Showing 132001 words to 133887 words out of 133887 words

Chapter 45 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

558

Allah, na ji na yi laifi, ina ba ku hakuri dukkanku.
Sosai ya ji tausayinta, domin tuni har kwallah ta taru a idanunta.
Ba za mu hakura ba, sai in kin yarda ki samo mana kani ko Babata Habibah a yau.
Zaro idanu ta yi, Haba-haba Abban Khalipha! Ku ji tausayina mana!
Sosai ya ga tsoro da fargaba cikin fararen idanunta, duk kuwa da dadin da ta ji na jin cewa da ya yi zai yi wa Habibah marigayiya takwara. Mikewa ya yi ya dauke yaron daga tsakaninsu ya maida shi gadonsa. Dawowa ya yi ya daga duvet din ya shige jikinta sosai.
Ni, da ke, da shi, wa ya fi cancanta a fi tausaya wa? Ni da na shekara babu mata,a gabadayaya shekarun kusan uku da aure baifi sati biyar kacal na mallaki matar ba, da ke da ki ke tsoron wani cikin bayan kina cikin koshin lafiya, ko kuwa shi da ko yau aka haifi wani zan taya ki mu yi ta rainonsu?
Hafsat ba ta iya ta yi magana ba sakamakon sakonnin da ya soma aikawa cikin illahirin gangar jikinta. Ga son mijin, ga kewarsa, ga kuma matsanancin tsoron rainon ciki da gumurzun nakuda. Su suka taru suka hana mata nutsuwar da Abdulazeez ke so ta yi. Ya fahimci halin da ta ke ciki, kuzarinsa ya ragu kashi talatin cikin dari, ya rungume ta sosai cikin rawar murya ya ce
I will not to anything without your consent (bazan yi komai ba sai da amincewarki), ko da hakan na nufin ni zan cutu, sai dai na yi alkawarin zan taya ki da hidimarsu ko kullum za ki haifo min dozen.Ina da yadda zan kula da ku Hafsah, da zan iya zan cire miki ciwon nakudarsu, amma da ba zan iya ba zan yi wanda zan iya. Its a promise.
Hawayen tausayi da kauna suka kwaranyo mata. Ba ta yi magana ba, amma martanin da ya soma karba daga gare ta shi ya tabbatar da amincewarta. Ita din mai kunya ce ya sani, amma yau ta ajiye ta a gefe. Burinta daya ta faranta amsa da iyakar iyawarta ko da hakan na nufin duk bayan wata daya za ta haihu. Idan za ta haife kasuwar Kwari duk shekara in dai da Abdulazeez ne, tana maraba da ita.......!!!

A wannan ranar, sai ya zamanto kamar dukkaninsu are new to the system..... Kamar koyar da juna suke yi... Kamar kuma directing juna suke yi..... Kamar kuma wani abu makamancin hakan bai taba faruwa a tsakaninsu ba!!! Kowannensu tsoro yake ji, tsoron kada ya bude ido ya tarar mafarki yake yi, mafarkin cewa haka za su rayu da juna har karewar numfashinsu.





