Showing 57001 words to 60000 words out of 133887 words
taba ganinsa cikin wannan halin ba. Ga shi alamarin har yana so ya shafi aikinsa. Abdulazeez din da ba ya barinsu su yi kuskure ko kankani yau shi ake yi wa gyara mai girma haka.
Gyara zamansa ya yi ya fuskance shi sosai.
Me ye matsalarka Barrister?
Yau karo na farko a rayuwarsa neman wanda zai budawa cikinsa yake yi, ko zai samu wata shawara wadda ta fi tasa inganci. Ya yarda ya gama lalata rayuwarsa in bai je Jimeta a gobe ba har takardarsa ta je hannun mahaifiyarsa. Ba hukuncin da zata yi masa yake tsoro ba; bazata taba yarda da dawowar Suhaanah gareshi ba! Ta sha gaya musuopportunity comes only once in life (dama tana zuwarwa dan adam sau daya ne a rayuwa) kuyi amfani da ita a sanda kuka sameta. Yau ba yana son Hafsat-Suhaanah don Mammah ba ne, sonta yake a karan-kansa da soyayya mai azabtarwa. Bai san sanda ya buda baki ya ce da Ahmad.
In an yi saki, ya ake a gyara? In an yi alkawari aka kasa cikawa daga baya ya ake a yi kaffara?
Gaban Ahmad sai da ya fadi, bai san sanda ya ce a tsorace, You mean ka saki Hafsat? Auren shekara daya kacal?Kai kuwa me tayi maka haka da zafi?
Kamar zai kife shi da mari ya ce, Ya zan tambaye ka, kuma ka bi ni da tambaya?
Ai ban san sakin wane iri ba ne. Ya fada cikin sanyin jiki.
Abdulazeez ya kwantar da kansa a kan teburinsa. Murya a raunane ya ce. Thisis the deadly mistake ive ever made, na sake ta Ahmad, amma ina so in dawo da ita. Dubi yadda na zama cikin sati daya kacal da yin sakin. Da farko na yi zaton Muazatu nake so a kanta, yanzu da babu ita cikin gidan na gane Muazatun ba ta da matsayi mai yawa a tare da ni. Ka taimake ni Ahmad ba ni da idea.
So yake ya ce da shi. Ai mun gaya maka, watarana za ka so yarinyar nan ko da za ka yi mata kishiya. To amma tausayin Abdulazeez din ya hana shi fadin hakan, yanzu ba lokacin raddi ba ne. Lokacin neman mafita ne. Kuskure ne ya riga ya yi shi sai a nemi hanyar gyarawa in mai gyaruwar yayi. Bai nemi baasi ba, cike da fargaba ya ce.
Sakin guda nawa ne?
Ba tare da ya dago ba ya ce, I think daya ne. A gurguje ma na rubuta ina tsoron ta zo ta ganni ina rubutawa. Ahmad proffession dina bai kare ni da komai ba da na kasa gane ba hanyar samo Muazatu na bi ba, hanyar kara tsanarta a zuciyar mahaifiya ta na bi. Hanyar kara nesanta kaina da ita na bi. A karshe in kare da babu ko dayansu muddin zancen sakin ya je kunnen Mammah.
Ahmad ya dafe kai.
Yanzu ina Hafsat din?
Tana garinsu Jimeta.
Just call her now (kira ta yanzu) ka ce da ita na maida ke dakinki, shi ne muhimmi kafin komai. Ko ta yarda ko bata yarda ba; ta maidu.
Wayar ya janyo cikin kasala duk da ya san ba samun nata zai yi ba, amma haka ya yi ta gwada jera kiran yana katsewa. Ya dubi Ahmad cikin rauni.
Ta dade da yanke communication da ni, na tabbata ta dade da ganin takardar, da kyar in bata canza layin waya ba.
Ahmad dai haushin Abdulazeez kamar ya kashe shi. Wai a kan wata da yake hange a waje ya saki ta gida, ba dole hakki ya rikide masa zuwa soyayya ba?
