Showing 120001 words to 123000 words out of 133887 words

Chapter 41 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

544

kofar. Hafsat ta yi arba da kyawawan matan turawa guda biyu, amma dai da fararen kayan maaikatan jinya a jikinsu. Wani murmushi suka kashe ta da shi, kowacce ta kama hannunta daya suka yi gaba da ita zuwa farar ambulance din da suka zo a cikinta. Ta waiwaya hagu da dama babu Abdulazeez babu alamarsa, ya gudu ta inda ba ta sani ba. Ta so yi musu gardamar kin shiga motar, ta ga za su gwada mata karfi duk da dai lallashinta suke yi, amma fa ba ta ga za su yarda da abin da ta ke so ba. Sai tsintar kanta ta yi a wani kyakkyawan asibiti.
Abin da ta ke gudun shi aka fara yi mata, tana kuka tana komai. Ta sha allurai kala-kala, kulawa dai zallah kamar tana gaban Mammanta. Zuwa washegari dai kam da kanta ta nemi abinci white rice and stew, haka suka kawo mata. Lallabata suke kamar kwai in ta tambayi mijinta su ce sai ta daina kukan allura za su barshi ya zo. Kwananta uku ta samu karfin jikinta sosai, haraswar ta tsaya, sai mugun cin abinci kamar tashin hankali. Magungunan da za su kara mata karfi da lafiya suka bata suna kara jadda mata ta dinga sha kullum kuma ta dinga kula da kanta. A daren ranar suka sallame ta, ba ta ga Abdulazeez ba sai lokacin. Bai ce komai ba ya kamo hannunta yana sakar mata wani irin murmushi, suka shiga taxi ta kai su gida.
Suna shigowa falo ya wani irin juyo ya sure ta bai dire ta a koina ba sai dakin barcinsu. Ba don kar ya saukar mata da hajijiya ba juyi yake so ya yi ta yi da ita. Idanu ya zuba mata kamar zai cinye ta. Kafin ya mirginota ta dawo samansa, ya ce, Kin san wani abu?
Hafsat wadda duk ta bi ta tsorace da abubuwan da yake yi masu kama da na sabon kamu, ta ce, Aa, ban sani ba.
Har na soma hango ki kina breastfeeding Hafsat. Oh me! Ya rungume ta.
Hafsat wadda ta ji zancen a baibai ba ta fahimce shi sosai ba. Rokonsa ta ke ya gaya mata abin da yake nufi da hakan amma ya ki, hanyar faranta ran junansu yake bi kala-kala, lungu da sako kusufa-kusufa. Ranar yau ta kasance cikin jerin ranakun farin cikinsa a rayuwa, ba zai taba mantawa da ita ba. Its a SECOND day in historybayan ranar dawowar ta cikin rayuwarsa. Abin da ya ce mata kawai kenan. A karshe da suka koma cikin consciousness ya damka mata passport dinta da tikitinta. Muryarsa abin tausayi ya ce.
Na amsa wa Daddy da Mammah za ki koma gobe. Hafsat na ba ki amanar kanki da kanki da ta abin da ke cikinki. Ban yarda ki jigata shi saboda bokon nan naki ba. Ni ko third class ki ka fiddo in dai BABY na zai zo cikin koshin lafiya Allah ya sanya albarka. Aclass of degree ba shi ne matsayin ilmi ko kokarin dalibi ba. It determines the condition da dalibin yake ciki a yayin karatun, duk da kokarin ma yana taka muhimmiyar rawa. Iwill come soon... and I will miss you soon. Ya kwantar da kai a kafadunta. Yayi shiru.
Hafsat is speechless. Cikin tarin zantukansa masu kama da wasiyyar bankwana sentencedaya ta tsaya mata a rai, Amanar kanki da ta abin da ke cikinki. Which means ......an gaya wa Yaya Azeez she is pregnant a asibiti, dalilin farin cikinsa haka kenan. To shi cikin haka ake samunsa cikin dan lokaci kalilan? Kamar kiftawar ido? Kamar a majigi? Shekara daya da doriya ba a same shi ba sai yanzu? Zancen zucinta ya subuce ya fito fili.
