Showing 3001 words to 6000 words out of 133887 words
rufa wa juna asiri.
Ganin karfe goma na dare ya sa shi yin saurin fitowa ya janyo kofar dakin. Ya karasa cikin gidan ya shiga dakin Baba Azumi da zummar ya tura ta ta kira Suhaanar. Ya yi sallama daga bakin kofar, ta amsa tare da yi masa izinin shigowa. Lekawa ya yi kadan yana fadin, Ba ki yi bacci ba?
Sai ya ga Suhaanar kwance bisa cinyoyinta tana lallabe mata sassalkan gashin kanta.
Ba mu yi ba, muna dakon dawowarka ne, sai kuma Adda ta ce in yi mata kalba kafin ka dawo.
To ga ni na dawo, kuma ina jin barci. Ku yi hakuri da kalbar nan haka.
Suhaanah ta mike ta lalubi dankwalinta ta daura. Ya wuce study room din da Mamma ta yi umarni, ya zauna yana jiranta yana kuma duba agogon hannunsa.
Hafsat ta dubi Baba Azumi cikin damuwa, Idan na je bayan ina wuni sai me zan ce masa?
Baba Azumi ta juya kai cikin murmushi, Ni ma ban sani ba.
Haba Baba Azumi, ba ku koya min abin da zan ce ba za ku tura ni in yi hira da shi? Ta fada kamar za ta yi kuka.
Baba Azumi ta kafe ta da ido, Ni da wa kenan?
Ta yi shiru, ta sunkuyar da kai. Jikinta ya bata tayi rashin kunya.
Ita me ya sa ba ki yi mata wannan tambayar ba, sai ni marainiyar wayonki ko?
Yi hakuri.
Toh, tashi ki je yana jiranki, kin ji ya ce bacci yake ji.
Ta mike a kasalce ta yafa mayafin abayar Oman ruwan makuba da ke jikinta, kusan shigarta kenan dogayen riguna kala kala da wuya ka ganta da atamfa ko leshi sai in zasu Kano, a cewarta zani yana mata wahalar daurawa shikuma lace nauyi yake mata, ta nufi dakin karatun nasu.
Kanta a kasa ta yi sallama ta shiga. Ya dago a hankali yana kare ma sigarta kallo. Doguwa ce, siririya, kamannin Habiba sun kara fitowa a jikinta, sai dai zaa kira ta mai kuruciya da gogaggen jiki fiye da Habiba sanda ta ke raye. Kuma Habiba ta fita kaurin jiki. Kwakwalwarsa ta soma daukan caji tana tuno masa wata hira ta karshe da ya yi da mahaifiyarta.....
Rai-rai-rai hirar ke dawo masa... anya tunaninsa a kan Addah gaskiya ne? Hafsat BA SHEGIYA BA CE... Inda amana shi zai gaya wa kowa cewa da ubanta. Sai dai me? He is not after that (ba wannan ne a gabansa ba), tashi rayuwar ce, ba ruwanshi da rayuwarta.
Ta dade da zama, ta gaishe shi bai ji ba. Ko ya ji bai amsa ba, ba za ta iya tantancewa ba.
Ba ki iya gaisuwa ba? Ya tambaye ta bayan ya dawo daga duniyar tunaninsa.
Na ce ina wuni tun dazu ba ka amsa ni ba. Ta fada fa accent dinta mai nuna har yanzu Hausar ba ta gama daidaito a bakinta ba, yaren Dutch (flemish) ya riga ya daddatsa harshenta.
Taushin muryarta kawai ya kara masa kwarin gwiwar za ta amince da duk abin da ya zo da shi, akwai innocence intonationa cikin muryarta.
Sake gaisuwar zan amsa yanzu.
Ta dan saci kallonsa don tabbatar da shi din ne Yayan su Halim din nan, ko ba shi din ba ne? Wancan ko a murya ba shi da kirki, wannan a cikin muryarsa akwai sassauci.
Ina wuni?
