Showing 42001 words to 45000 words out of 82431 words
masa kudin ya tafi yayi sati ko kwana goma ya dawo nima ta kan kirani lokaci bayan Lokaci mu gaisa auran nasu har mamaki yake bani kamar Dole,to ita tana son mijinta kuma mahaifinta yasan haka, shiyasa bazai yarda auran ya lalace ba shima Ai yana son matarsa da baya sonta da Tuni ysan mafitarsa.
Tun mai gidan nan na d'aga mana kafa,har yazo ya daina Sauraran ban hakurin Ishaq ranar da Safe yayi mana Dirar makiya Allah yasa yara suna makaranta da abun bai yi dad'i ba,Da kakkausan murya ya ce mana ya bamu nan da sati daya in bamu biya ko rabi ba sai dai mu bar gidan. Hankalin mu ya tashi bamu ijiye ba,ba kuma mu ba wani ajiya ba.
Yaya ishaq ko barcin kirki ba yayi duk ya bushe a tsaye gashi yana ganin Jamal a gida shima ba kudin abinci da pocket money ballatana ya koma makaranta har shi da kansa yayi ma Anty Binta mgana tace bata da kudi ta shiga adashe ne,ni kuma jarin hannuna duk yayi kasa sai na Bukatun cikin gida.
Mama ma duk hankalinta ya tashi,Mama a baya datake yar gayu yanzu wahala duk yasa ta tsufa kamar ba ita ba,Sai dai ya shiga D'aki yana Tufka yana warwara ba mafita Hafsah mganar kudin makarantar Jamal ta sani shi kadai takai labarin Karofi wajen Goggo,sai ga shi ta kira Jamal yaje wajenta ita da ya'yanta sun had'amai dubu sittin tace ya biya kudin makaranta,bayan ta hadamai kayan abinci,haka yazo mana da kayan arziki Mama sai kunya ya kamata har da kuka sai gashi ta Biyoni har daki tana cemin"Fa'iza ke kika yi ma Goggon taku mganar jamal hala..?
Ina zaune nace"Aa Mama inajin Hafsah ne da taje wannan satin"
Sai mama ta kasa mgana ta fita ta koma Dakinta abun mamaki sai ga Mama da shiryawa ta tafi karofi yima Goggo Godiya sai da ta kwana Biyu ta Dawo tana fad'in irin alherin Goggo da ya'yanta a raina nace da ba Hajiyar Dala ce kad'ai yar'uwar mijin ki ba,ashe kin san da Goggon,Hajiyar Dala da take ganin tana tare da ita ko jinta ma ba'a yi.
Yanzu naga Mama ta daina Takura min,ba kamar baya ba. Kuma bata shiga harkata, naga ma alamun Ta koma wata shuru shuru a d'aki kamar bata nan,Aranar da satin d'ayan da mai gidan ya bamu,zai cika kasa barci muka yi,a daran ranar har ce ma Yaya Ishaq nayi"Me zai hana ka yi ma zainab mgana ko akwai taimakon da zatayi maka ta bangaran su..?
Kai Tsaye yace"Aa bazan roki kowa ba Fa'iza ai susan ina bukata kuma basu Dauko sun bani ba. In sun bani zan karba in basu bani ba, bazan taba rokan su ba"
Sai ya bani Tsausayi daganan ban kara masa mgana ba, sanin da nayi tunda yace bazai yi mgana to bazai yin ba,Da Sassafe bayan ya raka su Amir makaranta gidan Anty Binta ya tafi,yana chan bai dawo ba sai ga yaron megidan da wasu matasa majiya karfi har gidan suka shigo Hafsa na makaranta Badariya ke gida tunda sunanta bai fito a bath A ba.
Tijara ya fara yima sannan yace watsi zai saka ayi mana da kaya,Mama ta fito nima na fito ni ke basa Hakuri Mama ko cikin gadara tace"Ka dad'e baka sa an yi mana watsi da kaya ba, ban da yanayin rayuwa kai har ka isa ka wulakantamu. shekaran da ta wuce kai baka isa kazo kana mana barzanar banza ba,rayuwa ce ta maida mu haka"
Ta fad'a cikin baci rai,ido cikin ido ya kalleta kafin yace"Tsohuwa ina daraja Furfuranki ammh ke baki gani ba ko..?
