Showing 60001 words to 63000 words out of 82431 words
har Yaya mariya tanan sai gobe zata tafi Yaya Asiya kuma aranar suka tafi da yammah tabi yan gidan su Ammi daman tare suka iso,Amarya na gidanta suna hutawa ita da ango Badariya na gidan tare dani zamu koma da yara.
Wasa wasa ina neman yin Sati a kaduna Gida duk ya watse,Nana Fatima ta koma Dutse,hakama Anty Fadila ta koma lagos,Abba ne ya Tsaidamu ni da Yaya Ishaq shiyasa bamu koma ba shima kanshi ya koma Office sannan ga wannan Hayaniyar Biki shiyasa bamu samu zama ba. ammh nasan Ba domin Yaya Ishaq na ganin girman Abba ba,bazai zauna ba,sai korafi yake min shi ya gaji da zaman wuri d'aya da cewa yayi zai tafi ya barni sai na Taho daga baya nace ya dai Tsaya yaji me Abban zai ce masa.
Sai Ranar Alhamis da Daddare suka samu zama da Abba. Tunda bikin ya watse ni nake yin girki,Umarnin Abba ne har kayan hadin zobo da kunin Aya an siyo da sauran lemuka ina ta Shagwabasu da cimata.
To ranar ma daddaran Lemun abarba nayi musu,sannan na soya musu kaji nayi pepe din su sai tashin kamshi yake yi,daman Tuwon shinkafa nayi miyar agusi da naman rago an kai musu sai Ammi tace na bi su da wannan su dora daga baya.
Sanye nake da Hijabi mai ruwan kasa har kasa Nana Khadija ta Dauko min Voul din kazan muka shiga Falon Abba sun ware suna ta Hira da Yaya Ishaaq Abba ne fa da ba ruwansa.
Har kasa na duka ina gaida Abba ya amsa yana fadin"My Dota me muka kara samu ne.?
Ina mirmishi nace"Abba pepe chikchen ne sai lemun abarba"
Abba ya bude kamshi ya Dakesa sai ya lumshe ido yana fadin"Gaskiya Ishaq kayi hakuri ku kara ko Sati d'aya ne nima na Mori yata da girken girken nan nata masu dadin Tsiya"
Yana mirmishi yace"Sai ayi haka Abba?
Abba ya kalleni kafin yace"Fa'i Allah ya kawo kudi Abba ya bude miki katon gidan abinci.."
Ina Dariya na amsa da Ameen khadija na gefe tace"Abba ga Vacany na farko kun fara samu nasan albashin zai yi tsoka"Abba yace"Aa sai mun yarda da kwarewarki bama son masu son jiki"Sai ta fara dira kafan Shagwaba da Sauri yace"Ni fa ba da nake ba"
Yadda yayi ne yasa muka Dara mikewa muka yi muka fice yana sakamana albarka.
Bayan sun taba kazan sun sha Lemun Abba ya koma ya kishingida yana fadin"Fa'iza ta shagwabani da abincinta gaskiya Maman Nana ta kara koya kafin tatafi in baso take na rika barin mata kayanta ba"
Ishaq yace"Baza'ayi haka ba Abba"
Abba yace"To a san yadda za'ayi dani Allah"
Haka dai suka yi ta barkwanci.
Abba baya so ya fara mai mganar kai Tsaye kada Ishaq din ya Dauka da wata manufa sai ya fara sako mai mganar aikin Gwamnati suna hira cikin Hiran ne Abba ke tambayansa ina yake aiki kansa na kasa yace"A baya dai nayi aiki da Hukumar Tattara Haraji ta kasa ammh yanzu bana aiki da su bisa ga wani abu da ya faru"Sai Abba ya gyara zama kamar bai sani ba yace"Subhanallah me ya faru..?kai Tsaye kuma Ishaq din ya warware masa komai, Abba ya jinjina kai ko ni bai yi mganar dani ba.
Yaya isa daya fadamai sai ya Tattauna da Goggo ta kara yi mai bayani ammh yanzu yaji wasu a bakin Ishaq din.
Kai Tsaye Abba yace"A abuja kace kayi aiki da su ko..?
Kai ya gyada yana fadin"Eh Daga katsina chan suka maidani nafi shekara Bakwai ina aiki dasu a wajen"Sai Abba ya muskuta yana Fadin"Nako san chairman din ku na wajen. Dr.Lawal Bako zan kirasa ko zai iya yin wani abu akai,ai bai kamata a bar shi haka ba, sai a tsananta Bincike har a gano gaskiya"
Da Sauri Yaya Ishaq yace"Kasan shi ne Abba?
