Showing 84001 words to 87000 words out of 133887 words

Chapter 29 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

571

shi da tsoka?
Sunkuyar da kai ya yi gabansa ya soma faduwa da ya ji sallamar Baffa a kansu. Farin dattijo mai farar aniya da nisan kwana. Mai son jikokinsa fiyeda Hamzah da ya haifa. Sai dai fa in aka yi ba daidai ba, baa jinta da dadi daga gare shi. Sai dai a shirye yake da ya dauki komai da kowanne irin hukunci daga gare su in dai a karshe zasu hakura su dawo mai da Hafsah! Zaunawa Baffa ya yi a kusa da shi ya bugi kafadunsa.
Lauyan duniya, idonka kenan? Dama kuwa ina nemanka.
Su Daddy suka duka suna gaida Baffan nasu. Amsawa yake yana sa albarka kamar yadda ya saba in ana gaishe shi. Sai dai ya lura duka da damuwa a fuskokinsu kada Abdulazeez ya ji labari. Baffa ya dubi Abdulazeez ya ce.
Neman duniya da harkallar cikinta ta sanya a yanzu ba kwa damuwa da addua, ba kwa kiyaye yin azkar din da kullum nake nusassheku daga ku har iyayenku, boko kawai ku ka sa a gaba. A kwanakin baya na yi ta mafarke-mafarke a kanka masu nuni dakana cikin sarkakiya da dabaibayi, na yi kwanaki ukku ina istikhara a kanka na kuma samu wani duhu cikin rayuwarka da ke bibiyarka ba tare da saninka ba. Na ga wata mace na farautar zuciyarka da tsafi. Abdulazeez ina sallolin darenka? Ina adduoin da kullum nake tura maka? Ina ka bar zam-zam da na ce ka ke alwala da shi akai-akai in za ka shiga kotu?
Shiru suka yi bakidaya, zuciyar kowanne da waswasi, a zuciyar Abdulkarim ya ce, Ko dai wannan yar Yarbawan ce? Daddy kuwa bai kawo komai a ransa ba ban da harkar aiki. Shi kuwa mai gayya mai aiki maganganun kakansa a tunani suka jefa shi. Tunda ya fara jin son Muazatu bayan a haduwarsu ta farko ya san ba sonta yake ba, daga baya zuciyarsa ba ta taba hutawa da azabtar da shi a kanta ba sai ranar da ya saki Hafsat! Ranar ne ya ji kamar sakin ya tafi har Muazatun, ranar ne ya ji shi sakayau (free from all worries and tortures), shin ko ita ce ta tsafe zuciyar tasa?
Jin shirun ya yi yawa Baffa ya muskuta, Ko ma dai mene ne ya wuce, sai a tari gaba a yi wa jiki kariya, a kuma kula da abubuwan da na ambaci cewa ana wasarere da su. Ba kai kadai ba har sauran yan uwanka. Akwai rubutu da na sa aka yi muku dukkanku yanzu za ka sha naka ku tafi musu da sauran har su Farhan. Yanzu dai na ganku da damuwoyi, me ya faru?
Abdulkarim ya yi gyaran murya, ya ce, Baffa ai Abdulazeez ya warware duk shirin nan da ku ke yi kai da shi, tunda ya saki matarsa!Ashe duk tsawon lokacinnan zaman yarjejeniya yake yi da aurensu ba da sanin kowa ba, wai zai sake ta sanda yaga dama ya auri wata, sai da komai ya damalmale masa yadda ba zai iya gyarawa shi kadai ba sannan muka sani.
Salati Baffa da Adda Hafsatu suka saki a tare, Addah ta ce, Yar amanar ya saki marainiyar Allah? Abdulazeez din ne ya maida auren nasu na mutayana sane ko yaya abin yake?
Baffa ya ce Auren da muka daura ta tsabtatacciyar hanya yaushe ya koma na muta? Abdulazeez ba zai yi haka da gangan ba. A sanina har a Saudiyyah ya yi islamiyyah, yayi haddar Alqurani ya kuma san hukunce-hukuncen addini balle ya yi aikin batan hikima irin haka.