Dariya sosai ta baiwa Abdulazeez ya dago kansa daga kafadunta ya dube ta cikin ido da idanunsa da ke sanyaya mata zuciya.
Saboda wancan lokacin its a crime in Nigeria. Yanzu kuwa baa Nigeria muke ba,it is allowed here in the U.S.
Ita ma sai abin ya ba ta dariya, ta tuno lokacin da ta zauna tana zancen da shi babu ko kunya. Kai ta rafka wauta a baya, kada Allah ya maimaita. A daren ya hada mata kayanta da tsarabar da ta dade tana jida. Har Baba Azumi ta samu dogayen riguna biyu masu kyau na masu jini a jika. A daren gabadayansa cikinsu ba wanda ya runtsa..., The farewell is very very emotional (bankwanan ma taba zuciya ne). Soyayyar cikinsa is an extraordinary (babu kamarta a tarihin rayuwarsu). Alkawururruka suke daukarwa juna kamar ba za su kara haduwa ba sai a Darussalam. Duk da bakin Hafsat ya mutu, tun daga jin labarin ta kusan zama UWA, uwar ma ta jikokin Hamzah Atiku da Maryam Dakata; mutane mafiya darajar girma da kima a gare ta fiye da kowa a duniya in ka cire wadanda suka yi silar zuwanta duniya. Shin ko adadi nawa za ta so wannan Dan? Mai cin tudun soyayya uku a zuciyarta???
Na farko na kasancewarsa Dan da ya fito daga mahaifarta, na biyu na kasancewarsa daga jinin jikin ABDULAZEEZ Hamzah Atiku; wani kwayan mutum guda daya da ta ke so da dukkan ruhi da zuciyarta da soyayyah marar misali. Na uku kasancewarshi jikan Mammah. Jikan ma na farko da bata taba dauka ba sai a kansa.

Sai da aka sanar cewa za a rufe jirgin sannan Abdulazeez ya raba Hafsat da jikinsa. Suna daga tsaye ya kowa ya shige ya barta. Ita ce karshen shiga ta zauna a (first class seat) dinta yadda tazo daga barin dama ta barshi tsaye ya zuba hannayenshi cikin aljihun bakin wandonNordstrom da ke jikinsa da farar T/shirt Tommy Hilfiger. Har ta bace wa ganinsa murmushi ne a kan fatar bakinsa, image din wannan yanayin da wannan ranar ya zauna mata a zuciya. Lokacin da jirgi ya karci kasa ya lula sama cikin hazo sai ta sa hannayenta biyu ta dafe cikinta. Wata amana da ta karba da hannu bibbiyu ta ke rokon Allah ya taya ta rikonta. Ta zame musu sanyin idaniya dukkaninsu, kuma nauin farin ciki ga iyayensu.

******
Hafsat ta sauka lafiya a Abuja. Kwananta biyu ta huta gajiya, sannan ta koma makaranta. Ta tarar Haleem ya koma makaranta, Ismael da Usman na shirin tafiya hidimar kasa. Baba Azumi jikin girma ya motsa ba ta da lafiya, yarta Harira ta zo daga Sokoto wadda ta zauna da ita a gidanta tana amarya tana taya Mammah kula da ita, Mammah ta yi sabuwar mai aiki Jummai daga Minna ta ke. Ita da Harira suke zaune da Mammah kafin Harira ta koma Sokoto, saboda ta baro mijinta da yaranta. Jummai na da kirki sosai da faram-faram nan da nan suka saba. Ta ji dadin ganin Harira matuqa, Mammah ta gaya mata kullum sai ta yi zancenta. Nan da nan suka taru suka debe mata kewar Abdulazeez kasancewar daga Harira har Jummai masu son barkwanci ne na a buga a jarida.
