Showing 99001 words to 102000 words out of 133887 words

Chapter 34 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

573

amma har ta ci awanni biyu a falon babu ko kamshinsa, dole ta koma daki ta shiga kulla wa kanta mai yiwuwa, tunda leken taga ma ba shi da wani amfani a gare ta.
Mafitar guda daya ce, takawa zuwa dakinsa na gidan, abinda ba ta taba yi a zamansu cikin gidan ba. Take kuma kallonshi a matsayin mafi darajar rashin kunya daga gare ta. To amma banda shi babu wata hanyar sake sanya shi a idanunta kafin ya tafi, sai dai ta wayi gari babu shi a gidan, ba ta da hanyar sake dora idanu a kanshi na tsayin lokacin da ba ta sani ba.
Mantawa ta yi da komai (tunanin Mammah, Baba Azumi, Ismael ko Usman wani na iya ganinta) musamman su Usman din da dakunansu ke daura da na juna. Idan ta mutu kafin gobe iyaka su rufe ta su binne su bi ta da addua babu mai dakon zunubanta da ba ta gama istigfarinsu ba kafin mutuwa ta riske ta. Shi wancan din shine kadai yardarsa zata kaita aljannah. Sanda ta hau jefa kafafunta don isa ga dakin nasa bata gama yiwa zuciyarta umarni ba.
Ga mamakinta ma har ta isa dakin ba ta ga kowa ba, tana dai jiyo karar talabijin daga dakin Ismael alamar shi din bai kwanta ba. Dakunan guda hudu ne a jere, biyu na kallon biyu cikin wata doguwar baranda in ka fito daga main parlour. Nashi da na Ismael na kallon na Usmanda na Haleem. Sallama ya kamata ta yi, amma tsoron kada Ismael ko Usman su ji muryarta ya sa ta yi knockingkadan sau biyu, daga ciki ya amsaa hankali.
“Yes.
Ba tareda tsammanin itace ko kadan ba, yafi zaton Ishma ne,sai ta murda kofar ta shiga.
Dakin ba shi da girma sosai, amma an kawata shi da abubuwa masu ban shaawa daidai da bukatar matasa yan boko kuma yayan gata ire-irensa. Daga can gefe akwai study-table da fitilar karatu dauke da manya-manyan littattafai da suka shafi aikinsa, kuma a gefensu ya dora kwanfutar kan tebir (desktop), dakin dai ba neat yake ba amma a tsaftace yake, Baba Azumin da ke sharewa ba ta san inda za ta aje masa wasu abubuwan ba don haka ta ke dagawa ta share ta mayar ta aje. Parmanent kamshin Creed-Aventus shi ya sanyaya dakin. Sannan sanyin da volt-care(air condition) ke fitarwa a speed na karshe ne. Ta san zai iya zama illa a gare ta a matsayinta na mai nimoniya, amma wannan ba shi ne gabanta ba; kallon hadarin kajin da ta karba daga Abdulazeez ne.
Tsaye yake jikin wardrove ta jikin bangon dakin yana fidda kayansa yana jerawa a trolley din matafiya. Da farko ta ci gaba da tsayuwa a jikin kofa bayan ta maida ita ta rufe. Amma ganin ba shi da niyyar ce mata komai kamar ma bai yi noticingshigowar mutum ba sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi. Da gaske fushi yake da ita har yau, fushin da ba ta ga dalilin yinsa ba. Takowa ta shiga yi har gaban gadon ta zauna ta jawo trolley din ta shiga gyara masa kayan ganin dannawa kawai yake ya daina jera su yadda yake yi da farko tun shigowarta. Dakatawa ya yi rike da trouser dinsa ya fasa jefawa.
Malama na sa ki ne? Ko na ce ina neman agaji?
Ba ta kalle shi ba, tana mai cigaba da kimtsa kayan ta ce.
Its my duty!.
Cikin mamakinsu ita da karfin halinta yace.
Cikin thousandsof duties din gaya min wanne da wanne ki ka sani? Ke nan har kina da guts na bugun kirji ki ce kina da wani duty na matar aure?
