Showing 90001 words to 93000 words out of 133887 words

Chapter 31 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

561

ke so ya je ya yi ko me?
Please ina son kadaici, hayaniyarki ciwon kai ta ke sa mini, ba don na tsufa ba da na dauko budurwa sabida tension dinki a kwanakin nan da ke neman nima ya hauhawar da jinina. Ko ba komai na san in na dawo zan samu mai yi min sannu da zuwa. Saboda auren yayanki duk kin lalata kyautatawar da ki ke yi wa naki auren. Don Allah je ki daga cikikiyi hayaniyarki ke kadai.
Rai bace ta wuce ta bar dakin, ta sanya kai za ta fita, Abdulazeez na sanyo dogayen kafafunsa zai shigo saura kadan su yi karo. Da sauri ya ja baya ya ba ta hanya. Mugun kallon da ta jefa masa sai da gabadaya hanjin cikinsa suka hautsina. Ya tabbatar ta bare da shi ne, amma da wuya in Hafsat ce ta fada mata laifin nan da ya yi mata. Salisu ya fado masa a rai. Ya yi catching breath dinshi sharplysannan yayi saranda ya shiga falon Daddy. Yana shiga shi ma bai barshi ya zauna ba ya soma karbar nasa rabon don bai gama hucewa ba.
Kai da uwarka so ku ke ku kwantar da ni ko? Ina lallaba tsufana cikin koshin lafiya shi ne abin da ba kwa so ko? Tunda ta fada maka abin da ba ta so ka bari mana har sai ta sauko? Ka san dai ba za ta dauki matarka ta aura wa wani ba ko tunda ka maida ta? To gajen hakurin na mene ne? Ka ba ta lokaci mana tunda ka san yadda zuciyarta ta ke kamar ta kuturwa ba mai sa ta ba mai hana ta? Not even her mother! Idan ka kawo ni bango ni ma korarka zan yi daga gidan nan....
Shi dai ya zauna a kan kafafunsa ya nutsu yana sauraro. Sai da ya gama tsaf sannan ya kwantar da kai da murya ya soma ba shi hakuri. A karshen ban hakurin nasa yace.
Kuma Daddy ba wani waje na kaita ba banda makaranta.......
Dr. Hamza ya kara harzukowa cikin hargagi ya ce.
Na tambaye ka? Na ce tambayarka na yi? Ko bangon duniya ka kai ta ina ruwana ba matarka ba ce? Im talking about your mother, dole ka guji bacin ranta idan kana so ka wanye lafiya.
Hakuri ya ci gaba da bayarwa sai da Daddyn ya ce ya ishe shi, ya tashi ya ba shi wuri sannan ya mike. Sai kuma ya dawo ya zauna ya fiddo takardun sponsorship dinsu na tafiya karo karatu ya karasa a hankali ya aje masa a kan tebir. Ya shiga yi masa bayanin komai. A karshe ya ce.
Amma Daddy ni na yanke shawarar ba zan je ba, zan koma Ibadan na yi.
Wata harara Dr. Hamza ya watsa masa, Ibadan? Aah ODUDUWA! Wallahi ka ji na rantse ka tafi karatun nan ka gama, salon ka je ka kara lakewa wata yar Attorneys din ko dangin Yarbawa? Su baka surkullensu cikin abinci kazo ka daga mana hankali? To ka sa a ranka cewa, in ka ga ba ka tafi karatun nan ba, bana numfashi ne.
Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya kasa tashi. Bakinsa ya shiga motsawa alamar akwai sauran magana a bakinsa. Daddy ya harare shi.
Me ya rage kuma?
Sunkuyar da kai ya yi, cikin fargaba ya ce,
Dama wai cewa zanyi wai.... ko in yi visa da Hafsat?
A nitse Ambassador Hamza ya dube shi, can kasan zuciyarsa tausayi ne fal! A hankali ya furta.
Ita kuma nata karatun fa?
