Showing 15001 words to 18000 words out of 82431 words

Chapter 6 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

194

Dawowa na Dukufa na fara aikin Hada Turaruka,araina ina jin duka matsalolina zan kauda su in na samu wannan riban aikin,Aikin zobo sai ya koma sau daya a rana kunin Aya ma sai da yammah Lokaci na bada kacokan kan hada Turarukan nan ban rufe kwana hudu ba, na gama su duka,Kwallachan ne ma ta bani wahala ita sai da nayi kwanaki ban gama ba,inagamawa na kira Hajiya sai tace na ijiye komai a Hannuna in su Laila sun gama gyaran jiki in zasu tafi sai su tafi dashi.
Haka ko akayi satin bikin Amaryan Laila mai kyau da ita yar gayu ga ilimi ga nasaba ga kudi,ma'aikaciyar banki ne a kaduna suke Raliya ta dinga rakota kullumn da yammah muke farawa sai shida,A tsakar gida nake bazamana Tabarmana a rumfar nan Ishaq na Daki baya fitowa ga Hafsah wani Lokacin harda Badariya sai abun ya kara armashi,Laila ba ruwanta ga sakin fuska Anty Fa'iza kasa da sama take kirana kamar yadda Raliya ke Kirana,Sannan jininta ya shaku ita da Anun ta dinga rokona in bar ta su Tafi Bikin ta kaduna da ita Amana Hajiya zasu dawo da ita ban yi mgana ba sanin Halin Babansu da Mama ba lalle su bari ba.
Sati daya nayi ina mata sai ga shi ta fito shar da ita abunka ga farar fata,ga jiki lawai lawai sai tashin kamshi take yi,Da naga ta matsa da mganar Tafiya da Anum sai nayi ma Yaya Ishaq mgana da kaina nayi mamaki da ya barta ammh yace kada ta Dad'e a dawo masa da yarsa. ranar Litini Laila taji Dadi tana ta Godiya Direba yazo ya kwashe su ranar karshe da kayan su aranar kuma Hajiya ta Turomin sauran kudina, na daka tsalle ina murna nayi sujuda na gode ma Allah.
Batare da sanin Yaya Ishaq ba,naje na yi ma Amir komai har Uniform an basa na Biya musu kudin Tahfeez sannan na shiga kasuwa na siyo mai takalmin makaranta da jaka da littafai,yanzu nima sana'a ta Budemin ido nasan sirrin shiga kasuwa lungu da sako.


*INGANTACCEN ZANCE*.

*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*
*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.*
*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*08032773332.*
✍️.



*Janafty*
*KNKB2005*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Ranar monday da safe bayan yaran sun shirya Hafsah tayi musu abun karyawa,Musty sai tura baki yake yi shi bazai je makaranta ba yau.
Na kallesa ina kokarin saka masa safa yana Turje kafa cikin haushi na mangarar da kansa ina fadin"Zaka tsaya ko sai na dake ka..?
Sai ya fara kokarin sakin mun kuka na ko zare mai ido ina fadin"Na dake ka ne da zaka min kuka..?
Amir na gefe da ya shirya Tsaf yau zai fara zuwa makaranta yace"Umma cewa yayi bazai je ba, saboda Anum bata nan yau"
Na kallesa da mamaki sai abun nasa ma ya bani dariya na jawosa jikina na Rumgume ina fadin"Haba babban mutum na Umma.Anum din ai yau zata dawo yi hakuri ka saki ranka kaji"
Cikin muryan kuka yace"Da gaske yau zata dawo..?
Da sauri na amsa mai da Insha Allahu sai ya saki ihu Ahmad na tayasa Amir na gefe an saka hannuwa aljihun wandonsa kamar wani babba na kallesa ina Dariya Hafsah ta fito daga Daki tana fadin"A'a yan jss ba zama ne yau..?a tsaye zamu tsaya..?
