Showing 33001 words to 36000 words out of 82431 words
Tausayi wane ni na manta da Badariya da Sanadinta na samu Rufin asiri, batare da sanin kowa ba na bata Dubu goma nace zan cika mata in na samu shima Dubun goma Sa'adatu ce chan inda muka taso ta samo min wata mata mai son Turare Humra,to da yake ina da Sauran kayan amfani sai nayi mata amfani da shi na samu ba laifi,Sai na koma ina Fafutukar yadda zan sama mata cikon sauran ga shi kuma salla ya matso,Allah ya taimakeni na samu aikin zobo da kunin aya na masu son da yawa da sallah dakyar na had'a mata dubu biyar na kara mata godiya har da kuka ta Rumgumeni tana fadin"Nagode miki Anty Fa'iza yadda kike jin kanmu Allah ya baki wanda zai ji kank'i watarana Allah ya Dauwamar da farinciki da arziki da wadata acikin rayuwarki gabad'aya"
Na amsa mata cikin fara'a ina Fadin"ke meye na kuka share hawayen ki ko sai na kira miki Ya'yan ki ne..?jin haka yasa ta goge Hawayenta,ni na hanata nace ko yayanta kada ta fad'amawa ana saura kwana Hudu sallah tazo da murna tana Fad'amin Hajiyar su Raliya ta biya mata kudin sannan ta bata dubu goma tayi dinkuna sai tace zata maidamin da kudina na riga nayi niyya sai na karbi biyar din da na bata Daga baya na barta mata goman nace tana da bukatu tayi amfani da shi,Badariya ta yi murna tayi murna kamar bakinta zai yage addu'a kam na shata ni ko tana da Muhimmancin da bazan manta da alherinta gareni ba.
Atamfa taje ta siyo da less sai mayafi da takalmi da jaka,Sai kayan shafa ina D'aga kayan ina fadin"Ehee! kaga yan mata."
Tana Dariya tace"To Anty Fa'iza mace sai da kwalliya mazan nan, kuma suma kyale kyalen suka fi so"
Na aminta da mganarta yasa nace"Hakane Allah ya kawo miji nagari"ta amsa tana rufe fuska ni kuma ina binta da Dariya sai da Yaya Ishaq yaga kayan ne ya tsareta sai ta fad'amai gaskiya kallo na yayi yana fadin"Lalle kina da d'aure ma karya gindi ke baki bukatar kayan kwalliyan sai ita..?
Ina dariya nace"Me Fa'iza zata yi da kayan kwalliya ai wannan sai irin su Badar mata masu kyau da nasaba"
Ita Badariya bata gane mganata ba sai ta karb'e da fadin"Kai Anty Fa'iza wlh kwalliya bata zaba bace.Mu mata kowa yasan yan ado ne da kwalliya"
Shi kuma da yasan kan mganata sai yayi gum ya koma yana kallona ni ko na basar da shi,Daga ni har shi bamu san Zainab da yara zasu zo mana sallah ba,Mun samu tallafi shinkafa da naman sallah Daga gidan Hajiya Daga Korofi kuma Goggo ta aiko mana da kaji da kayan miya mangyada su maggi da sauran Cefane,an yi idi lafiya an sauko ranar nayi mana shinkafa da miya sai nayi mana cowslow,Sai zobo da kunin Aya Saboda Sallah Jamal ma ya dawo da da bai da kudin mota, yayan yace ya zauna chan yayi sallah nace hakan bai kamata ba na hada dubu hud'u aka turamai nace ya taho gida yayi sallah cikin yan'uwansa.
Ranar idi da yammah sai ga Direba ya kawo zainab da yara,Gida sai ya Rud'e da Murna su Anum nata tsalle da Murna ganin kannensu Farhan na ganina ya Nufeni bakinsa har kunne yana fadin"Umma.."
Na daukesa na daga sama yaro kamar balarabe wajen kyau yana bangalamin Dariya nace"Farhan d'an Umma"
Tazo da naman sa an soya tare da naman kaza anyi pepe dinsa ga su cake samosa da su sprill role, ta zo da kantan kantan na lemuka da biskit, ta ce min Saboda sallah ko kuma in mun yi baki,Nace mata"Angode. Sai dai gaskiya sai kunin aya da zobo ya kare tukunnah"
Tana dariya tace"Ga abun arziki wazai bi ta na kwalayen bature masu shegen zaki"
Ishaq basa gidan shi da jamal sai dai suka dawo suka ganta kuma daga alamu uban gayyar yaji dadin ganin matarsa, Dakin mijinta na Sauketa,Yaran kuma suna tare dani Direban daya kawo ta bai koma ba. tace zai tsaya sati d'aya zasu yi zai maida su sai aka sauke sa Dakin Jamal.