Wannan karon Abdulazeez ya kasa jurewa, kuka ne ya kwace wa idanunsa. A sanda yake tsarawa Hafsat su yi contract marriage ya san ba abin kirki yake shirya musu ba, amma bai zaci hakan yana da wani babban effect ga addini ba, duk karatun islamiyyarsa bai taba karanto wannan shafin ba, bai zaci abin zaiyi girma a gaba yadda yayi a yanzu hannun iyayensa ba, shi kawai hanyar auren Muazatu yake nema...He is desperate to have her... Shi a wurinsa dabara ya kulla wadda za ta kai shi ga cikar burinsa. Bai taba jin wannan kalmar wai muta da suke ambata ba, shi ba malamin addini ba ne, amma yana da sani daidai nasa, kuma babban gibinsa bai tsawaita bincike a kai ba. Ya yi nadama yadda ba zai iya bayyanawa ba. Ga wani irin tsoro da ya zo ya baibaye shi; tsoronsa na farko kada Baffa ya ce aure ya haramta tsakaninsa da Hafsat har abada. Tsoronsa na biyu kada ya ce mayarwa da ya yi mata bata yiwu ba. In hakan ta faru shi da aure har abada! Hawayen da yake zubarwa akai-akai ya tada hankalin Baffah, ya kashe kuzarin duk wani batanci da ya yi niyyar yi masa. Cewa ya yi da Uncle Abdulkarim ya yi masa bayanin komai yadda zai gane kan matsalar. Nan ya warware masa yadda Abdulazeez ya fada masa. Adda Hafsatu sai tafa hannuwa ta ke tana fadin, Kurucci dangin hauka!.
Daddy da tun bayan fara maganar bai ce komai ba ya dubi Addah Hafsatuya ce. A sanda ya shirya kwangilar sa shekarunsa sunfi talatin da daya ya girmi kuruciya, zan fi yarda in ya ce ba ya zuwa islamiyyar da nake tura shi, ko babu islamiyya ai akwai abinda da ka ji shi ka san daidai ne ko ba daidai ba ne. Na san dai ba ya son Suhaanar aka yi auren nan, amma ya yaudare mu daga baya ya ce ya amince bayan ya gama bore-borensa. Daga ni har Maryama a lokacin mun sa a ranmu in kwanakin da muka diba masa yayi shawara suka cika yazo da gamsashshiyar amsa ta rashin amincewa da auren Hafsat zamu hakura ya auri zabinsa. Amma ya yaudaremu yayi wasa da hankalinmu a karshe ya bige da sabawa Ubangijinsa. Shi ya sa ko na so ganin laifin Maryama kan kafewarta kada a maida aurennan sai in mata uzri. Gabadaya suka dauki idanu suka zuba masa har Baffa cike da alajabi da takaici.Abdulazeez ya gurfana gaban Baffa ya ce, Ku yi hakuri Baffa don Allah, wallahi na yarda na yi ba daidai ba, ba tun yau ba. Na yarda Allah ke hukunta ni da zunubin saba ma dokar aure da na yi da kaunar Hafsat a yanzu. Baffa ban taba sanin hakan haramun ba ne, na san dai kawai ba abinda kirki nayi ba, kuma tun kafin na yi sakin na soma kaunarta. Na yi don in kubuta daga dafin alkawarin da na yi wa Muazatu....
Baffa ya kara harzuka,da kakkausar murya ya ce Wace ce haka? Ashe cika alkawarin da ba na bin Allah da Manzon sa ba wani abin kiyayewa ne? Ashe akwai biyayya ga wata halitta wajen sabawa Mahalicci?
