Showing 9001 words to 12000 words out of 82431 words

Chapter 4 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

190

naji ya bani Tausayi Namiji har namiji ammh lokaci kadan ya nemi ya susuce,batare da Tunanin komai ba ko shawara da wani ba,ina da kudi a banki na sun kai dubu dari da Hamsin daman shawaran Yaya Isa nabi da ya ce na tara wani abu ko Fili na siya kaddara ne saboda watarana,Washegari da Safe na bama Hafsah Atm dina zata tafi makaranta nace ta ciro kudin dake ciki Duka ita kanta tayi mamaki sai dai bata tanka ba.
A hanyar dawowarta ta tsaya ta ciro kudin Dubu Dari da ashirin ta bani na adana su sai da Daddare da ya dawo Futu futu daman ya Dauki Takardunsa ya fita,Ko da ya dawo ya gaji salla ma acikin gida yayi ta ya kasa fita tun safe bai ci komai ba,Ruwan Citta da kunfari na Dafamai yasha cikinsa ya warware sannan ya Dora da abinci.
Inda na fahimci damuwa ta masa yawa su Anum tana kiriniya bai bi ta kansu ba sai na saka Hafsah ta tarka su zuwa Dakin su nace su Dauko Littafan su,kafin su kwanta
Sai da suka bar Falon sannan na shiga Daki na fito mai da kudin hannuna na basa da farko kin karb'a ya yi sai da nace ya karba sannan ya karba cikin mamaki yana fadin"Wannan kudin fa Fa'iza.?
Ina zama nesa da shi nace"ka biya ma Jamal kudin makaranta shi da Yaran nan, zaman haka bazai yuyu ba tunda an fara sai a karisa"
Sakin baki yayi yana kallona Lokaci daya yana kuma kallon kud'in bakinsa na rawa yace"Duka wannan kudin Fa'iza na waye..?
Kai tsaye nace"Nawa ne dubu dari da ashirin ne Allah yasa zasu isa"
Kai tsaye ya maidomin da kudin a gabana yana fadin"Bazan karb'a ba"
Nima sai na turamai ina fadin"Kayi hakuri ka karba dukkanmu bamu da zabi ne"
Sai yayi shuru ya kasa mgana,cikin wannan shurun ne wayarsa dake gefensa ta dau kara ina gani ya Duba yaja tsaki ya kashe haskenta ya mike daga zaune ya koma kan kujera yana fadin"Fa'iza duk ina kika samu  kudad'e haka?
Cikin mamakin Tambayarsa nace"Ina sana'a ai ka sani"
Yana kallona yace"wata sana'a kike yi haka da ta ke kawo miki kudad'e haka..?
Ina yar dariya nace"Kunin Aya da zobon da kake sha kullum,to shine abunda nake saidawa"
Ido ya zaro kamar bai sani ba ahalin nasan ya basar ne ban bari ya kara mgana ba,na tashi da kudin na karisa gabansa na sauke mai saman cinyarsa ina fadin"Don Allah ka karb'a"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Dauki kudin yana fadin"Zan karba ammh ba kyauta ba,bashi.In na samu aiki na warware zan biya ki kudin ki"
Sai nace mai shikenan na amince nan ya zauna yana lissafin kudaden ya Dago yana cemin"Zai iya isa na biya ma su Anum kudin makaranta ammh Amir fa?
Nazari nayi kafin nace'Shi ka kyalesa gaba sai a saka shi in an samu"sai ya jinjina kai yana fadin"Nagode Fa'iza"
In yayi min godiya har mamakin sa nake yi tun ina mamaki har na daina adaran yaje ya fada'ma Mama kuma har aka bama jamal kudin ya koma makaranta ko mganar batamin ba nima don Allah nayi ban damu ba,daman  bana jiranta.