Lafiya lau, kun wuni lafiya?
lafiya alhamdulillah.
Ya yi dan jim kafin ya ce, Mammah ta sanar da ke aure za ta yi mana ko?
Ta sanar da ni. Ta amsa kamar cikin rada, ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba zai ji ta ba.
To ke me ye raayinki?
Ba tare da ta dago ta dube shi ba, ta amsa. Hawaye nuna son ci kowa a idanunta.
Ni ba ni da wani raayi sai nata, ni abin ikonta ce, ni mai biyayya ce ga dukkan umarninta.
Sai ya ji yar kunyar kansa ta kama shi. Ba ta haife ta ba, shi ta haifa, ita a shirye ta ke da ta yi mata biyayyar, shi da ta haifa ya gaza.
Shiru ya ratsa, kafin ya kira ta a hankali, Hafsah!
Wani irin sauti ne mai taushi da ba wanda ya taba kiran sunanta da shi a duniya, don haka ta dago don ganin wanda ya kira ta da shi din. Abdulazeez Hamzah Dakata ne.
Like father like son.
Ta fada a zuciyarta. He looks so much like his Dad.
Ba ta zurfafa kallon nasa ba, ta sunkuyar da kanta, ba ta zaci yana da sassauci haka ba a yadda ta sanshi a baya, duk da dai ta fahimci a kanta ne kawai yake zama tough din a kan sauran kannenshi ba haka yake ba, shin ko hakan na da nasaba da cewa don ita ba jininsa ba ce, ba ta da mahaifi? Za ta so watarana ya amsa mata wannan tambayar.
Mene ne babban burinki a rayuwa? Ina nufin bayan auren da Mammanki ke son ki da shi, me ki ka fi so a rayuwarki?
Ta dan daga kanta sama alamar tunani, kafin kalaman su fito a nitse daga bakinta.
In ci gaba da karatuna, karatu mai yawa har PhD.
Ya tsaida idanunsa a kan ta.
Sai kuma me?
Ta dan yi nuku-nuku ta kasa fada sai motsa baki ta ke yi.
“Hafsah feel free with me, bayan matsayina na Yayanki ni din kuma yanzu mijinki ne in Allah ya yarda. Ina so ki saki jiki da ni ki gaya min me ki ke so a rayuwarki komai wahalarsa ko tsaurinsa?
Ta dan samu nutsuwa kadan, ta waiga ta tabbatar babu kowa cikin dakin karatun, daga su sai Allah! Ta saci kallonsa kadan, sannan ta ce, Ina so....inaso in nemo mahaifina a duk inda yake, na san mahaifiyata ta rasu, Halim ya taba gaya min ta rasu ne wajen haihuwata, amma shi baa sanshi ba, ba a san inda yake ba. Na sha tambayar Mommah sai ta ce in bar zancen sai na yi shekara goma sha takwas, yanzu kuma shekaru na sha bakwai.
Abdulazeez ya nutsu yana saurarenta, da ta gama, ya sarke yatsunsa cikin junansu, yana kallonta kanta a sunkuye. Da kyar yake gane abin da ta ke cewa da Belgian harshenta, amma duk da haka yana ganewa, ya ce.
Hafsa, na ji dukkan bayaninki, na kuma fahimta. Na farko na amince zan barki ki ci gaba da karatu, da kaina zan cike miki JAMB da ake yi a nan Nigeria, am sure za ki haye daga nan zan kai ki jamia ki zabi duk abin da ki ke so ki karanta. Burinki na biyu ganin mahaifinki ko?
Ta daga kanta a hankali tana wasa da yatsun hannunta.
Na yi miki alkawari ni da kaina zan nemo miki shi insha Allahu. Na san garin da yake.
Ta dago kanta da sauri, ta ware manyan idanunta a kansa. Amma ta kasa magana.
Da gaske nake Hafsah. Har yayye ne da ke guda uku, amma ban san maza ne ko mata ne ba.
Kawai sai ya ga hawaye ya gangaro kan kundukukinta, masu dumi, wasu na korar wasu.