Abdulazeez ya sake rikicewa, Astagfirullah!Astagfirullah!!Astagfirullah!!!. Ya jera ta har sau uku a lokaci guda ba tare da shan numfashi ba. Ya rike tafin kafar Baffan. Don Allah Baffa ku maida min ita. Na yi alkawarin zaman aure na hakika da ita datsabtatacciyar niyya har karshen rayuwarmu, ba zan kuma maimaita kuskure makamancinsa ba, ko kusa dashi bazan kara zuwa ba, zan baiwa Mammah hakuri za ta huce ta sa mana albarka, musamman idan na maida ita. Babban burin ta shine ni da Hafsat mu rayu tare karkashin inuwar aure, Baffa zan yi zama na soyayya da amana da Hafsah har karewar numfashinmu ba don Mammah ba, sai don zuciyata da ke son ta da kaunarta.
Babu wanda cikinsu da jikinsa bai yi sanyi ba. Abin da zai sa Abdulazeez kuka tabbas ba karami ba ne sun sani. Tun filazal shi jarumi ne tun yana karami, wanda bai jingina a jikin kowa don ya rayu. Yau ga shi a gabansu yana kuka don ya rayu da Hafsat. Hannunsa Baffa ya kama, ya dago shi ya ja shi ya zaunar a gefensa.
Abdulazeez! Ya kira sunansa.
Bai amsa ba, amma ya dago da jikakkun idanunsa ya dube shi.
Abin laakari shine, idan sakinRajaiyne (Talaq Rajah) wato (revocable divorce) da turanci, idan kafin a gama iddah miji yayi kome wannan babu ishkalimatar tana cikin zummar mijinta tunda saki (rajaiy) ne ko ana gobe zata gama iddah zai iya dawo da ita ko ba da amincewarta baidan har saki daya akayi ko saki biyu. Amma idan iddar (Talaq Rajah ) wato(revocable divorce)ta kare ba tareda anyi kome ba ya zama (irrevocable divorce) matar bazata komawa mijin ba har sai in ta amince, kuma an sake daura auren da sabon sadaki. Babu sabanin raayin malamai akan wannan fatawa; maana duk sun hadu akan hakan.
Mutum ya yi aure da niyyar bayan wani lokaci zai saki matarsa malamai sun bada fatawa mabanbanta a kai. Manyan malamai daga mazhabobi daban daban sun ce haramun ne; saboda ya saba hikimar aure a shariah, sannan akwai yaudara a ciki. Wasu bangaren mafi rangwame na masana sun ce; ba haramun ba ne, amma shariah ba ta so, wato ya shiga cikin karhanci. To amma duk ba wanda ya bayyana cewa, auren bai yiwuba, ko in an yi sakin bai yiwu ba. Saboda haka; wasu malamai sun karhanta auren (sun ce makaruhi ne), wasu sun haramta shi bakidaya.Idan aka ce abu makaruhi ne ana nufin abinda sharia ba ta so, amma babu hukunci a kai. A takaice aure a kan yarjejeniya batacce ne babu shi a shariah, kuma musulunci bai yarda da shi ba. Don haka in muka dubi masalarka ta fuskar addini aurenku yana nan; mu muka daura aure, kumamun daura auren bisa dokoki na shariah (sadaki, waliyyai, shaidu), kayi saki daga bayadagagurbatacciyar niyyakuma ka gaggauta mayar da aure kafin matarka ta cika idda da kyakkyawar niyya, wanda shi ne abin da shariah ke so. Wancan sharadin da ku ka yi na farko babu shi yanzu a zukatanku. Wancan auren dama an gina shi ne a kan doronmutua sai aka sake niyya zuwa auren sunnah, shi kenan! Sai a nemi gafarar Ubangiji bisa kuskuren niyya da aka yi da farko.
: .SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

A yammacin ranar Azumi ta dawo. Kusan Abdulazeez ya fi kowa farin cikin dawowar Baba Azumi, mai sonsa da jin kansa. Ya tabbata za ta taimaka masa sosai wajen shawo kan Mammansa.
