Showing 117001 words to 120000 words out of 133887 words

Chapter 40 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

562

zarrah kasancewar shi akwai hasken addinin musulunci a tare da shi da cikar zati da kamala. Wadanda suka samar da wani irin kwarjini a tareda shi. Sanye yake da dogon wando da riga Long-sleeved(Burberry Hartford) ruwan makuba. In ta ce;he is handsome is not enough to convey thehandsomeness, ta san hakan tun tana karama da ta ke ganinsa a gidansu a Jeddah. Ta kuma sha fadin hakan a zuciyarta cewa ya fi duk yan gidan kyau mai daukar hankali, sai dai kuma duk sun fi shi kirki. Har gobe hakan ne a wurinta, sun fi shi saukin kai da dadin muamala, ya fi su Psychological Charisma.
A haka ta mike cikin sanyin jiki, za ta ja jakarta ya sanya hannu ya dauka, suka jera zuwa harabar airport din inda motocin haya suke jiran fasinja. Tun kamin su karasa wani siririn bature ya iso gare su ya karbi trolley din daga hannunsa yana tambayarsu inda za su je. Hannunta ya kama ya rike cikin nasa suka shiga farar taxi din mai matukar lafiya da sabunta. Sai da suka fara tafiya Abdulazeez ya ce da shi.

NewHaven Towers!.


NewHaven TOWERS, gidan bene ne mai kunshe da gidaje masu yawa(apartments)da mafi yawan daliban Yale ke zama, ana kiran daliban Yale University da (Yalies).Apartmentsdin ba iri daya ba ne, ya danganta da yadda ka ke so, single room, onebedroom, two bedrooms ko three bedrooms. Suffofin New Haven TOWERS sun hada da proximity ga jamiar Yale, wuraren siyayya, wuraren cin abinci, libraries, museums, parks da duk wasu ababen dabe kewa da dalibin Yale zai buka. (New Haven Towers) yana nan a Downtown na birnin NewHaven County. Idan aka ce Downtown ana nufin mahada ko cibiya ta kasuwanci, aladu da tarihi, siyasa da Geographical heart. Sau tari downtown�? synoymous ne da (CBD) na kowanne gari, wato Central Business District ko kuma a kira downtown da city-center ya fi saukin fahimta.
Abdulazeez Dakata na zaune a two bedrooms apartment a cikin New Haven Towers�?. Daga (New Haven Towers) a kafa yake takawa zuwa makaranta kullum sabida bauchi nisa (trackable distance) ne. Da taxidin ta sauke su a daidai kofar shiga ginin TOWERS din shi ya dauki jakar ta har handbag dake hannunta suka hau ta lifter. A kofar apartment dinsa ya ciro makulli a aljihunsa ya bude, jakarta ya fara shigarwa sannan ya ba ta hanya. Sai wani dauke kai yake yi ya ki yarda su hada ido. Wucewa ta yi ciki ta samu lallausar kujerar wadataccen falon ta zauna, sannan ta warware lullubin kanta ta shiga karewa falon kallo. Matuka tsarinsa ya ba ta shaawa, komai neatandclassycikin tsari irin na bature, a can gefe study-table ne, manya-manyan littattafan law sun cinye filin tebirin sai inda zaa aje littafi ayi rubutu kadai suka bari. Ga study light mai ban shaawa komai na falon har labulaye brown da milk ne (ruwan kasa da ruwan madara). Akwai talabijin ta jikin bango, amma da alama ba’a kunnata sam. Kujerun wasu yan gujib-gujib na leathermasu tsananin taushi kalar su ruwan madara zallah. Daya daga cikin dakunan barcin guda biyu ya shiga bata kara ganinsa ba.
