010*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000*
*09069067488*
Har ga Allah na taya Badariya damuwar halin data ke ciki,Saboda ina aiki in abun ya fad'o min a rai sai na tsaya nayi mata addu'a acikin raina ballatana da naga tafi kwana biyu kafin ta warware sai nayi amfani da wannan damar na kara jawota a jiki ina kara nuna mata in dai tayi yakini da Allah ke yi to ta saki ranta mun rokesa kuma shi Allahu Rahimun ne,yana share ma bayinsa hawayensa da haka na samu ta saki jikinta. sai ya kasance in yara sun tafi makaranta Hafsah ta fita zata fito taimaka min da aikin gida,wani Lokacin har da na sana'ata muna yi muna hira hakan sai ya rika debe mata damuwa.
Ba'a fi sati da dawowarta ba ranar sai Yayan nata ya kirata,ina falon lokacin na shigo da bahon da na jera gorunan zobo zan shiga kitchen na jera a frezer ta ma shigo ta tayani ne ya kirata,Kasa kunne ba Halina ba ne ballatana da nake da raunin ji da nasan ko na kasa kunnen ba lalle bukata ta biya ba,sai ban damu da naji abunda yake tambayanta ba, na shige na cigaba da aikin gabana sai ita ne ta shigo bayan ya sallameta tana cemin"Anty Fa'iza kiji Anty Binta"
Sai na dago ina fadin"Me ya faru da Anty Bintan..?
Cikin yatsina Badariya tace"Wai yaya Ishaq ta kira tana fad'an wai daga mun yi hatsaniya da Halisa ko sani batayi ba na hado kayana na dawo gida"Mirmishi nayi kafin nace"To shi yayan me yace?baki ta tabe bakin tace"Me kuwa.?fad'a ya yi min wai na rika hakuri da rayuwa"
Sai na cigaba da aikina ina fadin"Ya fada miki gaskiya. Ke uwa kike ga Halisa bamai sauya wannan sunan a wajenta har abada"
Daga haka bata kara mgana ba illah hmm!da tace min ta zo ta kama min muna jera gorunan tare ganin haka nima sai na saki mganar muka kama wata,Yadda shi ma bai min mganar ba haka nima nayi kamar ban sani ba ni nasan ina da miskilanci kuma abun nawa ya had'u ne sanadin mijin da nake aure da irin yadda ya tafiyar dani wajen zamantakewarmu,shiyasa na zama ba komai nake mgana a kai ba.ballanta na nuna na sanin din na koya ma kaina ga duk abunda ba'a ce Fa'iza zo kiji ba, ko zo ki gani ba. na fahimci bawa zai fi zama lafiya in ya bar abunda ba ruwansa hadisi ne guda kan haka.
Fargaba na d'aya shekara ta na neman kare mana acikin wannan gidan akwai Karin Dawainiya na kudin Haya,kudin makarantan yara,ga jamal da sai wannan shekaran zai gama ga abinci da Hidimdimun yau da kullum,har takai ga mun fara awon abinci saboda komai namu ya kare sai abunda ba'a rasa ba,da na rasa mafita sai na auno masara aka nika nayi Tsaki da gari yau tuwo gobe fate jibi dambu sannan na kira Goggo nace ta saka ayi min garin Danwake da Taliyan murji ,Hafsah zata zo satin karshe ta taho min da shi ban fito na gayamata muna cikin wani Hali sai dai hikimarsu ta manya yasa sai ta Fahimceni,sai tace ba sai na aiko Hafsah ba,Yaya Isa zai shigo katsina Ranar jumma'a zai taho min da shi
Da haka muka rabu saboda na lura komai in baka Tsara ba sai ka kwana aciki,a kwana a tashi na fara yi ma dan jarin nawa Rugu rugu ga masu siyan zobo da kunin aya sosai ammh kuma ba da yawa nake yin sa sosai yanzu ba,Nafi son ma a bani aikin Had'in Turaruka nafi samu sai dai shi zobo da kunin Aya sana'a ce ta cikin gida da zata tallafi Hidiman da bata gaza dubu goma zuwa kasa ba,duk yadda Yaya Ishaq nake ganin yana cikin Damuwa iya wanda na gani ne acikin Ransa bansan zafin da yake ji ba koda yaushe cikin fad'i yake yi"Kiyi hakuri Fa'iza na barki da wahala.Kiyi hakuri"
Ammh duk da haka ban barsa ya zauna bai je ya duba Zainab da yara ba,tun bayan tafiyarta yafi wata bai je ba ni na matsa mai sai kawai yace min"Kina ta matsamin naje naje..To ina naga ma na motan zuwa ko a kasa kike son na tafin..?