Fuska yayi bai yi mgana ya Dauki Sabuwar Jakarsa ya rataya yana fadin"Umma yaran nan su zo mu tafi"
Na bisu da Allah ya kiyaye hanya bayan na rike ma Ahmad jaka zan rakasu kofar gida Hafsah ta daga murya tana fadin"Amir shine ba mgana..?zaka zo ka same ni ne.."
Muna gabda fita daga falon naji muryan Yaya Ishaq a sama yana fadin"Yaushe Amir ya fara zuwa makaranta ban sani ba..?
Su sun riga sun fice sai na mikama Hafsah jakar Ahmad tabi bayan su ni kuma sai na Dawo tsakiyar falon, yana daga kofar Dakinsa alamun yanzu ya fito sanda zamu fita daga falon zuwa waje.
Cikin sanyi na, na gaishesa ya amsa a gajarce yana sake fadin'Ko ba shi ba ne nagani da kayan makaranta ya fita da su Ahmad ba.?
Kai tsaye nace"Shine ni naje nayi biya komai ranar jumma'a yau suka ce ya fara zuwa tunda karatu yayi nisa"
Sai kawai ya tsaya yana kallo na Fa'iza ta sauya sauyin dake basa mamaki bai isa in zata yi abu ta nemi shawaransa ba, ance mai hali baya fasa halinsa kawai sai ya fara fada yana fadin"Meyasa kika raina ni ne Fa'iza kin ware ni kan sha'anin ya'ya na ban isa ki fadamin Amir zai fara zuwa makaranta ba sai dai ki rika yin komai kanki tsaye..?sai yanzu na yarda da mganar Mama, kina ganin yanzu kina samun kudi kina Dauke laluran kanki da na gida shine kike ganin zaki iya yanke hukunci kan ya'yana to baki isa ba,ba na so.."
Ya karishe fad'a har yana nuna min yatsa kawai sai na saki baki ina kallonsa na kwaso gauron numfashi zan tare sa da mganar ya wuceni Fuu kamar kabubuwa ya fice sai Dakin Mama na bisa da kallo hannuna sabe da Haba na a fili na furta"Yau naji karfin hali ko na gani zencen ni Fa'iza"
To in ba karfin hali ba sai yanzu kasan da ya'yan ka ne?a baya da kake banzar ta dasu ka zabi wasu akan su ba'ayi maka mgana ba sai yanzu ne kake da bakin mgana..?
Kawai sai nayi tsaki na cigaba da Harkan gabana abun karyawansa ma sai Hafsah ya ma mgana ta basa, ni Daki na shige na kwanta a raina nace bazan sake yarda ka rika sakani Damuwa ba.
Daman da kullatan fad'an safe ya shiga kuma Dakin Mama ta kara ma Wutar fetir, da yammah sai ga Direban Hajiya ya kawo Anum da sha tara na arziki kaya akwati guda nata ga kayan wasa har da karamar Ipad na game din yara,da Sabuwar jakar makaranta da littafai da kayan biki cike da Jakar bikin ga Hoton Amarya da ango nan sannan ga kudi dubu goma Sabbin yan Hamsim Hamsin a Cikin wata farar takarda,Harda takalma masu kyau sai sweet da chaculate na su musty,Anum da shigem kaud'i sai murna take yi bakinta ya tsinke da Labari har Yaya Ishaq dake ciki sai da ya fito,Yana kallon kayan Anum na ganinsa ta nufesa ta rikesa bakinta yaki yin shuru an bata kaza sun je kaza sun je kaza.
Fuskarsa ba fara'a ko kad'an,kamar ta Fahimta ne yasa ta bar ta batunsa ta kwashe kayan taje ta nuna ma Mama Hafsah taso ta hanata nace ta kyaleta ta shiga ba dad'ewa sai gata tazo kiransa in ji Mama, ya tashi ya tafi ba jimawa sai ga shi ya shigo ina faman tattara sauran kayan da Anum ta watsar ya daga murya yana fadin"Daga yau ya'ta bazata kara zuwa wani gida kwadayi ba"
Sai na Dago ina kallonsa ni yanzu ya Daina bani mamaki a baya sai nake ganin Rayuwa tasa yayi sanyi ammh daga Safiyar yau na Fahimci lambo yayi.