Tunda gobe weekend ne za ka iya zuwa Jimetan, make sure ka kwace takardar ka kuma gaya mata ka maida ita ta ji da kunnenta. Ita kuma wannan Muazatun ajiye zancenta a gefe sai ka dawo da zabin mahaifiyarka. Abdulazeez kana tune da hakkin mahaifiya kuwa da karfin ikon da Allah ya ba ta cikin rayuwarka? Allah (S.W.A) Ya ce a bi ta, a bi ta, a bi ta kafin ya ce a bi uba. Amma budurwa??? Kana son ganin albarka cikin rayuwarka? Ta aura maka mace har mace mai daraja irin wannan ka saki? Inda hali mu tafi tare, mu hau jirgi don mu yi sauri. Ireallywant to help.
Daga office din kai tsaye gida ya wuce, ya samu Mammah da Daddy a falo suna cin abinci. Sun masa tayi, amma yau sam ya kasa cin abinci. Jiransu ya yi har suka kammala, Daddy ya dawo tsakiyar falo ya zauna a kujerun falon na alfarma. Budar bakin Daddy sai cewa ya yi.
Za ka wakilce ni a graduation din Ismael da Usman a America da Brussels jibi, zaka fara halartar na Ismael first,sai ku wuce Brussels na Usman tare dashi, ni ayyuka sun min yawa, passport dinka daka bani na sabunta maka watannin baya ya jima a wajena don haka tuni na gama maka shirin komai, thumb print kawai zakaje kayi da safe namaka bookingma, sai ka zaba tsakanin jirgin safe ko na dare. Na gayawa shugabanku dazu ya baka leave na sati daya na tura ka wakilci kuma ya amince, zakayi sati daya sai ku dawo tare da su duka. In an kwana biyu kuma ni sai in je wa Haleem visit a Sweden.
Dukkansu babu wanda bai lura da yanayin canzawar fuskarshi ba. Wata irin canzawa kamar an aiko masa da sakon mutuwa, fuskar har wani brown ta koma. Da kyar ya iya hadiyar miyau, cikin damuwa ya ce.
Daddy Jimeta za ni gobe.
Mammah ta ceJimeta kuma? Cikin mamaki sosai, ta cigaba da cewa. Dan zaman da za ta yi cikin yan uwanta na sati biyu kacal za ka haramta mata karashe shi? Ina ce next week za ta dawo? To ban yarda ba, wannan rashin hakuri da rashin kawaici har ina?.
Daddy ma yana bayan Mammah, ya ce, Ba za ka je Jimeta ba sai ka dawo daga graduation din nan sai kaje ku taho tare.
Ya amsa a ladabce,kansa na kasa, kasancewar yasa a ransa bazai kara jayayya da iyayensa ba har karshen rayuwarsa! Amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci bai so wannan tafiya ba. Tamkar wata obstacle ce ga isa ga Hafsat da gyara gundumemen kuskurensa da wuri. Zuciyarsa na lallashinsa da cewa, Hafsat-Suhaanahwill not expose his shortcomings, za ta yi masa uzuri kamar yadda ta saba, za ta rufa masa asiri kamar yadda ta saba, zata jira shi har ya dawo kafin ta dawo Abuja bazata dawo ita kadai ba komai dadewar da zai yi balle sati daya kacal, tunda ma ai shi zai je ya dauko ta wanda dole a jira ya dawo.
Abin da Abdulazeez Dakata ya manta shi ne duk yadda muka kai ga tsara wa kanmu alamura sai Allah ya nufa. Bai yiwuwa mu yi ta tafka kuskure yadda muke so mu ce zamu gyara komai a lokacin da muka ga dama. Allah yana ara mana dama mai dumbin yawa a rayuwa mu yi ta yin abin da muka ga dama, rana daya in Ya tashi kama mu ba Zai ba mu damarrepentingna minti daya ba. Wasu alamuran na zuwa cikin rayuwarmu don su zama iznah a gare mu.
8SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ta zura hannu cikin jakartatana lalubo wayar, sai ta ji farar takardar cikin ambulan. Zaro ta ta yi ta juya ta a hannunta ganin an rubuta sunanta HAFSAT a jikin ambulan din. Sai dai abu daya ya ja hankalinta, handwriting din Abdulazeez ne wanda ya riga ya zauna a memory din ta sabida yawan duba takardunsa data ke yi in ya bari a falo. Ta maida ita inda ta dauko ta don ta ga bai kamata ta bude agaban Mammah ba batasan ko menene a ciki ba. Mammah ta ce.
Wasikar mene ne wannan kamar rubutun mijinki?
Cikin jin kunya irin nata ta sunkuyar da kai, ta ce, Ina jin shi ya saka.
Mammahbata ce komai ba ta yi musu sallama ta bi bayan su Adda Hafsatu, Suhaanah ta koma dakin Dada rike da jakarta.
Har karfe goma sha daya na dare Hafsat da kakarta Dada ba su kwanta ba. Hira suke yi tana ba ta labarin rayuwar mahaifiyarta. Da duk abin da ya kamata ta sani na zuriarsu. Ita kuma Hafsat na ba ta nata labarin rayuwar a gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku har zuwa aurenta.
Dada ta ce, A duniya da ma akwai sauran mutane irin wadannan? Alherinsu ya bi su har yaya da jikoki.
A cikin labaran da ta ke baiwa Dada ba ta taba kuskuren cewa Daddy bai karbe ta a baya ba, ta riga ta shafe wannan daga tarihin rayuwarta, ko Daddy bai yi repenting kuskurensa ba ba za ta gushe tana mai yi masa uzuri ba da kallonsa matsayin uban da ya haife ta.
Suna shirin kwanciya tana kakkabe gadon bonon Dada da gefen zaninta don ta kwanta, Dada ta shimfida sallaya za ta dasa sallar daren da ta ke cinye rabin dare tana yi sannan ta kwanta. Ta bawa Dada baya tana ta kakkabe gadon, ta ji muryar Dada na zolayarta.
Tun ganina da shi na farko na ji ya kwanta min a zuciya kamar autana Nuru. Da Hajiya Mairamu ta sani ta barki kin bi mijinki kun yi kwanan sallama, tunda za ki kwana biyu a nan a kai ki ki ga sauran dangi da ba ki gani ba, kuma Babanki ya ce za ku je Numan ya kai ki wajen nashi yan uwan.
Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba, a ranta ta ce, Maaurata na hakika su suka damu da juna har in za su rabu na wani dan lokaci su damu da su yi sallama da juna ban da mu Dada! Mu namu auren suna ne kawai.
Ta shiga tunanin ita yaushe rabon ma ta kwana daki daya da Abdulazeez Dakata? Tun wani zamani can da suke cikin zama na aminci kafin ya rikide mata ya canza kamar wahainiya, har gobe in za a kashe ta ba ta san ina Abdulazeez ya sa gaba a aurenta ba. Idan ta yi kokarin fassarawa sai ya rikide ya canja wanda ya nuna shi kansa ba shi da direction. Tunowa ta yi da takardar dazu da ta ciro a jakarta har Mammah ta gani, ta yi mamakin yaushe ya sa takardar a jakarta ba ta sani ba? Ta kuma cika da dokin son ganin me takardar ta kunsa? Don haka da ta gama gyaran gadon, kayan barci ta sanya ta jona wayarta a caji, sannan ta dauko takardar ta bi lafiyar gadon audugar kakarta, ta rufe rabin jikinta da bargon Dadan ta bude takardar ta soma karantawa.
Ga abin da Abdulazeez Dakata ya rubuta wa matarsa Hafsat-Suhaana.