Bansan cewa zaman Hafsah a gidan nan na damun Mama ba, sai da ta kirani a gaban Yaya Ishaq tace yanzu ba da ba ne nasan ba shi da shi ammh na kara kawo mai Dawainiya ina ganin suma suna fama da kansu,Ni dai har tagama mganar ta ban ce komai ba ina mamakin me zaman Hafsah ya tare ma Mama..?ban da abinci bata cin komai agidan nan,kudin mota da duka Dawainiyarta da Sana'ata nake yi mata Yaya ishaq ne ya tare mganar yasa Mama ta kyaleni sai abun ya dameni a cikin raina kamar Goggo ta sani tace Ko Hafsah zata nemi Dakin makaranta ne ta koma, ni ko naga ina garin kamar bai dace ba da ma ace bana nan ne,shine ammh Tunda ina nan ta zauna a wajena ai nima ina moranta ta bangaran sana'ata.
Sai kuma korafi na biyu ne,mama ta fito da Tsirfan Masu zuwa a bani kunin Aya da zobo sun fara damunta ballatana da taga ina samun ciniki da yake akwai makarantar secondaryn Gwamnati ta mata dake kusa damu, tunda suka gane ni, shikenan arana sai na Dafa zobo fin sau biyu kunin Aya da yawa nake yi,Masu sari in basu zo da wuri ba sai dai su samu kad'an sai ta fara fadan ana damunta da Hayaniya sai na Fahimci bakincinta da na d'anta  take so na zauna ya kasheni ni ko nace araina, bazan miki Rashin kunya ba ammh kuma baki isa ki hanani sana'ata ba.
Amir ne ke taimakamin tunda yana gida sai Hafsah in tana gida Badariya ma ba'a barta a baya ba, Kuma Maman tana sha kuma in tayi baki ina basu,ammh bata gani ba tamin mgana ban ce mata komai ba shima ta same shi ta mai mgana inaga shi ya kashe mgana bata kara tara ta da mganar ba.
Ni dai na toshe kunnuwana na cigaba da sana'ata ganin wannan abun da tayi bai sa na dakata ba ko kuma shi Wanda take gani bai taka min Burki ba, sai ta fara fadin ina barinta da yunwa ina chan ina sana'ata sai rana ta take nake dafa abinci har da kwanciya ciwo sai da aka kai ta Chemist,ulcer ta kamata saboda zama da yunwa Anty Binta ta zo ta kirani dakin Mama ta na ta masifa Yaya Ishaq na jinta bai ce komai ba nima har ga Allah ban yi niyar mgana ba Saboda ni dai nasan ina dafa abinci akan Lokaci tunda na safe kafin tafiyar yara makaranta ne na rana kuma shi nake fara dorawa in na Dafa Zobon Farko na Dare kuma duk latti na bayan isha'i na gama abinci na kai mata ammh ban tsira ba.
Sai da naji Anty Binta tace zan daina sana'ar da nake yi tunda Saboda ita zan kashe musu uwa da yunwa sai alokacin na dago na kalleta ban ji tsoro ba nace"Gaskiya Anty Binta ki yi hakuri ammh bazan daina sana'a ta ba.Domin banga ta inda hakan ya zama Takura ba"
Sai ta saki baki tana kallona kafin ta kallesa tana fadin"Kana jinta dai ko..?
Rashin kunya zata min a gabanka baka ce komai ba..?
Sai ya muskuta kafin yace"Anty Binta mu bi komai a sannu in zaki ce mata ta gyara sai ki yi mata fada ammh babu Adalci mu hanata sana'arta"
Mama na kwance ta daga kai tana fadin'"Ki yi shuru Binta ta siye shi da kud'i tunda yaga ta fara nuna tausayawa garesa shikenan bai iya tsawarta mata"
Cikin mamaki ya kalli Mama kafin yace"Mama wannan wata irin mgana ce..?
Mama ta zabura ta mike kamar daman chan lafiyarta kalau tana fadin"ai gaskiya na fad'a kada dai ta manta kafin tayi maka uban ka ya fara yi mata gata, sannan ya rufa mata asiri, kaima kazo ka rufa mata,ka zama gatan ta, in adalci kuma zatayi ai jarin  ba Ita ta ginama kanta ba kai ka gina ma ta shi"
Da sauri yace"Aa wlh bani da hannun akan sana'arta ban san komai akai ba"
Anty Binta ta koma ta zauna tana fadin"Shiyasa naso na dauke Mama ka hana ashe zaka bari matarka ta gana mata azaba ne ban sani ba..?