Tun dawowarta ta fahimci yadda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta tadda su, ba wani ci gaba daga bangaren uwargijiyarta. Ita ta ci gaba da kula da komai na Abdulazeez, tsaftar dakinsa da toilet dinsa da cikinsa. Ba tun yau ba ta san ba komai yake ci ba. Su sun yi rayuwa cikin turawa don haka suna amfani da ire-iren abincinsu sosai-sosai musamman kayan gwangwani. Abdulazeez kuwa na son Nigerian Food musamman na Yarbawa su Amala, sakwara, miyar ganye;su Ugu alayyahu, egusi, water leaf, da kifi da ganda saboda zamansa a kudu (Ibadan da Lagos gidansu Muazatu), su ta himmatu wurin yi masa nasa daban, wani lokacin su Hafsat rai na biyawa ta ce kuma ba mai ci har Maman nasu. Mammah kan kyabe baki ta ce,
Ina ruwan oduduwa dangin Yarbawa. Shi ya sa duk halinsu na naci kun diba. Ban da haka na ce a bar min gidana, a bar min ya ta, a je a auro yar Yarbawa kun ki, har asalin uwarta na jiyo ba yar Jigawa ba ce yar Ogun ce. Uban ne dan Jigawa.
Baba Azumi kan rausayar da kai ta ce, Kin san wani ba ya auren matar wani, jiya mun ga aurenta a obashin (ovasion magazine) Ismaeela ya kawo mana. Mammah ba ta kara bi ta kansu ba.
Su Hafsat sun fara C.A don haka a dan tsukin ba ta da sukuni, test-test da assignment kawai suke yi. Yau litinin, Mammah za ta je ganin likita kuma ya yi daidai da lokacin shigar Hafsat test. Ba yadda ta iya ta ce Salisu ya kai ta, in ya ajiye ta sai ya dawo ya same ta a Diff Hospital. Ita ya fara ajiyewa a asibitin, sannan ya karya kan motar suka nufi NILE shi da Hafsat.
Danja ce ta tsaida su a wani shatale-tale. Barrister Abdulazeez Dakata a nashi motar, cikin shirin office yake (fully robed). Ya yi tsakin bata masa lokacin da danja tayi don ya makara, ya dan juya gefen damansa sai ya hango Salisu da motar Mammah, a kujerar baya Hafsat ce ta warware handout tana ta karatu. Magana ya yi masa ba ta san suna yi ba, sai ji ta yi Salisu ya gangara ya faka a gefen titi. Ta dago don ta tambaye shi me ya tsaya yi zai makarar da ita, sai ji ta yi an bude kofar side din da ta ke. Mutum na karshe da ba ta zaci gani ba, suna yin kwana uku a gidan ba su hadu da juna ba sabida yanayin aikinsa da lokacin dawowarsa very late gefen maghriba. Lokacin ita ta shiga sallah, sai wajen cin abincin dare kawai suke haduwa, ita kuma ta tsame kanta. Don ko ta zauna ba iya ci ta ke ba saboda idanun Abdulazeez da na Mammah, kowanne na kokarin ganin cewa idonsa ya hana abin da ba ya so. Mammah ba ta son wadannan idanun na Abdulazeez su yi tasiri wajen karya lagonta, tunda ta bi kowacce kafa ta communication ta toshe. Shi kuma nasa idon so suke su fahimtar da ita how miserable and helpless they aresaboda rashin ta cikin rayuwarsa yanzu. Don haka ko da ta daina zaman cin abincin Mammah ba ta ce don me ba, ta ma fi son hakan. Amma tana tabbatarwa Azumi ta kai mata nata daki kuma ta ci. Da safe kuma Azumi a basket ta ke sanya masa karin kumallo ya tafi da shi office ba ya son abin da zai makarar da shi, mutum ne mai tsantseni a kan aikinsa da muhimmancin lokaci.
Ajiyar zuciya ta yi sakamakon tunanin da ya tafi da ita kawai saboda arba da Abdulazeez a inda bata zata ba. Fuskarsa babu wasa ya ce.
Fito, ni zan karasa da ke.
Cikin damuwa ta ce, Ni ba zan fito ba, Mammah.....
Wallahi kin ji na rantse ko ki fito ko in dauke ki na fiddo ki, a kan me wani gardi zai fita da matata ni me ye amfanina? Kawaicin da nake yi ne ba ki san ina yi ba sai na fito da true colour dina?