Abba yace"Yes Tare muka yi Mastering Degree din mu a Buk kano Shekarun baya"
Sai Yaya Ishaq ya murmusa kafin yace"To ai surukina ne. Ina auran yarsa Zainab"
Abba ya ware ido kafin yace"Au daman kana da wata matar ne bayan Fa'i.?sai ya gyad'a mai kai cikin Mamaki Abba yace"Ikon Allah to tana ina ban taba ganinta ba..?
Kai Tsaye yace"Tana chan Abujan Abba.."
Abba sai ya kasa mgana ya Dauko wayarsa yana fadin"Ammh kuma duk da wannan dangantarka bai saka an tsananta bincike ba? domin daga gani kamar Trap ne aka had'a maka acikin kuma ma'aikatan naku ne"
Yaya Ishaq yace"Gaskiya ba'ayi ba. Lokacin dai an ta fad'i tashi Saboda Shigar EFCC kan mganar"
Abba yace"Suma EFCC din ina da wanda zan kira kan mganar ammh bari na fara kiran Dr.Lawal din ina da lambarsa mukan taba juna Lokaci bayan Lokaci"
Kai tsaye ko ya lalubo lambarsa ya Doka masa kira ya kuma sakata a amsa kuwwa kira uku ana hud'u ya Dauka cikin Dariya Dr.Lawal yace"Kaga Matatar mai da kanta ba Sako ba. Allah ya taimaki Engr"
Abba yayi mirmishi yana Fadin"Dr bako kana lafiya..?ya iyalai..?
Shi Dr.Lawal yaje ya karo karatu ne har yazama Dr,shi kuma Abba bai yi ba,aammh dukkansu Chemical Engerniaring suka karanta a makaranta.
Bayan sun gaisa Abba yace"Kai ashe mun hada suruki d'aya bamu sani ba..?Dagachan Bangaran Dr.Lawal yace"Suruki wani surukin nawa kenan..?
Abba yace"Suruki nawa gareka..?
Dr.Lawal yace"D'aya mijin Zeey ne, Ishaq dan katsina ne"
Abba ya yi dariya kafin yace"Shi fa. Nima ai yana auran y'ata"
Sai Dr.Lawal ya mike daga kishingid'en dayake yana fadin"Wata y'ar taka Kuma Engr.?
Abba yace"Sunanta Fa'iza abokiyar zaman ita yar taka kenan"
Sai ya mike tsaye a razane yana fadin"Dama yar ka ce ita..?
Abba yace"Diyar kanwata ce mai Rasuwa. Ga ni ga Ishaq din sun zo Daurin auran Abdul'Ahad ne muna Hira sai muka tabo bangaran aiki, To yana gayamin a office din ku na Abuja ya taba aiki nace na sanka shi kuma yace ai surukin sa ne kai"
Dr.lawal ya share zufa yana fadin"Ikon Allah.."
Abba yace"Kaji fa."
Dr.Lawal yace"To ai baka gayyace ni bikin yaron namu ba".?
Abba yace"Kaina yayi zafi ne kuma kasan mun jima bamu yi mgana ko ta waya ba"
Daganan suka cigaba da Hira Abba ya Sako mganar Ishaq da Tunanin a saka Kwamitin Bincike a gano bakin zaren mana Dr.Lawal yace"Ai hukumar EFCC ke cikin mganar Engr shiyasa"
Kai Tsaye Abba yace"Kada ka damu ni dai ka nad'a kwatimin bincike ta bangaran ka, ni kuma zan yi mgana da megidana Engr mahaifinsa Shine Chairman na EFCC a yanzu haka so nasan zai taimaka mana insha Allahu"
Dr.Lawal a ransa yace aiki ga mai kare ka,Sun dad'e suna mgana yace zai nada masu binciken tunda zai shiga mganar nan take ya kira Megidan nasa bai same shi ba sai ya kalli Ishaq yana fadin"Zan kirasa kuma ina gayamai Cikin Satinan za'a dauko Fayel dinka a Sabunta bincike da ikon Allah za'a wanke ka"
Yaya Ishaq nata godiya,ni bansan me suka Tattauna ba. washegari Direban da Abba ya bamu aka maidamu gida a jeep dinsa ni da yara da Badariya da Hafsa da zata koma makaranta booth din mu cike da kayan Biki.