MURFI
BAYAN SHEKARU GOMA
Abubuwa da yawa sun faru a wadannan shekarun guda goma masu kama da kiftawar ido. Auren Ismael da masoyiyarsa Waseela Faruk, Usman da Halima diyar Anty Luba, Arch. Haleem Dakata da amaryarsa Saima diyar Anty Mariya. Wadannan dukkaninsu manyan maaikata ne yanzu, Haleem na aiki da kamfanin gine-gine na Julius Berger, Ismael software Engineer ne da kamfanin Microsoft Corproration reshen birnin Honk-Kong din China, Usman maaikacin kamfanin oil and gass na Oriental Energy mallakin Muhammed Indimi. Yayin da mai gayya Yayan kowa Uban Abubakar ke ta taka matakai na nasara kala-kala a aikinsa (as a Civil Lawyer) mai tsayawa alummar kasarshi Nigeria masu rangwamen gata da aka zalinta ko aka dannewa hakki dadukkan karfinsa,ilmin sa har ma da aljihunsa,da jerin hulunan nan masu wuyar samu guda uku; LLB (Civil Law), BL, L.LM (Civil Law), tare kuma da jerin yayansa guda biyar, maza hudu mace daya; Abubakar, Umar, Usman da Aliyu, ga kuma auta Habibatu (Hibbah). Bayan kwashe shekaru goma yana (practicing Bar), yayi applying a (Judicial Service Commission),bada jimawa ba aka yi shortlisting dinsa cikin masu yin jarrabawar (conversion from Bar to Bench)yayi interview. Kamar koyaushe Abdulazeez mai nasara ne balle akan aikinsa da wannan enthusiasm din nasa na komawa Mai shariah daga Bar.
A wannan lokacin Hafsat-Suhaanah Allah ya cika buri; B.A ED, M.ED, PhD in Geography.Dr. Hafsat Hamza Atiku kenan uwargida ga Justice Abdulazeez Hamza Atiku. Ta fito da kwalin doctorate ne a wannan Shekarar. The tsruggle contineous as an educational researcher....... Yau an kawo hula ta karshe komai ya zama tarihi. Bayan kammala Doctoral dinta da shekara daya a yanzu haka shirin bude makarantarta ta kanta iyayenta da mijinta Justice Dakata ke yi wadda za a bude a garin Jimeta/Yola. Makarantar sakandire ce mai hade da Primary da Nursery.
Ba da jimawa ba aka yi luncheon din bude makarantar mai suna HABIBAH BABBAH MODEL SCHOOL. Wannan makaranta private school ce, amma ba mai tsadar da mai karamin karfi bazai iya biya ba. Yan uwanta maza uku Modibbo, Imaamu, Abdurrahman da kawunta Nuru autan Daada wanda dama tsohon malamin makaranta ne su suka kama mata komai. Don haka yanzu tana yawan zuwa mahaifarta Jimeta a matsayinta na principal. Abbanta wanda yanzu ya yi ritaya shi ya maida ita ta maye kujerarsa a FUTY (as a part-time lecturer). Duka yayanta maza suna hannun Mammah, Hibbah ce kawai tare da ita, wadda ta zame mata cingam a duk inda ta shiga, ita ma don ba ta isa shiga makaranta ba ne Mammah ta kyale mata. A cewarta mutanen da ba sa wuni a gida ba za ta bar musu yaya a hannun su ba da ranta da lafiyarta tunda ita bata aikin. Ko basa wannan jigilar ayyukan nasu butin Mammah ne rike dukkan jikokin ta. Abdulaziz din ne dama mai kulaficinsu ban da Hafsat wadda ke jin ko yaya dari ta haifa Mammah ta ce ita za ta rike a shirye ta ke da yin hakan wholeheartedly, sai dai shakuwar Abubakar (Khalipha) da mahaifinsa wata irin shakuwa ce ta daban data sauran yayan da kowa ya san Abdulazeez ba zai iya barwa Mammah shi gabadaya ba. Duk Jumaah in ya taso aiki yake sa wa a dauko shi tunda a weekend suna gida shi da Addah sai lahadi da dare ake maida shi Asokoro.
Sun dade da tashi daga gidansu na Sun-City, Abdulazeez ya yi gini da kansa a Apo. A cewarsa gidan Sun City mallakin Abubakar Sadik Khalipha ne.
Amintarsa da abokan aikinsa, Ahmad, ESQ Abdallah da Taufeeq sai abin da ya yi gaba, wanda zumuncin ya shafi matansu da yayansu, Sagir kuwa wannan mai dungurugum ne matsayinsa na kawun Hafsat. Duk da yanzu kowannensu ya bar Abuja da tarin ci gaba; Ahmad na Lagos, Taufeeq na Court of Appeal ta jihar Oyo, Abdallah na garinsa na haihuwa Taraba da kotun jihar (Magistrate Court) matsayin Judge, surukinsa Sagir kuwa an maida shi Porthercourt.
Hafsat ba ta yada Rabia Sada ba, bayan sun gama degree a Nile aka yi wa mijinta Sadik sauyin wajen aiki suka koma Kaduna. Har kaduna Abdulazeez ya kai Hafsat wajen Mami saboda ta gaya masa irin taimakon da ta ke yi mata in ta kara hutu, haka da laulayin cikin Khalipha Mami ta taimaka mata sosai. Hafsat ta gane cewa, kawaye da ta ke gudu ba duka ne bara gurbi ba a kan Rabia Sada, tsakani da Allah Mami ta ke kaunarta, tuni ta sallama suke zumunci ta waya har gobe. Mammah ma na bayan wannan kawancen, don haka ko hanya ce ta bi da su Kaduna in za su Kano sai sun tsaya wajen Mami.
Mammah ta samu surukarta Wasila matar Ismael ba yadda ta ke tsammani ba, ta gane ba duka yayan masu kudi ba ne marasa tarbiyyah. Ba duka girman Abuja ba ne marassa kunya ba. Ya danganta da tarbiyyyar cikin gida da yammatan suka samu. Wasila dai a Abuja aka haife ta, ta kuma girma a can ta yi karatu a kasar Russia amma yadda ta ke bin Ismael sau da kafa ta ke karrama ta kamar sauran ya sa Mammah ta yi saranda. Ba a gane mutum mai tarbiyya by social status, abin a zuciya ne. Mutum na gari Allah daban yake halittar sa. Duka surukan nata ba ta da mastala da su, don Saima da Halima ita ta karasa rikonsu a gidan mazajen a hannunta suka bude ido da rayuwar aure. Ko gobe suka hadu da Ismael sai sun yi ta sun kasa jituwa har gobe. Wasan kanin miji mai shegen zafi (sunan wani littafin TAKORI).