Kai Tsaye Mama tace"in kana Daraja Tsufana ai da baka tsaya ina fad'a kana fad'a ba"
Kai tsaye yace"Gidan nan ai ba na tsoho ba ne ko?to in dai bana Tsoho ba ne sai kin fita daga gidan nan,yau na zata abun naku na mutumci ne. kuma Darajan d'anki kikaci wlh da yau sai kin raina kanki ina ruwana da rayuwarki a baya wama ya sani ko a lokacin baya d'in da kike da arzikin ba alheri kika shuka ba tsiya ce shiyasa kika ga karshen ki?
Ai sai Mama ta saka kuka tana fadi'n yayi mata rashin kunya na riketa ina fadin"Haba Mama ba girman ki ba ne ki Tsaya kina tanka tanka da shi"
Sai mama ta kasa mgana nan na saka Badariya ta shiga da ita ciki D'aki sai kuka take yi.
Wani Lokacin masu gidajen haya kalilan ke da burb'ishin mutumci saboda nasan bamu da gaskiya Kuma a maganar Gaskiya Mama ta zak'e da yawa ne shiyasa.
Hakuri na rika basa ina fadin"Kayi hakuri don Allah ,ya fita ne ya dawo yanzu zai shigo"
Kai tsaye ya kalleni ba wani babba ba ne, bazai wuce sa'an Yaya Ishaq d'in ba kawai dai irin ya'yan masu kudi'n nan ne, kallo na yayi yana fadin"wanchan tsohuwar ai ta bata komai Hajiya.Kai ashiru ku shiga ku fara fito musu da kayan su waje"
Sai na durkushe a gabansa na had'a hannayena ina fadin"Kayi wa girman Allah kayi hakuri.In kayi mana watsi da kaya ka tona mana asiri ina zamu..?ka da ka manta mu musulmai ne kuma duk inda musulmi yake dan'uwan musulmi ne,In ka rufamana asiri ka suturtamu sai kai ma Allah ya Suturtata taka ranar gobe kiyama. kayi hakuri don Allah zamu biya ku kudi'n ku da zarar mun samu"
Na fad'a cikin magiya sai kawai ya Tsaya yana kallona cikin Tausayi kafin ya ce na mike sai na mike ammh ban sauke hannayena ba cikin Tattausan murya yace"bakomai naji rokon ki na yi muku lamani ku zauna ammh kuyi adalci ku biya da zarar kun samu"
Da sauri nace"Wlh zamu biya.In sha Allahu"
Daga haka ya gyad'a kai ya yi ma samarin mgana suka fita tare ajiyar zuciya na sauke, na koma kan kofa na zauna ina kuka ahaka Yaya Ishaq ya shigo futu futu kafafunsa, dani ya fara cin karo ina kuka cikin tashin Hankali yace"Kuka Fa'iza me ke faruwa..?
Ya fad'a yana zama kusa da ni da Sauri na Share hawayena ina kallonsa Daga sama har kasa ganin yadda yayi Futu futu kamar wanda yayi tafiyar kasa cikin mamaki nace"A kasa ka tako..?
Bai bani amsa ba ya kara fadin"Me ya faru ne..?
Sai nayi masa shuru yana shirin kara mgana ba sai ga Badariya ta fito ita ya tambaya ta maida masa yadda akayi har yadda na duka ina rokon su sannan ya amince ya d'aga mana kafa cikin d'aga murya ya kalleni yana fad'amin"kika duka mai Fa'iza..?kika dukamai fa..?
Saboda wani dalili..?
Yafad'a cikin bacin rai sai kawai na mike ina fadin"Ba dukawa bace roko ne da neman alfarma, in ban duka ba da yanzu kazo ka ganmu a kofar gida an fara yi mana watsi da kaya"
Daga haka na shige daki sai kawai ya bini da kallo ga takaicin yaje bai samu Anty Binta ba, sun fita da mijinta a kasa ya tako tunda batagwarawa har Ajiwa,sai kuma yazo ya iske wannan tashin Hankali D'akin mama ya shiga ya isketa tana kuka dakyar ya Lallasheta tayi shuru tana fadi'n wai mai gidan ya zageta yasan halin Mama shiyasa ya kalleta yana fad'in"Mama bafa kowa ya ke da ragowa ga manya irin ku ba. Sannan kema Mama me ya kaiki sa'in sa da shi.?mu ne fa bamu da gaskiya hakkinsu ne a kanmu bamu biya ba kuma sun yi mana Hallaci bai kamata ki nemi zaginsa ba"
Ganin ya rufeta da fad'a yasa ta sauya mganar da cewa"Ka samu Bintan? ya kuka yi..?