Bai fad'amin yadda suka yi da Abba ba, sai bayan kwana Biyu da muka natsa sannan yake gayamin nayi murna sannan nasan tabbas tunda Abba yace zai shiga mganar an yi an gama.
Har Mama ya fad'amawa sai addu'an Allah yasa adace take yi,da fatan a gano gaskiya.
Ko da aikinsa bazai dawo ba,ammh yana da kyau kada sunanka ya zauna a matsayin barawon Gwamnati.
*Janafty*
*KNKB2016*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Wannan shekaran data zagayo. bamu sha wahalan rayuwa ba,saboda Abba ya tsaya mana,shi ya biya kudin makarantan yara da sauran bukatumu na yau da kullum. hatta da kayan abinci ya cike mana wannan bangaran,Yace komai muke bukata mu kirasa bamu da damuwa Ishaq kuma daman ya fad'a masa shi a D'a ya dauke sa ba suruki ba, shima uba yake garesa kamar yadda yake uba gareni
Shikenan shima sai ya saduda yana karban komai da girmamawa,Mama ma haka tana ta min godiya,ni ko nace mata bakomai,Badariya ta koma kano wajen Hidimar kasarta Jamal ma ya koma makaranta sun shiga Semister karshe a makaranta.
Gefe daya ina cigaba da sana'ata ban Dakata ba,Sannan ayyuka sun karu min yanzu saboda akai akai nake hada Turaruka yanzu daga chan kaduna da kano ko'ina akayi mganar Turare sai Ammi tace Fa'in mu tana Had'asu masu kamshin Dadi,in nayi sai dai na bama Hafsah ta kai tasha a saka a mota kuma kudin aikina cas a Hannuna,Allah yasa ma Anum na gida ta gama primary zata shiga JSS Section.
Muna waya da su Nana Fatima kusan kullum muna sanin Halin da juna ke ciki,Yaya Ishaq yaki ya gyara wayarsa sannan yaki ya siya wata. Matarsa sai kirana take yi ni na zama alkali a Tsakaninsu wani Lokacin sai ta kira baya gida sai ya barni da gayamata ya fita,gajiya nayi ranar muna zaune da Daddare shi ya gama yi ma yara karatu sun kwashi Littafan su zuwa Daki,Hafsah na kitchen tana Dafamin zobo wanda zan yi na safe da shi,ni kuma ina gefe zaune a kasan cafet,shi ko har ya koma ya kwanta a saman kujera.
Dagowa nayi ina kallonsa kafin Nace'"Na manta. matarka ta kira d'azu baka nan"
Yana ji na bai yi mgana ba sai na tura masa wayar gabansa ina fadin"Gaskiya ka siya waya. ko ka gyara taka, nagaji da Damuna da matarka take yi, kana kuma barina da bayani in baka gida"
Sai alokacin ya bud'e ido yana kallona cikin shakewar murya yace"Ba zan siya ba sannan ban yi ra'ayin gyarawan ba"
Ban yi mamaki ba daman nagansa yau sai a hankali yana jin yan tsiyan nasa, sai na rabu da shi aiko ko tashi bamu yi a wajen ba sai ga kiranta na leka naga itace na mike na fice daga Falon zuwa tsakar gida ina faman kaye kaye ban sanin masa ba ko sun yi mgana. ni dai da nadawo naga wayata nan saman kujera na Dauki kayana na wuce Daki.
Abunda na lura Zainab da mahaifinta sun sauko suna neman sulhu da Ishaq shi kuma yaki basu wannan damar Saboda bayan kwana Biyu ta sake kirana baya nan domin yakan d'an fita ya mike kafa ina ji a gefenta tana mgana tana fadin Daddy wai baya nan ya fita sai naji an yi mata mgana kafin tace min in ya dawo nace ya Kirata Daddy zai yi mgana dashi.
Da ko ya dawo na bi shi har Daki na Fad'amasa sannan na bar masa wayan a wajensa sai gashi ya biyoni nima har Daki ya mikomin wayata yana Fadin"Ki daina kawo min wayar nan Fa'iza wai sau nawa zan fad'a miki ne.?
