Showing 6001 words to 9000 words out of 82431 words

Chapter 3 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

187

tace ya shiga wanka Amir na ba ma wayar shi ya nemo min Lambar Hafsah ya kiramin nayi mgana da ita tace min tunda na dawo gida gobe zata dawo nace yauwa gwara ta dawo din.
Ina cikin Gyaran gado na Anum ta shigo da gudu tana fadin"Umma Daada yace ki hado masa Tea"
Sai na amsa mata da Toh sai da na gama gyara gado sannan na fita na Dora ruwan zafi na saka mai citta da kanunfari,da Top tea suka Dahu tare na tace sannan na juye mai cikin karamin Fulas din da na siya,Tunda na siya sabbin kayan aikin Kitchen,su dai da suke nawa Tsoffin na Sadakar ne ammh na falo kam suna cikin wani Daki dake haraba kwashewa kawai nayi na sauya sabbi,nasan Halin sa tsab in yaji tijaransa zai ce ina kayansa Tunda shi ya saka komai na gidan kafin mu dawo.
Da kaina na shiga na kai mai yaran dai ke ta duduma afalon shi bai fito ba na sauke mai saman Karamin Center table din dake falon na kalle su ina fadin"Dare yayi aje a kwanta gobe akwai makaranta"
Anum sai ta dira baki tana fadin"Umma mu wajen Daada zamu kwana."sai na rike baki kafin nace"Da wajen Daadan kika saba kwana..?zaki wuce ko sai na mangareki"
Nayi kamar zan kai mata Hannu sai ta goce ba zato kawai naji tace"To Umma Anty in tazo tana kwana anan ke ko baki taba kwana a dakin Daada ba.."
Ta fada daidai Lokacin da ya fito daga cikin Daki yana sanye da jallabiya yaji kuma abunda tace ni ma mamakinta ya sandar dani na shiga tafa hannu Cikin mamaki ya kalleni nima na kallesa sai kawai na kauda kai na sukunci Ahmad da ya barci ina Fadin"Sai da safe..Amir riko Musty kuje ku kwanta"
Daga haka na fice sum sum suka bi bayana Mazan na fara kula har suka kwanta sannan na dawo Daki mamakin Anum ya gama kamani na tashe ta tayi fitsari sannan ta koma ta kwanta araina nace yara ma kada a raina su,su na ankare da motsin kowa Allah mai iko har nayi barci da Tunanin Anum a raina.
Haka muka cigaba da gungura rayuwar mu,Yaya Ishaq sai zaman gida ba inda yake zuwa sai ya bani tausayi magidanci ne fa da ya saba fita aiki da Zirga zirga yanzu ya Dawo sai dai ya kwanta in ya gaji ya zauna,Mutane na zuwa masa jaje cikin mutanen Mama,ko jamal yazo su wuni yana tayasa Hira,Hafsat ta dawo ita na Tura ta shiga kasuwa ta siyo min kayan da bani da shi na kunin Aya da zobo sai na Hada Turaruka ina da nayin Dilka na Halawa ne ta siyomin.
Yaya Ishaq na da sati biyu da Dawowa na Fara sana'ata,yana shashensa bai fito ba sai dai komai ina yi masa,fita ko sai dai yaje gidan mama da daddare ya Dawo,tun Safe da na tashi ban koma ba ranar sau biyu nayi zobo Safe da Yammah Saboda yan sari ko da ya fito da yammah ya ganni ina ta Jera Robobin a katon Frezer na bai min mgana ba,nima ban yi masa ba yadai ce zai shiga gidan mama nace a dawo lafiya.
Ina matukar Tausayamai Saboda akwai Tausayi ga wanda ya samu karayan arziki da kuma rasa aiki,Tunanin inda zamu koma nake yi, saboda ina lissafin saura Kwana goma Wa'adin da suka bamu ya cika yadda bai min mgana ba nima na zura masa ido ranar da yadawo yake fadamin abokan aikinsa daga Abuja zasu zo su yi mai Jaje akawai abincin da zan iya Dafa musu? nace muna da Cefane sai ya kalleni cikin mamaki kafin yace"Wa yayi muku cefanan..?
