Showing 48001 words to 51000 words out of 82431 words

Chapter 17 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

712

da Hafsah muna masu Farinciki ko da muka koma gida yara sun dawo makaranta Mama abun mamaki ita ta dafa musu Taliya Jallop muna shigowa Musty da Ahmad suka zo suka makaleni suna kiran Umma Umma daman nayo musu Tsaraban su Chaculate,Dakin Mama na fara shiga na gayamata na dawo ganin yanayi na fara'a yasa ta kalleni kafin tace"Ina fatan su Goggon lafiya..?
Cikin Tsananin Farinciki nace"Lafiya lau Mama. Daman Abba ne yayan Tamadina ya zo yau shine goggo ta saka aka daukomu"
Mama sai ta kasa gane kan mganar Cikin Mamaki tace"Bangane ba Wani Yayan tamadinan..?
Cikin zakwad'i na fara bata labari Cikin karin mamaki Mama tace"Ikon Allah ashe tana da dan'uwa kuma shima yana da iyalansa..?.
Kai tsaye nace"Sosai ma don ma tafiya ta kamasa yanzu, iyalan nasa kuma suna kano biki ammh yace da zarar ya Dawo zasu zo gabad'ayan su ganmu mu gansu muma..,"
Sai Mama ta kasa mgana mamaki duk ya cikata Dakina na shiga Anum ta tare ni tana fadin"Umma nayi miki wanke wanke."
Amir kuma ya amsa min da cewa"Umma nayi miki shara"
Ina dariya nace"Allah yayi muku albarka ya'yan Umma"
Ahmad ke dane kafata yana neman kadani na murde kunnensa ina fadin"Umman zaka kada ko..?
Sai ya fara Dariya Musty na tayashi,Kan kujera ta na fada ina Sauke Hijabin Jikina Hafsah ta shige Daki Amir har ya shiga kitchen ya zubomin abincin Ya kawo min kenan yana fadin"Umma ga abinci na kawo miki ruwa..?
Kafin nayi mgana Anum ta Ruga taje ta Daukomin ruwan na karba ina fadin"Amun di'na ta zama yan mata fa"
Sai ta rufe fuska wai kunya ina ruwan Anum,Mama ce ta kwalama Amir ya kira ya fita sai ga shi ya Dawo da kudi wai cinikin zobon da akayi bayan ba na nan mamakin Mama ya kamani itace har da siyar min da zobo..?ban dai ce komai ba sai da na Huta naci abinci na leka nayi mata Godiya bata amsani ba,Ranar cikin Farinciki muka karishe yini,Yaran har sun Fahimci ina cikin farinciki sai da Amir yace"Umma kina ta dariya ko kin samu kudi ne..?
Dariya na saka ina mamakin wayon Amir yasan dariyata yasan Bacin raina,Kansa na shafa ina fadin"Sosai Amir, ammh ba kudi na samu ba abunda yafi kudi Daraja da Tsada na samu"Amir na mirmishi yace"Umma menene shi..?
Cikin bayyana Murnata nace"Zan gayamaka kaji"
Daganan sai ya bar mganar,Bamu yi mgana da Yaya Ishaq ba,sai washegari ban gayamasa ba ammh yanayin murna na sai da ta bayyana a waya sai da yayi min mgana yace"Fa'iza hala yau an kwashi cinikin zobo da kunin Aya ne kwasha kwasha naji jiki cikin Fara'a.?
Dariya ya bani har sun Fahimci in na samu kud'i ina murna sosai ban gayamasa ba na bari sai ya Dawo kwana Biyu Tsakani sai ga shi ya Dawo,ban kai ga ma gayamasa ba Har Mama ta rigani sai da daddare yake min mganar na kallesa ina da'gama masa kai alamun hakane cikin kallona yace"Na tayaku murna.."
Cikin farinciki nace"Mungode..Yace ai in suka zo har kai yana son gani"
Cikin mamaki yace"Ni kuma..?
