Showing 87001 words to 90000 words out of 133887 words
kanki da wuta. Shin ni ba mutum ba ne, ba ni da feeling? Shekaruna talatin da uku har yau ban san ya ya aure yake ba. Hafsat ko ba kya sona dole ne ni ma ki yi min biyayya yadda ki ke mata. Ko kuwa shi kenan saboda na yi laifi ni rayuwata ta kare?
Kuka ta soma yi a hankali, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta, shi da Mamansa sun sa ta a kwana, kowanne gani yake shi ya kamata ta yi wa biyayya, a wannan lokacin ba ta san me ya kamata ta yi ko ta ce masa ba banda;
Me ka ke so in yi maka yaya Azeez? Hannunta da ke cikin nasa ya janyo a hakali ya hade ratar da ke tsakaninsu. Ajiyar zuciya kawai suke yi dukkanninsu cikin motar. Wata irin nutsuwa da suka dade rabonsu da ita ke overwhelmingdinsu tun daga kwakwalwa har babban yatsar kafarsu. Tsawon mintuna ba wanda ya iya yin magana a cikinsu. Hafsat ce ta ankara mutane na gilmawa jefi-jefi suna aje motocinsu. A hankali ta zame jikinta daga nashi ta koma cikin kujerarta sosai ta zauna, ta lumshe idanunta, karfin scent dinsa da na air-freshner din motar suka hade da sanyin A.C suka bada wata atmospheremai dadi a cikin motar. Kansa ya kwantar a kan sitiyarin yana regaining hargitsewar bugun zuciyarshi. Sun jima a haka kafin cikin raunin murya ya ce.
Gidanmu nake so mu koma Hafsat direct daga wajen nan. Na roke ki kada ki ce min aah...
Kai ta shiga girgizawa da sauri showing resentment (cikin nuna rashin yarda) I cannot do this to Mommah (bazan iya yin haka ga Mammah ba).
Dagowa ya yi daga kan sitiyarin ya dube ta sosai cikin tsakiyar idanunta, duk da ta ki yarda su hada idanu ta san idonsa akanta yake. Then blame yourself kan duk abin da na zaba mana!.
Ya tada motar ya fita daga harabar kotun kasa, ya hau kan titin da zai kai shi titin Aguiyi Ironsi. Hafsat dai ikon Allah ta ke kallo, gabanta na tsananta faduwa don bata san me yake nufi ko ina zai kai su ba, sai dai zuciyarta na gaya mata... ko me Abdulazeez zai zaba musun nan ba alheri ba ne gare su.........!!!Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe. Kada ku damu, tare suke. Taku har abada Sumayyah Abdulkadir Takori
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
A ganinta hakuri da biyayya shi ne abin da ya kamace su daga ita har shi. Duk abinda hakuri bai bayar ba rashinsa ma bazai taba bayarwa ba! Hafsat dai sai dago kanta ta yi daga tunaninta ta gansu a harabarRockviewHotelAbuja.
Kallon tsoro ta fara yi masa, amma ya ki ko ya dubi inda ta ke. Tana nan zaune ya je ya dawo ya bude kofar side dinta, jakarta ya fara daukowa sannan ya ce,
Mu je daga ciki.
A raunane ta ce Yayan Haleem,Hotel? Hasken fararen idanunta kadai da yadda ta wargazasu a kansa, suka gusar da duk wani tension da yake ciki. Yadda ta yi maganar ya kwaikwaya. To ko mu ma yan abin nan dinne ne?
Tsoron zuciyarta ya ninka na farko ganin Abdulazeez na nade hannun suit dinsa da zummar daukanta a gaban mutanen da ke shige da fice. Sauri ta yi ta fito, kiris ya rage ta fashe da kuka ta wuce gaba ta barshi a baya. Sai da suka shiga reception ta dakata har ya cimmata don batasan ina zata nufa ba, hannunta ya rike suka wuce cikin lifter. Suna shiga lifterta kwace hannunta ta harare shi ta gefen ido. Jinjina kai yayi, ya ce.