Kai tsaye nace"ni mana"
Cikin karin mamaki yace"ina kika samu kudi..?
Ina Yar dariya nace"Baka ga ina sana'a ba ne..?
Sai kuma yayi shuru bai kara mgana ba,washegari suka zo sun kai su goma
Hafsah bata shiga makaranta ba ranar ita ta tayani muka yi musu abinci mai rai da lafiya na hada musu da Kunin Aya da zobo na da ke saidawa.
Suka ci suna ta santi,Daganan gidan Mama ya kaisu sai dare ya Dawo,kwana uku tsakani yace min Mama ta kirasa kan mganar gida zai je yaji,da zai tafi na basa dubu daya nace yayi na adaidata sai yaki karba wai yana dashi ni nasan bashi da shi,bazai karba ba ne sai na kyalesa na cigaba da Harkan gabana.
Daya dawo daddare karo na farko Tun aure na da shi ya taba zama ya yi shawara dani,sai ranar wai mama nata saida kayan gidanta na wuta da kayan katako tana so ta had'a kudin gida ne muma tace abunda zamu Dauka mu fara hade su waje daya Sauran sai a saida su.
Ni ko sai naga kamar tsarin bai yi ba na kallesa nace"Ni ko da zaka bada shawaran da kudin da za'a siya gidan da zamu zauna me zai hana mu kama Haya na shekara daya..?kada ka manta akwai Hidima fa gata abinci gata yau da kullum ga na Makaranta da Dawaniyar yara ga Jamal yanzu yake aji Hudu Badariya wannan Shekaran zata gama ga Laluran Mama duka suna kanka ne shine naga sauran kudin in aka kama Haya sai a toshe wasu ramukan da su ko ya kagani..?
Sai yayi shuru yana kallona kafin yace"Kuma fa Hakane Fa'iza ni sam ban yi wannan tunanin ba"
Har acikin raina ni na fadi ra'ayina ne ban dauka zai ji mgana ba ta sai ga shi har su Maman da ya kawo mganar sai suka aminta,Mun fara shiryen shiryen tashi,na hada kayan da zamu Dauka wadanda kuma za'a saida aka fitar har da Tsoffin wad'anda na fitar duk aka saida su gabad'aya.
kayan bangaransa yace a saida su duka,Katifa kadai yace za'a bar masa ta ishesa ni dai na ware gadona da na yara sai kujeruna sai kayan sana'ata da kayan amfanina na Kitchen, sauran kuma aka kira Dilallai suka yi musu kudi hakama gidan Mama kusan rabin kayan duk sai da su akayi abun akwai tausayi sosai
Yan'uwa ma sun mana kokari Goggo ashe bata zauna ba ta saka ya'yanta suka hada kudi Dubu dari ta kawo tace a kara ita Hajiyar Dalan ma ba wanda ya kara jinta Ina gani Yaya Ishaq nata sunne kai kunya duk ta kamasa.
Da kudin da Anty Binta ta hada da wanda mijinta ya taimaka harta Dangin mama suma sun taimaka aka Hada Miliyan Daya da rabi da su,aka samu gida acikin gari sai kuma Allah ya saukaka mana abun kusa da makarantan yara ne, ko ba abun hawa zasu taka da Kafarsu,Gida ne flat na daidai misali,Shashen Farko falo da Bedroom guda uku sai Kichen sannan kowani Daki akwai tiolet sai dayan Shashen Bedroom biyu da falo ba kitchen sai tsakar gida sai daga wajen Koridon kofar waje akwai wani Daki sai akace Jamal zai zauna anan.
Tun kwana Biyu kafin Wa'adin ya cika kayan mu suka fara yin gaba mu zamu zauna a mai Dakuna uku, mama kuma da Badariya zasu zauna a dayan Shashen,Allah sarki Rayuwa Daman KANA NAKA ne shima Allah ya riga ya gamasa nasa,ranar da zamu tashi yara nata murna zamu tashi,har gwara Amir shi ya fi so wayau.