Lafiya kuwa..?
Sai na girgiza kai ina fadin"Ban sani ba ya dai ce dukkan mu yake son ganin mazajen mu"
Daganan sai bai kara mgana ba,nima ban kara cemai komai ba kudin hannuna Jarin zobo na da kunin Aya na kara,Sannan nayi Humra makotan mu wata Amarya ta bani na yi mata,har da kwallacha.
Kwana Takwas da zuwan Abba Ya kira Hafsah yace gobe shi da duka iyalansa,Daman su Nana Fadila Daga biki basu koma ba ya Tsaida su yace sai sun zo anyi zumunci Yaya Asiya daman ta kwana Biyu a karofi,Murnan kamar zan zuba ruwa a kasa nasha,Har chan karofi ya kira Goggo ta saka aka gyara bangaran Hajiya na gidan Yaya isa inda za'a sauke su,sai kuma mganar abinci Matan Yaya isa da Yaya Salisu zasu ji da komai,Ga Yaya mariya da itama mun yi waya tace zata shirya musu abinci mai da rai da lafiya ni kuma nace zan yi zobo da kunin aya na Taho dashi a goben dani da yara da Yaya Ishaq da sai da Daddare na fadamai.
Yayi shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Allah ya kaimu goben"
Mun yi zencen da Badariya da yake ta dawo shekaranjiya tace itama zata je kawai da Safe sai Yaya Ishaq ke fadamin Mama ma tace zataje ban yi mamaki ba araina nasan zataje ganin komai ne,kenan duka gidan zamu tafi,Itama Yaya Asiya mijinta aranar zai kamo Hanya da sauran yaran ni ma dani da iyalaina,Har girki sai da nayi jallop din shinkafa mai rai da lafiya da taji kayan lambu da nama nayi zobo da kunin Aya mai yawa,Na daukan mana kaya tunda dawowa badai ranar ba Kulle gidan mukayi,Tashar Mota Ishaq ya samo mana har kofar gida,Karfe d'aya da wani abu muka tashi Hafsah suna ta mgana da Yaya mariya har da Abban sun yi mgana yace Tafiyar ta su ta Motace,suna hanya sun Tsaya su yi sallah ne ammh sun kusa karisowa
Mun isa karofi Biyu da wani abu na rana, gida cike su Anum nata murna sun zo Karofi,har alokacin basu iso ba ammh sun ce sun shigo katsina suna gabda karisowa.
Yaya Asiya ta fimu murna saboda ita basu taba Haduwa ba ammh mu kanmu murnan ya cikamu,Yaya Isa da su Yaya ishaq da mazajen su Yaya mariya suna kofar gida,mu kuma muna cikin gida muna Dakon zuwan su.




*Janafty"*
*KNKB2013*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Wajen misalin karfe uku na rana mukaji diran motoci da Hayaniya daga kofar gida,mu muna cikin gida sai muka kasa zama muka mimmike kan kafafun mu,muna masu kurama kofar falon Goggo ido domin ganin masu shigowa.
Yara ne almajirai daga waje suka fara shigowa da jakunkuna da akwatina, sai kuma bayan su wasu fararan yara kyawawa mace da namiji suka shigo mace iyakar ta sa'ar Anum namijin kuma kamar Musty ne,Da gudun su suka shigo daidai Lokacin suma su Anum sun kwasa aguje zasu fita waje sai suka had'e da yarinyar nan,Tsayawa suka yi suna kallon juna kamar susan juna sai kuma dukkansu suka washe baki suna Dariya Anum tace"Laa..Ke.."
Itama yar yarinya sai tayi dariya sai da Kumatunta suka loba kafin tace"Kema kinsan Gidan nan ne..?