Ki harareni yadda kike so. Za ki yi bayani ne Hafsah.
A ranta ta ce Allah na kowa ne, tuni ya riga ya zame min gata.
Katin kofar ya sa a jikin kofar kawai ta bude,ya bata hanya ta wuce tukunna ya mayar ya rufe sai faman cin magani take yi. Fuskar nan kamar kunun kanwa sabida kirnewa. In ma ya lura to ba abinda zai iya tasiri bane akansa a wannan lokacin. Tun daga bakin kofar Hafsat ta gane yau ta shigo wata koma da taimakon Allah ne kadai zai fitar da ita. Ta san dai ya yar da jakarta da ke hannunsa a muhallin da bata tantance ba. Ya kuma raba ta da mayafi da dankwalin kanta cikin wata irinnutsuwa. Idanunsa na fidda wani chemistry zuwa cikin nata mai bayyana intent and in depth sorrow din da ya kasance ciki na rashinta lokaci mai tsawo. Sauran alamuran da suka biyo baya sun fi karfin ta iya bayyana su; Is a kind of gentle romance wanda ba ta taba sanin akwai irinsa a duniya ba. Tashin hankalinta ragagge ne sanin cewa she is safe a yau kam. Kwananta biyu da karbar bakonta kuma a iya saninta na addini da na boko mace mai alada miji ba ya kusantarta.
A yadda ya santa da tsoron ta shiga hannunsa ya yi mamaki da yau ba ta tsorata sosai ba, karewa ma she contributed a lotdonganin ya samu nutsuwar da bai da ita,wanda hakan ya zo masa kamar a mafarki. Don haka duniyar da suka fada mai nisan zango ceda ta shallake tunanin su. Sai da komai ya kankama ya gane Hafsat shigo-shigo ba zurfi ta yi masa (abun mata ce a jikinta). Alamarin da ya jefa shi cikin wani hali wanda ita kanta sai da ta tausaya. Gefen gadon ya koma ya zauna ya dafe kansa da ke tsananin ciwo hade da ciwon mara mai tsanani da ya bakunce shi, kodayake ya dade yana damunsa a kwanakin nan tun dawowarsa gidansu da Hafsat din da yake yawan gani kodayaushe tana gilmawa ta gabansa. Itama Hafsat din shiru ta yi, tayi tsuruu a gefensa kamar wadda ta yiwa sarki karya. Tana farin ciki da kubutarta, amma hakika tausayin Abdulazeez ya mamaye farin cikin. Ya cancanci samun farin ciki komai kankantarsa a yau daga gare ta. Duk da tana da tabbacin ko lafiyarta kalau ba za ta amince ba.
A hankali ta iso inda yake zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, ta kwantar da kai a bayansa. Cikin sanyin murya ta ce,
Im sorry.
Bai ce mata komai ba, wayarsa da ke ta kuwwa a kan bedside din ya dauka. Ya yi sliding kiran ya amsa.
Tunda ka san ba halina ba ne in zo in kuma fitan, kasan ina da uzuri ne. Ya jefar da wayar ya janyota ta dawo jikinsa. Wani irin kallo yake binta da shi da sai da ta kasa jurewa ta rufe fuskarta da hannunta daya.
Dole ki rufe fuska tunda kin san kin yi nasara a kaina, Mammah ta san haka ki ka girma kuwa Hafsah? Ita kullum tana miki kallon babynta a Jeddah acikin incubator? Anyway I appreciate, and I must thank Hafsah for this great moment.
Wata irin kunya da ba ta taba ji ba a rayuwarta ita ta lullube ta a wannan lokacin. Mikewa ta yi tana kumburi irin na nade tabarmar kunya.
Please Yaya Azeez mu bar wajen nan, ba mutuncinmu ba ne.
Ni mutunci na ne. Ya fada bai da alamar tashi sai wani lafiyayyen kallo da yake ta binta da shi.
Abubuwanta ta soma tsincewa a dakin wadanda yayiwa fatalin Allah-tsine, ta daura kallabinta ta yafa mayafi ta juya masa baya. Dariya ce ta kama shi ganin zip din rigarta ta baya bakidayaa bude, ya ce. InnaHafsatu saura zip din.