Kamar zan yi mai mgana sai na fasa na zata shikenan kawai sai naji yana fadin"In ke zaki je kije, ammh kada ki kara tura ya'ata wani gida da sunan kwaad'ayi."
Sai na sake dagowa ina kallonsa ban yi nauyin baki ba nace"to ai in dai kace naje kamar kace itama taje ne.Saboda ni ya'yana na zaba akan ka.Kai kuma ka manta ka zabi Zainab da iyalanta a kaina da ya'yanka..?
Tsuramin ido yayi nasan yana mamakin kalamai na ne ni kuma ganin yaji mganata yasa na juya nayi shigewata Daki na barsa nan bansa ya yakare ba, Anum ta dawo da kayan ba jimawa su Amir suka dawo da ga makaranta sai Ihu ya tashi Anum ta Dawo labarai ta rika basu na abunda ya faru a chan har da abunda taci ta kwaso musu kayan suka yi min Baja baja da falo sai da na fito nayi musu fad'a Amir ya hau taya Anum tattara kayan yana fadin"Kiyi hakuri Umma zamu kwashe"
Sai na Sassauta ina fadin"Lokacin sallah yayi ayi alwala ku tafi masallaci Anum tazo muyi namu a gida"
Da haka suka kwashe kayan suka maida Dakinsu mazan suka fita alwala Babansu na dakin Mama ya tarasu suka tafi masallaci mu kuma mukayi namu agida ba abinci sai Hafsah tayi Taliya jallop,ta sa ka kazan da Anum tazo da shi na biki aciki,ita muka ci da Daddare kafin mu kwanta na raba ma yaran kayan Fulawan da Anum tazo da shi na Bikin harda lemuka na kuma aika ma Mama nata,ta kuma karb'e ko kunya, sai da safe na Kira Hajiya nayi mata godiya.
Daga wannan lokacin sai ya Dawo sak Yaya Ishaq din da na sani mara ragowa sannan mai tsanani sai na Fahinmci,wani abu har da zafin Talauci ya sake firgitasa sai dai bai min tijaran da ya saba da agaban mama ko mutane, saboda yaga bakina ya bude yanzu zan maidasa mganar da bazai so ta fita wani yajita ba.
Duk nayi biris da shi domin har ga Allah ba ina zaune saboda ina son sa ba ne,babu wani birbishin so a cikin zuciyata in a baya na so shi Saboda yana Uban ya'yana yanzu ko wannan Darajan bana dubawa,abu d'aya na sani ina zaune ne saboda ya'yana ba saboda shi ko jiginannen auransa ba. Shiyasa nake kama kaina ina chan ina Hidimar sana'ata da ga shi Har maman bana ta kansu,Anty Binta ma ta rage zuwa akai akai su Anty Mahma ma sai dai su leko mu ni kuma ban fasa abunda na yi niyya ba,Kananun lalurori har manyan ma ina Daukan su da sana'ar da nake yi,wannan zafin ran da na Talauci ban yarda na zauna ya saukemin ba,Ya saba in ya gama min Tijara na rika basa Hakuri ammh yanzu da ya fara in bana jin mgana zan bama banza ajiyarsa ko na bar masa wajen.
A cikin wannan takun sakan da muke yi ne, kayan abinci suka kare dole ni na fidda kudi na siya Mama da gadara duk abunda take bukata zatace na bata kaza kamar ita nake yi ma wahalan,sai dai ban taba biye mata ba, ina ganin ta a matsayin uwa shiyasa ban taba Daga kai akanta ba. shi kuma komai nayi sai yace na rubuta in ya samu aiki zai Biyani ni ko nace shi ya Lissafa da kansa mana
Muna cikin haka zazzabi ya Sarke sa kamar wasa ya kwantar da shi Ranar kwance ya yini Dakin mama,Yadda bai fad'amin ba shi da lafiya ba, nima ina da Miskilanci ko lekawa Dakin Maman ban yi ba ballatana nayi mai sannu Abakin su Amir naji Daada bai da lafiya, Mama ce ta leko da kanta Dakina da bata taba shigowa ba, sai dai ta tsaya daga bakin kofa tana ce min na bada kudi Amir ya raka Ishaq kemis  bai jin dadi,kamar nace bani da shi sai kuma ban ce ba na ba ma Amir dubu biyu suka tafi a ka mishi allurai da mganguna ashe maleria ce ta kamasa,ni iya dakina da dakin yara nake siyan ma mganin Sauro na kunna sai Dakin Mama ban yi tunanin yana jin cizon sauro ba ma.