A wata sharia da Abdulazeez ke jagoranta a Federal High Court Abuja, rannan cikin lauyoyin shariar ya ci karo da Muazatu Rufai matsayin lawyer mai kare wanda ake tuhuma. Ya gane ta, ita ba ta gane shi ba saboda canzawar da kowannensu ya kara yi. Dadin dadawa ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan matakin ba. Bayan gama shariar ita ta yi winning. Kamar yadda yake mai sharia shi ke fara tashi bayan kammala shariah. Muazatu tana tattare takardunta lokacin da Justice ya mike zai wuce ta hanyar da ya shigo, karaf! Suka hada ido. Murmushi ya yi ya dan dakata ya ce da ita, Congratulations Barrister Muazatu, I know you can make it tunda na hangoki.
Itama murmushin ta yi cikin kore shakku da dimbin mamaki.Thank you My Lord. I Absolutely believed you will come to Bench someday, but I never ever thought it will be so soon like that. A gaida SUHAANAH.
Jinjina kai ya yi, tare da yi mata godiya da fatan alkhairi. Ta bi shi da kallo har ya kulewa ganinta, wani abu na dan taba zuciyarta mai kama da tasowar tsohon miki, amma da ta tuna Barrister Muntada da irin rayuwar farin cikin da ta ke samu tare da shi, ga albarkar zuria har shidda, a take ta daga hannu ta godewa Allah.
Ta ce a ranta, Ba duka abin da muke so a rayuwa muke samu ba, in mun yi tawakkali mun bi iyayenmu, sai mu zauna lafiya.
******
Lokacin da zaayi bikin baiwa Abdulazeez (Chief of the Justices of the Federal High Court) ma sun sake haduwa, wannan karon Hafsat da yayanta suna tare da shi itama tareda mijinta Muntada da nata yayan. Kallo daya Hafsat tayi mata ta gane ta, ko don hotonta da ya shekare mata a falo. Ko taji wani abu a ranta yau kam tafi karfin kishin ta. Duba da cewa Muazatun bata nuna komai ba sai kauna da kulawa ga yayanta. Itama sai ta ja nata a jiki har sukayi hotuna tare.Sun zo ne musamman tun daga jihar Lagos don halartar wann kasaitaccen bikin karin girma da kasar Nigeria ta baiwa Justice Abdulazeez Dakata sakamakon jajircewa da sadaukar da kai irin nasa na tsahon shekaru ga kotunan Nigeria, ba kuma karkashin gayyatar kowa ba sai kasancewar su karkashin umbrella guda na aiki da proffession. Justice ABDULAZEEZ HAMZAH ATIKU da HAFSAT-SUHAANAH nima ina fatan alkhairi.
-Takori
June, 2019



Masha Allah laquwwata illa billah.
Nan na kawo karshen littafin AUREN KWANGILA. Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah Ya yafe mini. Darussan alkhairin da ke ciki Allah Ubangiji ya hada mu cikin ladan ni da ku baki daya.

Sai mun hadu a sabon littafina AALIMAH nan ba da jimawa ba insha Allah. AALIMAH sabon salon rubutu ne a cikin jerin littattafan Takori. Idan nace yafi min sauran ko nayi kuskure to kadan ne don ina ji da shi (on its own). Mu hadu da Aalimah Mansour Raazee a cikin littafin AALIMAHdon jin irin nata kaddarorin and her journey to diaspora..
Taku har abada,
Takori.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login