Showing 36001 words to 39000 words out of 133887 words
ta bi ta gigice, ba ta taba jin Mammah na fada haka ba. Hannunta sai rawa yake haka hoton, ga shi ta kasa cire shi. Tasowa ya yi ya iso gare ta, gabadaya jikinsa ya mutu,
Lemme help.
Ya fada mata cikin kunnuwanta da tattausan lafazi.
Zagaye ta ya yi cikin hannayensa kamar ya rungume ta, a haka ya ciro hoton ya sauke shi kasa. Mammah ta bi su da kallo, duk su biyun sun sunkuyar da kai, sai ta kasa ci gaba da fadan. Suka koma inda suka tashi suka zazzauna. Ismael ya ce,
Ni wallahi ma kamar na santa.
Abdulazeez ya galla masa harara, Mammah ma ta ce, Ah toh, ni ma kaina kallon sani nake mata. A ina ta santa? Ta jefa tambayar ga Abdulazeez.
Shiru ya yi kamar ba da shi ake ba, sai da Mammah ta kara maimaitawa. Cikin sanyin murya Hafsat ta ce, makwabciyata ce.
Tana da aure?
Girgiza kai ta yi a hankali alamar babu.
Hajiya Maryam ta ji kamar ta rufe Adda da duka don haushi, wane irin kwantaccen kai ne da ita? A yi mutum kamar sakarai bai san halin da duniya ke ciki ba sam? Ko dai ba ta kishin mijin ne? Watakila don ba sonsa ta ke ba, amma ko yaron goye ai ya san kishi. Zuciyarta ta zo wuya da yawa, in ta ci gaba da kallon Hafsat dukanta za ta yi. Mikewa ta yi tana gyara daurin zaninta da mayafi alamar tafiya.
Baba Azumi ma ta mike, Ismael tattara kwanukan nan ka kai mota, mu za mu wuce, sai gani na biyu.
Idanun Hafsat suka kawo ruwa, ta tabbatar ba karamin bata wa Mammah rai ta yi ba. Zuwanta gidan kenan na farko tunda ta aurar da ita, amma ba ta tsinci komai cikinsa ba sai bacin rai. A kan laifin da ba nata ba. Hasalima wanda ya yi laifin ya yi ne don ya wulakantata ya nuna mata ita ba wata tsiya ba ce a gare shi. Ga shi ta juye komai a kanta don shi ya tsira daga fushin mahaifiyarsa.
Ga mamakinta ta kasa yin nadamar abin da ta yi, gara ranta ya baci da na Abdulazeez dinta! Duk yadda ya so su hada ido don nuna mata godiyar da ke cikin idanunsa ta ki yarda. Ba ta yi don ya gode mata ba, tunaninta yanzu na yadda za ta shawo kan Mammah ne ta daina fushi da ita.
Har mota suka rako su, ta bude wa Mammah kofar mazaunin baya ta zauna, Azumi da Ismael direba na gaba. Kasa rufe murfin motar ta yi ta tsugunna a kan gwiwoyinta a kan cinyar Mommah ta soma kuka. Baba Azumi ta ce,
Me ya yi zafi Addar Mamanta? Ba za ki yi ba daidai a yi miki fada ba?
Kin san shagwababbu ba su yarda sun yi kuskure, Mammah da kin kyale mata hoton ta har Yaya Azeez ya ji yana son Faizar ya auro ta mu ga karshen kawance. Cewar Ismael.
Ciro kai ta yi fuskar nan jage-jage da hawaye ta ke harararsa. Dariya yake sosai, ya ce, Ni ki matsa in ja mota za ni zance wajen Wasilata.
Duk yadda ta so Mammah ta sakar mata fuska ta ki yin hakan, har Ismael ya ja motar Danfulani ya bude musu suka hau kwalta don barin shiyyar rukunin gidajen (Sun-City).