Sai gabad'aya mamakin su ya kamamu kafin mu samu mu fita daga mamakin Ina Anum ta san wannan yarinyar mai kyau da ita,sai ga wasu mata Farare yan gayu sun biyo bayansu,da yi sallama sun shigo d'ayar Babar itace ke dauke da karamin yaro a Hannunta sai d'ayan da bata kai ta Tsawo ba tana rike da jakunkunansu na Hannu da wayoyinsu dukkansu Bakin less ne mai adon pink ajiki da mayafansu, a kallo farko in kayi musu zakasan yan gayu ne sannan masu ilimi ne da Nasaba mu dai muna ta bin su da maraba ji kawai ka ke yi ana"Maraban ku."
Sannunku da zuwa"
Goggo kuma ita ke faman fadin"Maraba da baki maraba da bakin mu"
Suna amsawa cikin sakewa lokaci daya suna kallon mutanen dake falon bayan su kuma wata matashiyar yarinya ce tsawon Hafsah inaga itace Nana Khadija itama kayanta iri Daya da na yan'uwanta,tana tafe da wata karamar jaka ta mata a bayanta,Daga ita sai ga wata Farar Mata ta bayyana Tare da Inno dukkansu cikin Fara'a mu dai bakin mu bai daina kiran musu sannun su da zuwa ba.
Gabadaya waje suka samu suka zazzauna,Yaya Asiya tayi ma Inno barka da zuwa data zauna a kasan Cafet ta mike kafa Saboda gajiyan zaman mota.ta kalleta lokaci d'aya tana fadin"Mariya ce ko.?
Kan Yaya Asiya na kasa tace"Aa Asiya ce"
Sai Inno ta rike baki tana fadin"Asiya..Sannu Asiya kece bamu had'u wanchan zuwan ba,ba shakka Allah ya jikan Hafsatu da rahma"
A ka amsa da Ameen Nana khadija tace"Don Allah ina so zan shiga toilet"ina kusa sai na kalli Hafsah ina fadin"Hafsah rakata"
Sai Hafsah ta mike tace tazo ta rakata ta mike suka shige bedroom kowa ya bisu da kallo gwanin sha'awa.
Yar farar matar nan tace"Inno lalle Jini d'aya ba wasa ba, kinga Nana khadija kamar ta da wannan yar sa'arta ta ta, hala tana cikin ya'yan da marigayiyar ta bari ne..?
Inno tace"Itace Auta Hafsatu kenan. Ga Asiya nan itace Babban su sai Mariya sai Fa'iza gasu nan kun gansu ku bari Shi Baban Nana ya shigo shi da Abdul'ahad zaku ji sauran bayanin"
Daganan Goggo tace ko zasu yi sallah sukace sun tsaya a bisa hanya sun yi sallah,Sai dai aka fara kokarin gabatar musu da abinci Farar matar nan da daga ganinta itace mamansu tace"mu fa ba baki ba ne mun tsaya a inda muka yi sallah mun ci abinci zamu ci anjuma mu da mun zo kenan sai mun gama Zaga dangi gabad'aya ai abinci sai kun gaji da Dorawa kuna saukewa ko Inno..?
Tafad'a cikin barkwanci Inno tace"Kwarai kuwa"
Goggo tayi Dariya kafin tace"Ina shi Alhajin bai shigo ba..?
