Showing 6001 words to 9000 words out of 133887 words
jiki da Hajiya Haliman za ta turo ta fara gyara amarya daga yau har ranar da za a kai ta dakinta. Wannan shi ne gudunmawarta.
Sosai Mammah ta yi godiya, ta daga murya ta kira Hafsa wadda ke dakinta tana gyaran kayanta da aka kawo daga wanki da guga. Ta ajiye rigar hannunta ta fito ta tadda Mammah a falo, tun kafin ta zauna Mammah ta ce.
Ki yi shiri gobe za mu wuce Kano, kuma Hajiya Halima ta turo mai gyaran jiki za ta zo ta fara miki daga yau, tare da ita za mu tafi kano.
Suhaana ta ce, Mommah me jikina ya yi da za a gyara shi? Na yi dauda ne?
Dariya Hajiya Maryam ta yi, ta rike hannunta cikin nata.
Kullum Adda ta tsaf ta ke, kal-kal kamar tarwada saboda wanka. Shi gyaran aure daban yake, ba irin wanda ki ka saba yi ba.
Hafsat har tausayin Mammah ta ke ji a ranta in ta yi duba da yadda ta dora ranta a kai ta ke kuma zumudin auren nasu. Ba ta taba ganin abin da Mammah ke farin ciki da shi a duniya irin auren nan nasu ba. Ya ya za ta ji a ranta idan ta gaya mata na wucin gadi ne ba mai dorewa ba ne, ta kyale wata mai gyaran jiki? Ai ko Ya Azeex bai ce ta boye ba, ita a karan-kanta ba za ta iya fada ba.
Karfe shida na yammacin washegari suka isa birnin Kano, ta Dabo ci gari, jallabiyya babbar hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka, mai Dala da gwauron Dutse, Kano tumbin Giwa, ta sarki Ado Allah ya yi maka rahma.
Abdulazeez bai taho tare da su ba, yana Abuja sai ana saura kwana daya daurin aure zai taho tare da tawagar lauyoyin chambarsu. Mai gyaran jiki mai suna Fannah ta shiga aikinta a kan Suhaana. Eh, lallai, ta yarda da abin da Mammah ta ce, shi gyaran auren daban yake, kuma wannan da ake mata ba karami ba ne. Ganin yadda cikin kwana uku fatar jikinta ke wani irin salki da sheki. Ga Addar babu kawaye sai yayan dangi ne suka zama kawayen nata su Halima yar Anty Luba, Saima da Khalisa yayan Anti Mariya da Anty Furairah duk da ta dan girme su don cikinsu ba wadda tayi candy. Gayya sosai Hajiya Maryam da kannenta suka yi. Ta bangaren maza ma ba karamar gayya Dr. Hamza ya yi ba shi da sauran yan uwansa. Baa maganar Minister Abdulkareem Dakata ya yo babbar gayyata ta manya zuwa daurin auren jikan nasa.
An yi kamu ranar alhamis, jumaa aka yi wunin biki a nan mainhouse nasu. A yammacin ranar wato ana I gobe daurin aure Abdulazeez da abokan aikinsa suka iso. Tsohon Minista Abdulkareem Dakata mai masaukin baki ya yi musu masauki a gidan saukar baki na Tahir Guest Palace.
Washegari asabar karfe goma daidai na safe daruruwan jamaa suka shaida daurin auren Abdulazeez da Hafsat a kan sadaki naira dubu hamsin lakadan, wanda ya fito daga aljihun Abdulkarim Dakata. Aka yi adduoi masu yawa aka shafa. Daga nan maza suka wuce liyafar cin abinci acan Tahir wadda Dr. Hamza ya shirya, mata kuma suna shirin tafiya Mothers Nighta daren ranar a (FABS EVENT CENTRE) wanda Hajiya Maryam ta shirya.