Shi dai Abdulazeez ba baki sai ido, hannun damansa ya sanya cikin tarin sumar kansa yana cakudawa. Daya daga cikin aladunsa in ya san yayi ba daidai ba. Yau ba don wasu dalilai masu yawa ba tsugunnawa zai yi ya goya Hafsat-Suhaana, ya kai ta har tsakiyar gadonsa. Duk da haka zai gaya mata ya gode da irin godiyar da ta dace. Su Mammah na ficewa ta yi cikin gida da sauri ko kallonsa bata yi ba. Da hoton Muazatu da suka sauke ta fara cin karo. Tsaki ta yi ta bi ta kansa da takalmi ta wuce dakinta. Ta turo kofar za ta rufe ya sa hannayensa ya tare.
Karfi ta sa wajen son rufe kofar ya nuna mata nata karfin rabin cokali ne, domin turowa daya ya yi ya shigo dakin ya maida kofar ya rufe. Jingina ta yi da kofar ta rufe idonta hawaye na zuba.
Habarta ya kama da hannun damansa ya dago fuskarta, ji yake kamar ya sanya halshensa ya dauke hawayen da ke zuba kamar an sunce famfo, wata zuciyar na hana shi. Maimakon hakan, yatsunsa biyu Hafsat ta ji a saman fuskarta suna share hawayen. Sosai ta kara tamke idonta sakamakon jin wani abu mai kama da jan wutar lantarki na bin jikinta.
Yi min komai da zuciyarki ta ga Ideserve as a punishment Suhaana, amma ki kwantar da hankalinki, ina mai tabbatar miki Mammah ba za ta iya dogon fushi da ke ba, so kawai ta ke ta nuna miki kin yi wauta, amma ba fushi ta ke da ke ba.
Magana Abdulazeez ke yi kasa-kasa, ta yadda ba don ta kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba za ta ji shi ba.
Wata irin kasala ta ji tana saukar mata, bude idonta ta yi a hankali ta dube shi. Damuwarsa kadan ce a kan abin da ya faru. Ji ta yi ya janyo ta jikinsa a hankali ya hade su sun zama mutum daya. Sosai ta ji nutsuwa na shigarta hawayen idonta na daukewa. Kamshin jikinsa na jefa ta cikin wani irin shauki mai wuyar fassarawa. Dankwalin kanta ya zame ya fadi kasa gashin kanta ya wargaje ya rufe hannayen Abdulazeez da ke zagaye da ita. Ba ta iya aune ba ta ji hannayensa cikin gashin kanta, bakinsa kuma cikin nata. Kissing dinta yake yi tun daga kololuwar zuciyarsa. Alamarin da ya jefa su cikin wani irin yanayi dukkaninsu da ba su taba ji ba a rayuwarsu. Daga can tsakiyar unguwa aka kwada kiran sallar laasar. A yau duk jarumtar Hafsat ta kasa yin protest din, ta kuma kasa yin kowanne kokari na juya wa Abdulazeez baya, ta nemi duk wani kyakkyawan tunani da ke cikin kanta ta rasa.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ladanin ya ci gaba da kwada kiran sallah har tsakiyar kwanyar Hafsat. Tana cikin mutane masu matukar kiyaye lokacin sallah. Zame jikinta ta yi, an yi saa rikon da ya yi mata ba mai karfi ba ne sabida shi kansa ba shi da karfin, dukkansu zubewa sukai a kan marbleskowanne na kokawar nemo consciousness dinsa. Kafin kunya matsananciya ta zo ta lullube Hafsat, ta sanya kanta cikin kafafunta ta kasa dagowa. Abdulazeez ta ji ya kwantar da kai a bayanta ya yi shiru kamar ba ya jin kiran sallar da ake ta yi. Muskutawa ta yi cikin jin nauyi ta yi masa magana.
Yaya Azeez ana kiran sallah?
Ina ji Hafsat, na kasa tashi ne.
Ko in daga ka?.
Ya jinjina kai, dariya na son kama shiduk da halin da yake ciki,wai ta daga shi kamar wani dan ta, har yanzu bai sauke kai daga gadon bayanta ba, Its not easy daga kato iri na. Amma tunda kince zaki iya zo ki gwada. Above all (fiye da komai) a yau, kuma a yanzu, ina so in ce miki NA GODE!