Ba ta ce komai ba, kayan ta ci gaba da fiddowa tana jerawa, ta lura rigima yake so su yi, ita kuma ba abin da ya kawo ta kenan ba. Ba irin sallamar da ta ke so su yi kenan ba. Jinta ta ke kamar a kan gajimare, tana shawagi a cikin sky-blue rainbow.At least dai ga shi a gabanta.Fada yake yi kamar ba shi bada kakkausar murya da bai taba yi mata magana da ita baamma a kunnenta ji ta ke kamar sarewa yake busa mata. Duk da haka ba ta kallonshi aikin shirya kayan kawai ta ke yi.
Tsayawa yayi akanta hannayensa biyu bisa kugu.
Malama. Nace ki bari ban sa ki ba, afterall ba ki san wadanda nake da raayin diba ba, sai faman danna min kaya kike.Cigaba ta yi ba ta fasa ba.Hakannan bata dago ta dube shi ba. Kafin kuma insubdued(cikin karayar murya) tace.
Sunana Hafsatu ba Malama ba!!!.
Tsaki ya yi. Ki fita don Allah akwai abubuwan da ke gabana ban gama dasu ba,kada ki kara min tension�?.
Kyawawan idanunta ta dago gabadaya ta zube su a kanshi cikin wani irin slowmotion.
Abdulazeez korata ka ke yi???�?

Cikin ido suke duban juna, da wani irin yanayi cikin idanun su, wannan karon shi ya fara kawar da kansa kada ta hango weakness dinsa. Yana kallon wani gefen daban yace.
“Im not sending you out, kawai ina gaya miki kin sa dakin ya yi min kadan.
Kiran sunansa na asaliin full(cikakke) ta yi a yau ya fi komai kassara shi.She spells the name correctlyfiyeda kowa a duniya.Ci gaba ta yi da shirya kayan, sai da jakar ta cika taf! Sannan ta zuge ta. Mikewa ta yi ta tsaya a gabansa, bai fi taki biyu ne ratar dake tsakaninsu ba, idonta fal hawaye.
Tunda nasa dakin ya maka kadan, zan tafi, dama sato jiki na yi na zo duk da risk din da hakan ke da shi in Mammah ta gane na zohar nan,don kawai in ganka, (in yi bankwana da kai), in nemi afuwarka ko na yi maka wani laifi ina sane ko bana sane. Yaya Azeez na ji za ka yi tafiya ne shiyasa na zo, wadda ban san ta mece ce ko zuwa ina ne ba(ko ta tsayin wane lokaci ce). All Icometo say is; all the best. Allah ya yi jagora.
Ta juya za ta fice daga dakin, sai da ta kama handle din kofar dakin ya kira sunanta muryarsa na sarkewa. Kafin ta yi aune hawayen data ke ta makalewa sun zubo, sharr!. Gefen mayafinta ta sanya ta tare su, sannan ta murda kofar ta fice ta rufo masa kofar silently.
Gadonta ta fada ta soma kuka, ba kukan gwasalen da ya yi mata ta ke yi ba, kukan rashin sanin ina za ta sanya kanta in ya tafi ne. Wani irin so ke bin jikinta tun daga ranar da ya furta saki a gare ta, zuwa rana irin ta yau zuciyarta bata taba hutawa ba.Watakila Allah ke hukuntasu su duka kan kuskurensu, da wannan azabtacciyar soyayyar. Ga jarrabawa a gabanta. Ta yi zaton zai biyo bayanta su sasanta, amma har wayewar gari babu ko mai kama da shi balle scent dinsa cikin dakinta. Ko dai wannan na nufin..... wannan na nufin... son da ta ke zaton ya fara yi mata ya daina???
Wannan tunanin ba karamin tashin hankali ya zame mata ba, saboda in ya daina son nata ita yanzu zuciyarta ta sa damba a sonsa da kaunarsa! Idan kuma hakan jarrabawarta ce tana rokon Allah ya ba ta ikon cinye ta da A1s, amma hakika za ta bashi sarari kamar yadda ya bukata.