Inno tace"Ya tsaya da mazan dake waje"
Bata ma gama rufe baki ba sai ga su sun shigo,Yaya Isa ne yayi musu jagoranci,Abun mamaki da zugan yaran nan su Amir kamar sun san shi Bayan shi kuma wani zankaded'en Saurayi ne kamar shi, sai dai shi Saurayin fari ne sannan ya fishi jikin Murjewa,suna shigowa yaran na biye da su zuga guda Maman Nana tayi dariya tana fadin"Baban Nana baban yara kenan"
Baya ya juya yana fadin"Ina ya'yan nawa..?ku shigo mana ku ai ba surukanta zamu yi ba,Duk ya'yana ne ku ku shigo nan ai duk mun zama Daya"
Sai ga su Yaya ishaq sun shigo da mijin Yaya mariya da na Yaya Asiya sai Yaya Salisu waje aka basu suka zazzauna aka shiga gaisawa da tambayan Hanya,sannan muka tashi dukkammu muka durkushe a gabansa muna gaisheshi ya amsa bakinsa har kunne ya saka hannuwansa Biyu ya Dagomu yana fadin"Ku tashi ku zauna ya'yan Abba"
Gabadayamu muka zauna a gabansa yabi mu da kallo kafin ya yi mgana Yaya Asiya ganin yana kallonta yasa tayi Saurin cewa"Asiya ce Abba'
Gabadaya sai da akayi dariya shima Dariyan yayi yana fadin"Zan kama sunan sai kika rigani Ase ase ya gida da yaran..?kanta na kasa ta amsa mai sai ya fara waige yana fadin"To ni jikokin nawa yawa ne dasu kai yara maza kowa yaazo wajen mamansa mu gani"Kamar suna jira kowannen yazo ya rabe jikin uwarsa Anum har da kwantomin saman wuya rad'a take so tamin a kunne ban jita ba.
Abba ya kallemu ya kara kallonmu sai ya juya yana kallon Inno Lokaci d'aya yana fadin"Alhandulillah yar'uwata ta bar min zuru'a inno"
Inno ta gyad'a kai tana fadin"Ba shakka nima ai duk ta kara min yawan magidanta da kishiyoyi"
Abba na Dariya yace"Inno Maman Nana sai dai tayi hakuri Kishiyoyo gareta Rututu ba adadi"
Maman Nana ta washe bakinta fararan Hakoranta suka bayyana Lokaci daya tana fadin"Bakomai ban damu ba dad'in abun ma duk na Roba ce nice dai uwar Nana ta karfen"
Gabadaya dariya akayi daga ganinta itama akwai barkwanci su Mama na gefe suna Dariya Saurayin ya dago ya kallah yana fadin"Babban yaya ta kanka zan fara fa"
Mirmishi yayi mai kayatarwa kafin yace"Girman ka ne Abba"
Badariya ta kara kallonsa ita tun shigowarsa taga kamar ta san shi, sai dai ta kasa tuna a ina shi kuma bai ma Lura da ita ba D'aya bayan d'aya ya fara Gabatar da mu kafin ya karishe da fadin"Duka wad'anan kannenka ne nauyi ya kara hawa kanka Babban yaya.kamar yadda kake tafiyar su da Nana Fadila haka zaka tafiyar da su ya'yan yar'uwata da na baku Labarin bamu had'u ba har Allah ya Dauki ranta wad'anan sune iyalan data bari"
Cikin gamsuwa yace"In sha Allahu zaka sameni mai kulawa da kannena kamar ko yaushe"
Jinjina kai yayi kafin ya Kallemu yana fadin"Fa'iza Asiya,Mariya da Auta ga yayan ku nan sunan sa Abdul'Ahad zai yi muku Jagoranci kamar yadda zan jagorance ku, ku gaisa da shi"
Daya bayan d'aya muka rika gaishe shi yana amsaawa cikin Sakewa kafin Abba ya yafito Nana Fadila ta matso kusa da shi Tana fadin"Na'am Abba."
Cikin Dattakonsa ya nuna mu yana fadin"Ga yan'uwanki nan.Kinga Asiya itace kamar age mate din ki to ki riketa Amana ku zama kamar yadda kike da Nana Fatima"
Cikin gamsuwa tace"In sha Allahu Abba"Nan itama muka gaisa ya yafito Nana fatima ya gabatar mana da ita yana fadin"Ga age mate din ki nan Fa'iza ki kula da ita kamar yadda zaki kula da Nana khadija tana da raunin ji Hallita ne haka aka haifeta ki kula da ita"Da sauri ta rike Hannuna tana fadin"Ni daman Abba ina ganinta naji ina sonta"gabadaya sai akayi Dariya Abba ya Kira Nana khadija da Hafsah ta Dawo rakata Tiolet ya had'a su da Hafsah sai Yaya mariya taga an wareta Cikin damuwa tace"Abba ni wa zaka damka ma Amanata?