Sai na kallesa kafin nace" A bun bai kai haka ba,Ko ita ka fad'ama baka da na mota ai zata turo maka ka tafi din"
Wani kallo yayi min kafin yace"Sai na gayamata bata fiki sanin bani da shi ba ne..?
Ina jin ya harzuka sai na kama bakina ni kadai nayi kulla kulla na, na had'a cinikina na kwana Biyu, dubi biyar nabasa nace yayi na zuwa na dawowa bazai gagara ba,Ranar naga fad'a kamar zai dageni ya watsar da kudin yace na kwashe su bazai je ba, naki jin mganarsa na barsa masa su a tsakar daki na fice. ina jinsa yana fadin"Fa'iza ki dawo ki kwashe kudin ki nace,Haba matar nan so kike hakkin ki ya kamani.?gabad'aya kin Lullube rayuwata da alherin ki,so kike na mutu Allah ya sakani a wuta ko Fa'iza ai shikenan kin kyauta"
Ina jinsa sai da nayi dariya wai ina so ya mutu ne ya shiga wuta Allah na Tuba daga taimako ni bana so auran su ya samu matsala ne sannan na dandana rashin miji a kusa bana fatan itama ta dan'dana duk da rayuwata ba irin nata rayuwar ba ne, ita tana da gata gaba da baya ba irina bace da gatan kalilan ne.
Bansan ya akayi ba bayan kwana Biyu ya shirya yace zai tafin duk da bani da Tabbas nasan Mama ce zata matsa mai tana chan ne ammh na tabbata hankalinta na nan gani take yi yanzu tunda bata nan to sai a hankali,da ya tafi kwana goma yayi ya dawo. Sai dai yazo da kudad'e sun kai dubu hamsin yace Mahaifin zainab ya basa sannan ana ta dai kokarin neman aiki a ma'aikatu Dabam Dabam a bangaran da ya karanta wato na'ura mai kwakwalwa, ni ko a raina da fili sallata da zama na ina rokar masa Allah ya kawo masa aikin da zai amfanesa da kasa bakid'aya.
Da kudin da ya samo ya siya mana kayan abinci,duk da Goggo ta aiko mana har da shinkafa da Yaya Isa ya kawomin sakon nan kuma na bashi kudin yaki karba yace tace kada ya karbo na kirata ina ta godiya sai tace"Babu godiya tsakanin mu Fa'iza da ina da shi abunda yafi haka ma zan miki shi"na aminta da mganarta yanzu Goggo ba irin da ba ne mijinta Tuni yayi Ritire yana gida sai kudin Fashion yaran ne ke kula da komai harta kudin makaranta Hafsa sune ba abunda zamu ce da goggo sai godiya,Sauran kudin kuma ya ijiye amfaninsu zai iya zuwa kwanan nan sai yabi shawarana ya bar min kudin a hannuna na adana.
Tunda ya dawo na lura ya dawo da Dama daman da yake yi dani,Sai na fara shan jinin jikina,wani abun ma Saboda Badariya na gidan ne yasa yake ragamin,daya fara shigemin nake zaraf na shige dakin Mama ko na fito Tsakar gida na kirkiri aiki,haka kurum bana so mu kadaice saboda gudun kada ya ruguzamin shirina.