Yaya Ishaq yace"Anty Binta ki bar wannan mganar matukar ina raye Hakkin kula da mama da su Jamal yana wuya na ne sai dai in ciwo ko mutuwa sun kwantar dani"
Ina zaune ina jinsu so nayi na tashi na fita ammh kada suce na raina su,yasa na zauna kaina na kasa ina tsintar wasu mganganun su.
Mama da ranta ya gama baci tayi Kyafci kafin tace"Ta gama da shi ne Binta shiyasa kiri kiri yaje ya Duba Zainab yaki zuwa itama ai tana da Hakki akansa wajen wata daya da rabi bai je ya ganta ba,wannan ai sai mahaifinta ya yi fushi da shi Tsakani ga Allah wannan bawan Allah babu abunda bai yi mana ba ammh nasara uban me ishaq ke yi acikin gidan nan da bai tafi ba"
Mamaki ya kasheni wato Zainab ce matar so ni sanda yake tafiya sai yaga Dama yazo ai bata taba cewa ina da Hakki akansa ba takaici yasa nayi mirmishi mganar ma ta gundureni sai ya kashe zaman nawa da cewa"Je ki abun ki Fa'iza"
Mikewa nayi na fice a raina ina fadin daman ya koma chan wajen zainab din domin da zamansa da akasinsa duk daya ne a wajen fa'iza ba abunda suke Tunani ba ne.
Bansan ya suka kare ba ammh sun kai ruwa rana domin ina jin tashin muryoyin su shi da Anty Binta ina Dakina bansan tafiyar ta ba,mama bata so ta gansa yana zaune agida gani take yi kamar wani abu yake min ko zamansa wani Dadi yake yi min,Abunda bata sani ba ni mantawa nake yi ma yana gidan tun safe in yara suka tafi makaranta zan kama sana'ata Amir na tayani in Hafsah bata gidan ita a tunaninta na tsare shi a Dakina ne yana bani wani abu tunda ta Furtamin da na shiga gaisheta washegari ta kalleni sama da kasa kafin tace"Ki sakar min d'a Fa"iza na rasa me kike son ya baki bayan wanda ya baki a baya ke ko gajiya da nanikan namiji bakya yi ciki ko goyo ne baki gaji da yin sa ba ko me..?
Mganarta sai ta bani Dariya sai da na Murmusa kai tsaye nace mata"Ko d'aya Mama haihuwa ai Fa'iza ta gama shi in dai a nan gidan ne na bar ma Zainab ita ya dace ta cigaba da tara miki Jokoki"
Tasan mgana na gayamata ammh sai bata kara mgana ba,ai kunyan marasa kunya a sara sannan tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazai nauyin yarfa sa da kasa ba.
Hajiyar su Raliya bata san mun sauya gida ba,taje camoron kanwarta zata aurar da Diya su Raliya kuma sun je lagos hutu gidan Yayan mahaifin su,suna dawowa suka hadu a makaranta Badariya ta fadamata ranar tare suka suka zo,a shashena suka zauna tare da Hafsah,suka ci abinci suna Hira Raliya tace Hajiya bata sani ba ammh zata dawo kwanan nan zata gayamata.
Mama taji Haushin shigar su Dakina da Raliya ta shiga mata sallama har da ni sai harara ta takeyi har tana fadin''Haka ake yi sai ki shigar da yarinyar daki ai ba wajen ki tazo ba sai ki bar ta da Badariya kawar tata"
Daganan na Fahimci Kishi Tsagwararon shu Mama ke yi da ni a baya don bamu zauna waje d'aya ba ne yanzu kuma Abun nata na fitowa ,Cigaba na ne bata so tafi kaunar ganin na wulakanta ko na Tozarta to ai ba ita ke da Rayuwata ba,in ita tana nata ne shi Allah kankat ne ya riga ya gama nasa tsarin mutum bai isa ya hana faruwar kaddara da ya Riga ya zana ba.
