Showing 81001 words to 82431 words out of 82431 words
tuna Lokacin da Anty Binta tazo ita da Mama suna min watsi da kaya akan sai na bar gidan,meyasa yau don nace zan tafi sai su damu..?
Wani tukuki ya taso min dayasa har jiri na fara gani cikin Duhun ido na juyo ina fadi'n"daman kuna so na tafi,Aurena ba alheri ba ne ko ba haka kuka fad'a ba..?meyasa don yau nace zan tafi kuke magiyan kada na tafi..?Wlh kaina tuni ya Dauki Dumi kuka na kara Fashewa dashi na juya ga ya'yana da suke kallona cikin rauni hatta Amir da ba kasafai ake ganin kukan ba yau har da majina,Ahmad kuwa da gudu ya nufeni ya rumgume ni yana fadin"Umma zan biki ni dai"
Musty ma ya kariso yana kuka ya rikemin Hijabi gam yana fadin"Nima Umma ke zan bi na fasa zuwa Lagos din"suna mgana kukana na karuwa Anum ma ta rugo ta makalemin jiki ta fashe da kuka tana fadin"Umma nima ke zan bi"
Ina Kuka suna kuka Amir na Tsaye shi bai zo ba na dago ina kallonsa cikin kuka nace"Amir ku yi hakuri ka zo ka taimaka min ka lallashi kannen ka"
Sai kawai shima ya rugo da gudu ya Rumgumeni yana fadin"Umma zaki tafi ki barmu?don Allah kada ki tafi Umma kada ki tafi ki barmu"
Sai kuka yadda suke kukan ne yasa naji gabbaina sun yi sanyi in na tafi na barsu yaya rayuwarsu zata kasance?sai na juya ina kallon Ishaq da idanuwansa suka kad'a jajir,sai kawai naji Duhu ya rufeni da Hanzari na yakice su a jikina na duka Bisa gwiyoyina dukkansu na rike hannayensu cikin nawa sannan na Dauki na Amir na rike ina fad'in"ba inda zan je ina karofi gidan Goggo zan koma,In ina bukatar ganin ku zan zo ko ku kuzo wajena,sannan zan rika kiran ku a wayar Anynku muna gaisawa kun ji ko?
Ahmad ya makale kafada yana Fadin"ni dai umma zan biki"
Musty ma yace haka Anum Sarkin kuka tace"Umma ki tafi damu chan gidan goggon mana"
Ina girgiza kai hawaye na zubomin nace"Bazai yuyu ba Anum. ku kuna da Baba sannan ga kakar ku nan bazai yuyu ku bini ba,ni kuma bani da uwa ba ni da uba,Goggo itace gata na shiyasa zan koma wajenta ku kuma Babanku na da mata Antynku ga kannen ku su Farhan,ku zauna lafiya da junan ku ku zama masu jin mgana Amir kai ne Babba ka rike kannen ka Amana ka ja su ajikinka a matsayinka na Babban Yaya,ku zama masu jin mgana da Tarbiya Anum ki kula da Ahmad kin ga shine karamin cikin ku kada ku takurama Antynku komai tace ku yi kuyi kun ji ko..?.sai suka kasa dagamin kai ina kokarin Dauriya na saki Hannayensu na rika bin su daya bayan d'aya ina share musu hawaye ina fad'in"kada ku ce zaku rika saka Anynku mgana,Amir karatu ka rika duba na kannenka,Karatun Qur'ani ku rika bita kada ku manta da azkar din safe da maraice,ban da abokan banza sabon waje ne bakusan kowa ba,kada ku manta da Tarbiyan da na baku Anum kece mace ki rika taimaka ma Antynku da ayyukan gida kuna ji ko..?
Sai gabadayansu suka bare min baki Amir jikina ya fad'a yana fadin"Umma mu ba ma a son Antynmu ke muke so.."
Hawaye suka kwaranyomin na kamkamesa ina kuka Anum ta ruga wajen Babansu tana fadin"Daada kaje ka ce Umma kada ta tafi.."
Tana fada tana jan Hannunsa,sai ya biyota har gabana shima dukawar yayi,yana fadin"Don Allah Fa'iza ki duba yara nan"
Ban ko amsa mai ba na hada ya'yana na Rumgume gabad'ayanmu muka saka kuka,Mama na gefe sai ta juya kawai ta fice tana kuka Anty Binta ma duk jikinta yayi sanyi in Fa'iza ta tafi ya kuma abubuwa zasu tafi?Zainab wannan yar son jikin da bata iya komai ba, ta ina zata yi da Dawainiyar yara?akwai matsala babba kuwa.
Suna kuka ina kuka da na ga bazai Fissheni ba na rarrashi kaina na koma ina ba su hakura suka makaleni suna kukan sai sun bini Hon din masu mota ne ya ankarar damu suna jiranmu,Ishaq ya marairaice yana fadin"Na siya mana Ticket Fa'iza asaran kudina kike so nayi..?
Kai tsaye nace"Ai ban ce ka siya har dani ba. Tunda ban ce maka zan bika ba"
Cikin wani yanayi yace"To dukkanmu mun fasa bazamu tafi ba, mu tattara muje karofi a warware komai"
Cikin yak'e nace"Kada ka biyoni Karofi Ishaq ka lallaba ya'yanka ku tafi,kada ka manta aikin. ka fara ba jimawa rashinka a office zai iya zame maka matsala sannan meyasa bayan ka kashe kudin jirgi zaka fasa?