Abdulazeez ya ji duniyar kanta ta tsaya masa cak! Da ya san abin da karatun nan zai zame masa kenan da baa fara shi ba. Shi ba abin ya ce zai nema mata wani a can ba shekara daya kacal zai yi. Ci gaba ya yi da zama ba shi da niyyar tashi. Tausayi ya cika zuciyar Dr. Hamza, daurewa kawai yake yi. Ganin Abdulazeez ba shi da niyyar tashi, kuma ana ta kiraye-kirayen sallar magriba ya ce da shi.
Idan zuwa lokacin uwarta ta sauko, zan duba possibility na zuwanta wajenka hutu har ka kammala, ka fada musu su fito mu yi sallah.
Godiya ya yi sosai, sannan ya bar dakin. Tare suke yin sallar magriba da isha wani lokacin in har dukkansu suna gida.
Saboda kunyar Mammah yau Hafsat kasa fitowa ta yi daga daki tun shigewarta. Abincin dare ma Baba Azumi ce ta kai mata.
Washegari Hafsat ta shirya tana jiran fitowar Mammah ta sauke ta. Shiru-shiru ta ji babu ko motsinta a gidan. Dole ta yi gammon kunyarta ta fito zuwa kicin. Baba Azumi ce kadai tana ta aikace-aikace, ta gaishe ta sannan ta tambaye ta Mammah, ta ce ita ma yau tun safe bata ganta ba kuma Daddy ya jima da fita.
Juyawa ta yi zuwa dakin Mammah, a darare ta yi sallama ta shiga. Fitowarta daga wanka kenan tana shiryawa. Gaishetata yi, ta amsa ba yabo ba fallasa, wannan ya ba ta karfin gwiwar cewa.
Mammah, dama na jiki shiru ne, na leka kicin Baba Azumi tace ba ki fito ba.
Ki je ku tafi da mijinki, nawa mijin ya hana ni kai ki.
Dan jimm! Ta yi, jin kamar cikin gatse ta fada, ta yi kasa da kanta, Ki yi hakuri Mammah abin da ya faru jiya wallahi....
Addah! Did I ask anything?
Ta girgiza kai tare da hadiyar miyau, mukut!Mommah to ai na ga kamar....kamar kin yi fushi ne?
Murmushin takaicinsu su duka biyun ta yi, sannan ta dube ta. In ba so ki ke yau ma ki bata min rai ba to ki wuce ki neme shi ku tafi. In kun ga dama ku wuce gidanku daga can. Im just trying my best to protect your dignity,in kuma kwato miki darajar ki da ya bi ya wulakanta sabida wata mace yar uwar ki da bata fi ki komai ba, amma na lura aikin banza nake yi. Adda kina da wayonki dana ke ganin baki da shi, tunda har kinsan ki yimin karya sabida Abdulazeez. Don haka bana cikin shaaninku, ku barni in yi alamuran gabana.
Kukan da ba ya yi mata wuya ta soma, Mammah ko ta kula, ta ratseta ta wuce zuwa closet dinta, kaya ta saka ta fito ta wuce ta gabanta ta bar mata dakin.
Makarantar da ba ta je ba kenan saboda rashin dadin zuciya. Inda Allah ya taimake ta ma ba su da gwaji, kuma lacca daya gare su. A yinin ranar bakidaya Mammah ba ta shiga harkarta ba, Azumi kadai ke kula ta, ita ma ta lura yau ta yi tsami tsakanin Mammah da yar gaban goshinta. Amma an ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi balle irin nasu, da in ka sake ka shiga koda da ba da hakuri ne kai ne da shan kunya.SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Washegari bayan ta shirya ko breakfast ta kasa, labewa ta yi jikin tagarta sai da ta ga ficewar Abdulazeez daga parking space na gidan. As usual cikin shigarshi da ke tafi da imaninta;dark grey suit da farin tie a wuyansa rike da black robe dinsa da wig a hannu, ya bude mota ya shige. Ya ajiye su a kujerar gefensa ya gyara tie din wuyansa ta hanyar sassauta shi, sannan ya kunna motar.Har ya bar gidan a kan idonta.