Yana dariya yace"Amanarki tana hannu nagari D'iyata. Maman Nana ga wata amanar na kara miki Dukkansu ya'yanki ne kamar su Nana fadila ki zama uwa tagari garesu kamar yadda na sanki kada ki kara bari suyi kukan maraicin rasa uwa"
Da Sauri ta Gyada kai Lokaci d'aya tana jawo Yaya mariya ta Rumgume tana fadin"In sha Allahu Baban Nana,Mari babban kifi rabu da wad'anan yaran ke da uwa kika samu sukutum ga Abdul'Ahad da zan saka yafi shagwabaki"
Yana dannan wayar sa yace"Itace fv sister di'na ma daga yau Ammi"
Nana Khadija ta shagwabe fuska tana fadin"Kai yaya ni din fa..?.
Yana tabe baki yace"Kin zama tsohon yayi"Sai dariya gabadayanmu Farinciki ya samu muhalli a zukatanmu Abba ya gabatar da su Baba ati ne a matsayin Goggon su kad'ai data rage mu su sannan ya gabatar da Maman Nana a matsayin matarsa uwar su Fadila sai su Goggo a matsayin Dangin mahaifin mu.
Badariya ya gani ya nunata yana fadin"Wannan fa ban ganeta ba..?
Da Sauri nace"Kanwar mijina ne Badariya Abba"
Cikin gamsuwa yace"Itama ya'ta ce sannu Badariya"kanta na kasa ta amsa tana gaishesa sai lokacin Abdul'ahad ya lura da ita ammh shi karon farko ya gane ta,har Hoton wayarsa ya Dauko yana gani to ai dolensa ya ganeta duk kan Hoton Raly dake wayarsa rabin sa tare da wannan kawar nan tata take yi, in bai manta ba sunan  kamar Badar sunan ta, in suna tare wani Lokacin har gaisawa suna yi ta kalleshi shima ya kalleta ammh ganin kamar bata ganesa ba sai shima ya basar.
Yaran duka Abba yasa muka yi masa bayaninsu,muma muka tara su wajen shi muna fada musu Abba ne su gaisheshi Amir ya karisa ya gaishe shi ya Dagosa yana fadin"An ya Fa'iza bazaki bani abokin nan nawa ba yaron ya burgeni akwai natsuwa sosai'
Ina dariya ban yi mgana ba Da Sauri yace"Kada ki damu in dai bangaran megidan  ne ke da shi Duka ya'ya ne ina da iko a kanku da ya'yan ku gabadaya"Nana Fatima na gefe tace"Allah ya bar mana Abba"
Nana Fadila da Inno na tayata Dariya shi bai ma jinsu ba Hankalinsa na wajen Anum kuke tana faman tambayansa"Kai ne Abban Umman mu.?ya gyad'a mata kawai sai ta kalleni tana fadin"Umma ba kin ce Baban ki ya rasu ba har muna addu"a ba?