Ranta ya soma baci da wannan tarba da Abdulazeez ke mata, a kalla ya nuna mata dakin da za ta shiga ta sauke lalurorinta, ko ba zai yi mata magana ba. Idonta ta ji ya kawo ruwa da ta tuna salloli uku ne a kanta, ta taho tun daga Nigeria har America saboda shi, amma daga sannu da zuwa ko sannu ba ta kara samu ba. Tana wannan tunanin ya fito daga dakin da alama wanka ya yi, ya yi sallar magriba da isha a gefe duk tana zaune. Sannan ya sake komawa dakin ya sauya kaya ya fitohar da takalmi a kafarsa alamar fita zai yi. Kallonta ya yi da mamakin har yanzu tana a inda ya barta? Kamar ya wuce ta, sai kuma ya iso gabanta ya tsaya, sanyin turaren wankan sa na dunhillduk ya cika mata hanci.
Dakin ma sai na ce ki shiga za ki shige shi? Ai kuwa kina da aiki kuma zaki kwana anan wajen tunda ba ni na gayyato ki ba. Ya sa kai ya fice abinsa.
Ci gaba da zaman ta yi tana shaqar bacin rai, daga bisani ta ji fitsari na neman kwace mata. Dole ta mike ta suri jakarta ta murda dakin da ke daura da wanda ya fito. A nan ta lura ya ajiye mata trolley da tun shigowarsu ba ta ga inda ta yi ba. Kofa daya ce tal a cikin dan kyakkyawan dakin barcin wadda ta san toilet ce. Can ta nufa da hanzarinta, fitsari na barazanar zubo mata.
Sai da ta yi shi ta samu saida. A gurguje ta daura alwala ta fito ta kintaci gabas ta nada mayafinta ta tada sallah. Sai da ta rama sallolinta a nutse sannan ta kara da shafaI da wutiri ta mike ta soma rage kayan jikinta don ta shiga wanka. Wanka ta yi sosai da ruwa mai dumi don garin akwai sanyi duk da bai yi nisa ba, nisan da zai soma zubar da kankara. Tana wankan ta ji motsinsa a dakin da rufe kofarsa.
Da ta gama wankan sai da ta leko da kanta ta tabbatar ba ya dakin, sannan ta fito gaba-gadi. Ledoji ta gani ya ajiye mata guda biyu wanda ko ba ta bude ba bata raba daya biyun abinci ne. Ga lafiyayyen kamshi na tashi. Kwalliya ta tsaya ta yi sosai da daya daga cikin dinkunan da Mammah ta yi mata na wani material light bluemai santsi, an yi masa doguwar riga fitted gownda aikin duwatsu a gaban rigar sosai, ta murza daurin kai kamar mai shirin zuwa dinnerparty. Ta sa dankunne da sarka deep colour na material din na dutsen (cubic zirconia). Ba ta shafa jambaki ba, sai ta yi amfani da wet-lips mai taushi da kamshi. Har za ta zauna ta ci abincin ta ga gara ta je falo ta ci a can?Na me za ta kunshe kanta a daki don maigidan ba ya maraba da ita? Ai gara ta je ya yi ta ganinta tana harkokinta, in zamanta ya takura masa ya maida ita gaban iyayenta.
Falon ta fito rike da ledojinta, akwai dining table a gefe mai cin kananan kujeru uku, amma ba ta hau ba, tsakiyar rug ta baje ta fiddo kazar Kentucky Fried Chicken da chips da gwangwanin pepsi mai sanyi har guda biyu ta hau cin kayanta hankali kwance.
Zaune yake a study-table yana rubutu, wando ne three quarter a jikinsa da farar singlet ko sanyi ba ya ji. Tun fitowarta yana hankalce da ita ta gefen idanunsa, yana kuma ci gaba da hada assignment dinsa duk a lokaci daya. Ganin alamarin yake kamar a mafarki, yau ga shi ga Hafsat matsayin cikakkun maaurata a KARO NA BIYU! Its indeed a day in history wadda ba zai taba mantawa ba. Godiyarsa ga Ubangijin halitta wanda ya halatta AURE ya kuma halicci SOYAYAYAH ba za ta taba gushewa ba. Sosai yake enjoyingsharetan da yake yi musamman ganinyadda damuwarta a kan hakan ta fito karara. Dazu yana kallonta har kananan hawaye ta yi saboda bai nuna mata dakin kwana ba. A ransa ya ce.