Sosai wannan sallar tayi mana Dadi,babu abunda yafi kwanciyar Hankali Dadi ni nake hidiman abinci na gida da na yara, Zainab sai da tana tayani da Hiran duniya,Farko da na sauke Zainab a dakinsa samu na yayi yana min mgana wai meyasa sai Dakinsa na sauketa,dakina fa..?
Na kallesa ina fadin"Saboda mene?sai mu gamutsu da ni da ita da Anum kamar ba bu wani da'kin..?
Kuma nan din ta saba sauka in tazo a Dakin naka shi yasa na sauketa anan"
Sai kawai ya juya yana fadin"Ki bude dakin Mama ki sauketa anan mana"
Mamaki ya bani Namiji sai a barsa da gulma ya gama wannan borin kunyan, sai ga shi suna kulewa a daki bamai jin su ammh yazo zai min dad'in bakin su na maza.
A gida muka cinye sallar mu sai ranar washegarin sallah da kwana uku Zainab ta matsa sai na shirya mun fita. da zamu tafi,na saka atamfata da Hajiyar su Raliya ta dinka min,Zainab tace ban isa ba ta dinka mana Less mai kyau iri d'aya,har dinki daga Abuja aka dinko ta matsamin sai na saka Saboda kada tace ko ban karb'i kyautar nata ba ne,yasa na saka Doguwar riga A shape dinkin ya fita haka ya fitar min da Shape dina in kika ganni a lokacin bazaki taba yarda na haifi Yaro dan shekara sha biyu kamar Amir ba.
Ina nan da kuruciyata sai dai kowa yasan Fa'iza yar gargajiya ce,ammh zainab bata barni haka ba,Hijabi na saka tace ban isa ba Dole na Dauko mayafin data aikomin da shi da Takalmi da jakata na saka,sai gani na fito ras dani na yarda da Hausawa da sukace kowa ya gyara ya sani ni kaina sai nake ganin kamar bani ba.
Zainab ta kalleni sama da kasa kafin tace"Komai yaji ban da abu d'aya"
Ina dariya nace"Ban yi kyau ba ko..?
Sai tace"Aa fa.Lalli ne yayi miki cikas"
Sai kawai na wuceta ina fadin"Lalle ai naku ne na fararan mata yan gayu"
Domin tayi nata Hannu da kafa, abun ka ga farar fatar kamar don ita aka fito da zanen jan kunshi tana bi na a baya muka fito daga daki Lokaci daya tana fadin"Wlh ko ke kika yi ba karamin kyau zai yi miki ba Maman Amir"
Ina jinta ban ce mata komai ba, ina jan abu zai fito a wannan bakar fatar tawa ina fitowa yaran na Falo suka dago suna kallon mu sai kawai Anum da Amir suka hada baki wajen fadin"Laa! Umma kin yi kyau wlh.."
Musty da Ahmad ma suka karb'a Farhan na jin haka shima yace"Umma jin yi kyau"
Fadil na gauranci yace"Chauu.."
Gabadaya muka saka Dariya,Ni na sabe Fadil na rike yaran duk sun ci yan kanti mazan kaf iri d'aya Zainab tayi musu Anum kuma an cakare da Doguwar riga da takalmin yan gayu Badariya ta kaita akayi mata jan kunshi da kitso da yake bata dauko suma na ba,tana da gashi an yi kitson gaba yaji bit sai yanga take da farko ma kin saka Hijabi tayi sai da nayi mata jan ido,Zainab ta hana sai ta Dauko mata wani karamin mayafi ta nad'a mata, muka fita daman ta fad'ama megidan zamu fita gari gidan Anty Binta mu gaisheta yace to.
Ban kulle dakin ba tunda suna waje da Jamal jakata na Hannun Amir na Zainab na hannun Anum ta kama ta rike in ka ganmu bazaka taba cewa muna cikin wani hali ba,ko mijin mu bai da aiki ba kila in an fad'a maka ma bazaka yarda ba.