kafin na samu amsar bata ya amsata da cewa"Wani Sabon Abba ta samu ke kuma kin samu sabon megida ko bakya so na..?.sai su Anum aka noke kai ana dariya kafin tace"Ina sonka mana ammh sai na girma zamu yi aurre"Gabadayanmu muka saka Dariya Ammi tace"Kaji min yarinya Daga haduwa sai fashin miji"Abba ya Dora t saman cinya yana fadin"Maman Nana dai ana ta kishi"Sai dariyan barkwancin su muke yi, Sai yarinyar da suka fara shigowa naji Nana Fadila na kiranta Falaq,ita tayi ma mamanta Rad'a a,kunne sai ta Dago tana kallon Anum kafin ta kalli Ammi tana fadin"Ammi Kin ji Falaq tace Anum tazo bikin uncle Junaid ta ganta a gidan Anty Laila"
Sai kallo ya koma kan Anum tana jin haka jikinta na rawa tace"Nima na ganta"Sai mamaki ya kamani Ammi tace"Haba ni fa ina ta yi ma yarinyar nan kallon Sani sai da Falaq ta fad'a na tuna kunga yara da rashin mantuwa ko..?
Nana Fadila tace"Ko ita ce Anum d'in da kika Dameni da zencenta da kika koma gida.?sai yarinyar ta Daga kai sai mamaki gabadaya ya kamamu Abba yayi mirmishi kafin yace"To yara dai sun san juna sai aji ta ina aka haihu a ragaya"
Ammi ta kalleni tana fadin"Fa'iza ko har dake aka zo bikin Lailan ne bamu hadu ba.?Laila ta kaduna..?
Sai alokacin na tuna bayan Amir yayi zaraf yace"Umma Anty Laila da take zuwa ita da Anty Raliya"
Da Sauri nace"Laila..Oh na tuna ta Aa Anum kad'ai taje bikin ita ta roki babanta ya barta suka tafi da ita"Sai da ake mgana Badariya ta tuna inda tasan Abdul'ahad da Sauri ta kallesa tana fadin"Abdul'Ahad right.?
Sai ya jinjina mata kai yana fadin"Yes Badar ko..?
Sai ta fara Dariya kallo ya koma kansu ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza kinsan waye..?wanda zai auri Raly ne fa."sai na bude baki ina fadin"Raliyar ki.?sai ta gyada min kai sai na kasa mgana Ammi tace"ikon Allah kusan Raliyar da Abdul'ahad zai aura kenan..?kusan Hajiya Aisha Saulawa kenan?
Kai tsaye nace"Nasan ta sosai akwai zumunci a tsakanina da ita da ahalinta. Raliya kuma yar gidana ce Aminiyar badariya ce, kanwar mijina"
Sai mamaki ya kama kowa,Ammi ta bude baki kafin tace"Ke Fa'iza ba dai ke bace mai Turaran kamshi na Katsina ba..?
Sai ta bani dariya na gyad'a mata kai lokaci daya sai na Tuna da Sauri nace"Ba dai ke ce yayar mijin Laila da na hada turare humra da Kwallacha wajen ki ba..?
Sai ta fara Dariya tana fadin"Baban Nana diyar taka fa sananniya ce.
Ba shakka ina turaren da nace maka naga Amaryan junaid dasu masu kamshi na tambayi inda akayi mata tace Daga katsina kawar mamanta Hajiya Aisha ta bada akayi mata?ka manta har kana min tsiya shegen son kanshi bazan iya siya a kaduna ba sai na lula har katsina..?
Sai ya daga mata kai yana fadin"Duk na tuna"Da sauri tace"To ai di'yar kace mai hadawan Allah mai iko sannu Fa'iza"
Sai kallo ya koma kaina Nana Fatima tace"Ammi wai turaran da na sace din nan da nazo duba Inno..?
Dakuwa tayi mata tana fadin"Asirin ki ya Tonu kaga barauniyar gidan ka Baban Naana ina fad'an an dauke min Turare kace baka da barawo a gidanka to wannan fa..?
Gabadaya dariya muke cikin Had:e rai yace"Yayi mata kamshi ne ta ara ko Nana Fatima..?
Da sauri ta daga kai Lokaci daya tana fadin"Fa'izata zata sake had'amin nawa Ammi na dibar miki"
Dakuwa ta sake yi mata tana Dariya AbdulAhad na dariya nace"Nana Fatima kamar itace mujaheed d'an sandan farin kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login