Ba'a rufe sati ba sai ga Hajiya Tazo Raliya ta rakota tayi ta min fadan meyasan ban kirata ba ni dai hakuri na bata,Tana ta kallon gidan cikin wani yanayi,da zata tafi ta bani Dubu Hamsi sannan taji dadin yadda sana'ata bai tsaya ba tace na cigaba da yi in sha Allahu watarana sai na bama kaina mamaki sai da zata tafi ta shiga Dakin Mama suka gaisa,Ta bata dubu goma mama nata godiya.
Har waje na rakata tace min Direba zai kawo min sako ba yawa,Sannan tace akwai Bikin diyar kawarta da zasu yi a kaduna tana tunanin kwangilan Hada turaruka ni zatace a bamawa sannan tana tunanin Amaryan zata zo gidan sai nayi mata gyaran jiki ina ta Murna daman ta wannan bangaran ita kan kawo min Costumer,sau daya na hada Turaren Rushi da na Humra da muka dawo gidan nan shima na riga na karbi kudin aikin su ne tuni yana hannuna.
Da Daddare naje kai ma Mama abinci sai da tambayeni a wulakance wai a ina nasan Hajiyar Raliya..?
Kai tsaye nace mata"Su ne shugabannin kungiyar da suka bamu tallafi bayan sun koya mana sana'o'in hannu domin Dogara da kanmu"
Sai ta tabe baki kafin tace"Ina ce sanadin Badariya kika santa?
Sai na daga mata kai sai kawai tayi tsaki kafin tace"Aikin mur in ji tusa."
Ban tanka ta na fice washegari sai ga Direba da kayan abinci shake da Mota Ishaq na gida Lokacin nayi mai bayani sai kawai ya kalleni yana fadin"ina fatan ba rokon ta kika yi ba ko..?
Sai abun ya bani haushi na wuce sa na shige daki ina fadin"To ba dole fa a fada masa ya juya da kayan kawai"
Daganan ko kara bi ta kansu ban yi ba, sai naga ana shigowa da kayan a raina nace abun ma iskanci ne sai da na natsa na kirata nayi mata godiya tace bakomai indai ina bukatar wani abu na kirata kamar uwa take gareni nace mata in sha Allahu.
Muna da wattani biyu da kwanaki a sabon gidan da muke ciki,Yaya Ishaq ya tafi Abuja ranar wata asabar shima din Mahaifin zainab ya kira sa akan yazo yana nemansa ba shi ko da kudin Mota Mama ta kira Anty Binta ta bashi ya kama hanya sai da ya bar gidan nan Hankalin Mama ya kwanta.
Kamar yau ya tafi washegari Goggo tazo ganin wajen da muka koma Yaya Isa ya kawota,shima Hafsah ya kira tayi mai kwatance Dakin Mama ta fara shiga suka gaisa anan Mama wai ke Tambayan Goggo ina Hajiyar Dala..?
Goggo tace"Baki sani ba ta tafi raka mijinta kasar awaje a duba lafiyrsa"
Sai Mama ta kasa mgana tunda da Yaya ishaq ya fito daga hannun jam'an tsaro Mama bata kara jinta ba tun tana kiranta ta na bata uzuri har dai ta daina samunta goggo mamaki ya cika ta  daman ana jin kan Saudatu da Fatima ne..?
Da mamakin ta baro dakinta zuwa shashena ta iskemu muna ta Dura zobo a gorina,Goggo na zolayata fad'i take yi"A'a kaga Hajiya fa'i mai zobo da kunin Aya"
Amir da Hafsah suka kwashe da Dariya Yaya isa na gefe yana taya su, shi sauran na jiya da yammah mai sanyi nace Hafsat ta kawo masa yana sha yana fadin"Goggo gaskiya Fa'iza ta iya hada zobo sosai yake da dad'i"
Goggo ta kalleni kafin tace"Ke fa'i taso ki saka ma yayan ki waigi ya fara santi"
Gabadayanmu muka fashe da Dariyan mganarta, shima Dariyan yake yi yana gyad'a kai kamar wani kadangare.




*INGANTACCEN ZANCE*.