Mamaki ya kama shi ainun, amma bai bar hakan ya nuna a kan fuskarsa ba.
Na yi tunanin abin da za ki ji dadi ne, amma sai in ga kina kuka?
Ta sunkuyar da kanta, sannan ta share ambaliyar hawayen da bayan hannunta.
Ni ma ban san me ya sa ni kukan ba, amma watakila kukan farin ciki ne.
Ya ce, Yadda zan zama sanadin farin cikin nan naki, nake rokon ke ma ki zama sanadin nawa farin cikin da ba mai samar da shi gare ni sai KE!
Ta dago jikakkun idanunta ta kalle shi.
Ni me nake da shi da zan saka maka wannan farin cikin da za ka ba ni? Iya tunanina ba ni da komai.
Ya sauko daga kujerar da yake kai, ya zauna dabas a gabanta. Idonsa ya kai ga yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle yan sirara da su. Ya dawo da kallonsa kan fuskarta cikin nutsuwa, ya ce.
Ba abin da za ki ba ni Hafsah, kawai amincewarki nake nema mu yi planning contract marriage (AUREN KWANGILA) tsakanina dake na tsawon shekara daya da wasuwatanni kadan.
Contract Marriage? Kana nufin auren da Mommah ke nufi mu yi, da ma (contract marriage) ne? Ta tambaye shi cikin yamutsa fuska na rashin fahimta.
Ba haka nake nufi ba. Bana so ko kadan Mammah ta san wannan zancen. Zai tsaya ne a tsakanina da ke kawai, zan cika miki manyan burikanki na rayuwa da izinin Allah kafin cikar waadin nan. Ke ma kuma za ki taimaka min wajen cikar nawa burin, ki samu farin cikinki, ni ma a karshe in samu nawa ba tare da kowa ya san me muke ciki ba har zuwa karshen waadin.
Ban gane ba har yanzu, mene ne waadin? Sannan ta ya ya za a yi hakan ba tare da wani ya sani ba? Mene ne ma naka burin? Meyasa Mammah bata gaya min hakan ba?
Ta fada cikin tsananin shiga duhu, fuskarta da yanayinta gabadaya sun nuna hakan, sun bayyana tsananin rudun da kalamansa suka jefa ta.
Gaskiya hausarta da shekarunta sun yi kadan su fahimci abin da yake nufi kai tsaye. Tana bukatar ayi mata gwari-gwari.
Hafsah ina da wadda nake so in aura ne, sunanta Muazatu. Mahaifinta Malamina ne shekarunmu biyu tare kenan, mun fahimci juna mun amincewa juna. Sannan mun yi wa juna alkawarin aure komai runtsi to the very end.
Amma Mammah ta ce ba ta amince ba, Daddy ya mara mata baya sun ce ke zan aura ba ita ba. Hafsah kamar yadda ki ka fada min burikanki a yanzu, da yadda ki ke matukar sonsu, da burin ganin cikarsu. Ni Muazatu ce burina a yanzu. Bayan ita duk wasu burirrikana na rayuwa zan iya ce miki Allah ya cika min su (Alhamdu lillah).
Za a yi mana aure kamar yadda Mammah ke so, mu zauna gida daya in sanya ki a makaranta, ki yi ta karatunki. Aurenmu babu takura, domin kowa zaman kansa zai yi kamar yadda dai ki ke zaune yanzu a gaban Mammah, gida kawai za mu canza bayan shi ina tabbatar miki ba abin da zai canja.
A cikin wannan lokacin zan nemo miki inda mahaifinki da yan uwanki suke. Da gaske ne mahaifiyarki ta rasu a kan idona, ba zan taba mantawa ba. Ba zan ce miki komai a kai ba, ki jira Mammah ta gaya miki kamar yadda ta yi alkawari. Idan na yi miki hakan ina ga na gama cika burikanki ko? Sai ni ma ki cika min nawa burin wanda ba shi da wahala, abu ne mai sauki Hafsah, shi ne ki amince in lokacin da na dibar wa Muazatu na aurenta ya cika za mu rabu, wato ZAN SAKE KI. Mu hadu mu bai wa Mammah uzuri da cewa halinmu bai daidaita ba, ko kuma haka kaddara ta tanadar mana. Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure halin dan uwansa.