Murmushi ta yi duk da ta san ba kallonta yake ba.
NAGODE din ta me ce ce?
Dagowa ya yi daga kwanciyar da ya yi a bayanta ya juyo da ita gabansa suka fuskanci juna, kwayan idanunsa ya kalmashe a cikin nata ta yadda ba za ta iya dauke su ba in ba shi ya aminta da hakan ba.
For everything!.
Ya ba ta amsa da murya mai cike da mazantaka. Tana so ta dauke idonta amma ta kasa sabida bai ba ta damar hakan ba.
Ban yi don ka gode min ba Yaya Azeez, yi wa kai ne. Amma ni ma ka yi min alfarma ka maida hoton Aunty Muazatu dakinka, tunda ban fiya shiga ba.
Abdulazeez bai taba jin ya ji nauyin mace a rayuwarsa irin wadda ya ji yau na matarsa Hafsat ba. Ko ba ta fada ba bai yi niyyar maida hoton Muazatu falo again ba don mahaifiya ba wasa ba ce. Ba ya son tuna kalaman da Mammah ta yi amfani da su a kan Muazatu wadanda sun kara farkar da shi ya san cewa akwai babban aiki a gabansa. Mammah ba za ta taba son Muazatu ba komin sauyin da lokaci zai kawo. Shi ma kuma ba zai daina sonta ba komin sauyin da lokacin zai kawo.
Babban kuskuren Abdulazeez tunda ya fara soyayya da Muazatu bai taba bai wa Allah zabi a kai ba. Abin da ya sani kawai yana sonta, dole ya samar wa zuciyarsa abin da ta ke so don bai iya jure zama loser a komai. Not even in the court of justice. In aka kada shi (wanda da wuya ake samun hakan) har ciwo yake yi. Allah ya halicce shi mutum mai nasara a dukkan abin da ya sa gaba. Yana da yakinin a gaba ma zai yi nasara, zai samu Muazatu kuma zai daidaita da mahaifiyarsa a kanta.
Ita dai Hafsat tunda ta samu kalamanta suka jefa shi a tunani ta sulale ta yi bandaki. Sanda ta fito babu shi a dakin, sai kamshin turarensa. Ajiyar zuciya ta yi ta matsa gefen ibadarta ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallah ta yi nafilfilinta sunkuyawa ta yi ta fada a tunani, abin da ya faru tsakaninsu yan mintuna kalilan ta ke tunawa da shauki mai yawa.Fondest thought! Wato tunani mafi soyuwa a zuciya. Ko ba a gaya mata ba, wannan shi ne romance na tsakanin miji da mata da a shekarunta da rayuwar da ta yi ta tsayin lokaci a cikin masu jajayen kunnuwa ya kamata a ce ta sani. To amma ai kuma masoya ke yinsa kuma ba ya faruwa sai da soyayya. Wannan na nufin..... wannan na nufin... tsakaninta da Abdulazeez Dakata akwai SOYAYYAH???
Tambaya ce da ta yi tsananin zurfi a kwakwalwarta har barin kanta ya soma ciwo. Wata murya ce daga can kasan ranta ta ke cautioning din ta.
Ki yi a hankali Hafsat! Be very careful!! Wannan rayuwar da Abdulazeez ya soma jefa ki a ciki kuma zuciyarki da gangar jikinki suka karbe ta da hannu bibbiyuwill ruin your entire future.tunda ya ce MATAR WUCIN-GADI ce ke, wani abu da Hausawa ke kira dandani haukaci, ya maida ke emotional, kuma ya yi dumping dinki ya dauki wadda yake yi wa so na hakika. Da ma dai a ce zai dauke ki da irin matsayin da zuciyarki ta dauke shi a yanzu ne, amma ki ja babban layi a kan wannan alamarin kowa ya tsaya a limit dinsa har zuwa karshen tafiyar.