Rana ta farko da fuskar Hafsat-Suhaana ta soma daukan make-upna zamani a rayuwarta. Ta koma tamkar wata sabuwar kyakkyawar halitta ta daban wadda aka baro daga cikin kwai don kyau da ban shaawa. Hatta Anty Zuwaira da ke adawa da auren a zuciyarta sakin baki ta yi tana kallon Hafsat, ta kuma yarda har ranta yarinyar kyakkyawa ce tun asali, kawai ta raina asalinta ne har gobe tana ganin wautar Hajiya Maryam na hada wannan auren, yaro irin Abdulazeez yarinya yar asali, yar gata, yar babban gida ta dace da shi ba yar mai aiki ba. A raayinta fa. Amma tunda ita ta haifi abinta wa ya isa ya yi magana? Ta yi tsaki ta dauke kanta daga kallon yarinyar.
Wadda Hajiya Maryam ta shirya cikin wani rantsattsen leshi baki mai ratsin silver, goggoron kanta silver, dankunne da sarka, takalmi da purse duka silver. Duk wanda ya daga kai ya dube ta sai ya ce, Masha Allah.
Hannunta cikin na Mammah wadda ita ma ta sha nata adon cikin koreni tattausan leshi, kawayenta su Anty Halima na take mata baya cikin tasu shigar ta alfarma suka shiga motoci zuwa (Fabs Event Centre).
Taron na mata ne zalla, don haka babu bukatar zuwan ango da abokansa. Sai dinnerta gobe da za a yi a Abuja ne zasu halarta, washegari lahadi za a yi ta (by- couple), wato kowa da mijinta. Iyakar (programmes) din da suka tsara kenan, kuma alhamdu lillah komai ya kayatar. An ci an sha, an yi hotuna da vedio don tarihi aka watse.
Suna fitowa daga mota za su shiga gida Abdulazeez da wasu abokansa biyu, Barrister Abdallah da Barrister Adebayo na tsaye a dakalin kofar gidan suna magana. Yana cikin farar shadda kal (hilton) da babbar rigar rataye a kafadunsa. Hasken fitilar kofar gidan ya haske masa yaran yammatan dake fitowa daga mota, fuskar Hafsat tarwai a tsakiyar yammatan. Ya gyara tsayuwa yana kallonsu suna shige shi daya bayan daya zuwa cikin gida. A ransa ya ce, ina ruwan (sweet sixteens), gaba daya kawayen ma wadanda duk ya sansu a dangi yara ne kamarta. Abin ya ba shi dariya sosai, sai da ya yi murmushi.
Adebayo ya ce Wow! Abdulazeez you have a beautiful wife, looking gourgeous.
Abdulazeez ya galla masa harara, ita ma ya juya ya galla mata tata, ya dauke kai suka ci gaba da maganarsu da Abdallah.
Ta ga hararar da ya yi mata sosai, don wajen akwai wadatar haske duk da dare ne. Jikinta ya yi sanyi da ma a sanyayen yake. Tun lokacin da aka tabbatar mata an daura mata aure jikinta ya mutu, bakinta ya mutu. Mammah ta lura da hakan, amma ba ta ce mata komai ba. Is normal ai, mace ta canza sanda aka daura mata aure. Nauyi ne babba ya hau kanta, ta zama karkashin mulkin wani, ta zama UWA, ai kuwa nauyin ba karami ba ne.
Washegari da safe kowa na gidan ya tashi ne da shirin wucewa Abuja. Karfe tara daidai motocinsu suka tashi zuwa Abuja dauke da amarya shi ma angon da tashi tawagar sun kama hanya, zuwa azhar suna cikin Asokoro gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku. Nan kowa ya ci abinci aka huta. Su Anty Halima suka wuce gidan amarya don kara gyaggyara komai, wato jeren da suka tsaya maaikatan kamfanoni suka yi.
Sai shirin tafiya dinner wadda za a yi a (A-class). Ana yi mata kwalliya, amma gabanta faduwa yake yi jin ana fadin har da angon da abokansa za a yi dinar, idan ta tuno da muguwar hararar da ya zabga mata a Kano ba laifin tsaye babu na zaune. Amma sai Abdulazeez ya bada mamaki, har aka yi dinnar aka kare bai ba da wata matsala ba. Ko nuna wata kafa da zaa gane baya maraba da auren Hafsat. Da aka tashi ne dai ya bi abokansa bai tsaya bi ta kanta ba ko motar da ta kawo su tare, sai ita kadai aka dauko a motar aka dawo da ita gida.