A wannan lokacin na san ba su da wani zabi sai su barni in auri Muazatu, ke ma ki auri wanda ki ke so. Ga mahaifinki da yan uwanki a gefe da kuma karatunki, ina fatan kin fahimce ni?
Ta yi shiru na tsawon lokaci, idanunta na hango mata ranar da za ta kammala karatunta ga mahaifinta da danginsa a gefe, dasu Mammah kamar yadda aka yi wa Abdulazeez a (Law school). Hakika ranar za ta zamo ranar madaukakin farin ciki a gare ta wadda babu irinta...
Me ki ka ce Hafsah?
Ta tsinkayi muryar Abdulazeez mara amo kuma mai taushi a can tsakar kanta. Ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi mai nisan zango. Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta daga kanta a hankali ba tareda wani dogon tsinkaye ba ta ce,
Na amince.
Ya gyada kansa shi ma, Haka nake son ji, idan da amincewarki to komai zai tafi daidai babu tangarda har zuwa lokacin da (contract) din zai kare. Mammah ba za ta yi irin fushin da ki ke tunani da mu ba, za ta fahimce mu, in har ki ka gaya mata da amincewarki aka yi komai, kika nuna mata ke ki ka zabi sakin don ba za ki iya da halina ba. Ni ma na fada mata na kasa jure halinki ne.
Sai dai ina so wannan ya zama babban sirri a tsakaninmu Hafsah. Sirrin da babu wanda za ki fada wa mun yi shi duk duniyar nan.
Sannan bayan rabuwarmu insha Allahu zan zamo mai taimaka miki ta kowacce fuska a rayuwarki, na yi wannan alkawarin, I promised.
Sai da ta daga kanta alamun ta fahimce shi, sannan ya mike yana sanya wayoyinshi a aljihu.
Ina ga iyaka abin da za mu tattauna din kenan, dare ya yi. Ki je ki kwanta.
Ya mike ya nufi kofar fita daga dakin karatun kai tsaye without giving her a second look(ba tareda ya kara kallontaba).
Yaa Azeez!
Ya ji ta kira shi a hankali.
Sai ya ja birki ya tsaya a inda yake dab da kofar, hannunshi na kan handle din kofar. Cike da mamakin kiran sunansa da ta yi. Ba ta taba yin hakan ba ko da wasa a kafatanin rayuwarsu. Duk da cewa ta kira sunan ne kamar yadda sauran kannenshi ke fada amma a kunnenshi sai ya ji kamar wani abu daban ta fada ba sunan nasa ba. Ya juyo ya fuskanceta daga inda yake tsaye ba tare da ya dawo ba.
Ba ta ko motsa daga inda ya barta ba, har zuwa lokacin kuma tana ta cakuda kyawawan yatsunta cikin junansu. Kanta a sunkuye.
Na gode!.
Ta furta tana mai dago kai ta kalle shi.
Ji ya yi kamar zuciyarsa ta yi tsalle ta fice daga kirjinsa ta dawo, da gaske ne (shes so innocent) in ba haka ba me ya yi da har zaa gode masa? Shi a nasa tunanin ma in zaa dubi lamarin da idon basira ai babban laifi zai aikata a gare ta (saki a wajen diya mace). A gefe guda ga kuma tsallake maganar mahaifiyarsa da zai yi, ai kuwa bai cancanci godiya ba ta kowanne bangare. Sai dai ko ta wajen Muazatu wadda zai tsallake umarnin iyayensa a kanta saboda farin cikinsu shi da ita.
Bai san me zai ce mata ba, saboda haka kawai ya daga kai sannan ya juya ya fita daga dakin karatun.