Ashe babu dadi?
Da ta gama cin abincin ta nufi kofar da ta gane kitchen za ta kai ta, murmushi ta yi tana bin madafin da kallo. He still cooks. Ta fadi in a whisper (cikin rada).A shara ta zuba ledoji da kasusuwan kazar da ta ci ta wanke hannunta a sink da sabulun wanke hannu.Kawai sai ta hau gyara kitchen din. Kitchen ne na zamani, amma ya hadu da girkin namiji. Komaiout of order sai dai babu kofi ko kwanon da bai wanke ya killace ba ya rufa farin tawul akansu. Ta bude firji da freezer yana da kayan abinci daidai cikinsa. Da gani ba kullum yake yi ba, sai a (leisure time) dinsa.
Falon ta dawo ta nemi kujera ta zauna ta zuba tagumi. Wannan karon ya gama rubutun ya koma typing dinsa cikin laptop dinsa. Kamar bai san da zaman mutum a falon ba, zuciya ta soma zo wa Hafsat wuya duk kuwa da cewa ba halinta ne fushi ba. Ta ga in ta ce kuka za ta yi ta yi kan wulakancin Abdulazeez ta fadi ba nauyi. Gara ta dinga damunsa yadda zai yi gaggawar maida ita gaban masu kaunarta.
Mikewa ta yi ta isa ga T.V ta hau kokarin jona ta, ko banza ta samu abokin hira kada bakinta ya soma ciwo.
Cikin saa kuwa ta hada ta, ta dauki remote tana neman tashoshi, ta dire a bollywood wato tashar fina-finan India ta saka murya sosai suna ta raye-rayensu. Duk yadda ya kai da son ci gaba da abin da yake yi, hakan ya faskara. Hayaniyar ta dame shi, shi tunda ya zo bai taba jona T.V ba. Tsaki ya yi ya daga murya yadda za ta ji ya ce.
Please ki kashe. Banza ta yi amsa kamar ba ta ji ba. Tasowa ya yi a fusace ya je ya kashe ya koma ya ci gaba. Mikewa ta yi ta je ta sake kunnawa ta dawo ta zauna. Ba ta gama zaman ba ta ganshi a gabanta, cikin bacin rai ya ce.
“Are you here to disturb me (kin zo ne don ki dame ni)?
Hafsat ba ta taso ta ga ana tsiwa a gidansu ba, sannan ba ta cikin halayenta, amma yau ta yadda komai hali yake yi, kuma in ka ce ba za ka iya abu ba, to tabbata condition din bai same ka ba. Domin samun kanta ta yi da mayarwa Abdulazeez martani cikin launin nata bacin ran.
Kana iya mayar da ni inda na fito, tunda zama na takura ne a gare ka!.
Da sauri ya amsa.
Da ni na kawo ki? And I think you have your return tickets in your handbag?(Na yi zaton kina da tikitin komawarki a jakar ki?)�?
Duk dauriyarta sai da hawaye suka silalo ta mike ta nufi daki. Kayanta ta jawo ta soma dannawa da ma ba ta jera su a wardrove ba suna cikin trolley din. Wadanda ta fitar da ta yi wanka ta ke dannawa, ta zuge ta saka hijabin sallarta. Keeeeeeeyyyy! Haka ta janyo jakarta ta tadda shi a falon yana ci gaba da aikinsa. Gabansa ta isa ta tsaya fuskarta babu ko digon hawaye ta goge su tsaf a daki.
Na fito Yaya Azeez, kai ni airport.
Da farko ko dagowa bai yi ba. Shi kansa ya san yanzu kam ba daidai yake typing dinsa ba. Yana yi ne kawai kada tasan ta birkita nutsuwarsa. Dagowa ya yi ya dube ta cikin ido da shanyayyun idanunsa.
Ki ka taho tun daga Nigeria ke kadai sai zuwa Airport ne zai gagare ki???�?