Ni kaina sai da nayi hawaye inda ka saba da kewar yanayin rayuwa su Sa'adatu duk da su muka kwashe sauran kayana sannan nace don Allah ta gwada sana'ar zobo saboda mutanen dake barayin kada ciniki ya Gudu bayan na tashi,tace in sha Allahu zata jaraba.
Su Mama su ma a ranar sukayi parking din komai,Goggo bata zo ba ammh Anty Nasara tazo ita da Yaya Asiya muna tare da su da Hafsat da makota na bangaran su mama kuma yan'uwanta da su Anty Binta.
Yaya Ishaq da jamal su suka samo motocin da suka kwashe kayan suma sai da suka Chaji kudad'e masu yawa.










*Janafty*
*KNKB2003*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Kafin mu karisa chan gidan sai ga Matar Yaya isa tare da kanwarta,Yaya mariyasa nasan bazata zo ba.duk da ta bada uzurin bata jin dadin jikinta,ammh ni nasan dalilin ta.
tare da su da makotana su Sa'adatu muka tare a daidaita zuwa anguwar Ajiwa,koda mukaje mun iske su Mama achan,Gidan mai kyau ne saboda sabon gida ne sannan wanda ya zauna agidan bai dade ba ya tashi. kuma basu lalata gidan ba,ammh dai yaya Ishaq ya sake fenti ya gyara bayika sannan an gyara glop din wuta in da suka samu matsala shi kan shi da'n wannan gyaran sai da ya ci kudad:e sosai.
Mun iske su Anty Mahma har sun gyara barayin da mama zata zauna,bata dawo da wasu kaya ba Falon kujeru biyu aka saka sai cafet. sai Dakin Badariya katifa da Wardrope sai kayanta, Dakin mama ne aka jera mata gadonta da wadrope dinta,Da muka zo sai da muka shiga Shashen Mama muka ga waje muka saka albarka yara daman tuni Jamal ya taho da su nan muka iske su sun warware suna ta murna abun ka ga yaro Amir ne kadai muka zo tare da shi.
Da taimakon Anty Mahma da su Yaya Asiya suka share bangaren da zan zauna suka gyaramin, sun maidamin kujeruna a falo da Cafet sai tibi. wanda naso a had'a a saida Yaya ishaq yace a barta tunda an saida na bangaransa,Duka kayan kitchen dina sun koma Saboda yana da girma har babban Freezerna,na kasuwanci ya samu waje da Buhu buhun robobina da sauran aya da ta ragemin sai Ganyen zobo da sauran kayan abincin da muka dawo da su, suka jeramin a Store din kitchen sannan suka gyara Dakin Yaya ishaq kusa da Dakin yaran ne da aka jerama gadajen su da wadrope din su,Shima katifa ce kadai sai akwatin kayansa sai Cafet karami na tsakar daki ni kuma suka maidamin gado na da sauran kayyakina kafin yammah waje ya fito ya yi kyau suka wanke tsakar gidan tas ya bushe gwanin ban sha'awa abun da yafi burgeni ta bangaran shashena akwai Daga gefe wani karamin Rumfa kamar na shan iska inda a raina nace zan rika hada hadar da sana'ata a wajen.
Hafsatu ta yi abinci na saka aka dibar ma su mama,aka akai musu da shi,Saboda Dare dukkan nan suka kwana Anty Mahma ce ta koma gidanta har Anty Binta nan ta kwana Yaya ishaq kuma suka kwana Dakin korido shi da Jamal, sai da safe bayan an karya suka fara shirin tafiya.
Yaya Asiya da Anty Nasara suna min fada da nasihan kan sai na ninka Hakura na wajen iya zama da mama, in a baya zama bai had'amu ba yanzu kuma ya had'amu sai na zama mai Taka tsantsan da kiyayewa.
Ban ce musu komai ba. ammh ina ji a raina zan iya zama da mama a kowani Hali ai ni ba bakuwar cin mutumcinta ba ne  na riga na saba da Hallayarta na zauna da ita tsawon shekaru fin biyar naci wahalarta bayan kuma na auri Dan'ta ban tsira ba, to ban ga abunda zai bani tsoro akan hallayar Mama ba.