Mammah kula ta ke da Hafsat da mugun cin abincinta yadda ya kamata da duk abin da mace mai juna biyu ke bukata. Salisu ke kai ta makaranta ya dauko ta, da daddare in za ta kwanta sai ta girke mata (food flask) a gefen gadonta saboda tashinta cikin dare cin abinci. Bayan wannan ba ta fuskanatar wata matsala, ko kwana biyu ba ta yi ba daga Jummai har Harira sun gane matsalar Hafsat din duk da Mammah bata fada musu ba. Sai suka kara zage damtse wajen taya ta kulawa da surukuwarta ko kofi ba sa bari ta wanke.
Baba Azumi na jin jiki sosai, ciwon kafa da ciwon baya daga karshe sai kwantar da ita aka yi a asibiti gabadaya. Kullum da daddare suna midnight call dinsu don lokacin ne kadai Abdulazeez yake free, komai ta yi a rana sai ta sanar da shi, shi ma duk abin da yake ciki sai ta ji. Harira ce ta ke kwana da mahaifiyarta Azumi, Mammah da Jummai na jigilar abinci, Hafsat ma kullum ta taso makaranta can ta ke fara biyawa sai dare suke komawa gida tare da Mammah. Asibitin yana da kyau sosai wanda iyalan gidan ke zuwa ne (Diff hospital) Hafsat ma anan take ganin likita, tana samun kulawa sosai. Kullum sai Hafsat ta gaya wa Abdulazeez damuwarta a kan ciwon uwar goyonta, ko tafiya ba ta iya yikuma Mammah ba ta bari ta kwana. Hakuri yake bata, ya ce. Ke ma patient ce. Insha Allah za ta tashi, girma ne.
Washegari Mammah ta tura Salisu da babbar mota har Sokoto ya debo yayan Azumi gabadaya su zo su duba ta, suka kuwa taho kwansu da kwarkwatarsu da yayansu sai da Salisu ya biya kudin motar haya bus guda daya suka taho tare, saboda motar ta gagara kwashe su. Baba Azumi sai budar ido ta yi ta ga yayanta maza da matan zagaye da gadonta kamar a mafarki. Sai da ta yi kuka don dadi, ta yi ta yi wa hajiya Maryam adduar alkhairi.
A tsakiyarsu ta hango Hafsat rungume da daya daga cikin jikokinta ta saje a cikinsu sai hira suke yi. Hawaye ya kara zubo mata ta ce a kirawo mata ita, hannunta ta kama tana ta yi mata addua tana fadin Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya ba ki dan albarka irinki. Allah ya zaunar da ku lafiya ke da mijinki. Allah ya cika miki burikanki na duniya da lahira. Tabbas ke yar halak ce wadda ta san halacci, kin so ni kamar ni na haife ki, mijinki ya kaunace ni kamar ni na haife shi. Allah ya hada kawunnanku ku rayu tare, rayuwa mai tsayi da albarka.
Duk dakin amsawa suke yi da, Ameen-ameen. Ban da Hafsat da haka kawai jikinta ya yi sanyi da wannan doguwar addua da Baba Azumi ke kwarara mata a yau a bainar jamaa. Zamewa ta yi ta koma can karshen dakin ta zauna kanta yana sarawa, don ko ya ya ta yi doguwar tsayuwa sai ta ji hajijiya da ciwon kai. Hirar ta koma tsakanin Azumi da yayanta da jikokinta har Mammah ta iso kawo abincin dare. Ta kuma ce da su su yi sallama ta tafi da su gida su huta gajiyar hanya, su ci abinci.
A guest house dinsu aka sauke su duka, Jummai da Harira na ta shigar musu da abinci na alfarma. Suka kwana cikin jinjina mutunci irin na Maryam Dakata. Uwarsu kam ta zauna da mutanen kirki babu irin alherin da ba ta samu a jikinsu ba, su ma kansu sun huta da su ba wanda bai ci arzikinsu ba. Da safe bayan sun karya kumallo kowa ya yi wanka aka yi shirin komawa asibiti. Sai aka bugo wa Hajiya Maryam waya, Azumi rai ya yi halinsa da asubahin ranar.