Washegari ita ce farkon fitowa. Tun shidda ta yi wanka ta shirya, takwas na safe za ta shiga dakin jarrabawa ta fito goma na safe. Ta shirya tsaf ta fito kitchen cike da tunanin wa zai kai ta makaranta yau? Dole Usman zai kasance tare da Yayansa a airport. Salisu shi ne last hope dinta, amma ba za ta iya tuna rabon da ya kaita wani waje ba, Mammah ba ta sanya shi, amma dole yau shi din za ta nema. Burinta ta riga Abdulazeez fita daga gidan nan. Cikin ikon Allah ta tadda Usman a kicin ko me yake yi? Oho! Kayan barci ne a jikinsa yana tsaye jikin firji yana shan ruwa. Ido ya gwalalo,yana mata duban tsoro. Hey! Mrs Mungo park! Ba dai har kin shirya ba? Ba sai 8am za ki shiga paper din ba?.
Marairaice fuska ta yi yadda zai ji tausayinta. Ban karanta komai ba ne jiya shi ya sa nake so in je da wuri in nutsu in durawa kaina wani abu kafin lokacin ya cika, don Allah ka taimaka. Ba ta taba nadamar rashin koyon tukin mota ba sai yau. Mammah ta yi-tayi da ita sai ta ce tsoro ta ke ji. Ya rufe firjin ya ce.
Kin yi sallama da mijinki?
A gajarce ta ce. Na yi.
“Wouldnt you take him to airport?
“You are too inquisitive. Ta ce a gundure.
Kada kafada ya yi irin na (bai shafe ni ba), sannan ya ce. Mu je.
A kofar(library) ta zauna ta bude handouts dinta. Ita a dole ba ta da damuwa banda ta yadda za ta tsarge course din. Amma sai me? Shafi bayan shafi, layi bayan layi fuskar Abdulazeez Dakata ne yana murmushin nan nasa. A karshe rufewa ta yi ta sanya kanta cikin cinyoyinta ta baiwa tunanin nasa da soyayyar tasa fili su sha sharafinsu, ta bar wa Allah komai. Idan tana da rabon cin wannan course (Introduction toHuman Geographies) Allah ya yi kudurarsa a kanta.
A kan idonta masu kula da labirare suka bude. Ita ce farkon shiga, a can ta cinye lokacinta, ban da tunani da bege babu komai a cikin kanta. Tunanin ko za ta sake ganinsa nan kusa? Ko zai sake tunawa da ita, ko kuma wata sabuwar Muazatun zai je ya samo? Ko suna da rabon sake zama tare? Ko Mammah ta datse auren kenan har abada? Tunaninnika ne ga su nan fal wadanda ba ta da amsar ko daya. Ban da zafin zuciya da azabtar da kwakwalwa ba abin da suke sanya mata. Agogon hannunta na bakar fata samfurinpolo ta duba sai ta ga saura mintuna talatin a shiga paper.
Wani irin kuzari ya shige ta da taimakon Allah ta soma fahimtar bugaggen rubutun takardar da wanda ta yi jotting da hannunta. Kafin karfe takwas ta cika ta samu abin da ta samu da yake shes born gifted. Sau uku in ta bi topic kawai komai yawansa ya zauna mata.
Sai takwas ta tattara ta fito daga dakin karatun. A kofar lecture hall ta hango Rabia Sada, daga nesa suka daga wa juna hannu, sannan kowacce ta shige.
Usman bai zo daukarta ba sai karfe goma sha biyu na rana. Daga airport suka zarto bayan sun ga tashin Abdulazeez. Abin mamaki ta gansu (full house) duk a cikin motar. Motar da Daddy ya fi ji da ita duk cikin motocinsa. Wata ash-colour (Hyundai 2018 model) mai cin mutum takwas. Mami ba ta kara tsinkewa da lamarin Hafsat Dakata ba sai yau. Daddy ne a gaba, sai Ismael direba. A kujerun baya Usman ne da Mammah. Tare da Rabia suka iso jikin motar ta gaida su Mammah, ta amsa da faraa haka Daddy ya sa mata albarka.