Dauke idanunta ta yi daga kallon cikin idonsa sakamakon wani maganadisu da ke fita daga tsakiyar idonsa, yana shiga natamiraculously. Ba abin da za ta iya karantawa cikinsu a wannan lokacin ban da rashin damuwa da lamarinta. Gefen hijabinta ta kai ta rufe fuskarta ta soma kuka. Tashi ya yi tsam da takardunsa da laptop dinsa ya shige dakin kwanansa.
Sai da ta yi mai isarta sannan ta bai wa kanta hakuri ta koma dakin da kayanta. Ba ta da kudi a hannu, amma tana da credit cards�? har biyu. To amma ta koma gida ta ce wa Mammah me bayan ta gama gargadinta gidanta ba space na yaji? Babu kawo kara, su je su zauna su yi HAKURI da juna, to ko wannan shi ne hakurin da ta ke ikirari?
Haka ta kwana bacin rai da sake-sake. Amma da yake akwai gajiya sosai a tare da ita ba ta san yaushe wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita ba, har sai da ta makara sallar asubahi.
8/13/20, 8:13 PM - Mmn Nasreem: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Tun Hajiya Maryam na kidayar kwanakin dawowar Hafsat tana jiran Abdulazeez ya kira ta ya ce rana kaza za ta taso, har lissafin ya subuce mata. Hafsat dai tunda ta saka kafa kasar America Abdulazeez ya raba ta da wayarta. A cewarsa gabadaya lokacin nasa ne, sai ya yi covering shekarar da ya yi asara har da doriyar watanni biyar a banza,cikin yan satittikan da suka zamo nasa. Sati uku suka cika, aka shiga na hudu, shi ma ya kare aka shiga na biyar Abdulazeez bai da niyyar maido mata Hafsat ta koma makaranta. Ta yi fadan har ta gaji kullum da uzurin da zai bayar.
Uzuri na karshe da ya ba ta shi ne, Hafsat ba ta jin dadi yana tsoron sako ta a jirgi ita kadai, a bari zuwa wata mai kamawa sai ya yi kokari ya kawo ta da kansa, ko kwana biyu ne ya yi ya koma. Dan jim! Mammah ta yi kafin ta ce, Me ya same ta?
Cikin damuwa ya ce, Ni ma ban sani ba, ba dama ta dora girki dai sai ta yi amai, wai ba ta son kamshin abinci. Idan na siyo ma bata ci ba tare da ya dawo ba. Snacks kadai da Pepsi ke zama a cikinta...
Bai karasa ba ya ji Mammah ta kashe wayar, sai da gabansa ya fadi, cike da tsoron ko wata mummunar cutar ce da bai sani ba ya fadi symptoms dinta? Ya juya ya dubi Hafsat din wadda ke kwance a dandaryar marbles kamar wadda tayi wata uku tana jinya, damuwarsa ta kara nunkuwa. Ya ce, Don Allah Hafsat ki yarda mu je asibiti, na yi miki alkawarin ba zan yarda su yi miki allurar ba, kuma ki tashi daga tayal din nan sanyinsa zai cutar da ke.
Kukan da ta kwana tana yi ta ci gaba, da kyar in ba mutuwar da Ismael ya yi mata fata ce ta iso ba, ba tare da ta ga Danta da Abdulazeez ba. Yau kwananta biyar cikin wannan halin ta ki yarda su je asibiti, honeymoon ya guntile ya koma jinya. Ta yi-ta yi ya sa ta a jirgi ta tafi ya ki, shi a wahale ita a wahale, yana cutuwa ta fannin karatunsa sosai, ita kuma ba abin da ta ke tsoro a duniya irin a huda jikinta da allura, ta san yadda ta ke vomiting din nan abu na farko da asibiti za su yi mata shi ne, saka drip. Ya taso daga inda yake rubutu cikin system dinsa ya dago ta daga tiles din ya hada da jikinsa. Sai kawai ta fasa kuka tana fiffizgewa, ita dai ya kyaleta ta fi jin dadin can. Zama ya yi a kasa ya rungume ta kamar shi ma zai yi kukan. To ni ki kwanta a kaina duk yadda ki ke so, kiyi birgima kiyi ta kukan yadda yayi miki, amma ba zan iya kallonki kwance a kasa ba sanyin nan na huda jikin ki.