Kai tsaye yace"Bata nan sun fita da megidanta a kasa na dawo duk nagaji"
Mama ta yi tagumi kafin tace"Allah ya warware mana ko zakayi ma Zainab mganar ne..?
Da Sauri yace"Aa Mama Allah zai kawo wata hanyar"
Sai bata kara mganar ba,sanin halinsa Tunda yace a'a to bazai kara bi ta kanta ba,Batare da sanin kowa ba, ta Kira Zainab ta fada mata komai ita Zainab d'in ne ta kirani tana fadin"Haba Maman Amir sai ki boyemin wannan abu haka..?
Sai nayi mamakin a ina taji nadai san bashi ya fad'a mata ba,sai da naji tana fadin Mama ta kirata ta fad'amata sannan nayi mata bayani sai tace bari ta kirasa to bansan ya suka kaya tsakanin su ba, ta dai turo masa kudin kuma ya biya mana kudin Hayan ranar da ya Tura ma mutumin kudin har sai da yace mai"Gaskiya kayi sa'an mata mai hankali da iya mgana."
Da ko ya dawo gida tasani yayi agaba da masifa da fad'a wai na fito ina ma wani gardi magiya kallonsa kawai nayi kafin nace"Yaushe ka fara kishin Fa'iza..?
Kai tsaye yace"Ke Fa'iza ki fita daga idona. ko a baya bana barin ki sakakaka.nasan abunda nake yi kada ki kara batamin rai da mganganun ki na banza"
Daga haka ya barmin wajen yana ta masifa a raina nace topah Sabon Salo Tusa a lasifika.
Hankalin mu ya kwanta tunda Allah ya Rufa mana asirin duka,Badariya Sunanta ya fito a Bach B, an tura ta Camp yola Raliya kuma Abuja suka barta,Hajiyar su Raliya ta bata kudin mota da kudin kashewa na har ta dawo,Hajiya ta Dauke mana wannan nauyin ta tafi da tarin nasihan yayanta da mama akan ta kula da kanta,Sati uku tayi ta dawo gida,Sai kuma cuku cukun yadda zata dawo kusa gida tayi bautar kasarta.
Haka muka cigaba da Rayuwa yau fari gobe Tsumma Goggo na lekomu ita da su Anty Nasara nima nakan lekasu,Makota na su Sa'adatu basu manta dani ba,Nima ban manta da su ba, ina leka su wani Lokacin sana'ata ne baya barina fita har kuma yau Yaya mariya bata kara takowa gidana ba.sai dai mu yi mgana da ita ta waya.
Hajiyar Dala ko ba wanda ya kara jinta ko garin ta shigo bata zuwa Anty Binta kuma ta maida hankalinta wajen Shirin Bikin Halisa daya rage Saura wattani bata cika zuwa ba ma.
Ina zuwa gidan Hajiya gaisheta Lokaci bayan Lokaci anan ne har tace Yaya Ishaq ya kawo takardunsa daga barayinta tagani ko za'a dace da murnanta nazo nayi mai magana sai kawai ya kalleni kafin yace"Ina fatan ba zuwa kika yi kikace kina so ta nema min aiki ba..?.
Wani Haushi ya bani, ba ka da ko sisi sai shegen girman kai hararansa nayi ina fadi'n"Sanarwa na bada a masallaci baka ji ba..?
Sai ya maida abun wasa ya taso zai rikeni na matsa baya kafin nayi mgana yayi saurin tareni da fadin"Kai na bisa wuya afuwan na manta ne"
Sai kuma ya bani Tausayi yadda yayi mganar,ni da kaina naje na kai ma Hajiya Takardunsa,a amsa da yakinin acigaba da addu'a za'a dace.
Ana cikin haka Badariya ta samu aka ijiyeta kano inda zatayi bautar kasarsta sai Mama tace ta zauna gidan Hajiyar Dala Badariya tace bata son zama,Maman ta had'a ta da Yayan nata yayi mata fad'a Nima nayi mata nasiha sosai ina fadin"Kiyi hakuri kije ki zauna ke mace ce yafi ki zauna a inda baki sani ba,duk tsiya ke yarta ce bazata ce zata kore ki ba"
Da haka Badariya ta amince ta tattara kayanta ta tafi kano Bayan,Maman ta samu tayi mgana da Hajiyar Dala Anty Binta dai sama sama take da Badariyan acewarta ta mata rashin kirki,tunda abun da ya faru tsakaninta da Halisa da har yanzu ita da Badariyan basu koma Daidai ba, ba sa gaba suna mgana da juna,ammh sama sama.