Ya koma dakinsa idonsa cike da bacci da gajiya. Ko da Muazatu ta kira shi don su yi hirar daren da suka saba (midnight call) cewa ya yi da ita, ta yi hakuri bacci yake ji. Kuma ya yi magana mai yawa saboda ita a daren nan. Ya yi alwala ya yi nafila rakaa biyu, ya roki Allah ya rufe bakin Hafsah kar ta tona masa asiri a wajen Mammah komai runtsi.
Duk da dai ya lura yadda ta ke son cika burikanta, zai iya danne komai, wanda haka yake har zuciyar Suhaanan.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
*****
Kwana ta yi tana juya maganganun da suka yi na karatunta da nemo mahaifinta a zuciya da kwakwalwarta. Su kadai ta ke tunani a matsayin matsalolinta yanzu a rayuwa, ga shi ta samu wanda ya yi alkawarin dauke mata su. A kan me kuwa ba za ta yi masa yadda yake so ba ita ma? Auren ko kadan ba ya kanta dama, bata da wani hopea kansa ko experience kan abin da ya kunsa sosai balle har ta sa shi a lissafinta. Ta amince ne dama saboda Mammah don ta amince wa ranta babu abin da Mammah za ta nema a wajenta ta kasa yi mata, amma sam ba ya gabanta.
Sai ga shi a yanzu ya juye ya zama sanadin alkhairi a gare ta, sanadin da zai kai ga cikar burikan rayuwarta (karatu da mahaifinta). Ta faranta wa Mammah, sannan ita ma ta samu farin cikinta. Har ila yau, shi ma ya samu nasa cikar burin. A iyaka dan kankanintunaninta, me ya fi wannan kwangilar sauki da riba kuwa???????
*****
Gadan-gadan Tsohon ambasada Hamza Atiku da maidakinsa Hajiya Maryam suke shirye-shiryen auren yayansu, auren da suke so ya bar tarihi a dangi don haka ba karamin shiri suke masa ba.
Soyayyar Abdulazeez da Muazatu sai abin da ya karu, kullum suna tare a waya, ko ta biyo shi office ko shi in ya tashi ya je can inda ta sauka gidan Antinta har ta koma gida Lagos ba abin da ya sauya.
Ba ya yi mata zancen komai game da aurensa, ita ma ba ta tambaya, ba ta taba neman sanin yarinyar da za a aura masa din ba, shi ma bai taba yin wannan gwanintar ba. Zai iya cewa daga ranar da suka yi magana ta farko shi da Suhaana ko a hanya ba su kara haduwa ba, duk da cewa gida daya suke kwana. Yana riga kowa fita a gidan, sannan ba ya dawowa da wuri. Mammah ma ba ta kara damuwa da su kebe din ba don su kara fahimtar juna, shirye-shiryen biki kawai ta ke, hankalinta kwance, don ta lura yar damuwar da Suhaana ta ke ciki bayan ta yi mata zancen auren tun daga ranar da suka yi magana ita da Abdulazeez ta rabu da ita, ta saki ranta tana ba ta hadin kai a kan komai.
Biki ya rage saura sati uku tuni an bugo I.V an fara rabo cikin dangi. A yadda Mammah ta tsara za su taho Kano ne, a nan za a yi komai, liyafar cin abincin dare (dinner) kawai za a yi a Abuja washegarin daurin aure. Kullum za ka ganta tana waya da mutanen Dakata ana ta shirye-shirye. Ta fannin Daddy kokari yake ya kammala ginin da yake yi wa Abdulazeez a Estate din (Sun-City). Wani kyakkyawan Mansion mai hawa daya da ya dauki shekaru yana gininsa yana dakatawa tun yana Ambasada, yanzu ya maida hankali yana so a kammala komai cikin lokaci.
Mammah zaune a kayataccen falonta cikin kwalliya ta kece raini kamar kullum. Waya ta ke yi da aminiyarta ta cikin Abuja, Hajiya Halima matar Controller, magana suke yi a kan babarbariya mai gyaran