Suna tsaye suna mgana da Jamal yaran suka fara fitowa ganin su shar da su yasa yafara washe baki Jamal ne yace su jere a dauki Hoton Tarihi ko da muka fito har Baban duk suna ta Hotuna Zainab ce a gaba sai ni a baya ina rike da Fadil zainab nata min Tsiyan na nad'a mayafi a kaina,nace mata ban iya saka shi a saman kafad'a ba ne.
Tunda muka fito idonsa ke kaina kallo kamar zai fad'i,har yana wani bude ido sai ji nayi kawai ya kira sunana"FAA'IZAAA...!
na dago ina kallonsa Fadil dake ta mika masa hannu alamun ya Daukesa bai ma gansa ba ya saki baki da hanci yana kallona Ya nuna ni yana fadin"Fa'iza ke ce.?
Sai dariya ta kamani nace"Ba Fa'iza ba ce Wannan Uwar Fadil ce"
Sai nan ya gano abun da yayi sai ya fara sosa keya Jamal yayi dariya yana fadin"Matar bro ba bro ba,koni ban gane ki ba da farko".
Hararansa nayi ina fadin"Uhm ka manta ne"
Karaf ko Anum tace"Daada yaga Umma tayi kyau ya saki baki yana kallonta"Zainab ta kwashe da Dariya tana fadin"Yes my Daugther"
Sai kunya ta kamani na sadda kaina ya matso ya karbi fadil daga hannuna ammh sai da ya gogi jikina Lokaci daya yana fadin"kin yi kyau,Sannan kamshin yayi dad'i"
Sauran Humran da nake hadawa ce in ta ragu sai na ijiye ban ma cika shafawa ba yau ma Zainab ce ta matsamin sai da na shafa,da sauri nayi baya ina yake sai ya basar ganin Zainab kusa dani sai ya kalleta yana fadin"Matan Abuja sun yi kyau"
Hararan soyayya tayi masa tana fadin"Ai yanzu ta zama matar katsinawa"
Dariya mukayi gabad'aya Fadil ne ya fara kuka yana mika hannu muna juyawa muka ga yara har sun rigamu shigewa mota nayi dariya ina fadin"Dole fadil yayi kuka yaga za'ayi masa kan ta waye"
Mikamin shi yayi yana fadin"Sai kun dawo, kada kuyi dare jamal fita zai yi ni kad'ai ne agidan"
Zainab ta wuce tana fadin"Honey sai fa mun zaga gari ka ma yi hakuri kawai"
Ni dai ban ce komai ba muka shige mota wata bakar Jeep ce kaf ta Daukemu su Anum an kame agaba kamar motar gidan su dariya ma tabani,Gidan Anty Binta muka fara zuwa mun iske har su Anty Mahma,suna gida sun yi mamakin ganin mu dukkanmu a tare sannan cikin shiga mai kyau Anty Binta haka take ta kallona kamar idonta zai fad'o ina gaisheta ta amsa min cikin wani yanayi.Anty mahma ko ihu ta Buga tana fadin"ku zo ku sha kallo wajen Hajiyar Zobo da kunin Aya"
Badariya na gidan tace"Kin manta harda Turaran humra da kwallacha"
Dariya suka bani Zainab tace"Maman Amir yadda kika san bata haifi Amir ba"
Anty mahma tace"Fa'iza nada jiki mai kyau gaskiya"
Mun dade agidan kafin mu yi sallama Anty Binta dai sai kallo na take har muka tafi, sun yi mgana da zainab tace yaushe tazo tace shekaran jiya Daga gidanta Badariya ta biyomu muka taho tare da ita,jin nace har gidan hajiya zani mata yawan sallah.
Ba gidan Hajiya mukaje ba da muka fita ba,sai da muka fara zuwa anguwan da muka tashi. Allah sarki gidanmu an buge sa ya zama sai Filin gwamnati Sa'adatu da Habiba sun yi murnan ganin mu sosai,na kullo musu nama da lemu da Zainab ta zo mana da shi, duk wanda yayi maka mutumci kada ka manta da shi, gidan Hajiya sai yammah muka je bata gidan sai su Raliya da yayyinta da suka zo sallah, ammh sun kirata a waya nan muka yi sallar mangariba muka ci abinci sai gata ta Dawo tana shigowa su Anum suka nufeta suna oyoyo Hajiya ta tarbesu tana fadin"Oyoyo Ya'yan Hajiya"
Zama tayi muka gaisa Zainab ta gaisheta ta amsa sai na gabatar mata da ita sai ta kalleta tana fadin"Maraba da Fa'iza da Zainab naji dadin wannan ziyaran Allah ya hada kawunan ku"
muka amsa da Ameen ta karbi Fadil tana fadin"Wannan ne kama da yan sudan di'n fa..?