Raliya kuma kaduna aka ijiyeta,Sai ta zauna gida kawar Hajiya gidan su Laila kenan.
Tafiyar Badariya ba jimawa sai ga waya daga Abuja akan wani kamfanin Sarrafa fattu da Mahaifin zainab ya taba kai takardunsa sun nemesa,Dole ni nayi murd'a murd'a na basa kudin mota ya tafi,bayan tafiyar sa mun yi mgana da shi sau d'aya ya samu sun yi interviuw sai jiran kiran su bai dawo ba ne saboda baya so bayan ya koma su sake kiransa,To yana zaman jiran kiran nasu ne,Zainab ta fara rashin Lafiya har da kwanciya a asibiti,Ashe ciki gareta da sauran rabo a Tsakaninsu.
Daya kirani ya fad'amin ne bayan suna asibitin da ita nace in ta farka ya bata waya na gaisheta sai dare ya samu ya Had'amu na gaisheta bai fadaminciki gareta ba, ita ce tace min"Maman Amir bakin ki dai ya amsu,zai zo miki da Farhan ki yaye min shi tunda Honey yaki bari na huta hakanan"
Daganan sai na d'ago mganarta nayi murna sosai da Fatan alheri da ta basa wayan nayi masa murnan karuwa sai kawai sai yayi yar murya yana fad'in"Saura ke. kema na kusa har ba miki alluran.."
Da Sauri na katse wayar ina mamakin a gaban matarsa yake fadin hakan?a fili na murmusa,sannan acikin raina nace haihuwa ai na bar ma, matan so ba irin mu da rabo kan rantse ba.
Kamar cikin na bata wahala ne an dawo da ita gida kwana biyu jikin ya rikice sai da aka kara maidata ita asibitin shiyasa bai dawo ba,Kuma har yanzu basu kirasa ba kuma yace an kira Mutane biyun da suka je interview tare,ni dai na lallashe da cewa Allah ne mai yi kuma shi ke ba da aiki in alheri ne Allah ya basa in kuma ba alheri ba ne, Allah ya musanya masa da wanda yafi alheri.
Ya shafe kusan wata a Abuja ba yara ba ni kaina ina kewarsa kaji Fa'iza da Samun waje wai ina kewar mijin aro.?da Sauri na cire tunaninsa a raina na cigaba da Sabgan gabana ni nake rike da karfin gidan duk da muna da sauran kayan abinci, sannan daga Gidan Hajiya ma ta aiko mana da shi,Sannan na samu aikin yin Humra da kwallacha da kudin nake ta riritawa muna cefane da Hidiman yara..
******
Wata ranar asabar data kama kwanan Yaya Ishaq Talatin da hud'u da tafiya Abuja mun yi waya da shi a daran jiya har da yara suka gaishe da Antyn nasu tana gida an bata Bedrest,Da gaske yake da yace yayi kuskure kuma yayi nadama zai gyara kuskuransa,yana kokarin kirana in dai baya garin sannan zai ji ya gidan yake tafiya mganarsa kenan"Nagode Fa'iza Allah yayi miki albarka"
Safiyar ranar sai da na zane Musty sannan yaje Tahfezz da shirin sa bazai je ba,ya zauna yana min rigima na shiga jikinsa da Bulala,Daman tun jiya nake jin jikina ba dadi,da Safe kuma sai fama da sanyin jiki Hafsah ta shiga makaranta zasu su yi wani aiki ita da Sauran yan ajinsu tunda ta fita ina kwance afalo ban yi komai ba sai dai in masu siyan kunin aya da zobo sun yi sallama na mike na basu, Tunda jiya nayi da yammah shiyasa yau da Safe nace bazan yi ba sai da yammah.
Wayata na cikin Dakina na baro ta ana ta kirana ban ji ba,barci ne ya kwasheni nan saman kujera acikin barci sai na ganni a gari Dabam ba karofi ba kuma ba katsina ba,bakon wajen da mutanen da ban sani ba,Kamar kuma acikin barci naji ana kiran sunana a firgice na mike ina Salati sai naga Mama a saman kaina, na mike zaune ina raruman da'nkwalina da ya fad'i saboda barci lokaci d'aya ina fadin"Mama.."
