Showing 51001 words to 54000 words out of 82431 words
wajen Lauya mgana"
Abba yace"To Za'ayi mata taron dangin abun kuma ma nasu ne.daman haka abun yake ba gashi da aka had'u ba yara suka fara shaida da juna ba"
Nan fa falo ya kaure da Hira suma basu da bakunta sun saki jiki suna ta Hira damu,Ammi ko ta shige cikin mu ba ruwanta Inno dai Goggo tajata Daki don ta Huta Mama ba baka sai ido ta zama kamar mujiya afalon da na gabatar da ita a matsayin uwar miji na, cikin girmamawa Abba ya gaisheta sau taga ba ma raina gorin asalin datake yi min sai da ta raina kanta da taga Abba da Ahalinsa.
Abdul'Ahad kuma na gefe ya Kira Raliya sun yi mgana da yace ga wata su gaisa sai ya bata Badariya tayi matukar mamakin inda suka Hadu sai Badariya ta bata labari tuni ta bazama Dakin Hajiya tana gayamata yadda komai ya wakana Daman tun a satin Abdul ya gayamata zasu zo katsina wajen dangin mahaifinsa tana ta mamakin daman su ba yan kano ba ne..?sai yace eh asalin Babansa haifaffan garin karofin katsina ne.
Abba da shi da yara aka barsu suna ta Budiri da kuma mazan su Yaya Ishaq kowannen ya gabatar da kansa garesa,Duk rashin sakin jikin Yaya Ishaq ya saki jiki da Abba Saboda yana da Dadin zama sallar la'asar ya fitar da mazan zuwa masallaci mu kuma muka yi namu acikin gidan yaran kuma tuni sun hade kansu suna wasa.
Bayan an dawo sallah ne aka zauna zaman cin abinci,su Abba a kofar gida suka baza musu tabarma suka zauna mu kuma muna cikin gida,Girkina aka ci daga karshe zobo da kunin Aya har ana Fada da Nana Fatima da Nana Khadija Goggo na Dariya tace"sai kun gaji da sha duk sana'ar yar'uwan ku ce gatan nan Fa'iza"
Ammi ta saka salati tana fadin"Allah mai Hikima sannu Fa'iza kai masha Allah"tana sha itama tana santi hakama abinci da akace ni nayi ta kalleni Lokaci d'aya ta kalli goggo tana fadin"Goggo Fa'iza yar baiwa ce gaba da baya fa ba'a sani ba"
Nana Fadila ne ta kara mata jaka a baya da sunan waigi ta ko mako mata Dakuwa suka koma gefe suna Dariya,ashe suma mazan sun yi santi sai da Daddare bayan an sake Taruwa a tsakar gida ciki zafi ga ba wuta ana Hira Abba yace"wacce cikin ya'yana tayi shinkafar nan mai dan karen dadi?
Da sauri Nana Fatima tace"Abba Fa'iza ta ce"Nana fadila tace"Ji bakinta Fa'izan mu dai malama ai bataki ke kad'ai ba ce"
Sai suka fara gaddama muko murna da Farinciki yaki barin mu,Abba ya raba rigiman da fadin"Naji fa'izan kowa da kowa ne shikenan"
Daganan sai ya kashe mganar ya kalleni yace"Fa'iza komai da ruwan ki kenan..?masha Allah Allah yasa albarka"
Aka amsa da Ameen sai ya kalli Ishaq dake dauke da Ahmad Lokaci da'ya yana fadin"Ishaq ka yi dace gaskiya zaka karamin Sadaki saboda wannan girkin da zobon data kware akwai cikon Sadaki"
muka saka dariya gabadaya Ammi tace"Baban Nana zaka zama surukin zamani ne..?
Da Sauri yace"Daman nace miki ni surukin da ne..?
Yadda yayi mganar ne ma Dole sai da mukayi Dariya Allah Sarki Rayuwa daman haka Allah ya kan shirya lamuran bawa, sai kusan sha Biyu su Abba suka tafi masauki bangaran da aka gyara musu ,Mijin Yaya mariya gida ya koma ya kwana kuma shi ya sauki su Yaya ishaq a gidan iyayansa Dakin kaninsa shi da mijin Yaya Asiya muko duka nan gidan goggo muka kwana har da Mama da Badariya mu da yan'uwan mu raba Dare mukayi muna Hira kamar mun shekara tare Nana Fatima na zama Fa"izanta abu kad'an sai kiji tace"Fa'ina kaza kaza"
Ita ya'yanta Biyu,Jidda da jalil kanana ne,Saboda sai da tagama Service dinta tayi aure Nana Fadila ke da uku FalaqFahad,Da Fairuz,Yadda kuka san mun dade da sanin juna saboda yadda muka shaku daga Dare zuwa Safe suma suna da Tarbiya daidai gwargwado Ammi ta basu tarbiya itama irin Abba ne akwai barkwanci.