Wani karfin zuciya ne ya shigi Hafsa a wannan lokacin. Ta yarda gaskiya ce zallah super ego side dinta ke gaya mata psychologically. Ta ci gaba da karfafawa kanta gwiwa da cewa, gara Abdulazeez ya yi ta fushi da ita, amma za ta tserar da martabarta no matter what! Yana son kansa da yawa duk da akwai adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta so kanta, ta tanadarwa mai sonta na hakika abin da zai yi alfahari da ita. Wanda ba komai ba ne sai cikakkiyar Addah Hafsatu...... Haka kawai ta ji kuka ya zo mata, wanda ba na komai ba ne sai na tausayin kanta.
A masallacin unguwarsu irin fadan da Abdulazeez ke yi wa kansa kenan. To amma ya ya zai yi ne? Shi kansa yana mamakin alamarinsa da Hafsat, yadda yake zama ba shi ba muddin za su kadaice. Yana bukatar amini da zai gaya wa damuwarsa, ya ba shi shawara. Sai dai kuma Allah ya halicce shi wani mutum mai son rike duk wani sirri da ya shafi iyalinsa. Hatta Muazatu ba ta san tsakaninsa da Hafsat ba. A tunaninta rayuwa suke kamar kowadanne maaurata in ta yi laakari da yadda ta kusa rasa shi a kan kalamanta a kan aurensa. Gabadaya manyan abokansa Abdallah, Taufeeq, Esq Ahmad and co. Kalamansu na alkhairi ne a kan Hafsat tun lokacin aurensu. Yarinyar da komai nata da kamalarta sun kayatar da kowannensu, duk da sun lura kamar Abdulazeez ba ya sonta. Ba tare ya yi karatu da su ba, wajen aiki ne ya hada su, don haka ba su da labarin Muazatu kowani abu da ya shafe ta. Abdallah ya taba gaya masa ko bai son yarinyar nan wani lokaci zai zo da zai so ta, ko da zai mata kishiya. A lokacin ya ce da shi, Allah ya kiyashe ni zama da mata biyu. Kuma haka yake har kokon ransa.
Bai taba mafarkin zama da mace sama da daya ba a burikan rayuwarsa. Yana kuma rokon Allah kada ya jarabce shi. Ga shi lokaci sai gudu yake yi yana tunatar da shi manyan alamuran da ke gabansa. Tafe yake daga masallaci zuwa gida yana tuki a hankali yana tunani cikin neman mafita ga rayuwarsa. Yadda yake tafiyar da motar tsammani za ka yi tayoyinta sun lalace ne. A haka dai har Allah ya nufa ya zo gida.
Yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi. Ya fahimci Hafsat ba ta fito ba. Dakin nata ya leka duk jikinsa a sanyaye yake, tana durkushe a kan sallaya ita ba sallah ba, ita ba barci ba. Ya dade rike da murfin kofar yana kallonta, abubuwan da suka far a dakin mintuna kalilan da suka gabata na dawo masa. Wani gajeren lokaci ne da ya kasa gushewa a cikin rai da zuciyarsa. Ajiyar zuciya mai nauyi ta subuce masa, wadda ta ankarar da Addah wanzuwarsa a dakin, duk da kafin hakan kamshin jikinsa ya ziyarci hancinta. Ba ta kawo shi ba ne, saboda yadda suka cakuda da juna a yau sosai ita kanta kamshin creed aventus ta koma yi bakidayanta. Kasa dagowa ta yi ta dube shi sabida nauyinsa da ta samu kanta a ciki tun faruwar alamarin. Kamar wannan shi ne karo na farko, sai da ya kira sunanta.
Dagowa ta yi ta zauna sosai ta dafe gado da hannunta na dama, amma ga mamakinta ta kasa kallonshi. Murmushi ya yi ya shigo har tsakiyar dakin ya tsaya, hannayensa duka biyu zube cikin aljihun bakin jeans din da ke jikinsa.
Yau da wuri zan kwanta, saboda gobe lahadi ina so zan yi sammako, za mu je jihar Adamawa daurin auren kanin wani abokin aikina a Yola, zan samu abokiyar kwana a dakina? Bana jin dadin jikina, ina tsoron kada cikin dare zazzabi ya rufe ni.