Abu kamar wasa daga zazzabi sai zawo cikin dare haka ya kwana zagayawa,da safe har da Amai duk  karfinsa ya kare,washegari daga zuwa bayi sai dai na je na daukosa duk ya bata jikinsa da amai da zawo duk yadda nake kauce ma wata mu'amalan ganin sirin juna tsakanina da shi sai da na yaye wannan Hijabin ranar,Tun kafin auran sa da Zainab ko Hannuna sai da kuskure yake gegata ballatana ganin juna a yanayin da bai dace ba,Sai ranar ni nayi masa wanka Maman dai bata yi masa rana ba,Ina yi ina kauce kauce shi kuma jiki yayi lakwas duk yayi laushi sai abun yayi min wani barambaram kwai namiji da suna Hajara.
Bayan na yi masa wankan na koma na wanke bayin da kuma kayan shi da ya bata, sannan na fita baya damu kad'an inda Chemist yake na kira mai zaman wajen yazo ya gansa ya dora masa karin ruwa da allurai abu kamar wasa nan take sai da ya chajeni dubu Hudu,kada mutum ya raina ciwo komai kankantarsa,Yara sai dai suka Dawo makaranta suka iske sa rashe rashe ana masa karin ruwa,sai duk jikinsu yayi sanyi sai da nayi ta lallashin su sannan suka saki jiki yasha wahala rana zuwa dare duk ya fada abinci ma,ya kasa ci sai da Anty Binta tazo mai da Ferfesun kayan ciki ya samu ya ci kad'an yace bakinsa D'aci ga zazzabi ga amai da gudaawa.
Anty Binta bata neman zaman lafiya sai da tayi korafin wai meyasa ba'a kaisa asibiti ba? Mama tace mugunta ta ta ce ta tashi kuma ina da kudin naki kaisa asibitin,ni bana biye musu sai na nuna ma ban jisu ba Mama fa sai ciwon d'anta ta taba shiga bangarena ita kuma Anty Binta in asibitin banza ne meyasa bata Dauke sa ta kai sa ba..?
Wlh na yarda da maganan Hausawa da sukace in kana da abun yi,ba komai ke damunka ba. a baya ne in Mama ko Anty Binta sun min wani abu yake damuna nayi ta kuka yanzu na manta rabo na da kuka akan su,To ayyukan gabana ma sun isheni inaga naga Lokacin sauraransu ko suna yi baya Damuna, kamar irin na riga na zama Jan wuya a lamarin ballatana yanzu da nake yawan samun masu son Turaruka ta bangaran Hajiya sai ayyukana suka yi min yawa.
Ashe sun raina kulawar da nake basa balle da suka ga kurajen baki sun fito mai yaba yaba na alamun wucewa Mura, sai Mama ta saka Anty Binta ta kira Zainab na ta fad'amata wai tunda bazan iya kula dashi ba,yana da wata matar zata zo ta kula da shi,Sanda akayi ma bana gidan naje kasuwa da na Dawo Hafsah take fadamin sai nayi mirmishi ban ce komai ba.
Ashe ko sun kirata sun zuzuta abun Hankali tashe ta d'au alfarma a wajen aiki ta taso,ita da Fadil Farhan saboda makaranta ina tsaka da Hidiman Zobo na ta shigo,Direba na binta da kayanta A karamar a kwatinta kwata kwata ban yi mamakin ganinta ba, na tsallake komai na tarbeta sai dai Mama bata bari ba,ta janyeta zuwa Dakinta chan ta sauka a fili nace a gayyas.