Kafin azahar suka koma karofi narakasu har bangaran Mama suka mata sallama bamu fahimci yanayinta ba,sama sama ta amsa tare da yi musu godiya,sai da suka tafi naji wajen yayi min bambarakwai irin baka Saba ba Hafsah dai tana ta kara gyara dakunan,su Anum kuma suna ta Murna Musty har ce min yayi"Umma ina son sabon gidanmu'
Nayi mai mirmishi kawai ban ce komai ba araina ina jinjina yarinta Amir ne kadai yasan halin da ake ciki Anum kuma uwar Shiriritace Dadi suke ji ganin har da Mama ta Dawo gidanmu da zama basu Dakinta basu Shashen da muke basu tsakar gida suna murna,Abu daya yasa gidan ya sakeni Burgeni akwai ruwa sosai domin akwai Famfo a tsakar gida, sannan suna da wuta kamar anguwan da muka taso,sai dai ita wannan anguwan tafi cika da mutane daidai misali ba kamar na masu  hali da dukiya ba.
kwanan mu biyu a gidan sauran kud'aden da suka rage Hannun Yaya Ishaq ya yi mana siyayyan kayan abinci da su, da suka dawo siyo cefanen kayan abincin.Dakin Mama suka sauke komai ina cikin Dakin yaran ina gyara musu kayan da yake duk an hada kayan ne waje da'ya basu raba musu ba, ni kuma da na samu natsuwa sai na zauna ina ware ma kowa nashi ina saka musu a inda ya dace.
Sai ga Anum tazo kirana in ji Daada na kalleta cikin mamaki sanin baya nan tun safe ya fita cikin yanayin mgana nace"Ina Daadan yake..?
Kokarin hawa kan kayan da nake kan gyarawa tayi na hanata ina Hararanta sai ta juya tana Tura baki kafin tace"Yana Dakin Mama"
Jin haka yasa na tsaida abun da nake yi na fita falo na Dauki Hijabina Hafsah na zaune a kasan cafet tana Duba Littafinta Amir na gefenta kamar yana gane me take rubutawa na Fice ina fadin"ina dakin Mama"
Suka bini da toh da sallama na shiga,Na iske Mama zaune kan kujera jamal na gefenta yana danna waya Yaya Ishaq na nesa da ita ga kayan abincin nan a falon ta Badariya bata nan taje gidan Anty Binta da Safanan.
Har kasa na duka na gaida Mama da gida ta amsa a Dake kafin ta kalleni tana fadin"Kayan abinci ne ya rikita da Sauran kudin da suka rage a hannunsa ya siyo.Shine yayi mganan za'a sauke a bangaran ki zaki rika Dafawa kina bamu nace ya kiraki gaki ga shi ga ni,ki fad'a da bakin ki in zaki iya dafa mana abinci kina bamu bana son abunda raina zai rika baci Daga baya"
Kalamanta sai suka bani mamaki na Dago ina kallonta shima na juya muka Hada ido sai ya Dauke kansa nima sai na maida kaina kasa cikin Ladabi nace"Ai mama ko ba na auran Yaya Ishaq kina da hakkin da zan dafa abinci na baki indai muna zaune waje d'aya bakomai bazai gagara ba, da yardan Allah"
Kai ta daga sama kafin ta karkace kai tace"Shikenan a kwasa a kai dakin ki"
Har na mike zan fice tace"Sai a bi a hankali kin dai gani ba irin baya ba ne lokacin da akwai, yanzu babu. sai kiyaye da barna Ahto"
Ban ce komai ba na fice a raina ina mamakin Mama yadda bata kaunar taga na zauna lafiya cikin Aminci sai ta Kirkire wata mgana da zata zama cin Fuska a gareni.