Hannu ta kai ta shafo wajen. YaIlahi! Wata harara ta juyo ta zuba masa tamkar idanun sa fado.Tasowa ya yi cikin takun nutsuwaya iso gabanta, idonsa kan bakin data ke ta turowa gaba.
“Lemme help.....(bari in taimaka).
Ta zumburo baki tareda ja baya. Bana so, ka bari!. Ya daga hannuwa sama daga taimako? Da na sani na yi shiru Mammanki ta gyara miki da kanta. Ya fada yana ja da baya cikin hadiye dariya.
Kansa ta yi da wani sabon kuka da ya zo mata nan take kamar mai shirin rufeshi da duka, data tuno rashin kyautawar data yiwa Mammah. Ya kuwa yi mata wata irin kyakkyawar runguma ya hade bakunansuin no space measure.Hawayen ya shiga daukewa..., ko kadan bai barsu sun sauko kan kundukukinta ba.... Komai ya dawo sabo kamar baa yi shi ba. Hafsat ta tausayawa kanta a wannan rana don har azahar Abdulazeez bai barta ta huta ba,amarcinsa yake yiiri-iri kamar babu gobe. Sai da ya samu relief daga tsofaffin damuwoyin sa da suka dade yana fama da su a kan Hafsah sannan da magiya da roko har da hawayenta ta samu ya amince zai maida ita makaranta.
Test dai har biyu ta yi asararsu, amma Abdulazeez ya ce mata ladan da ta samu ya ishe ta shiga aljannah. In dai miji ke wa matarsa sanadin shiga aljannah, yau ya daga mata ta shiga cikin aminci Ud-khuluhaabissalaam!. Ya fada da larabcin da har yau bai manta ba. Wanda yasa Hafsat tuno birnin Jeddah with nostalgia.
Suna hanyar NILE ya na tuki, batareda ya juyo ya dube ta ba yace,
Karfe nawa za a dauke ki?
Ciki-ciki tace. Sai 5pm Mommah za ta zo.
A gaban department dinsu ya ajiye ta, kafin ta fita ya rike hannunta. Ta juyo ta dube shi idanunta narai-narai, sunyi wani irin maiko da kyalli, wani yanayi da yake matukar son gani cikin idanunta,a zuciyarta ta ce, “Oh ni! Me kuma ya saura?
“Take a look into my eyes Hafsah! Will you now believe it if I say I really love you?(kalli cikin idanuna Hafsah, yanzu zaki yarda dani idan nace ina matukar sonki?
Daga masa kai ta yida sauri sabida a kagare take data fita, sama-sama ma taji me yake cewa, hankalin yayi gaba, bata son a ja zancen da tsawokada wani tsautsayi ya gifta Mammah ta zo da wuri, ya cika hannun nata don ya fahimci yanayin da take ciki. A zuciyarsa yana jinjina kaunarta da uwarta da gudun zuciya irin nata, wani alamari da shi yanzu anzo gejin da bazai iya ba.Mammah ta kure duk wani hakuri da kawaicinsa.
Na gode Hafsatu, me ki ke so in ba ki? Ban taba ba ki komai ba.
Murmushi ta yi har hakoranta suka bayyana, Zo in rada maka.
Ya kuwa sunkuyo da kunnensa daidai bakinta. Keep loving me till eternity!.
Kafin ya farfado daga duniyar shaukin da kalamanta suka jefa shi ta dauke jakarta ta fice. Rufo masa kofar ta yi, ta yi waving dinsa sannan ta juya da dan gudu-gudunta ta barshi da murmushi. Ya dade bai iya tuka motar ba, sabida wata irin kasala da ta bakunce shi. Tana cikin rukunin matan da yake fatan samu a rayuwarsa, har fiye da yadda yake burin samun. Ashe baa judging mace a fannin auratayya da zurfin ilmi, yawan shekaru da wayewa? Halitta ce kawai ta ubangiji. A yau ya kara cursing perceptiondinsa.