Da daddare kuma baya samun dama Saboda yara ina yi musu karatun Qur'ani saboda Anum ma ta shiga ajin Hadda Baban ma yana yi musu na boko duk dare in mun gama su yi shirin kwanciya,ko yana son mgana dani sai nayi saurin jan Anum mu shige Daki mu kwanta ba Halin kuma wani abu saboda idon yara,da kuma idon Hafsah tunda tare muke kwana da ita.
Yau muna zaune bayan mun gama cin abinci da ni da yaran duka muna kasa ne ina musu karatun Qur'ani Anum tana izifi goma ne Amir kuma ya wuce ashirin,su Ahmad kuma suna kasa kasa izifi biyu,shi yana kishigid'e saman kujera yana kallon mu har muka gama,Sai Amir ya mike yana fadin"Daada yau ba zaka koya mana karatun ba ne,?
Yana daga kwance murya a shake yace"Ban ji dadi Amir sai gobe..yau ka famshe ni ka koya ma kannen ka"
Sai Amir ya amsa mai yace su Anum su dauko littafan makarantan su,sai suka dauko ya fara duba musu,ina gefe har na fara gyangyad'i saboda gajiya Hafsah daman in yana falon bata cika zaman falon ba,sama sama naji Anum na kiran sunana"Umma..Umma!
Sai na yi Firgigit na farka ina hamma cikin,lokaci daya nayi mika ina fadin"Nagaji ne menene kuke kirana..?.Amir yace"Umma kema ki zo mu yi karatun tare"
Wata Hamma ta kara kwace min cikin kasala nace"Amir nagaji wlh ka bari gobe"Amir ya ware ido yana fadin"Umma yanzu kin daina karatu fa?kila ma kin manta na baya"
Nace"in ji wa..?ban manta ba kawai Hidima ce ta sha kaina ammh zan dawo makarantar nan ayi hakuri dai yau mallam Amir"
Su Anum suka yi dariya ina tayasu yana daga kwance yace"Amir kai ne malamin Umman taku..?
Kafin yayi mgana fadi ba'a tambayeka ba ta mike ta isa garesa ta fara basa labarin Anum akwai shigen Surutu kamar wata aku,tana bashi Labari yana kallona yana mirmishi Lokaci daya yace"Kice Umma ta fara jin Turanci"
Anum ta kyalkyace da dariya tana fadin"Sosai Daada"
Gani ya yi ina mika bayana duk ya sake kawai sai ya mike yana ce ma Anum"Je ki ku cigaba karatun ku"
Sai ta koma wajen zamanta shi kuma sai ya taso da ina shirin mikewa ne sai naji mganarsa a kasa kasa daidai kunnena yana fadin"Naga duk kin gaji muje dakina na tayaki da Tausa, duk zasu sake kiji dadin jikin ki"
Ai ina jin haka na koma na zauna ina Kifta mai ido sai ya kuramin ido sai na zame masa kurma nace"E he..me kace..?mirmishi yayi kafin yace"Kinji ai me nace zaki iya tashi ne ko sai na Dagaki..?ya fada Lokaci d'aya yana dagamin gira sai na juya ina kallon yaran bakina sake shima sai ya kallesu hankalinsu baya kanmu alamun in tashi yayi min sai naki tashi sai kawai naga ya mike yana gyarawa ai ban san lokacin da na mike a guje na shige daki ba,tsayawa kawai yayi yana kallona yaran suka Dakata da karatun suna kallon sa Anum tayi farat tace"Daada me ya faru da Umma take gudu..?
Yana shafa kansa ya juyo yana fadin"ta gaji ne kafafunta sun sake, sai tayi gudu saboda su sauka''
Tana daga ido Lokaci daya tace"Exercise kenan Daada"
Yana zama kan kujera yace" yauwa my Anum"
Amir dai bai ce komai ba ammh sai Hararan Anum yake yi ta cika Kaudi da fadi ba'a tambayeta ba sai da ya mata mgana sannan ta daina damun Dadan nasu da mgana wanda ya shiga Zurfin Tunanin in fa ya tsaya biye ma Fa'iza to bazai samu daman gyara kurakuransa na baya ba, har sai nagaba sun zo sun iskeshi a ransa ya shiryamata wani wayau da bata isa wannan karon ta tsallake ba.