Jamal ya shigo da kayan ina Dakina Hafsah ta leko tamin mgana nace ta gwadamai inda zai saka su,Ita ta nuna mai Store ya shiga ya jera komai ba wani abun sakawa a fridge sai kayan miya,sai kayan lambu da suka siyo ba su da yawa,Tun daga ranar ni nake abinci Safe da rana da yammah har Dakina nake  kai ma su Mama cikin wata Cooler mai girma yadda zai ishe su ita da jamal da Badariya,Ni kuma na ji da Yara sannan da Babansu kamar yadda wahalan komai nasa ya dawo wuyana yanzu tunda yana gida bai fara fita ko'ina neman aiki ba, kamar yadda yace zai fara fita ya gani ko za'a dace.
Da kaina na shiga makotan mu gidajen da ke kusa damu muka gaisa na gabatar da kaina a matsayin makotan da muka dawo anguwan cikin Satin da ya gabata, na daina barin kaina Cikin Duhu tunda na san shiga mutane nada Dadi ban kara yarda na zauna agida ba.
Duk kuma inda na shiga sai yi musu tallar ina Saida zobo da kunin aya, sannan ina hada Turarukan wuta na Daki da Humra da kwallacha sannan ina Dilkar Amare na gyaran jiki,Sai girke girken suna biki ko walima na kuma ce su min tallah wasu har suna tambayata ko akwai zobon nace ban fara ba tukunnah,sai mun natsa agidan, sannan sun tabbatar min da zasu siya Insha Allahu sai naji dadi kwarin gwiwa ya shigeni Duk daman masu sari ta wajena basu hakura ba sun ce duk inda nake zasu biyo ni su siya Saboda inganci zobo na da kunin Aya na.
Su Anum sun koma makaranta ba nisa da safe ko Yaya ishaq ya rakasu su tsallaka titi ko Jamal,watarana har Amir ko Hafsah,Amir ne kadai ke gida shi da zai fara Junior section ga ba kudi ammh ina iya bakin kokarina ina so ya fara zuwa da wuri kafin wannan zangon karatu na farkon ya kare.
Muna da Sati Biyu da dawowa Sabon Muhallin mu na cigaba da sana'ata Ranar tare da su Hafsah da Badariya suka taimakamin muka hada zobon da kunin Aya,ta waya na kira masu sara,bayan yayi sanyi chan da yammah suka zo suka Dauka Mama sau daya ta leko komai batace ba ta tabe baki ta koma ciki Sannu Sannu sai ga shi an fara ganeni ana zuwa Siya,ballatana anguwan akwai Dandali na matasa sosai tunda suka gane shikenan da yammah haka nake Ciniki sosai,Daga Mama har Uban gayyar basu taba ce min ba nima ban ce musu ba ina kokarin kiyaye abunda zai saka a tozartani.
Jamal zai koma makaranta,ga kudin mota ga pocket money da kudin kayan abinci ga kudin makaranta Haka ma Badariya,Anty Binta tazo ranar sun dade a daki suna tattaunawa dukkansu sai dai har kwana Biyu ba wani mafita,Na lura shi kan shi Hankalinsa duk ya tashi a ranar suma su Anum aka basu takardan tunasarwan Biyan kudin makaranta Saboda damuwa abinci daren sa ma yadda na kai masa haka na koma na dauke sa bai ci ba,Da safe ma ruwan buni kadai ya sha ya fita ashe gidan Anty Binta yaje itama duk bata da wani kudi duk da su ta kwashe aka rufa asiri,Ammh tace ta ma mijinta mgana zai biya ma Badariya nata kudin makaranta sai dai a nemo na jamal ita zatayi kokarin nema mai na abinci kafin Lokacin tafiyarsa.
Haka naji yana Mama bayani da Daddare da ya dawo ni kuma na shiga
kai mata abinci.Mama tayi tagumi duk ta shiga damuwa kawayen nata da take takama da su,Duk sun janye daga gareta daman sai kana da shi ake yi da kai,Sannan itama babu jarin yin kasuwancin komai ya tsaya ita kanta duk ta rame ta Fige alamun ba natsuwa ba kwanciyar Hankali.
Sai da yadawo bangarena na zubo mai abinci naga ya kasa ci yayi Tagumi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login