Na fad'a ina kuramai ido gani yayi kamar na fara saukowa yasa da Sauri ya rikeni yana fadin"Fa'iza zuwan bashi da amfani idan baki kin sani ko?
Kai tsaye nace"Bazan bude baki nayi mgana ba.ka lallashi yaran nan ku tafi in kuma kace zaka bini karofi zaka Fallasa kanka da kanka. Daman na Fada maka da bakina bazan fad'i komai ba,sai dai in kai ka fad'a da kanka"
Shuru yayi yana ajiyar zuciya a Firgice kamar wanda yayi karya,Ban damu ba naja hannun su Ahmad da Musty,su Amir suka biyo bayana muna zuwa kofar gida masu motoci na jiran mu sawa nayi aka Fitomin da akwatina da jakunkuna na,nace a sakamin a karamar Golf din nan,Mama na gefe tana sharan kwallah,su Ahmad nata kuka har Lokacin sai na Daure saboda bazan bari su hanani Tafiya ba,key din gidan na isa gaban Ishaq na Damka masa ina Fadin"Key din gidan nan, ne Sauran kayana in ka sauwakemin zan zo na kwashe"
Makullin fad'i ya yi a kasa,ya kasa amsa ni kuma na juya ina goge kwallah na bude bayan mota na shige,Su Amir sun yinkuro zasu shiga na rufe kofar da karfi ina kuka ina ganinsu suna kuka suna dukan jikin mota ammh na kasa motsi,Direba ya shigo yana fadin"Hajiya yaran nan zasu hanamu tafiya fa"
Kai tsaye ina kuka nace"Glass.! d'agamin"
Ba musu ya d'agamin na Leko da kaina da sauri suka nufeni Ahmad sai fadi yake Umma nima zan biki shi da Musty,Amir na share ma Hawaye Na rike hannun Anum ina fadin"ba na ce ku lallashi kannen ku ba..? To in dai kuna kuka bazan dawo na Dauke ku ba"jin haka yasa suka daina kukan Amir yace"Umma to kizo mu tafi tare"kai tsaye nace"Aa ku fara yin gaba, ni zan zo daga baya..Ka kula da kannen ka kaji ko Amir"
Sai ya gyad'amin kai dukkansu na Shafa kansu ina fadin"Allah ya yi muku albarka"Sai kuka yaci karfina cikin kukan nace"Direba muje"
Lokaci daya na maida glass din na zuge,mun fara tafiya na juyo ina daga musu hannu Ahmad ya kwace yabi motarmu yana kiran sunana har yana Fad'i ina gani Baban yaje ya daukesa,Anum kuma Mutsy ta rike tana kuka Anty Binta ta rike Amir kasa Daurewa nayi na juya ina kuka kamar in ce Direba ya Tsaya sai kuma wata zuciyar tace"Fa'iza ki sani ko kin koma baki da wata daraja. Ishaq Zainab kadai yake so ke alfarma yake miki"
Ammh ya'yana fa..?basu saba da kowa ba sai ni wazai kula da su..?zasu fara sabuwar rayuwa a inda bani ya ya zasu tafiyar da rayuwar su.?Zainab bazata kulamin da yarana ba bazata iya ba,yar gatace bata saba da wahala ba ,yaranta ma yan aiki ke daukan mata su,Tarbiyan su da na dauk'i shekaru ina ginawa in ta rushe fa..?
Kuka nake yi da karfina har sai da Direba ya juyo yana fadin"Hajiya ki yi hakuri,In bazaki iya tafiya ba sai mu koma ko kuma ki taho da su naga yaran basu son tafiyarki hala rabuwa kuka yi da Baban nasu,duk da shima naga kamar bai so tafiyar ta ki ba..?
Irin dirobobin nan ne masu fad'i ba''a tambaye su ba.
murya shake nace"Karofi..Karofi zaka kai ni"
Na katse mganarsa lokaci d'aya ina cigaba da kuka zuciyata na Zafi kaina ya fara Dif Dif ga jirin danake ji. alama ce ta jinina ya haye sama.
Har mun yi nisa sai naji bazan iya wannan jarumtar ba ya'ya na,ya'yana kawai nake tunani.
Sai kawai na ce ma Direba"Tsaya mallam.."
Sai ya juyo yanaa fad'in"In tsaya..?
Sai kawai na gyad'a mai kai da sauri ina fad'in"Mu juya mu koma..! mai dani da sauri'
Ina haki na fad'a,Tunani na da zullumi na,kada kafin mu koma mun iske sun tafi.
Na fasa bazan iya nesa da yarana ba. tunda na iya kwashe tsawon shekaru goma sha, cikin tozarci na jure me zai hana yanzu bazan jure ba..?kuma yayi nadama zan karbi Tubansa zan bisa naje na zauna tare da yarana.
Muna tafe ina fadin"Kayi gudu don Allah ka yi sauri."
Yadda nake mganar zaka san bana cikin Hayyacina.
*K'arshen littafi na Biyu,Littafi na uku zai zo in na samu natsuwa insha Allahu,Ammh ba gabadaya zai zo ba,zai zo kamar yadda muka fara daga farko.*
*Nagode..Nagode da Soyayyarku Allah ya bar zumunci Ameen*
*Janafty*
*19/17/2023*