Kallona tayi cikin nazarina kafin tace"lafiyarki kuwa.?Isa tun dazu yazo yana ta sallama baki ji ba..?
Sai gabana ya fad'i na zare ido ina fad'in"Wani Isan.?Yaya isa."
Kafin na karisa ya d'ago labule ya shigo a gaggauce yana fad'in"Fa'iza maza dauko hijabin ki Karofi zamu tafi yanzu"
Gabana ya fad'i ras! Cikin Dafe kirji nace"karofi..?me ya faru ne..?
Na fad'a ina wuce Mama zuwa gaban Yaya Isa itama Mama sai tabi bayana tana fadin"Isa lafiya kuwa.?
Cikin natsuwa yace"Lafiya lau kada ku damu.Goggo tace na dauko su ita da Hafsah akawai wanda zai gan su ne"
Dagani har Mama sai muka bisa da kallo zan yi mgana da sauri ya tare ni da cewa"Ki sako hijabi muje sauri ake yi Fa'iza"
Jikina na rawa na ruga daki na Dauko Hijabi na fito ina fad'in"Mama su Amir"
Da mamakina sai kawai tace"kuje ko taliya zan dafa musu,tunda akwai komai kafin ki dawo"
Sai kawai nabi bayan Yaya isa da gudu daya riga ya fice gabana na fad'i jikina na rawa a raina nace kodai Goggo ce..?da sauri nace"Aa ba haka ba ne"
A mota na same shi na bud'e gidan gaba na zauna cikin Sauri yace"na kira hafsa tana makaranta zamu biyu mu dauketa"
Sai kawai na Sadakar Mun rasa goggo,kawai sai ji yayi na fashe da kuka cikin kukan nake fadin"Allah Sarki Goggo"
Tsawa ya dakamin yana fadin"Wayace miki wani abu ya samu Goggon.?
Cikin hawaye nace"To me zai saka kazo da gaggawa ka daukemu zuwa karofi..?
Hankalinsa na wajen tuki yace"To ba mutuwa ba ne abun farinciki ne, Dan'uwan mahaifiyarku ce ya bayyana, shi da mahaifiyarsa yau a karofi"
Na ji dai kalmar dan'uwan mahaifiyarku a kunnena sai na Dafe kirji ina fadin"Ta madina..?
Kai ya gyad'amin yana fadin"Shifa..Sauri suke yi shiyasa Goggo ta tasoni daga gun aiki tace na dauko ki keda Hafsah"
Daganan ban kara bi ta kansa ba farinciki da wani irin zumud'i ya sarkeni hannuwana na da'ga sama ina fadin"Alhamdulillah..Allah abun godiya"
Har muka isa makarantan su Hafsah bakina yaki rufuwa a waya ya kirata ta fito a gaggauce itama kamar ni duk ta Rud'e sai da yayi mata bayanin da yayi min sannan itama ta rud'e da Murna tana fad'in"Yaya Isa ya ka gansa? yana kama da Tamadina..?
Mirmishi yayi yana fadin"Tsammanin abunda baku yi tsammanin ba. muje dai zaku gansa labari bazai gamsheku ba."
*Janafty*
*KNKB2012*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Har muka isa karofi ban sani ba, na lula cikin wani irin farinciki da zakwad'i abun da ka dade kana hasashensa bai faru da wuri ba sai yanzu.
Wani irin farinciki ne ace yau ga wani naka daka jima kana jin labarinsa baka taba ganinsa ba, kafin isar mu gidan Goggo a cikin zuciyata na wasaafa yadda zan ga Dan'uwan Tamadina bansan iyaka ba nadai san bakina yaki zama waje d'aya na kasa natsuwa har Hafsah tafini mallakan kanta.
Tunda Muka iso kofar gidan Goggo sai kuma jikina yayi sanyi maimakon na zama ta farkon shiga gidan sai na kasance ni ce ta karshe na koma na rab'e bayan Hafsah kamar wacce tayi karya, gabad'aya sai naji gabbaina sun saki na fara tunanin wani irin tarba ko maraba zai yi damu alhalin bai taba ganin mu ba? sannan meyasa ya kai wad'anan shekarun batare da ya waiwayemu ba?har sai da Allah ya Dauki ran Tamadina basu gana ba?
Ya ya zamu gansa..?mu ma ya ya zai gan mu..?yadda ya zata ko ba