Iyakar kidimewa Maryam ta rude, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai ta ke ambata, wayar ta sulale ta fadi daga hannunta. Ta zame ta zauna a gefen gadonta tana ci gaba da salati da dayanta Allah. Ina za ta nemo karfin gwiwar kallon idanun yayan Azumi da jikokinta ta gaya musu gushewarta a doron kasa? Ga Hafsat mai yaron ciki... kawai sai ta fashe da kuka.
A haka Jummai ta same ta, jinta shiru-shiru kowa ya shirya ita ake jira a tafi asibiti. Hafsat ba ta nan tana makaranta. Jummai ta samu Mammah tana gursheken kuka. Tuni jikinta ya ba ta, Mammah ta ce ta hada wayar da ta tarwatse ta miqo mata. Kuka ta ke hawaye sun hade da majina. Jummai ta yi yadda ta ce, ta kira Daddy shi a lokacin ya isa office. Ta gaya amsa, shi da yake namiji ne cewa ya yi, ga shi nan zuwa. Asibitin ya nufa ya karbo gawar don yau Harira ma ba ta kwana wajenta ba, ta ga yan uwa kuma jikin nata ya fi na kowacce rana samun sauqi. Sai ta biyo su. Da nufin a dawo tare gabadaya da safe.
Suna tsaitsaye a harabar gidan duk sun sha wanka sun ci kwalliya, masu goyo sun goya yayansu sai gani suka yi get ya bude, motar asibiti zungureriya ta shigo. Kofofinta suka bude, malaman asibiti biyu suka sauko da gawar a kan gado. Babban danta Yushau shi ne mai karfin halin karasawa ya bude fuskarta da aka lullube. Ai kuwa ya fasa kuka wanda ya tabbatar wa sauran yan uwansa da zatonsu. Daidai lokacin da motar Daddy ta biyo baya, sannan ta su Ismael.
Gida ya rikice ta koina hatta Ismael da Usman kuka suke yi. Yushau ya matsa kusa da Daddy ya yi kuka ya koshi, Daddy na bashi baki, ya roke shi suna so su tafi da Azumi gida Sokoto su yi janaizarta a can. Daddy bai musa ba, nan ya shirya motoci har da shi da yayansa suka dauki hanyar Sokoto, Mammah ta ce za ta biyo bayansu daga baya saboda Hafsat ba kowa a gidan.
A kan hanyarsu ta dawowa gida ta ga Salisu ya dauki hanyar gida maimakon ta asibiti, ta ce, Salisu mu fara zuwa asibiti in ga Baba tukun.
Bai juyo ba ya ce, An sallame ta. Kamar yadda Mama ta tsara masa.
Hajiya Maryam kokari ta yi sosai ta danne alhinin da ta ke ciki, amma ba ta yarda sun yi tsayuwar minti biyar tare ba. Ta tambaye ta Salisu ya ce an sallame ta, kuma na zo gida ban gansu ba daga ita har bakin. Ba tare da ta dube ta ba, ta ce, Sun wuce gida Sokoto da ita, sun ce a can za su karasa jinyarta tunda ta samu sauki. Ni ma gobe zan bi su in kara tabbatar da samun saukin nata.
Ta ce, Mu tafi tare Mommah, na san ba za ki wuce kwana daya ba.
Kai ta girgiza, Kwana uku zan yi, ki zauna saboda makaranta, ko in kai ki gidan Hajiya Halima ko gidan Kawunku?
Ta girgiza kai don ba ta son harkar gidan Anty Zuwaira ba tun yau ba. Zan yi zamana ni kadai, ni da ba wuni nake a gidan ba?
Mammah ta ce, ba zan iya barinki ke kadai ba zan dauko Saadiyya yar hajiya Halima ta taya ki zama.
Ba tare da damuwa ba ta amince.
A daren direban Hajiya Halima ya kawo Saadiyya, budurwa ce ita ma a Nile ta ke karatu. Da suka gane yan makaranta daya ne, sai suka saki jiki da juna suke ta hirarsu. Mammah ta jaddadawa Saadiyyah yadda za ta kula da abincin Hafsat ita abin har kunya yake ba ta, yadda Mammah ke treating dinta ko a gaban waye kamar wata karamar yarinya.