Kunkuni ta hau yi tana zumburo baki,kaji wani sabon batu, ya kasa jin me ta ke cewa.
Sake matsowa ya yi ya zauna a gefen gadon daidai hannunta. Da sauri ta janye hannun, Aah Hafsah na fara cizo ne?
Ta yi masa shiru.
To zan samu yar tayin kwanan?
Sunkuyar da kai ta yi tana magana ciki-ciki, sauka ya yi daga gefen gadon ya zauna a gabanta sosai ko ya fahimci me take cewa. Ta yi saurin ja da baya. Da mamaki yake kallonta, ta sunkuyar da kai ta ki yarda su hada ido.
Wani abu ya faru ne bayan na fita? Ya tambaya da murya ta nutsuwa.
Girgiza kai ta yi, Ba abin da ya faru.
Ya ce, Na ga kina ta guduna ne, Hafsat yaushe ta kaimu da haka?
Kwalla ya hango ta taru a gefen idonta tana ta kokarin maida ita. Kafin ta ankara ya dago fuskarta sai kawai ta sake su ta ba su damar silalowa.
“Yaa Sattaru Sutrukal jameel. A fitata da dawowata na yi wani abu da ya bata miki rai?
Girgiza kai ta yi.
To tashi mu je na ce ki taya ni kwana, ina da tafiya gobe da asuba saboda a yammacin gobe za mu dawo.
Mikewa ta yi ba don ranta na so ba sai don a dan zamanta da shi ta fahimci shi mutum ne mai naci a kan abin da ya sa kansa, ba ya niyyar abu ya fasa. Wardrove dinta ta bude ta dauko kayan barci masu kauri ta shige toilet, brush ta fara yi sannan ta yi wanka ta sanya su. Kanta cikin shower-cap ta fito sai digar ruwa ta ke. Fatar jikinta ta kara yin fresh, ga mamakinta har zuwa wannan lokacin yana zaune a gefen gadonta, wayarta da ta sanya a caji ce rike a hannunsa, gallery din wayar ya shiga. Hotunansa ne duk a ciki wadanda Ismael ya turo mata da wadanda bai san a ina ta same su ba. Ga kuma na dinner dinsu da aka yi a A-Class.
Dagowa ya yi da zummar tambayarta inda ta same su, amma sai ya ji harshensa ya sarke. Kai ka ce ta fito ne daga jinsin Somali. Wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa. Turo baki ta yi tana tambayarsa don me yake mata bincike a waya? Budar bakinsa sai cewa ya yi, Don na isa!
Ta sake cuno bakin ta tsugunna a gabansa za ta dauki wayarta, ya ce, Wallahi ki ka sake cuno min baki I will kiss it...
Yadda ya ja lafazin kiiiiiissss din ya sanya ta ba shiri maida bakinta daidai. Za ta mike ya take hannunta mai rike da wayar. Wata yar kara ta saki, Yayan Haleem za ka ji min ciwo.
Ki gaya min abin da ki ke fadi don na ce ki taya ni kwana.
Ta runtse ido don zafi don sosai yake murje mata yatsu da yatsun kafarsa. Da sauri ta ce, Ba fa wani abu na ce ba, cewa na yi sai dai in a kwanta kai da kafa.
Me ye kwanciya kai da kafa?
Don Allah ka daga min hannu, sai in maka bayani.
Tausayi ta ba shi sosai ganin yadda idonta har ya tara hawaye. Hannun ya kamo ya rike cikin nasa yana murza mata, abinki da farin mutum har ya yi jajawur. Ta matse kwalla da hannun hagunta, So sorry! Ya ce, sake zumburo baki ta yi. Amma data tuna abinda ya fada yanzunnan tayi maza ta gyara shi.
Yi min bayani ina jinki, mene ne kwanciya kai da kafa?
Ka sanya kanka inda na ajiye kafata, ko ni in sanya inda ka ajiye kafarka.
Dariya Abdulazeez ya yi, Saboda me to?
Ta yi shiru tare da kwace hannunta ganin ya fara canza yanayin murza mata yatsun,