Zamewa ta yi ta koma inda ya dauko ta ta yi kwanciyarta ta juya masa baya. Abdulazeez ya rafka tagumi ya soma tunanin ko dai ya yi musu yadda suke so ne ita da Mammah ya maida ita gida? Duk da cewa zamanta tare da shi as a patient nauyi ta zame masa, musamman yadda karatunshi ya dau zafi a wannan dan tsakanin, ya fiye masa rashinta cikin gidan sau dubun dubata duk da yanzu babu abin da ta ke tsinana masa sai aikin kwashe amai da gogewa da ya hau kansa. Wanka ma shi yake mata, abinci sai dai ya sayo ita kuma ya sayo mata snacksda pepsi amma wallahi hes enjoying this new life fiye da farkon zamansa a gidan shi kadai.
Sai dare ya samu wayar Mammah, da sauri ya amsa a lokacin yana kan hanyar komawa gida ya fita sayo harpic na wankin toilet dinsu. Muryoyinsu su biyu ya ji ita da Daddy, da alama a handsfree suke magana, Daddy ya ce, Kana jina ko Abdulazeez?
Ya ce, Ina jinka Daddy.
Mammah ta ce, Kai kadai ne?
Ya ce, Eh, a titi ma nake.
Daddy ya ce, Ka je ka kira hospital din su zo su tafi da ita da kansu, kada ma ka tsaya a wajen ta ganka. Idan ta samu karfin jikinta ka sako ta jirgi ba abin da zai faru insha Allah.
Cikin damuwa ya ce, To Daddy.
A tare suka hada baki, Yauwa Abdulazeez Allah ya yi muku albarka.
Ji ya yi damuwarsa ta tafi gabadaya, ya amsa da karsashi, Ameen-ameen Daddy, ameen Mammah.
Hafsat na kwance ya shigo ya ce, Tashi ki shirya za mu yi baki yanzu.
Bata fuska ta yi zai katse mata kwanciyar jin dadinta ta kan marbles wanda ya fi komai dadi a gare ta yanzu. Da ya ga tana bata masa lokaci ya shiga ya dauko mata doguwar abaya da mayafinta kawai ya ciccibo ta ya hau saka mata, sai cin fushi ta ke tana mita.
Wadanne irin baki ne tun ina da lafiyata ba su zo ba sai yanzu da na koma gawa ta ki rami?
Dariya ya yi, ya ce, Ashe kin iya Hausa kike cewa baki iya ba?
Ta zumburo baki ya kama lebunan da yatsunsa biyu, Ki yi a hankali da ni kada na karasa gawar, kin ga ina tausaya miki kwana biyu, to ki lallaba ni in ci gaba da daga miki kafa har ki warware in koma angwancina.
Rufe idonta ta yi da tafukanta, Yaya Azeez ka dinga jin kunyata mana, ni fa kanwarka ce.
Hannayen da ta rufe idon da su ya dauke, ya dube ta cikin ido ya dage girarshi sama ya ce, Really?
Neman wajen boyo ta koma a jikinsa, shi kuma ya ki yarda da hakan, wai lallai ta dube shi cikin ido ta maimaita ita kanwarshi ce ba matarshi ba. Suna wannan diramar suka ji kararrawa. Mayafin ya dauko ya nannada mata a ka ya taimaka mata ta mike, Mu je mu bude musu, ga su nan sun iso.
Har takalami ya dauko mata. Cikin mamaki ta ce, To ka je ka bude musu mana? Na sani ko da maza?
Hannunta ya ja zuwa bakin kofar yana fadin, Aah mata ne.
Mata! Ta fada in exclamation! Tuni ya gano inda ta nufa, kawai ya yi dariya ya bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login