Ta ce, Kai Mommah ita kadai za ta dinga girkin? Tunda mu biyu ne mu yi tare mana.
Ta ce, Ban yarda ba, kin ji na gaya miki. Saadiyyah ko ferar dankali kada ki bata.
Tana dariya ta ce, Toh Mammah.
Hafsat akwai shagwaba, Mammarta ta daure mata kugun yinta.
Da safe Salisu ya kama hanyar airport da Mammah, bayan sun sauke su Hafsat a makaranta, suka wuce zuwa Sokoto.
8/13/20, 8:13 PM - Mmn Nasreem: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Mikewa ya yi ya tako har inda ta ke kyawawan tafukansa na mannnewa akan marblesya tsaya a gabanta, space din da ke tsakaninsu ba shi da tazara, hannayensa biyu ya dora a kafadunta, daya a kafadar hagu daya a ta dama. Ya rage tsawonsa suka yi kai daya sannan ya dube ta cikin idanunta da shanyayyun idanunsa,fitarnumfashinsu na sarkewa dana juna.
Da na sani Hausa na nema miki a jamia Hafsah.
Murmushi ta yi kumatunta suka lotsa sosai. Itama Hausar karantarta ake yi??
Kwarai kuwa, yadda ake karanta Geography.
Ya sa hannu ya soma warware mata lullubin dake kanta, ya saki mayafin a kasa, ya kai hannu kan hudar karan hancinta da barimar danyen gold yar kankanuwa ta dade da samun muhalli yana mai zagaye barimar da dan alinsa.Yana daga abinda yake so a kawatacciyar fuskarta maabociyar zati da kamala wannan hular hancin,sai kuma ya zarce da hannun damansa saman kanta ya shafo kwantaccen gashinta mai santsi da sheki tun daga farkonsa har karshensa.Sannan ya hada mikakken karan hancinsu wuri guda ya soma magana cikin wata irin kasalalliyar murya.
Mommanki ba ta gaya miki daga ranar da ta aura min ke mun zama sirrin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama marufar asirin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama abu guda ba babu sauran boye-boye ko kunya a tsakaninmu? Na dauka kunyar ta kare daga jiya Hafsah?Amma na gani cikin kwayar idanunki kina kokonton zama da ni Abdulazeez a dan tsukukun daki???�?
Dariya ta yi ta somakokarin sunne kanta cikin jikinshi. Ba dama tayi magana cikin ranta sai Abdulazeez dinnan ya karanta? Bai bata damar hakan ba (buyan) ya dago fuskarta yana so su hada ido ta rufe idon da azama.Thelong eye lashes.... suka bi idon suka kwanta luf; wani abu da ya dade da lura da cewa yana tsananin fizgar zuciyarsa zuwa gare ta ya sumbaci idanunta ko bai niyya ba. Fuskarta ya saka cikin tafukansa ya ce.
Kina min wannan lumshe idon Hafsat, za ki bari in yi assignmentdinnan kuwa?
Babu kuzari a cikin muryarsa a lokacin da yake fadin hakan. Bude idanun nata ta yi da sauri. Ni fa ba lumshe ido nake ba,ido ne bana so mu hada.
Saboda me toh? Hafsah in ba ki kalle ni ba wa za ki kalla? Ko ni in ban kalle ki ba wace pretty face zan kalla haka?
Murmushi ta yi sosai da jin kalamansa. Don Allah ka je ka yi assignment dinka.Ina so ka ci maki da yawa kafi duk abokan aikin ka cinyewa.
Dariya ta ba shi sosai, wai cinyewa kamar wani abinci.Ya janyo ta sannu a hankaliya rungume tsantsan a jikinsa, ya ce. Ashe kina sona haka da yawa Hafsat? Me ya sa ba ki gaya min ba tun muna gidanmu? Saidai ki dinga ga kallon hoto na a waya a cikin duvet?
Hannuwanta ya ji ta zagaya a bayansa ta rike shi gam-gam itama. Saboda na san ba ka sona lokacin Yaya Azeez, kaga fadar ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login