‘A zaman da muka yi na tsawon watanni goma sha biyar, in na ce akwai wata rana da ki ka bata min ko kika yi min abin da raina ba ya so ba bisa kuskure ba, na zalunce ki. Ta nawa bangaren ne akwai babban gibi da ya sa ni kasa ci gaba da zama da ke Hafsah, amma ba don ba ki cancanci a so ki ba, ko a ci gaba da zaman aure da ke ba. You are a darling (ke abar so ce) ga duk wanda Allah ya yi wa alfarmar samunki a matsayin mahadin rayuwa. Rauni na guda daya ne; INA SON MUAZATU! Na yi duk iya tunanina don nema wa aurenmu mafita na rasa Hafsat don shinge ne (barrier) a gare ni ga samun Muazatu, amma ba don ina kin ki ba. A bisa hakan, da wasu dalilai da dama na yanke igiyar aurenmu guda daya kamar yadda muka yi YARJEJENIYA. Allah ya ba mu mafita ta alkhairi ni da ke bakidaya.
Sa-hannu
ESQ Abdulazeez Dakata.
A hankali Hafsat ta lumshe idanunta, zuciyarta ta yi wani irin bugu sau uku; fat-fat-fat, a jere a lokaci daya. Ta shaki iska don ta fesar amma iskar ta makale ta ki fitowa daga huhunta. Kokawa ta shiga yi da numfashinta daga huhu zuwa makogaro amma iskar ta ki fita wanda hakan ya maida ita unconscious na lokaci mai tsawo. Sai numfarfashi ta ke ta baka kamar mai ciwon asthma da ta samu attack.
Dada ta yi sallama kenan daga sallar da ta idar ta ji numfarfashin Hafsa kamar na fitar rai. Da sauri ta yaye mayafinta ta wurgar ta yo kanta. Bakinta ta sanya cikin bakinta ta shiga ba ta taimakon farko irin wanda ake badawa mouth-to-mouth idan numfashi ya yi gardama.
Sun dauki mintuna biyar a haka kafin ta ji numfashin Hafsan na daidaita. Dago ta ta yi ta kwantar a kan kirjinta ta rungume ta.
Ko da Hafsat ta samu kanta runtse idanunta ta yi hawaye suka soma sauka wani na bin wani. A ganinta bai kamata sakin ya fitar da ita hayyacinta har haka ba tunda akalla ta san da wanzuwarsa. Lokacin karbarsa ne ba ta sani ba. Ya zo mata ne awkwardly(bagatatan) kamar fadowar aradu. Abdulazeez ya shammace ta, ya kuma tafi da dukkan farin cikin da ta ke ciki a yau wanda shi ne silarsa. Bai kamata ta ce ya karya zuciyarta ba, amma ya karya din. Rokon Allah ta ke ya sa mafarki ta ke yi, ire-iren mafarkanta na ranakun KWANGILA sun cika Abdulazeez ya sake ta. Ta farka ta ganshi yana shirin (office) a gefenta ko yana kumbing kanshi yana feso mata ruwan jikakkiyar sumar sa a fuska, amma ta yi duk wani kokari da za ta iya don ta farka daga mafarkin yau, wasu hujjoji masu yawa sun tabbatar mata na yaureality ne.
Hujja ta farko jinta jikin dattijuwa Dadanta, tana shafa kwantaccen gashin kanta tana tambayarta, shin tana da ciwon asthma? Da hausarta da ba ta fita sosai, amma kwarai ta ke gane duk abin da ta ke fada.
Ba ni da asthmaDada, amma ina da nimoniya (pneumonia). Ta amsa cikin dusashshiyyar murya.
Amma abin da ki ka yi dazu, ya fi kama da na mai ciwon asthma.
Hannu ta kai tana share hawayen da ke yin ambaliya suna bulbulowa daga idanunta.
In ma ba ni da Asthma Abdulazeez ya saka mini. Abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta.
Baccin da ba su yi ba ke nan, sai da aka yi kiran assalatu a kunnuwansu. Hafsat ta ga kuka da ciwon zuciya ba za su kare ta da komai ba tunda dai (he finally made his decision) ba ya bukatarta cikin rayuwarsa, bai boye ba ya gaya mata, ya kamata ta bude zuciyarta ta rungumi kaddararta da hannu bibbiyu...Ta karbi rayuwar a yadda tazo mata.