Daga amon muryarsa ta fahimci a matukar fusace yake, Mammah ta gwammace Salisu ya kai Hafsat makaranta a kansa, Salisu ne trusted dinta, shi kuma dan taadda mai cutar mata da ya. Jikinta har bari yake ta cizgo jakarta ta fito daga motar, ba tun yau ba ta san duk abin da ya fada zai iya aikatawa.
Shi ya bude mata kofar gaba ta zauna ya rufe. Ya zagaya ya shiga bangarensa. Da matsanancin gudu ya fizgi motar. Ban da faduwa ba abin da gabanta ke yi, tunanin Mammah kawai ta ke yi. Me Salisu zai je ya gaya mata? Ta shiga ukunta! A wannan dan tsukin burinta kawai ta ci gaba da yi wa Mammah biyayya a kan duk abin da ta ke so. Ta fahimci duk abin da Mammah ta ke so ta fahimta. Ta kamma kanta, ta bi abin a sannu. Kada tayi garaje, kada tayi gaggawa wajen komawa cikin rayuwarsa. Namiji ba abin yarda ba ne. Sannan ba dan goyo bane. Balle mai wayo da wayewar kai irin Abdulazeez Dakata, the smartest person she have ever know. Ba ya fadin sirrikansa sai dai reactions dinsa su nuna. Kamar yadda Mammah ta kafe a kai ne, how sure she is yanzun yana sonta? How sure she is ya daina son Muazatu? Duk da ko yana sonta ko ba ya sonta yanzun doesnt mattertunda ta yi aure ta barshi.
Amma Mammah a kan gaskiyarta ta ke, shekara daya da watanni da suka kwashe tare karkashin inuwar aure me ya hana ya so ta? Sai bayan ya yanke ta daga cikin rayuwarshi ta dawo gaban wadda take sonta da kauna ta har abada? Wata zuciyar mai tsananin so da kare Abdulazeez ta ce. Ke ma me ya hana ki so shi da farko, sai bayan kin zauna da shi? Wanda ke nufin dukkaninku abu daya ku ke bautawa;You didnt get to know each other well sai bayan zaman.You are not close to each other sai bayan zaman. Soyayya kuma bata faruwa sai da kusanci. Soyayyar bata huda kowannenku ba sai a cikin zaman. Give him a chance Hafsat, reason with him. Zuciyarta ta ji tana yin wani irin laushi wanda ya sa ko da ta ga ya bar hanyar Nile ba ta damu sosai ba.
Sai dai ta sa a ranta cikin kowanne hali shell not betray her mother! Shellstand by her not by him (ba za ta ci amanar Mammansu ba, za ta tsaya a bayanta baa bayanshi ba). Ginin da ya nufa da su ya tabbatar mata ofishinsa ya kawo ta, (Federal High Court of Nigeria).
Ya yi parking a parking lot ya cire wayoyinsa daga cajin da ya sanya su a motar. Ya dauko suit-case da jakar system dinsa, wig dinshi a hannu ya fita daga motar. Tsayawa ya yi yana jiran ta fito ya rufe motar. Hafsat ta ki ko da motsi. Kyale ta ya yi ya je office din ya ajiye kayan hannunshi ya dawo, da ya shigo cikin motar juya masa keya ta yi tana duban taga. Murmushi ya yi ya ce,
Me ki ke nufi da ni ne yarinyar nan?
Ba tare da ta juyo ba ta turo baki, Laifin me na yi da za ka kawo ni kotu? Test zan yi amma already ka sa ta subuce mini. Za ka iya jin damuwar hakan sosai a amon muryarta, domin ta shirya wa gwajin sosai ta kwana tana karatu.
Hannunta ya fizgo ta yi juyowar da ba shiri, a fusace ya ce. To hell with your test, duniya kawai ki ka sa a ranki ba kya tunanin lahirarki. Da kin san yawan zunubin da Mammah ke sanya ki kina kwasa da kin tausaya wa kanki Hafsat. Tana tare da mijinta kullum tana gyara aljannarta, ta nesanta ki da naki kina ta kusanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login