Ina dariya nace"Kanin Farhan ne"
Tana dagasa sama tace"Naga kaman su da Amadin ki".
Hajiya ba ruwanta tana da sakewa muna ta Hira da ita tun zainab bata saki jiki ba har ta saki yaran kuma tuni su Raliya sun jasa su cikin gida,duk yadda muka so mu tafi kafin isha'i sai da ta hanamu shi ko Babansu sai kira yake yi Zainab nace mai muna Hanya sai da muka yi sallar isha'i muka yi shirin tafiya ta bamu kyautan atamfofi super guda biyu,yaran kuma kudi sabbin yan Hamsin kowannen Bandir d'aya Badariya kuma tace ta dawo ta karb'i nata Sakon har haraban gidan ta rakomu ita da ya'yanta da sai tambayan Hajiya suke itace Fa'iza me Turare da dilka..?.Sai Hajiya tace itane sai kiga wad'anda basu sanni ba suna gaisheni cikin girmamawaa.
Sai da muka kamo hanyar gida sannan Zainab tace min"Yar'uwan ku ce Hajiyar nan..?
Na girgiza kaina ina fadin"Aa sune shugabannin wata kungiyar taimakon mata da marayu,wad'anda suka koya mana wannan sana'ar da nake yi. sanadin haduwar mu kenan sannan Raliya diyarta kawar Badar ce"
Sai ta rausayar da kai tana fadin"Tana da kirki sosai"
Na jinjina kai ina ba'a mgana,hirar ta muka rika yi har muka isa gida,Badar na fad'in irin kudin su ya'yan Hajiya manya maza duk ma'aikan gwamnati ne,matan ma suna auran manyan manya a garin katsina,itama aiki take sannan suna da manyan kungiyoyin mata na taimakon mutane"
Ko da muka koma Gogan ya cika saura Kiris ya fashe sai hararan mu yake yi,Zainab tace"Honey mun dawo"
Yana kwance kan kujera yace"Na ganku,sannan ku da zuwa sai a tube a sama min abunda zan ci"
Ina kwantar da Fadil da yayi barci akan kujera nace"Yunwa kake ji.?ina abincin da na bar maka a kula..?.
Yana daga kwancen yace"Ban yi ra'ayin ci ba,sabo nake so"
Ni da zainab muka kalli juna sai ta zauna wajen kafafunsa tana fadin"Maman Amir barayin ki ne wannan, ni bari naji da lallashi"
Ban damu ba,na shige dakina na sauke mayafina da kayan hannuna na shige kitchen. yaran kuma suna ta murna da Budirin kudin da aka basu suna nuna mai ya karb'a yana fadin"Tunda kun zama masu kudi kowa sai ya bani goron sallah"
Suka fara Dariya yana taya su bansan ya suka kare da Amaryansa ba, ni dai Shinkafa na sake dafamai sai nayi mai miyar albasa da naman kaza na kawo mai da maltina na iske suna hira da matarsa sai na shige daki nayi wanka na Sauya kaya na gaji ga barci yaran ma da kansu nace suyi shirin kwanciya,Fadil kawai na karb'a mukaje muka kwanta Farhan tare da su Amir zai kwana Anum kuma sai ta gama iyayinta zata shigo ta kwanta.
Mun so washegari mu je karofi ya hana,Sai da aka kara kwana sannan muka tafi gabadaya har da shi da Badariya da Jamal,sai dai su Goggo suka ganmu kamar daga sama mamaki da murna ya hana Goggo sakat sai fad'i take"maraba da bakin alheri. ni kadai da zaratan masu gida haka,Allah yasa kun zo da cefanen ku"
Amir ya zaro mata kudi yana fadin"Nawa kike bukata Tsohuwa..?.