Da safe bani da masaniyar abun da ya kulla yara sun tafi makaranta Hafsah ma kusan tare suka fita Badariya na Daki bata fito ba, ni kuma na gama kaye kayen daki kafin na fita Tsakar gida sai na koma Daki ina lissafin kudin da suka Rage a hannuna na bama Hafsa kudi kafin ta fita zata shiga kasuwa ta siyo min aya da zobo na wajena bai wuce yau ba zai kare, sai kayan maggin gida da man girki da nace ta Siyo min ko ba da yawa ba. siyan kullum duk baka gane masa kayi ta ganin kudi na narkewa ka rasa ina suke zuwa.
Na dukufa ina kirga kudin Hannuna har ga Allah ban ji motsinsa ba sai kawai naji mganarsa yana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin Aya ana ta lissafi ne..?
Sai a lokacin na dago na gansa ya Coge a kofar shigowa dakin yana kallona yana min mirmishi,Sai nima na maida masa martanin mirmishin nasa ina fadin"Ka manta baka cike mai Turaren wuta da kwallacha ba"
Sai kawai ya karisa shigowa Dakin yana Fadin"sana'a goma da ashirin wai Fa'iza yaushe kika zama yar kasuwa haka..?
Dariya nayi ban yi mgana ba na zata zai zauna ne sai naga ya coge yana miko min hannu Lokaci daya yana fadin"A bani in taya kirgawa mana."
Kai na girgiza ina fadin"ina kudin suke balle ka tayani kirgawa? riban wannan satin ne duka duka dubu hudu ne da yan chanji"
Sai ya gyada kai yana fadin"Ina laifi ai motsi yafi labewa Allah dai ya kara Rufamana asiri"
Na amsa da Ameen ina kallonsa sai ya yarfa Hannu yana fadin"Na gaji da zama ne waje da'ya shine zan dan fita na mike kafa"
Sai na jinjina masa kai ina fadin"Ya kamata to a dawo lafiya"
Har ya kama hanya zai fice ni kuma na mike sai kawai ya juyo yana fadin"Fa'iza na manta"
Sai na juyo ina kallonsa Lokaci daya ina sauraransa kai tsaye yace"Taimakawa zaki yi ki shiga ki gyaramin Shimfid'ata da daki na duk yayi kura kafin na dawo"
Yadda yayi mganar ba wasa ne yasa kaina Tsaye nace"Shikenan za'a gyara in sha Allahu"
Sai kawai ya fice yana fadin"Allah yayi miki albarka FA'I TA.."
A fili na amsa da Ameen har ga Allah a raina ban kawo wani abu ba Sai da na gyara Dakina da dakin yara,na falo daman na kimtsa shi,sai na shiga Dakin nasa na fara gyara masa,Tiolet na fara shiga na wanke na fito ina gyaran Daki na kakkabe Shimfid'a na gyara har ina sauya masa zanin gado naga nasa yayi datti sai na kudiri a raina zan hada da wankin yara na wanke masa da sauran kayansa da suka yi datti.
Ina cikin gyaran gado,ya shigo ban ji ko shigowarsa ba har ya samu nasaran rufe kofar damam abunka ga wanda ke da raunin ji,sannan gabad'aya hankalina yana ga abunda nake yi na duka ina saka zanin gadon jikin katifar na gama na mike kenan sai ji nayi an rumgumeni ta baya kam! Lokaci d'aya ana saki karfaffan ajiyar zuciya ni kuma har ga Allah na tsorata ban Zaci ganinsa ba gabana ya yanke ya fadi ras sai da kaina ya sara min jiri na neman kada ni, jinin jikina cak ya tsaya ya daina gudu ga shi ta baya ya rikeni sai na fara kokarin kwatan kaina ina fadin"Wa...ye..?
Cikin rawan murya hannayensa duka Biyu yasa ya zagaye cikina da karfin da na kasa motsi kawai sai na Dage iya karfina zan yi ihu zaraf ya juyo dani