Ko wani bai fada mata ba ta fahimci zuciyarta ta dade da kamuwa da so da kaunar Abdulazeez... to idan so cuta ne ya kamata hakuri ya zamo maganin cutar nan tunda an ce babu cutar da ba ta da magani a duniya.
Da wannan tunanin Hafsat ta kwarara zuciyarta, ta karbi butar da Dada ta cika mata da ruwa ta zaga ta kuma dauro alwala. Kafin ta yi sallah sai da ta tabbatar ta yi wa takardar sakinta kyakkyawan boyo, ta yi alkawarin kame bakinta ba dai wani ya ji wannan maganar daga bakinta ba, shi da ya aikata ya yi musu bayani in sun nemi baasin rashin dawowarta. Ta zo Jimeta kenan! Ita da Abuja sai da ziyara, ziyarar ma daga shekara sai shekara.
Ta dauki rayuwar da ta yi da Abdulazeez Dakata ta sanya cikin wani kundi (littafi) mai dadin karantawa. A yau ta kawo karshen karatun wannan KUNDI wato littafi ta rufe shi ta adana cikin tsohon akwatin karfe ta tura karkashin gado tare da duk wani alamari da ya shafe shi. Tana tausayin kanta da sabon sunan da alumma za ta laka mata na bazawara(before the age of 20), amma ta fi tausaya wa Mammah.Wadda ta dauki duk wani buri ta dora a kan aurenta da danta. Dan da a wurinta ba nata ba ne, ita ce yarta. Idan kalaman Abdulazeez sun so su yi mata ciwo sai ta yi maza ta kawo uzuri... iyakar gaskiyarsa ya fada... ya fadi zahirin abin da ke zuciyarsa ne. Yana daga cikin halayensa da ta ke so; fadar gaskiya komai dacinta... Bata da abubuwan da Muazatu ke da su, shi ya sa ya kasa ba ta gurbin matar aure!!!
Sallah ta ke, amma kuka ta ke yi, hawayenta na bilbila a cikin sujjadarta. Rokon Allah ta ke ya ba ta juriya ta karbi sabuwar rayuwar nan da ta zo mata!!!
******
Da dai a ce ba daki daya ya kwana da kakansa Baffa Atiku ba da Allah kadai ya san irin halin da zai kasance. To Baffan kamar ya gane yana cikin wani hali, ya kasa ya tsare ya hana shi tunanin komai. Idan Allah ya yi maka alfarmar rayuwa da kakanninka, to ka gode masa duk girmanka. Suna da wani feeling a kan jikokinsu da son farin cikinsu wani lokacin fiye da iyayen da suka haife su. Bai titsiye shi a kan sai ya gaya masa damuwarsa ba, amma ya lura ana ta kiransa a waya ba ya dauka, karshe ma da aka ci gaba da kiran wayar ya kashe ta bakidaya ya sanya ta a caji. Baffa bai bar kunnuwansa sun huta ba sai da bacci ya soma fizgarsa. Wani azababben barci da babu komai sai mafarkin Hafsat-Suhaanah, da halin da ta ke ciki a daidai wannan lokacin domin ya tabbata zuwa yanzu kyakkyawan sakonsa ya isa gare ta.
Kowa ya kalle shi a washegari sai ya tambaye shi ko ba shi da lafiya ne? Musamman Daddy wanda ya fi kowa shiga damuwar halin da ya ga Abdulazeez din a ciki. Ya zabge ya fyade a dare daya kamarwanda ya yi wata yana jinya, ya ce in ya san bashi da lafiya ba zai iya tuki ba su je Airport su hau jirgi ragowar su taho a mota, ya ce zai iya, kuma lafiyarshi kalau bacci ne bai samu ba. Wani irin kallo Daddy ke binsa da shi na rashin yarda.
Demsawo suka nufo suka yi sallama da kowa na gidan, Mammah ta ce da Hafsat tunda hutu bai kare ba ta yi zamanta sai hutu ya kare Abdulazeez ya zo ya taho da ita. A karshe ta ce, ta je yana