Da Safe ni suka yi ma chaa na shiga kitchen nayi musu abun karyawa da su Yaya isa suka jifgo cefane,ko wajen karyawan har sai da akayi santi Tunda nan mazan suka zo gidan Goggo aka had'u aka karya gabadaya.
Yaya Abdul'Ahad na shan ferfesun kayan ciki da nayi musu ya kalleni yana fadin"Ina fatan kina koya ma Raly irin wannan girke girken ko?
Sai Falon ya kaure da Dariya Ammi tace"Baban Nana saka ma d'anka waigi shima Cikin Dariya yace"Ammi ba fa santi nake yi ba"
Abba na gefensa yace"My son yi santin ka dadi'n abun ba kai kad'ai ba ne har da Baban Nana shima yayi santin"Kai Abba akwai ban dariya Ammi tace"Baban Nana kasan wa na ke tunawa in na samu abinci mai dadi haka..?
Yana shan tea ya zuka ya dawo da mug din yana fadin"Engr.mana"
Cikin gyad'a kai tace"Wlh shi ke fad'omin rai kasan shi da son abincin Hausawa na gargajiya da na zamani."
Abba yace"Ki bari musamman ace ya samu zobon nan na Fa'iza da shi da Maltina ko coke har abada,kinsan ya tsani lemukan ba gwamgwani ko da yaushe korafinsa Baban Nana duk kayan basir ne zakin su ya yi yawa"
Ammi tace"Allah sarki Engr kamar ba Jinin yarbawa"
Abba yace"To ai kinsan ya sirka ta bangaran Hajiya Shukra shiyasa zaki ga rabin sa bahaushe rabinsa bayarbe ba, ba domin ma ya tashi cikinsu ba sai in akace miki ya had'a iri da yarbawa sai ki karyata"Ammi tace"Nima ka manta ganin farko da nayi masa sai da na karyata"
Abdul'Ahad na gefe yace"Abba kana ji da Engr nan Sosai"
Abba yace"Mutum ne har da rabin mutum..Ya yi min abunda bazan taba mantawa ba yayansu.Engr ya goya mutane Dabam dabam irina da yazama madubin su kirkinsa nake fada'maka sai ka zauna da shi zaka san hakan"
Abdul'Ahad ya jinjina kai bai ce komai ba,Abba da Ammi suka cigaba da mganganunsa kan Engrn da su,suka san shi.
Haka dai muka gama karyawa cikin Nishad'antarwa da Annshuwa,ranar a gida muka yini ana ta hira sai yammah muka fita Lokacin Yaya Ishaq ya koma gida shi da Mama da yara wanda Dakyar na samu Anum tabisa da ta saka rigiman bazata ba nace bata isa ba makaranta,Badariya na tare dani sai gobe zamu koma katsina Tunda suma Jibi zasu tafi saboda ayyukan su Abba su, suNana Fadila kuma zasu koma gidan mazajen su.
Da yammah Karofi muka zaga har gidan su Tamadina da yazama duk ya rushe Abba yace zai saka a bige shi a gyara zai zama nan zasu rika sauka in suka zo,Baba Ati kuma da ita zasu tafi zata zauna tare da Inno a gidan Yaya mariya muka kai wajen goman Dare,Muna ta Hira,
washegari kafin mu wuce Katsina sai da muka biya Dutsemah gidan da Tamadina tayi aure har da Abba akaje sun gaisa da mutan gidan da shi kanshi megidan suna ta fadin irin Hallayar ta madina Abba ya cika su da kudi muka bar su,suna kwallah muma muna yi Daganan muka rabu da Abba,ya koma karofi,mu kuma
Direban Abba ya kaimu har katsina da Abdul'ahad shi ya rigamu yin gaba wajen Raliya yaje ,Gidana muka sauka Nasan ko ban fad'a ba sun ga yanayin gidan susan muna da karamin karfi,Nan muka ci abinci mukayi sallah mun iske Anty Binta a gidan sai kallon su Nana Fadila take da ya'yansu taga ba ma raina a wajen su,sai la'asar na rakasu gidan Hajiyar Raliya har da Ammi,inno na gidan goggo tace bata iyawa kafa ciwo Hajiya taji Dadi ta karbemu hannu goma kamar yadda ta saba.