Sai laasar ya koma office. A nan ne ya tadda dalilin kiran da su Barrister Abdallah ke ta masa yana kashe musu waya. Abin alkhairi ne ya same su su goma a ofishin. Takarda ce ta fito ta tura su karo karatu (L.LM) daga (Federal Government) zuwa Amurka wanda zai dauki tsayin shekara daya kacal.
Kowa a cikinsu murna yake, ban da Abdulazeez Dakata, sannan tafiyar za ta kasance wata mai zuwa, lokacin da suke da shi na shirye-shirye kadan ne.
Shi tun tali-tali kasashen turawa ba sa cikin yan kayansa. Baida shaawa a kansu. Yana da burin tafiya (L.LM) ko ba su tura su ba amma accross Nigeria. Duk wani pride dinshi yana kasar haihuwar shi. Ko zuwa graduation din Ismael da Usman a kan dole ya je saida Daddy ya nuna bacin rai. Don haka su ESQ Ahmad sun yi mamakin ganin babu wani farin cikin abin a tare da shi, da suka dame shi da tambayar dalili ya ce ba damuwar kowannensu ba ne.
Karfe biyar na yamma Hafsat ta fito daga dakin karatu ta doshi inda Mammah ta yi parking tana jiranta. Ta bude ta shiga suka yi wa juna dan murmushi kafin Hafsat ta ce.
Yaya B.P din Mommah? Hope doctor bai ce yana sama ba?
Ta tuka motar suka fita daga parkinglot ta hau kwalta sosai, sannan ta juyo ta dubi Hafsat fuska ba walwala. Yaya test din?
Shaf! Ta manta da zancen wata test duk da Mami ta gaya mata an yi, kuma ba ta samu halin taimaka mata da ko attendance ba, lecturer din ya kasa ya tsare. Inda-inda ta hau yi saboda a rayuwarta bata saba karya ba. Karya wani abu ce da Mammah ta rayu tana gaya mata mai yin ta dan wuta ne. Amma hakika yau zatayi karya ga Mammah, a inda bata da mafita.
Au... am, Eh....test din.. test din ba wuya sosai. Ta samu kanta da fada cikin daburcewa. Wanda ko daga yanayin data yi maganar ya gama fallasa ta. Sabida abune da baa raine ta da shi ba take kuma feeling guilty na yinsa tun kan a gane ba gaskiyar ta fada ba.
Abin da ba ta sani ba tunda ta shigo motar jikinta kamshin Abdulazeez yake yi. Duk cikin yayanta ba mai amfani da wannan turaren sai shi, ya dade da kame komai nasa, sannan ita Hafsan bata fesa turare in za ta fita. Bayan haka Salisu ya koma ya tadda ta a asibiti da wuri, ta ce ya aka yi ya yi sauri haka? Ya ce ai sun hadu da Barrister ne ya ce ya koma shi zai kai ta. Ta rasa me za ta yi wa Salisu ta huce don haushi da takaicinsa, don haka uffan ba ta ce masa ba.
Wani abun personal ne, kuma shi Salisu ya kwana da sanin waye Abdulazeez a gidan, kuma ya san Hafsat wace ce a gare shi. Ko babu aure ya isa ya hana Abdulazeez tuka Hafsat? Don haka ta kowanne bangare ta mishi uzri, amma za ta yi maganinsu. Kanta na bisa titi tana tuki.
A ajandar AUREN KWANGILAr naku, har da cewa bayan ya maida ke makarntar, ya kuma kore kin, zai dawo kuma dagabayaya hana ki karatun?
Hafsat ta ji numfashi ya dauke mata na dakika biyu. Tayi kokarin hadiyar miyau amma makoshinta taji ya bushe kyamas.