Sai na bude baki ina kallonsa cikin mamaki nace"To in ta kira sai nace mata me..?kai tsaye yace"ki fad'a mata gaskiya bana son mgana da ita"
Nima kai Tsayen nace"Tace ka kirata Daddy na son mgana dakai"
Yadda ya wurgamin wayar ya fice a Fusace ne yasa sai da nayi Dariya Allah yasa wayar kan gado ta fad'a,Na dauki wayata ina fadin"Bani na kar zomon ba"
Zainab bata barni ba, ta rika addabata da kira kunya sai na rasa me zan ce mata sai taga kamar ni ne bana son had'asu,Gajiya nayi nace gwara na fito nayi masa mgana Tattara yaran nayi zuwa Dakin Mama harda Hafsah saboda chan yafi kusa da tsakar gida yafi iska,Kayan sa da na wanke masa na ninke masa basu kawo wuta ba,ballatana na goge masa,Sai na Tattara na kai masa Dakinsa tun da ya shigo ya shige ciki sannu da zuwa ma dakyar ya amsamin Abincin sa Anum na bama ta kai masa ko da na shiga yana wanka domin naji karan saukan Ruwa a makewayi.
Sai na sauke kayan Hannuna saman katifarsa na zauna gefen katifar ina jiransa bai jima ba ya fito da Dogon wando a jikinsa,Kansa na digan ruwa yana gogewa da karamin Towel,Sai da ya tsaya yana kallona alamun yayi mamakin ganina ni kuma ganinsa ba kaya yasa na mike ina fadin"in ka shirya sai na dawo'
Ban jira cewarsa ba na fice shima bai Dakatar dani ba,Na koma Falo ina yan kaye kaye yara dai ba'a rabasu da Lalata waje ko sau goma zaka gyara shi kuwa,ba jimawa sai ga shi ya fito da jallabiya da farantin abincinsa a nan falon ya zauna ya ci abincin ya sha ruwa,sai ya koma ya kishingid'a yana Hamdala ni kuma falon na Tattara domin ina taka datti Musty ne yayi sharan,ba domin ya share dakyau ba.
Ina ta jira ko zai ce me nake son fadamai sai naji yayi kamar bai ma ganni a falon ba,Sai na samu gefen kafafunsa na zauna ina fadin"Mgana fa nake so mu yi"
Kai Tsaye yace"kunne ke ji ai"
Sai na bude baki zan yi mgana sai na Rufe saboda ina tunanin bazai karb'i mganata ba Sai ya dago yana kallona kafin yace"Uhm ina jin ki"
Sai na dukar da kai ina Fadin"Tsakani ga Allah baka kyautawa abunda kake yi"kai tsaye yace"Da na yi me kuma..?
Ina gyara mganata nace"Kan mganar Zainab mana ka barni ina mata karya. Haba don Allah baka je bafa tun zuwan nan da kayi kafin azumi,Itama ai tana da Hakki a kan ka, kuma Allah zai tambayeka akan hakan ka dauki waya ka kirata ku yi mgana don Allah"
Kamar bazai ce komai ba har sai da nace"Kaji.."
Sai ya gyara zama kafin ya mike ya zauna dakyau yana fad'in"Kina bani mamaki Fa'iza wai wani hakki kike mgana..?ke sau nawa ina zuwa wajenta na tare kuma tasan hakkin ki na shiga ammh bata taba min mganar naki Hakkin da ke kaina ba, sai ke ki bi ki dameni Haba."
Ya karishe fad'a yana Tsareni da idanuwansa da suka fara shigewa Ciki,sai na sunkuyar da kai ina Fadin"ni ba ruwana da wannan. Abunda na sani ne nake gayamaka kai ma nasan ka sani,Tunasar dakai nake yi ciki fa gareta tana Bukatar kulawarka"
Kai Tsaye yace"ke ciki nawa kika Dauka kika haifeshi batare da kulawata ba..?
Sai na kasa mgana kafin nayi mirmishin takaici nace"Ni sunana Fa'iza ni ba yar kowa ba ce. sannan ni ba yar gata bace Fa'iza ba Turanci komai nata zero ne Zainab kuma mai kyau ce yar gata yar Dangi tana da ilimi tana jin Turanci sannan kowa na sonta, kaga kenan Tsakanina da ita akwai Tarin bambamcin da ko a wajen Daidaito na miji bazamu zo Tsara d'aya ba".
Ina kallon cikin Idanuwansa na fadamai haka sai kawai ya rausayar dakai yana fadin"Ashe bazaki bar wannan mganar ba Fa'iza..?baki manta komai ba kenan..?
Ko daman kin fad'ane kawai baki yafe min ba..?