Ammi ta kalleta tana fadin"Hajiya ashe ya'ta ce ma ke turarukan kamshi bansani ba..?
Hajiya na dariya tace"To ba gashi yanzu kin sani ba!
Ammi tace"Wlh ai naji dadi kamshi har karkashinn Gadon Baban Nana insha Allahu"
Gabadayamu sai da muka Dara Raliya nata kunyana nace"Ni daman ai Antyn Raliya ce, ba kunya Tsakanimu Hajiya nata mamakin lamarin na zauna nayi mata bayani atakaice tace ikon Allah kenan itama Raliyan a bikin Laila suka had'u da Abdul'ahad duk da daman an san suna sanadin Iyayan Laila.sai dare muka baro gidan Hajiya da Sha tara na arzikin da ta hada mana, adaran suka koma karofi Washegari kuma suka koma gida Saboda a ranar Nana Fadila da Nana Fatima zasu koma gidajensu.
Kafin rabuwar mu Abba ya Tattauna damu kan abunda muke bukata sai muka kasa mgna sai yace bakomai Ko mazajen namu da bai samu zama Sosai da su ba, saboda ba Lokaci ammh zai gayyace su har gida su Tattauna mun raba ma junanmu Lambar wayanmu,Kwana uku muka yi tare kamar mun shekara tare Basu kyamace ni ba, duk rashin son mutane na, na shaku da su Nana fatima mutane ne masu karamci ilimi waye kudi da nasaba da sanin ya kamata.yaya Asiya ita yar gida ne Ammi yar kano ce Haifaffiyaa Dala ta kano,kuma daman ga bikin Raliya dake gabatowa mun zama iyalai D'aya kaduna zata yi diban manyan baki.
Badariya da Raliya sun fi kowa murnan wannan al"amarin,Ko Yaya ishaq sai da ya yabi kirkin Ahalin Abba gabadayansu.
Kuma kowa ya gansu yasan suna da kudi kuma sun taki gwamnati,Abba kamar yadda ya fada tare da Baba Ati suka koma Inno nata jin Dadi ta samu abokiyar zama tuni har Abba ya damka ma su Yaya Isa kwangilan gini an fara baje gidan ana sake sabon Faundation.
Sai da nafi sati ban koma da sana'a akan zobo da kunin aya na ba,Saboda rashin zamana waje d'aya,Muna yi da waya su sosai barin ma Nana Fatima har megidanta data koma sai da ta bani muka gaisa,Kowa ya ganni yasan na samu natsuwar zuciya da kwanciyar Hankali muma mun zama yan gata abu kad'an Abba yace me muke so..?Hafsah ta zama auta kowa ita yake riritawa yanzu haka ta kosa su samu Hutu ta gudu kaduna gidan Abba tayi Hutun ta achan.
Sati daya tsakani da zuwan su Abba ranar da Daddare muna zaune Yaya Ishaq yakalleni yana fadin"Abban ku aikin me yake yi?
Tunani nayi kafin nace"Na manta kamar ko a NN Me naji su Yaya Asiya na mgana?
Sai Yace"NNPC dai ko..?
Sai nace"To kila nan din ne".kai ya jinjina kafin yace"Akwai kudi gaskiya babban ma'aikatan matatar mai ne fa"
Ni dai ban ce mai komai ba, ammh kowa yaga Abba ai yasan ba karamin mutum ba ne.
Acikin watan Abba ya kira kowannen mu a waya kowa ta fadi abunda take so ni dai jari nace ya karamin yana Dariya yace"To Fa'iza aammh ai ni burin gina miki katon gidan abinci nake da shi, tare da shagon gyaran jiki da kayan kamshi"Sai na Bushe da Dariya ina fadin"Allah ya amsa Abba"
Dubu dari biyu ya turamin yace na rike a hannuna kafin yaga abunda Allah zai yi Dukkammu haka yabimu ya bamu kuma yace zai kira duka mazajemmu ammh sai yaje warri ya Dawo warkshop din da zasu je suyi na wattani biyu in ya Dawo zai nemesu,Sannan ya aiko mana da kayan sawa dukkanmu mu da yaranmu da mazajen mu,abun sai wanda ya gani da wad'anan kudin na cigaba da Rufamana asiri,sannan gefe daya muna waya da su Nana Fatima muna tsara shiryen shiryen Bikin Raliya da aka matso da shi kusa,Da sai bayan wata hudu za'ayi yanzu kuma an maido da shi bayan wata biyu Saboda Yaya Abdul'ahad zai tafi kasar waje karo karatu kuma da matarsa zai tafi.