*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*
*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.*
*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*08032773332.*
✍️.



*Janafty*
*KNKB2004*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Itama cire hijabi tayi ta shige cikin mu. tana tayamu zuba zobon a sabbin Gorunan da na siya,muna yi muna hira cikin Annushuwa lokaci d'aya muna darawa in abun dariyan yazo,Yaya Ishaq ne bayan ya gama shan na shi zobon zai shiga cikin gari ya mike yana fadin"Fa'iza zan dawo daukan Goggo dole na tafin ma da Madam zobon nan domin itama tana min labarin sa"
Hafsah na gefe tace"Yaya isa har da kunin Aya.."
Da sauri yace"Eh har da kunin Aya a had'amin dashi"
Gabad'ayanmu muka kara kwashewa da Dariya yana sosa kunnensa da key din motar dake hannunsa yace"Goggo kin jamin yara na min dariya ko.?
Goggo tace"Kayi abun dariyan ne.Ke Hafsah bisa ya kwaso min tsaraban Fa'iza kafin ya tafi"
Har zai fice daidai lokacin yaji Goggo na tambaya ta Yaya Ishaq sai nace mata ya tafi Abuja sai ya koma ya zauna cikin mamaki yana fadin"Daman bai daina zuwan Abujan nan ba..?
Goggo tace"Kaji wata mgana shi da yake da mata da ya'ya kake fadin bai daina zuwa ba"
Yaya isa yace"Haba Goggo.In a baya ya je yana aiki ne yanzu kuwa ba ya aiki ga wahalan rayuwa in a baya yana da motar kansa, yanzu ko babu ko na motar da zai rika zirga zirga ai wani abu ne mai zaman kansa shima ya kamata ya zauna yayi ma kansa Tunani haba.."
Ni da goggo kamar had'in baki ba wacce ta tankansa ya cigaba da fadin"In har tana son shi ta baro chan ta dawo nan, ai gidan nan shima ban ga laifinsa ba inda rayuwa ta juya dakai sai ka juya kai ma ka fuskanceta"
Goggo tace"Ya za'ayi ta dawo bayan achan take aikinta a kace"
Yaya isa yayi tsaki yana fadin"Mganar banza ne Goggo in dai tana son shi kuma ya isa da ita duk inda yake zata bisa.ammh gaskiya wannan tsarin bai yi ba, duk wanda yaji haka sai ya raina ma wayaun Ishaq. baisan zama ba aikin yi ba ne, yana ganin kamar abun wasa ne sai rayuwa ta fara kwallo da shi zai Fahimci Shayi ruwa ne"
Dariya ta kusa subucemin da mganarsa ta karshe ya mike yana fadin"Ita Fa'izan ba mutum ba ce, ba ga ta nan ta biyo sa inda yake a kuma yadda yake ta zauna da shi ba, sai ita yar gwal wahala ce bata ishesa ba Allah ya ba da sa'a"
Daga haka ya mike bayan yace Hafsah tazo ta shigo da kayan ni kuma sai nace Amir ya bita ya tayata bayan fitan su ni da Goggo bamu tada zencen ba sai muka shiga wata Hiran na Dabam Goggo ta kalli falon ta kara kallo kafin tace"Nan din ma ba laifi sai ku lallaba kafin muga Abunda zai yi"
Na gyad'a ma Goggo kai ina fadin"Ai anguwan nan tayi Goggo sosai nake samun Ciniki"
Goggo na dariya tace"Dakyau Allah yasa albarka Allah ya tunkud'o ciniki Fa'i ta biyamin hajji da kudin zobo da kunin Aya"
Ina dariya na rika fadin Ameen Ameen Goggo har da Umra ma goggo na Dariyan jin dadi tace'"Allah ya ida nufi Fa'iza"
Hafsah ne suka dawo da kaya Nasan Goggo da Dawainiya bata zuwa Hannu Rabbana tace su garin kuni ne mu lallaba ina ta godiya har da Taliyar yar muji garin Danwake garin Tuwo da tsakin masara kubewa danya,kuka daaddawa,da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login