Ta ce, Mommah ita ce ta yi covering dina duk abubuwan da suka wuce ni lokacin da na dawo daga Jimeta.
Madallah-madallah Mami Sada, Allah ya saka da khairan.
Daga nan suka yi sallama, sun ce ta zo su sauke ta, ta ce mijinta yana hanya, Mammah ta ce a ina suke zaune? Ta ce a Kubwa.
Insha Allah watarana Hafsat za ta zo gidanki, Allah ya yi albarka.
Sosai Maami ta ji dadi, a yadda ta gansu high class haka ba ta zaci za su yi wannan saukin kan ba. Daga ganin Baban nasu ba karamin mutum ba ne. Ta fadi a zuciyarta.
Suna tafe a hanya Daddy ke tambayarta ya jarrabawa? In ce ko ta rubutata da kyau? Murmushi ta yi, wannan jarrabawa ai sai taimakon Allah, in ta samo C she deserves a medal! Mammah ke gaya mata Haleem na zuwa gobe. A ranta ta ce, Wani na zuwa wani na tafiya, wanda Allah ya baiwa yaya da yawa nagartattu ya gama masa komai a rayuwa. Ko ba komai ta ji dadin albishir din zuwan Haleem din. Ta tabbata zai debe mata kewa, abokin kokawa, abokin wasan tseren keke, abokin kowacce dabdalar kuruciya.
Washegari Haleem Dakata ya iso, har da ita aka je filin jirgin saman Abuja dauko shi. Ya kara tsayi sosai, sai dai yaan nan da lange-langen jikinsa. A da tana ganin Usman ya fi kowa kama da Abdulazeez, ashe akwai wanda ya dame shi ya shanye cikin yayan gidan. Wannan har tsayuwarsa har tafiyarsa, har murmushinsa Abdulazeez Dakata ne. Yana saukowa daga jirgi ya cimmasu, babu Daddy tare da su yana office, su Ismael ya hau rungumewa, ya rungume Mammah har da kwanciya a kafadunta, ita ce ta ji kunya ta ture shi.
Ya ce, Mammah ki bar ni in ji duminki, wa ya yi dadewa irin tawa ba tare da ke ba?
Ta ce masa, Ka girma. You are no more a child now. You are Arch. HaleemDakata.
Lumshe ido ya yi, sannan ya iso ga Hafsat, Addar Mammah, an kara tsufa, kin haihu?
Harararsa ta yi, ta ce.Da na san abin da za ka yi min kenan da ban zo tarenka ba.
Yi hakuri, kada ku kai ni kotu, whereis he?
“I dont know!�?. Ta sha kunu sosai ta zumburo masa baki. Dariya ya yi, ya ce, Mammah ina mijinta?
“In the U.S. Ta fada a gajarce, sannan suka rankaya suka nufi mota. Sai hira yake saki kamar rariya.
Anyi girke-girke na musamman don tarbar Haleem. A raayin Hajiya maryam ba ta da son yan aiki barkatai su cika mata gida. Tun tana amarya yar aiki daya ta ke dauka a cikin gida, sai maza na waje don kula da harabar gida da aike,guest house da sauransu. Sai ko maigadi, hatta wanki da guga dry-cleaning suke kaiwa duk don kada ta cika gida da hadimai. Tana da kwazo, juriya da himmar hidimtawa iyalinta. Da wuya a yi mata girkin mijinta da yayanta sai bisa lalurori irin wanda dan adamya gada, kamar rashin lafiya ko tafiya.