Mama dai kam kamar bata gidan ko motsinta ba'aji ta daina shiga duka Hurumina,sai dai bansan tsakaninta da Da'nta ba,Anty Binta kuma tana ta Hidiman auran Halisa ba'a cika ganinta ba,Mganar aiki kuma shuru kake ji sannan har Abujan Mahaifin zainab ya kirasa ya koma ammh ba wani Labari.
Sai daga baya na Fahimci Saboda kawai ya rika zuwa yana zama da zainab ne,ammh tuni sun san akin bazai samu ba,tuni har ma'aikatan da aka dauka sun fara aikin su.
*Janafty*
*KNKB2014*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Zukata tuni sun kwanta,gabbai sun samu natsuwa hankula sunyi ruku'u sun rusuna.
Ta kowani bangare na juya na irin shafukan kaddara da kan bud'e ma bawa to ta kowani tsanani daman Allah yayi alkwarin sauki,hakan ce ta kasance dani duk lokacin da naga rayuwa ta chude'min ko tamin zafi da ikon Allah sai wata kaddara ta bude ma rayuwata sabon shafi da zai zama bango ko majingina gareni
Bayyanar Abba garemu daga Allah ne, sannan zamowarsa makwafin Uba garemu shine jin dadin mu,Sannan har makwafin uwa ya Dauke mana Ahalinsa kuma sun Dauke mana makwafin yan'uwa da Dangi,sai alokacin muka san muma ya'ya ne,Abba ko tari bai yarda mu yi ba tare da yasan Dalilin yin sa ba,Yace duk abunda muke bukata kiransa kawai zamu yi a waya mu gayamasa,to mu saka aran mu komai muke so mun samu,Yaya Asiya tuni har ta je gidan su Ammi a kano tasha karamci ta tabbatar mana da cewa Duka Ahalin Abba masu karamci ne,Tace sai nuna ta ake yi ana fadin"Diyar yar'uwan Baban Nana ne na kaduna"Ko'ina aka kaita sai an karramata duk da Ammi bata garin tana kaduna,Direba aka saka yakai ta har gida,Sannan sun karbi lambar wayarta da alkawarin zasu rika zuwa suma. Ammi suna da yawa a gidan su matan Mahaifinta hudu ne kuma duka sun haiyayyafa,Sannan tana da kanne maza sosai wasu duk suna garuruwan da suke aiki da matansu kamar mijin Laila Uncle Junaid Staff ne a kasu Kaduna State University. yana chan sai dai lokaci bayan Lokaci suna zuwa ganin gida shi da ita.
Azumi ne ke kara gabato mu ma wannan karon,Zainab saboda ban samu zama ba bamu kara mgana a waya ba tunda na gaisheta kwanaki da jiki,shi kuma Gogan bai min zencenta ba. Ni ma kuma ban cika Tusa kaina inda ba'a sakani ba, tunda muka yi alkawarin da shi ya daina matsamin ammh fa bai daina Takurani da kallo ba,ko kuma ya rika shigemin jikinsa na gogan jikina bana son haka nayi mai mgana sai kawai ya kalleni yace"Ba kyau Fa'iza wlh ba kyau. Ki bari kada Allah yayi fushi da Da ke"
da naji haka sai ban kara mai mgana ba,sanin gaskiya ya fada,Tunda bai sakeni ba har yanzu yana da Hakki a kaina kuma shi Allah ba ruwansa da wannan,mganar jinginan auran mu kuma wannan wani zama ne mai zaman kansa.
Sai na rabu da shi tunda na samu ya daina sakani gyaran Shimfid'a yana Rutsani sai na gode ma Allah,Abba Dubu Dari uku ya kara turo ma kowannemu mu yi siyayyan azumi har da su Goggo suma bai kyalesu ba,bakina yaki rufuwa Kana naka daman Allah ya gama nashi kuma nashi Tsarin shine daidai na zata Yaya Ishaq zai yi fad'a sai naga bai ce komai ba ya dai ce"Abban nan naku naji da ku Fa'iza"Sai na samu kaina da yin kayattacen mirmishi,Hajiya ma ta aiko mana da kayan abinci,Domin ita a di'ya ta daukeni ba kowa ba,Alherin Hajiya gareni mai girma ne da bazan taba iya mantawa da ita ba.