Ajiyar zuciya ce ta subuce mata, ba ta da idea na yadda ta yi kewarsa cikin kwanaki biyun nan. Mayafi ta yafa kalar atamfar jikinta ta dauko handbag dinta ta fito. A kicin ta tadda Mammah da Azumi ta gaida su. Azumi ta amsa, amma Mammah ciki-ciki ta amsa. Cikin marainiyar murya don Mamman ta ji tausayinta, ta ce,
Mammah ko Illaila yana nan? Zan je na roke shi ya kai ni makaranta.
Kamar ta rabu da ita, sai kuma ta ce, Ke ma kin san bacci yake, amma ai kina ji shi wannan din mai sammakon ya fita ko? Me ya sa ba ki fito da wuri kin bi shi ba?
Shiru ta yi, a ranta ta ce. Don kar in kara laifi. Sai ga Usman ya shigo, Mammah yake nema. Ya dube ta ya dubi Mammah da ke cin magani.
Ya aka yi ne senior Sis?
Mammah ta ce, Ka sauke ta makaranta in hanyar za ka yi.
Ya fada mata sakon da ya kawo shi, ya ce su je ya kai ta.
Kwana uku Usman ke kai ta makaranta ya dauko ta, ta ki yarda ta hadu da Abdulazeez ma, duk dai don kada ta kara laifi a wurin Mammah. Shi din kuma isvery busy shirin tafiyarsu kain da nain shi da colleaguesdinsa, wataran har tara na dare yake kaiwa bai dawo ba sabida cuku cukun visar su. Mammah ta san da zancen tafiyar, sai dai ba wanda ya ji ta bakinta a kai, ta ce da Daddy da ya gaya mata zancen Allah ya bada saa.
A cikin ranta damuwa ce tsantsa, kada kuma wannan karon ya je ya kwaso mata soyayyar baturiya.
Zuwa wannan lokacin ta sallama, ta hakura ta yi niyyar amincewa ta maida Hafsat gidanta bayan ta gama jarrabawar karshen semesterda za ta fara sati mai zuwa, sai kuma ga wannan zancen tafiyar ya taso.
Sati daya bayan haka suka wayi gari da baki na ba-zata, Malam Hashim Babbah Jimeta, uwargidansa Daada Zainabu da kafatanin iyalinsa maza da mata, masu aure da marassa aure. Wannan tafiya takakkiya ce ta godiya daga wannan zuria mai albarka zuwa zuriar Maryam Dakata da maigidanta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daga nan Abuja, Kano za su wuce gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Daddy ya san da zuwansu don yana office Malam ya kira shi ya gaya masa tahowarsu, ya kuma kira Mammah a take ya gaya mata. Nan da nan ta sa maaikatan gidan maza na waje su bude sashen baki su gyara duk da kusan koyaushe a gyare yake. Ita da Baba Azumi kuma suka shiga kitchen. Hafsat tana makaranta sai gefen maghriba ta dawo. Tun daga gate ta fahimci gidansu a cike yake, motocin buses(Yola Express) har ukku, tana kuma iya shaida motar Babanta Sienna da motocinsu Uncle Sagir data Modibbo. Tun Usman bai gama daidaita parking ba ta fice saura kadan ta fadi. Shi ya biyo ta da jakar hannunta cikin gidan.
Tana shiga falon farko ta yi arba da DAADA da gudu ta runtuma ta rungume tsohuwar, daga nan ta shiga bin matan daya bayan daya tana runguma bakin nan har kunne. A gaban Dr. Bashar ta dakata sai yashe baki ta ke. Cikin dan fillancin da ta koya wajen Dada ta ce da shi, Abba mi nani beldun larugo ma, noi lawol? (Abba na ji dadin ganinka, ya ya hanya?)
“Minma minani beldun larugo ma Ghaaji, on don jambe jaumu sare ma be saro ma(ni ma na ji dadin ganinki auta, ina fatan kina lafiya ke da mijinki da iyayenki)?
Mindon jam do hairu Abba (lafiya muke cikin alheri Abba).
Imamu ta kalla ta ce, Na yi mafarkinka Hamma Imamu, ashe ba da jimawa ba za ka zo.