A tasowar Hafsat-Suhaanah sai suka hada hannu musamman da suka dawo Nigeria inda Hafsat din bata zuwa makaranta. Ayyukan Baba Azumi sun fi karfi ga wanke-wanke da share-share, goge-goge da wankin bayan gida. Sai sauran hidimar kicin. A yanzu Azumi shekaru sun tura karfinta ya ragu sosai, tana so ta samu lokaci ta gaya mata ta samo mata wata cikin iyalinta mai kuruciya ba don ta sallame ta ba, sai don yanzu abubuwa da yawa nauyin shekaru ba ya barinta ta yi mata su yadda ya kamata. So throughout ranar saboda zuwan Haleem ta zama busy ba ta samu lokacin zama ita kadai ba balle tunani ya aure ta, kuma ba ta da paper, inda duk ta gifta don kawowa Haleem abin da yake bukata sai ya tsokane ta, kiranta yake Senior Aunt. Shi yanzu ya daina kokawa da ita. Shes lookingolder and older saboda aure. Mammah kadai ke tare mata, ta ce su din ma watanni uku ta ba su su fiddo matan aure, ban da shi tunda bai gama ba. Ismael sai ya shafo kai ya ce,
Mammah mu ai mun dade da wuce wurin. Na gaya miki kullum zance nake zuwa a Apo gidan su Wasila. Ke kawai muke jira ki ce kule mu ce casss.
Usman sai ya yi tsaki, ya ce, Kai wallahi ban ga me ka gani a Wasilar nan ba, yarinya baka kirin mai kirar samudawa? Ni Mammah ai irin auren Yaya Azeez za ki min, ki je Kano cikin yaran nan ki dubo min kawai.
Mammah ta dinga shi masa albarka. Ismael ba ta hana shi ba, amma har ranta ba ta son auren bariki, balle irin wadda Ismael ya kallafawa rai, ba ta zaton za a samu yadda ake so daga gare su a gidan aure saboda budadden ido da gata da yayi musu yawa. Sannan su zo su janye dan daga jikin uwarsa da yan uwansa. Ta sha wahala a kan soyayyar Abdulazeez da Muazatu, ba ta fatan a sake maimaitawa.
Da daddare bayan sun yi dinner, Haleem ya ce da Suhaana yana son kunun gyada, Mammah ta ce Azumi ta yi masa ya ce shi sam na Suhaanah yake so ba na tsohuwa ba, ko ita Mammah da kanta ta yi masa. Ta ce ita ta gaji da tsirfarsa tunda ya zo bai barsu sun huta ba.
Hafsat ta ce, Mommah, bari in yi masa mana? Bakonka Annabinka.
Ta mike ta shiga kitchen.
Tana cikin aikinta ta jiyo ihun Haleem cikin murna yana fada wa Mammah Yaya Azeez na kira, a sailin wayar Mamman ce a hannunsa yana daukar lambobin yan uwa da abokan arziki da ba ya da su don ya kirasu ya gaishesu, kawai yaga kiran lambobin U.S. Hafsat na jin yadda rigima ta kaure a kan wanda zai fara magana da shi. Daga karshe dole sai a handsfree aka saka kiran suka taru har Mammah. Kafin ya ba wa daya amsa daya ya jefo tasa tambayar. Duk dai a kan yadda ya sauka ne da yadda ya tadda wajen, how much suka yi kewarsa da sauransu.
Runtse idanunta ta yi tana jin wani irin fili fetal a zuciyarta. It was like babu komai a birnin zuciyar sabida kewa. Kamar an yashe komai da ke cikinta. Birnin zuciyar is just empty! Wanda ya yi gininnika a cikinta ya yi kaura tare da komai da ke cikinta. The feeling is emotional mai ratsa zuciya da ruhi. Ba ta kara gane me ta ke yi a cikin kitchen din ba ko me ya kawo ta. Ta ga dai shigowar Mammah da sauri ta nufi gass da azama ta kashe wuta na tashi daga cikin karamar tukunya. Ta dauke tukunyar da karamin towel ta jefa ta a sink ta kunna mata famfo. Ta dubi Hafsat da ta yi tsuru-tsuru ta ce, Addah are you alright?�?
Daga mata kai ta yi, To tunanin me ki ke yi haka na ji shirunki ya yi yawa? Daga dama kunun gyada, I then decided to check on you, sai ganin wuta na yi na tashi daga tukunya, in ce ko lafiya ki ke?
Kai ta daga mata cikin sanyin jiki ta gaza cewa komai. To ta ce me? Your son is drivingme crazy? Ba ni da tunanin komai sai nasa, ya maida ni emotional ya gudu ya bar ni? Da ta tabbatar ba za ta yi magana ba sai ta ce, Ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login