A satin za'a fara azumi yara sun yi Hutun makaranta suna gida da Safe muna waje ni da Anum da Amir muna wanke wanke Ahmad da Musty na fad'a kan shara nagaji da yi musu mgana ne na kyalesu sun ki bari ina jira na tashi ne yaro yaji a jikinsa,Hafsah na makaranta jarabawa suke yi ta kosa su gama ta gudu kaduna,Badariya na kano ammh suna chan suna ta shirin Biki ita da Raliya ta waya.
Daga Daki ya fito kamar an jehosa Fadi yake yi"Bazai yuyu ba. Wlh bazai yuyu ba in kika bari aka cire cikin nan na rantse da Allah Zainab aure na dake ya karem Bazan iya ba Nagaji haba.."
Yake fad'a cikin Tsawa da Daga muryan da sai da Mama ta fito daga Daki zani a hannu cikin wani yanayi ni kaina sai da na saki aikin da nake yi na mike gabana na faduwa.
Mgana yake a waya kamar kuma da Zainab yake mgana sai kara shan wallahi yake in aka cire cikin nan sai ya rabu da ita cikin bacin rai yace"Me kuka maidani daga ke har mahaifin naki.?sakarai shashasha ko sai yadda akayi da shi ko.?to wannan karon ba Kotu ba Allah yasa majalisar Dinkin Duniya zai kaini wlh sai kin yi zawarci ni bazan iya wannan auran naku ba da kuka fifita yahudanci Fiye da Islama acikin lamuran ku"
Kokarin yi mai bayani take ya Daka Tsaki ya katse wayar yana Huci,Mama ta kallesa tana fadin"Meke faruwa ne Ishaq.?
Sai ya kalleta Har idanuwansa sun cika da kwallah cikin wani yanayi yace"Mama ki duba fa ki gani,wai cikin yarinyar nan babanta yake so a zubar..'"
Sai ya kasa karisawa saboda yadda ransa ke Tukuki,Mama tace a zabure"Cire ciki kuma Saboda mene. ?Kamar zai yi kuka yace"Saboda Hujjar su na banza wai yana wahalar da ita, hala ciwo take ko kuma wani abun ne ya sameta ana raba mai ciki da laulayi ne mganar banza kawai,Mama ne Zainab da Mahaifinta suka maidani jani talau..?wannan wani irin kaddararren aure ne..?
Mama zatayi mgana kenan wayarsa ta fara kuka yana dubawa yace"Babanta ne"Yau ko arzikin Daddyn bai samu ba,kamar bazai Dauka ba Mama tace ya Dauka mu dai mun ga yana mgana Yaya Ishaq na cika ya bude baki yace"Daddy.."
Kamar katsesa ya yi yana mgana kamar kiftawan ido sai ji mukayi K'aras,ashe wayarsa ce ya buga da bango sai da ta dargargaje,A firgice muka yi baya har da yara da suka yi Tsuru tsuru basu saba ganin haka ba. Mama ta firgita ta rikesa da karfi tana fadin"Kai Ishaq ka natsu mana"
Haki yake yi kamar wanda yayi gudun mutuwa cikin hakin yake fadin"Shi ke auranta ko ni Mama.? A shari'an ce na fi shi iko da ita meyasa komai shi zai zartar da shi.?Rabon da wasu suke nema da kudin su,mu mun samu shine zai yi sanadiyar zubarwa saboda bai da Hankali yana Uba ammh uban banza wanda baisan ya kamata ba..?
Mama ta kara rikesa tana fadin"Kwantar da hankalinka ka natsu."
Cikin Hargagi yace"Wani iri na natsu mama..?Har ce min yake sai an zubar nayi abunda zan yi, wai akan ya'yansa zai yi iya yin komai wlh Mama indai aka zubda min jinina ba shege ba,d'an sunna wlh sai Zainab sai tayi zawarci aurena da ita ya kare har Abada,in ya'yana ne zan karbo kayana Fa'iza ta had'a da su Amir ta rike min su"
Mama ta yi saurin tareshi tana fadin"Abi komai a sannu Ishaq"
Ni dai nayi tsuru ina kallon ikon Allah Amir yaje