Murmushi ya yi, ya ce, Gaji abeddi vodugo (kin kara kyau). Barrister ya iya kiwo.
Kunya ta ji ganin Mammah ta kalle ta.
Ta ce masa Ya Futy? Are you done with your project?
Ya ce, Na gama, ina jiran su kira ni defence. Barrister ya gaya min you are studying Geography, yana so ki zama malamar makaranta sabida sanyin halinki, teachingsai mai hakuri. I told him that is how our mother was, she is very cool. Kin san kusan koyaushe muna waya da shi. Shekaranjiya ya ce zai zo Jimeta in the nexttwo weeks sallama, zai tafi karo karatu.
Maganganunsa sun jefa ta a kogin mamaki, sun yi nitso da ita a kara son Abdulazeez, sai dai magana ta karshe ta kidima ta, karo karatu? Yaushe aka yi wannan maganar?
Kasancewar falon ya gauraye da hirarraki tsakanin bakin da jamaar gidan kasancewar har Daddy ya dawo ya zauna cikinsu ba mai jin hirarta da Yayanta Imamu, Yayan da ya fi sauran (Modibbo da Abdurrahman) shiga zuciyarta saboda kulawarsa gare ta da personality dinsa na son karatu irin nata. Imamu rikakken dan boko ne, wanda son zurfafa ilimin bokon ne ya hana shi aure da neman aiki har yanzu, tun bayan kammala digirinshi na farko. Ba tare da ya lura da yanayin kidima da labarinshi ya jefa ta ba ya shiga ba ta labarin kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin mahaifinsu da Abdulazeez a yanzu. Da kuma su kansu ba tare da saninta ba. Ya kare zancensa da tambayarta ko tare za su tafi? In tare za su tafi ya ya nata karatun?
Ajiyar zuciya mai nauyi Hafsat ta sauke ta dubi Yayanta Imamu, gaskiya ta gaya masa ita ba ta san da maganar ba. Rokonta ya yitunda ba ta sani din ba, kada ta ce ta ji ta a bakinsa. Da ya san ba ta sani ba da bai fada ba. Dariya ta yi, ta ce, Wallahi babu komai.
An yi hira ta zumunci iri-iri, an ci abinci an sha ababen sha daban-daban. Sai wajen karfe tara Abdulazeez ya dawo ya tadda su duk da dai ya san da zuwan nasu, suna hanya Dr. Bashar ya gaya masa da suka iso ma Daddy ya kira shi ya sanar da shi ya ce yana office yana cike-ciken takardu kasancewar tafiyar tasu saura sati daya. Sai yanzu ya gama ya dawo. Hannu Dr. Bashar ya bude masa tun shigowarsa yana fadin,
Come here my son.
Kunya ya ji sosai, ya so ya fara isa gurin Malam Babbah, amma Dr. Bashar ya makale shi. Ismael dariya abin ya ba shi ganin reaction dinsa kamar mace a gaban suruki, wai Yaya Azeez ne da jin kunyar wani. Har karfe goma na dare suna falon, sannan kowa ya fara neman makwanci, mazan a hoteldin (Berkshire, Asokoro) Daddy ya yi musu masauki, matan suna guest rooms wasu suna cikin gidan. Hafsat ta ceDada bakuwarta ce gado daya za su kwana. Mammah kuma Aunty Kubra da Kaltum matar Modibbo ta kai nata dakin. A dakin Baba Azumi ma akwai su matan Yaya Tijjani, matan sauran yayyen marigayiya Habiba su biyar, sauran kuma suna guest rooms din gidan. Malam Babbah an ba shi daki daya a dakin bakin saboda ya ce ba zai iya kwanan hotel ba.