Da Sauri nace"Wlh na yafe maka duniya da Lahira"
Da Sauri ya Tareni da fadin"To me kike son nayi ne ki daina damuna da wad'anan mganganun ne"
Kai tsaye nima nace"ka Saurari zainab sannan kaje ka dubata tana bukatar kulawarka"
Sai ya kankance ido ya mike yana fadin"To bazani ba. Nace bazani ba,Sai ki sani naje dole..Haba mata kin bi kin dameni..?zaman ki nake yi a gidan da zaki rika min kora da Hali.?na riga nayi rantsuwan da bazan kara bin Zainab ba, in tana so na tasan inda nake zata Biyo ni. kuma kin ji ma na rantse bazaki sakani yin kaffara ba. Ba ruwanki in ta kara kiranki kada ki sake d'aga wayarta Umarni ne na baki ba Shawaran ki nake nema ba Fa'iza"
Ya karishe fad'a yana kureni da ido,na bude baki zan yi mgana ya saka min yatsa a saman bakina yana fadin"Shii..Mu rufe babin wata zainab mu yi mganar mu Fa'iza ina mganar mu ta kwana..?baki ga duk na galaibata ba ne saboda rashin ki..?
Kai Tsaye nace"Shiyasa nake so kaje inda zaka samu abunda kake muradi"
Sai kawai ya mike tsaye yana Nuna ni da yatsa cikin bacin rai yace"Rashin kunya zaki yi min Fa'iza don kinga ina Lallaba ki ko..?ko karfi na saka miki Bani da laifi Saboda ke Halaliyata ce. ina binki a Hankali ne Saboda nayi miki laifi ba domin kin fini iko da kanki ba"
Mamaki ya kamani kamar zan yi mgana sai na fasa sai kuma ya Saussauto ya koma ya Duka gabana ya Riko Habana ya dago fuskata yana Fadin"Don Allah Fa'iza ki manta komai mu bama auran mu wata Dama nayi miki alkawarin bazaki kara kuka dani ba don Allah. Wlh na wahala na fara susucewa"
Ya fada lokaci d'aya yana langwabe min kai kamar karamin yaro,sai nayi wuf na kwace fuskata na mike shima sai ya mike zan gudu ya rikoni kafin nayi wani motsi ya kamkameni a jikinsa duk mutsu mutsu na na kasa kwace kaina sai na Saduda kaina ya Dago yana kallon cikin Idanuwana yace"Saboda kin ga ina kyale ki ko..?ni kuma sai na bude baki zan yi mgana, sai kawai naji ya Had'e bakina da nasa waje daya ya fara sumbatata lokaci daya yana kara kaina da Hannayensa a cikin jikina. duk iya kokarina na kwace kaina na kasa tun muna Tsaye har muka zube saman kujera yana Jagwalgwalani fargabana D'aya kada wani cikin yaran nan ya shigo gashi yaki barin bakina ballatana na yi masa magiya sai da ya maidani Tubus ko yatsana ban iya dagawa, Saboda yadda Hannayensa suka Ladaftar dani,Mganar Ahmad muka ji daga kofar daki yana kiran"Umma.."Umma"
Shi ya ceceni zaraf ya tashi daga kaina Daman doguwar rigace ajikina ya Dagemin ita har wuya,saboda bala'i shi ya saukar min da rigan yana kallona takaici da bakinciki suka tasomin,Kallona yayi cikin yar dariya kafin yace"mganin ki kenan. na lura ni nake kyaleki"
Daga haka ya wuce dakinsa yana Dariya sai hawaye suka zubomin nayi Saurin sharewa,saboda shigowan Ahmad yana fadin"Umma barci nake ji"Cikin kasala ina share hawayena nace"je kayi fitsari ka kwanta"
Daga haka na mike na shige Dakina ina share kwallah kamar wacce aka daka kan gado na fada ina cigaba da kukana abu d'aya ya tsayamin a rai in ya cigaba da min haka watarana zai karyamin lagona kuma faruwar haka kamar rugujewar Burina ne.
Kuma ni bazan bari hakan ya faru ba,Wannan kudirin nawa ya Dade a raina cika shi tamkar wajibi ne.
Bansan adadin da na dauka ina kuka ba sai da naji shigowar su Hafsah naje na wanko Fuskata,nazo na kwanta Na rufe ido da suka shigo sai suka yi tsammanin nayi barci nan ko idona Biyu,Har suka yi shirin kwanciya suka kwanta,ni kuma na kasa barci ina Tunanin yaushe ne mafitan da na Dad'e da neman ma kaina zai cika..?
Shin zan iya yin abunda nake hasashe ko ba zan iya ba..?
A haka har barci ya kwasheni,Sai chan wajen ukun dare na tashi nayi alwala na fara