Sai shirin tafiya kai amarya. Nan fa ake yinta. Yau zaa raba Suhaana da Mommah, Suhaana da Baba Azumi. Kuka ta ke kamar na fitar rai, ko Mammah ta ji tausayinta ta barta su ci gaba da rayuwarsu tare. Ita kanta Hajiya Maryam dauriya kawai ta ke yi, amma zuciyarta ta gama karyewa. Baba Azumi dai sai kewaye ta shige ta kulle, sannan aka iya fitar da Hafsat zuwa falon Daddy. Albarka kawai ya sa mata ya ce su je da ita, zai biyo ta gidanta ya yi mata fadan. Kawai sai aka ga Mammah ta dauko mayafi ta yafa ta kama hannun Hafsat zuwa mota ta ce da ita zaa je. Su Hajiya Halima na tsokanarta wai surukar sabon qarni. Murmushi kawai tayi tana shanye hawayenta. Sannan ne Hafsat ta rage kukan motoci suka kama hanyar Sun-city.
A daidai wannan lokacin Abdulazeez yana dakinsa na gidansu. Ya kulle kansa yana waya da Muazatu, kuka ta ke yi masa sosai cikin matsanancin tashin hankali. Gani ta ke ta rasa Abdulazeez ta gama, yau zai shiga dakin amaryarsa shi ke nan fa! Shi kuma lallashinta yake yana kara tabbatar mata da alkawarinsu. Amma ina! Muazatu jinsa kawai ta ke, ta kasa yarda duk da ta san har zuciyarsa yake nufin alkawarin, amma tunda ta ga hotunan bikin da yarinyar da yake cewa ba ya so din a wayoyin abokansa hankalinta ya yi mugun tashi. Ta dauka wata bakauya aka aura masa da farko, ko wata wadda ba ta amsa sunan mace ba, amma idonta ya gane mata Hafsat-Suhaana kwance a kafadun mahaifiyarsa, ta kuma gansu tare a hotunan sun sha anko sun durkako (A-class) inda aka yi dinar kamar don su aka halicci juna. Tuni ta daina yarda da kalaman bakinsa duk da cewa duk cikin hotunan da aka nuna mata din babu inda ta ga ya kama Hafsat ko ya mannu da ita don nuna soyayya.
Da ya gaji da lallashinta, amma ta ki daina kukan, sai ya yi shiru. Amma bai kashe wayar ba, bai san kuma da kalaman da zai yi amfani da su Muazatu ta yarda da shi ba. A ganinsa duk wasu kalamai da yake da su sun kare. Ta sanshi ai, ta san halinsa, ta san babu karya cikin halayensa. Ya yarda ya auri Hafsat ne don ya samu hanyar aurenta, kuma babu soyayyarta ko kankani cikin zuciyarsa. Me ya sa ba za ta yarda ba? Shirun nasa sai ya kara tunzura ta, ta ci gaba da gursheken kuka. Zuciyarsa ta dinga bugawa fat-fat-fat, tsigar jikinsa ta dinga tashi.
Enough, is enough Muazatu, ki gaya min yanzu me ki ke so na yi?
An zo gabar da ta ke so don haka ta sassauta kukan.Abdul na dade ina yi maka tanadin kaina, ina tattala maka budurcina, ban taba wasa da shi ba. Ban taba shaawar bada shi ga waninka ba, kullum burina ya zamo kai ne za ka karbe shi cikin girma da daraja. A yau wata ta riga ni samunka, da ka kusance ta ta gama janye min kai, komai rashin son da ka ke mata. Wallahi in ka kusance ta na hakura da kai har abada ko kai ne autan maza. Zan roki Allah ya cire min sonka ko ya zama ajali na a kan in yi sharingdinka da wata, ni wannan ne kawai damuwa ta.
Shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi. Shi kansa bai san me ya sa ya yi shirun ba. Muazatu ta baro zance wanda shi kansa ya girmi kwakwalwarsa. A ganinsa bai kamata ta shiga wannan hurumin ba duk da akan-kansa bai taba kawo yiwuwar hakan cikin rayuwar auren kwangilar da zai yi da Hafsat ba, amma ai matarsa ce, koda yace da Hafsat kayyadadden zama zasu yi iyayensuda suka daura auren da tsarkakakkiyar niyya suka daura shi kamar yadda addinin muslunci yayi umarni, ba su san da wani abu bayan wannan ba, don haka ko ta ina aka je aka dawo sunan Hafsat matarsa, an taba gindaya wa miji hukuncin kada ya kusanci matarsa?
Koda yake son Muazatu shi fa ba sakarai ba ne da zai zauna mace ta gindaya masa abin da ta ke so ta ce dole sai ya bi ba. Don haka ransa ya baci sosai da maganar Muazatu kawai sai ji ta yi ya kashe wayar.
Matsanancin tsoro da mamaki suka taru suka lullube Muazatu. Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Tunda suke tare bai taba kashe mata waya ba, me hakan ke nufi??
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama
*****
Yan kawo amarya sun ajiye ta sun juya, Mammah kuwa da dabara ta samu ta fice. Aka barta daga ita sai Harira yar Baba Azumi a dakin da aka tanada don mai aiki a gidan. Harira matar aure ce da yaya hudu, lokacin da Baba Azumi ta gayyato su biki daga Sokoto Mammah ta yaba da hankalinta da kazar-kazar dinta don su suka yi ta tsaftace gidan lokacin biki da rabon abinci, ta roki Baba Azumi ta barta ta zauna da Adda ta debe mata kewa zuwa sati biyu kacal. Kafin lokacin ta saba da sabuwar rayuwarta ta saki ranta. Baba Azumi ta amince don haka aka bar Harira a gidan tare da Hafsat.
Tunda Harira ta shige dakinta ta rufe kofa ba ta sake fitowa ba. Hafsat-Suhaana ta ci kukanta ta gaji har ta gode Allah, hawayen suka tsaya don kansu. Kanta ya sara, ya soma ciwo ta kwanta lamo! A kan filo ta rufe jikinta da mayafinta, ta takure a can gefen gadon ta soma ajiyar zuciya.
Ko da ya kashe wayar da suke yi da Muazatu komawa ya yi ya jingina bayansa da kofar dakin nasa. Ya lumshe ido zuwa dan lokaci ya bude ya zura wayarsa a aljihunsa. Lokacin ya tuna su Abdallah suna kofar gida suna jiransa su raka shi gidansa. Toilet ya shiga ya yi wanka ya canja kayan jikinsa da wani sassalkan ya din filtex (milk colour) ya taje sumar kansa, ya sanya hular da ta dace da kayan nasa, ya daura agogon (swatch) a damtsen hannunsa ya fesa turare har kala uku. Ya janyo manyan jakunkunan da ya hada kayansa na dakin nasa ya sanya takalmi sabo dal! Ya fito da jakunkunan sannan ya janyo kofar dakin nasa ya fita.
Gidan babu kowa a falo, duk sun dawo daga kai amarya sun gaji sun kwanta, gobe kowa zai kama gabansa.
Har ya fice bai hadu da kowa ba, ya tadda abokansa a waje zaune kan fararen kujerun da ke harabar gidan suna hira. Yana fitowa suka mike suka karbe shi jakunkunan suka shiga motocinsu suka wuce (Sun-city).
Kofar gidan akwai maigadi wani Danfulani da Daddy ya samar musu, ya bude musu (gate) suka shigo da motocinsu, suka yi parking suka firfito. Dukkaninsu Lauyoyi ne na gwamnati da masu zaman kansu. Shi ya bude kofar falon suka shiga, kowa ya nemi inda ya yi masa ya zauna a lafiyayyen (European parlor) da Mammah ta shirya, in ka wuce shi za ka tadda (African parlor) wanda bai kai shi girma ba, wanda ya ji shimfidun gargajiya da adon carpet din fata na jikin bango da su tum-tum abin gwanin ban shaawa kai kace sun hada jini da sarauta ne. A cikin wannan (African parlour) kofofi ne guda biyu wadanda suka kunshi dakunan barci biyu, daya nasa, daya na matar gidan. Daddy ya kawo shi ya ga gidan tun sanda ake gininsa don haka ya san kansa. A kowanne dakin barci akwai makewayi, kicin (madafi) yana gab da shiga kofar falon farko, wato ba a cikin falon aka yi shi ba.