Wannan test din guda biyu, kin rubuta su ko ba ki rubuta su ba? Ta sake fada cikin son controllingtsananin fushin da yake yunkuro mata. Wani tashin hankali ya ziyarci Hafsat, sai ta ke ganin ai kamar Mammah ta ga komai ma a kan idonta. Sunkuyar da kai ta yi, wata matsananciyar kunya da guiltyconscience na lullube ta. Mammah ta yi kwafa, bata kara magana ba haka Hafsat din, har suka isa gida. Ta kasa daga kai balle ta dubi Mammah.
Suna zuwa gida Mammah sassan Daddy ta wuce ita kuma ta yi dakinta, bakin gado ta nema ta zauna a kasalance ta yi tagumi, ba ta da kalmar kare kanta yau a wurin Mammah, a kan-kanta ba ta da bayanin da za ta yi mata don ta yarda da ita, ta yarda ba da son ranta ba ne ta bi Abdulazeez, tana kan biyayyarta, ya fi karfinta ne da duk wani kokarinta na tsayawa a bangaren Mammah, sannan zuciyarta mai tsananin laushi ce a kansa sai dai idan ba su kebe ba.
Ba ta dade da shiga falon Daddy din ba Dr. Hamza ya fito daga bedroom dinsa ya ganta a falon a zaune. Kallo daya ya yi mata ya fahimci ranta a matukar bace yake, kuma ba abin da ke bata ranta a dan tsukin sai lamarin Abdulazeez da Hafsah! He is tired of all these yau zai kawo karshen komai.
Tun kafin ya zauna a kujera ta soma.
....Daddy ni fa na gaji da zaman Abdulazeez a gidan nan, ina tufka yana min warwara, sabida ya mayar da ni marainiyar wayonsa. Na samu matsala ban samu kai Addah makaranta da kaina ba, na tura Salisu ya kai ta, ya tare su a hanya ya dauke ta tun safe har yamma ban san inda suka je ba. Tana da test har biyu bai barta tayi ba.
Ya sake ta kamar yadda ya yi wa kansa alkawari, kun mayar da aure ban hana ba don an fi karfina,nace kome sai sanda na ga dama kun amince.To binbinin na menene?Karatun ma marufar asirin diya mace ba za ta tsira da shi ba tunda bata da soyayyarsa? Bana zalunci, bana goyon bayan yinsa! Ka ja masa kunne wannan ya zama na karshe da zai kara shiga harkar Hafsat.
Iyakar bacin rai ran Dr. Hamza ya baci, amma ya yi kokari matuka ya daidaita muryarsa yadda bacin ran bai fito a cikinta ba. Ya lalubi kujera ya zauna.
Da izinin wa ki ke zirga-zirgar tukin mota kai Hafsa makaranta da dauko ta? A kan karan-kanki kina tuka mota ki je unguwa?
Ta yi shiru ba amsa. Wani irin nutsatstsen murmushi ya yi ya dube ta sosai.
Akwai mai zalunci ma irinki a duniya?
Zaro idanunta ta bakidaya tayi a kansa, bai damu ba da yadda tayin ya gyada kai cikin karfafa ingancin furucinsa,ba tare da ya bata damar cewa komai ba ya cigaba.
Yara na son junansu kin dage sai kin raba su. Ba kya tukin mota amma saboda kiyi zalunci kin jureshi yanzu. Ita Hafsan ki tambaye ta mana da wadanne kafafun ta fita daga motar ta bi shi? Ko aka ya dauke ta ya canza mata mota? Ita da bakinta ta gaya miki sun je wani waje ba makarantar ba ko kuwa kwakkwafinki na balai?
Kin san Allah Maryama! Ki fita daga idona in rufe. Daga yau ban yarda ki kara tuka mota ba. Ban yarda ki kara kawo min zancen Hafsat da Abdulazeez ba in ba na alheri ba. Tunda ke ba kya afuwa. Shin da Allah ba ya afuwa a gare mu ga tarin laifukanmu, da mun kawo yau ne? Shin ke ba za ki yi afuwa ga dan cikinki ba ko don kwadayin rahmar Allah a gare shi? Ya biki, ya biki, ya biki har kin kai shi gejin da zai soma fandare miki. In bai saci matarsa daga wajenki ba, da ki ka bi ki ka kankane masa, zina ki