Da manyan jifa-jifan Daddy Ismael, Usman da Salisu suka yi ta jigilarsu zuwa hotel. Abdulazeez yana dakin Malam Babba, sabuwar hira suka bude, Malam Babba na son jin labarin rayuwar yarsa Habeebah a Jeddah da kuruciyar Hafsat.In ya tambayi Abdulazeez dayan wannan, murmushi yake yi ya ceMalam Habeeba ispious (mai ibada ce) as far as I know. Ba abin da ta ke so irin jumaah ta zagayo mu shiga cikin Haraam, mu yi umrah (dawaf, safah da marwah) ta yi ta sallah a maqama Ibrahim. Na dade da lura da hakan a tare da ita, sannan tana son karatun alkurani. Akwai islamiyyah da Daddy ya sanya ni ta Larabawa a can Jeddeh idan na je musu hutu, idan na dawo sai ta ce in karanta mata inda aka kara min. As for Hafsat ba zan iya karar da komai a kan kuruciyarta ba.
Saboda sun yi dukkan kuruciyarsu a wata kasar TuraiBelgium yayin da ni nake nan Nigeria. Dan sanin da na yi mata sanda suke Saudiyyah ne. An haife ta bakwaini, ta dade a cikin incubator;wata kwalba ce da ake saka jariran da aka haifa ba su isa lokacin haihuwa ba. Ban taba yi mata kallon rayayya ba; dalili na shine an haife ta bakwaini, kuma uwa bata mike ba, sannan ga pneumonia. Amma buwayar Allah da ta wuce misali. Tunda ta taso shakka ta ta ke, ban san dalili ba.
Ya dan yi shiru cikin jin kunyar abin da zai fada a gaba.
Kodayake laifina ne Malam, ban ja ta a jiki yadda ya kamata ba, na so Habeeba kamar Yayata, amma abin mamaki Hafsat ba ta shiga raina ba, shagwabarta ta yi yawa. It doesnt sound good ko Malam?
Malam Hashim na jin turanci, saboda ya sha gwagwarmaya a rayuwarsa, kuma ya yi alaka da masu ilimin boko. Furtawa a kan harshensa ne ba ya yi, don haka tsaf ya ji abin da Abdulazeez ya ce. Murmushi ya yi, ya ce,
Ga shi kuma an ce a so kare har jelarsa..
Dariya ya yi cikin jin nauyi. Tsorona ta ke ji sosai kamar dodo
Saboda ba ka sakar mata fuska. Inji Malam.
Ya tura hannunsa cikin tarin sumar kansa, wani murmushi ya subuce masa.
Sai kuma Mammah ta zo ta hada aure ba?
Saboda ta yi maganinka.
Dariya ya yi, ya ce. Na yi protest fa kala-kala Malam, ni da kai aminai ne, can we make a very tight secret?
Jinjina kai tsoho Hashim Babbah Jimeta ya yi, ya ce, Fadi da Hausa ko fullata.
Ya zama serious ganin yadda dattijon ma ya dauki seriousnessya dora a kamilalliyar fuskar dattijantakarsa, mai cike da farin gemanya. Na ce za mu iya yin sirri ba tare da kowa ya ji ba? Sai don ka roka min Mammah alfarma da afuwarta?
A shirya nake da yin hakan Abdulazeez.
Malam kowa yana kuskure ko?
Gyada kai Malam ya yi, Har Annabawa da sahabbai. Ban da Khatimul Anbiyae wa Imamul Mursaleena.
Wata nutsuwa Abdulazeez ya ji ta saukar masa, kaunar dattijon ta kara ratsa shi. Ya ji zai iya gaya masa komai tsakaninsa da Hafsat ko da ba zai yi masa uzuri ba. Komai ya farke masa tun daga ranar da Mammah ta bijiro masa da maganar bukatarta na ya auri Hafsat har gabar da suke kai a yanzu. Ya kare zancensa da cewa,
Shi ne kuskure mafi girma da na san na taba yi a rayuwata da girmana Malam. Ban san ya ya SO na hakika yake ba sai a kan Hafsat! Ban san cewa soyayyar aure daban ta ke da soyayyar matan waje ba sai da Mammah ta aura min Hafsat! Ban san wani abu mafi azabtarwa a rayuwata ba sai da ta kwace min Hafsat. Ban san ladabtarwa mafi wahala ba sai raba ni da Hafsah da Mammah ta yi a halin yanzu. Ta hana ni Hafsat tun bayan maida aurenmu da su Baffa suka yi, ko ganinta ba ta bari in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login