Akwai yar doguwar baranda a kofar shigowa falon, wadda aka aje fararen tukwanen fulawoyi masu kyawun gani da fararen kujerun roba. Harabar gidan za ta iya cin motoci uku ba tare da kowacce ta gogi yar uwarta ba. Dakin maigadi na jikin gate, dakin mai aiki yana daga bayan ginin falon, wato sai an fito daga main building din an zagaya ta baya za a tadda dakin mai aiki.
Yadda su ESQ Abdallah suka nemi wuri suka zauna cikin tausasan kujerun falon haka shi ma ya nema ya zauna. Barrister Taufeeq shi ne karshen shigowa yana janye da jakunkunansa yana daga tsaye ya ce, Dare fa ya yi, ka shigar da kayan Malam ka fito mana da amarya mu saya maka bakinta, mu yi muku addua mu koma namu gidajen.
Harararsa ya yi ya mike ya karbi jakunkunan ya yi ciki. A ransa ya ce, wai su saya min bakinta, to in yi me da shi?
Tsakanin dakunan biyu zai yi rantsuwa bai san wanne aka ba ta ba, wato ba zai iya cewa ga nasa ga nata ba.
Tsayawa ya yi yana kallon kofofin guda biyu da kallo mai kama da harara. Ba wata amarya da ya yi niyyar kai musu su yi abin da za su yi, kawai su tafi. Ya ce ta zo cikin abokansa ma ai sai ta raina shi. Ya yi kundunbala ya murda handle din kofar dama ya tura jakunkunansa. Cikin ikon Allah shi ne nasa, ya jefar da jakunkunan ya fito ya tadda su.
Yaya ina amarya ka fito kai kadai? Taufeeq ya tambaya, sauran kuma suka bi shi da ido kamar sa cinyeshi.
Ta yi barci.
Ya samu bakinsa da fadin hakan ba tare da ya shirya ba. Duk suka mike, To sai mu wuce, randa muka zo idonta biyu mun yi muku adduar dare ya yi.
Ni na yafe adduar taku in ba za ku yi min ni kadai ba.
Dariya suka yi, Taufeeq na fadin, Ka fadi gaskiya Malam.
Suka wuce Ahmad na fadin, Da gaskiyarsa fa, wannan aladar babu kyau ko kadan. Mai kishin iyalinsa ba zai yarda da ita ba.
Baki ya kama yana kallon Ahmad cikin takaici, Kishi? Ya ambata cikin sigar tambaya da nauyin baki.
ESQ Ahmad bai ba shi amsa ba, ya daga masa gira ya yi murmushi, ya ba shi hannu. Amma Abdulazeez ya noke ya hana shi nasa.
Ka yi min sharri, sannan ka ba ni hannu? Wuce ka tafi. Na gode zan rama.
Suka yi tafiyarsu kowannensu da irin dariyar da yake yi masa.
Da wannan haushin ya dawo ciki. Ya rasa abin da zai yi. Har ga Allah bai yi niyyar shiga inda ta ke a daren nan ba, sai kawai ya shige dakinsa ya rufo, ya dauki (remote) ya kunna naurar sanyaya daki ya hau shirya kayansa, daga jakunkuna zuwa sif din jikin bango.
Sai karfe biyu na dare ya gama, ya yi sallar nafila ya kashe wuta ya kwanta. Wayarshi da ya bari a kunne a gefen kansa ita ta tashe shi da kiran Muazatu da assalatun fari. Kansa ya yi masa gingirin sabida bacci da gajiya ba zai iya magana ba don haka ya matsar da ita gefe ya koma ya ci gaba da barcinsa. Wannan