Na koma dakina na cigaba da aikin da nake yi,Chan ba jimawa sai gasu sun shigo ita da Mama,Zainab na rike da Fadil sai alokacin muka gaisa kallo na take yi tana kare ma falon kallo Mama tayi mata Jagora har dakin Yaya Ishaq ni dai ban bisu ba saboda ba wanda ya gayyaceni sun dan jima aciki sannan suka fito sai ta kalleni tana fadin"Maman Amir zobo kike saidawa yanzu?
Ina yar dariya nace mata'"Eh wlh muna tabawa ya hanya..?ina Kika baro mana Farhan..?
Kai tsaye tace"Yana wajen mommy saboda makaranta"
Mama sai jiranta take yi daga waje ganin muna ta mgana yasa ta Dago labule tana fadin"Zainab muje ki yi wanka ki yi sallah sai ki ci abinci"
Sai ta amsa mata kafin ta fitan sai da tace min"Ashe Honey haka yayi ta rashin lafiya..?
Sai na gyada mata kai ina fadin"Ai yama ji sauki yanzu'
Cikin jimami tace"Ayya Allah ya basa lafiya"
Na amsa mata da Ameem sannan ta fice zuwa Dakin Mama ni ko sai da na gama zuba zobo na sannan na shirya ma zainab abinci daman da rana Shinkafa da miya nayi mana da Salat har dare saboda na gaJi bazan iya wani girki ba,har dakin Mama na bita da shi har da zobon na zuba mata
Bata a falo kila tana ciki Mama sai Hararata take yi ban bi ta kanta ba na sauke abincin hannuna na fice abuna.
Sai da na had'a kayan wanke wanke bayan yara sun dawo makaranta ni nace su shiga Dakin Mama su gaida Antynsu suka shiga gabadayansu suka gaisheta daganan bayan sun ci abinci suka shige Dakin babansu Fadil na Hannunsa suna ta wasa Amir ne kadai ke falo yana duba Littafansa na makaranta.
Da kaina na shiga zan dauko kololina da wanda na kai ma Mama nata,na iske zainab na zaune tayi wanka ta sauya kaya waya a hannunta tana ta Dannawa sannu da gida tamin na duka ina kwashe kwanukan da suka yi amfani da shi Mama na gefe nasan hira suke yi da na shigo ne Maman ta Dauke mganar ammh saboda salon cin Mutumci sai ta gyara zama tana fadin"Zainab nace ba.."
Sai ta Dago tana fadin"Na'am Mama"
Mama tace"Daman so nake naji ko zaki d'an kwana biyu kafin ki koma..?
Zainab ta yamutsa fuska kafin tace"Anya? hutun kwana biyu suka bani a wajen aiki"
Mama ta kalleni ta gefen ido tana fadin"Gaskiya gwara ki tsaya ki kula da shi.ita wannan baya gabanta ta sana'arta take yi tunda ta fara wannan sana'ar nata bata kallon kowa da Daraja kema matarsa ce shiyasa nace Binta ta kiraki kizo ke kila kya kula da shi yadda ya kamata"
Sai tayi Dariya batace komai ba ni kuma ina cigaba da Tattara kwanukana ina jinta daman tayi mganar ne saboda naji.
Ganin Zainab batayi mgana ba yasa Mama ta cigaba da fadin"Ni dama in kin tashi tafiya zaki tafi dashi chan Abujan,zan fi samun kwanciyar Hankali zamansa anan bai da wani amfani"
Na mike kenan Zainab tace"Mama naga Maman Amir fa na kula da shi"sai Mama ta wani yarfa Hannu tana fadin"Wlh bata kula da shi, wannan da kika gani ai muguwa ce ta sosai"
Tafad'a Lokaci daya tana nuna ni da baki kamar zan fita na barsu sai na fad'a kamar an min wahayin mganar na Tsaya ina kallon Mama kafin nace"Aiko baki ce ta tsaya ta kula da shi ba tunda tazo, na sakar mata komai Tunda itama matarsa ce, kamar yadda yake da Hakki a kaina itama yana da Hakkin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login