Ta ko warce kudin tana fadin"Duka nake so"
Sai ya fara fadin'Ke ko goggo baki san wasa ba"
Gabadayanmu sai da muka yi Dariya Yaya Ishaq dai duk yaji kunya,Kansa na kasa yana gaida Goggo ita ko a Fuska bata nuna masa wani abu ba,Su Anty nasara duk suna gida aka gaisa sai fa alokacin wasu suka san Zainab da su Farhan,mune har gidan su Yaya Isa achan muka sallar la'asar daganan muka isa gidan Yaya mariya tayi mamakin ganin mu sai kallo na take yi cikin gatse tace min"To su Fa'iza dai akwai ki da son a sani yawo da kishiya"
Allah yasa zainab ta shiga ciki tayi waya,da Yaya mariya tamin baramb'arama a gabanta,ban bata amsa ba ta kara kallona tana fadin"Naga kin yi wani d'anye ne ko dai ciki kika kunso ne..?
Dariya na kwashe dashi ina fadin"Ciki? ai mun bar ma masu mazaje a hannu"
Dariya ta yi lokaci d'aya ta daki kafad'ata tana fadin"Oh Allah! ji yadda Fa'iza ta koma shekaru biyar bqya, wazai ce Fa'izan nan ce mai shuru shuru da an yi mgana ta hau kuka tana kuyi hakuri"
Tafad'a tana kwaikwayon mganata ni dai ina ta Dariya Hafsah na gidan daga barci ma ta taso na kalleta ina fadin"Sannu yar hutu gidan Goggon kenan..?tana sosa ido tace"Yau fa nazo chan hayaniyar yara"
Yaya mariya tace"To ai ga hayaniyar nan Fa'iza ta tattaro miki har da gayyar sod'i ba katin gayyata"
Sigina na rika yi ma Yaya mariya ammh ta nuna kamar bata gane ba,Allah ya taimakeni da Zainab din ta fito sai ta gyara bakinta sai dai Taki sakin jiki da ita sai ma had'e rai da tayi shiyasa bamu dade ba muka tafi sai ko ta rakomu har gidan Goggo nan suka had'e Da Yaya Ishaq akayi kallon kallo ta Dauke kai abun mamaki ammh shi sai yace"Mariya ba gaisuwa..?to ni bari na gaisheki tunda ta wani fanni ni kaninki ne an yi salla lafiya ne ?
Ba ita ba har su Goggo sai da suka yi mamaki sai dai ba wanda ya nuna hakan,Yaya mariya ko da lafiya ta amsa mai kafin ta Dauke kai, daman taji labarin sa a wajen Hafsah kafin ta tafi sai da tajani gefe tana fadin"Ke naga wannan wawan mijin naki na wani rawan kafa akanki saboda yaga yanzu ba shi da komai, kina sana'a kina yi mai wahala to in kika sakar masa ke kika sani,kada dai ki manta da abubuwan da suka faru a baya wlh kada naji kin sakarmai ki bari sai ya samu aiki yi in har chanjin na gaske ne sai ki gani"
Ban ja da nisa ba nace mata toh kawai nasan halinta yanzu ina ta wata mgana sai ajimu daga waje,
Kafin mangariba muka tafi,da Tsaraban su gyada da aya,Sannan na taho da ayan na da ganyen zobon da Goggo tace na bada kudi ayo min Sautin su a kauye anfi samun sauki,To shine na ba ma Hafsah da zata zo ta zo mata da kudin, shine na dauko kayana ita dai Hafsah tace sai ta kara kwana biyu zata dawo.
Tunda muka dawo bamu sake fita ba muna gida muna warware gajiya,Zainab sati daya tayi ta koma Abuja ni kaina sai da naji kewa ballatana yara da suka saba da kannensu,shi ko Yaya ishaq ranar da ta tafi har ce min yayi yaji dadin tafiyarta kila na sauraresa yanzu kai namiji sai a barsa, nan yake shigewa daki da ita fa yana amfana ammh baazai yarda ba sai ya yi dadin baki.
An gama Hutun salla yara sun koma makaranta Mama dai taji dadin yamai bata dawo ba,Hafsat ta dawo saboda makaranta,Badariya kuma na gidan Anty Binta tsakani da sallah ba Dadewa suka yi graduation na gama makaranta,Raliya har walima Hajiya ta shirya mata agida,an yi