Showing 129001 words to 132000 words out of 133887 words

Chapter 44 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

566

cikin jin dadi, ta maida akalar zancen ga mahaifiyarsu. Adda ki roka min Mariya da Luba, su baiwa yayansu Usman da Haleem auren Halima da Saima, shi Ismael ya zabo wadda ta yi masa tuni, su kuma sun bani zabi da yake sun fi shi son kwanciyar hankalina. Ni kuma na hanga na ga gida ba ta koshi ba baa kai dawa ba. Yayan nan ina da su yammata har ukku, ban da Ismael ya kawo wata Wasila da sai a hada har Khalisa (yar Furera).
Hajiya maryam sai gani ta yi kannen nata sun fashe da kuka. Da fari ta tsorata kafin Mariya ta soma bayani.
Yaya Maryama anya akwai sauran mutane irinki a duniya? Yadda zumuncin zamani ya koma mutum ko ciki daya ku ka fito in shi ba shi da shi kai kana da shi ba ka jawo shi jikinka, neman yadda za ka nesanta kanka da shi ka ke, amma ke yayanmu za ki aura wa yayanki yan gata irin haka?
Ta ci gaba da kuka. Aunty Furera ta ce, Tunda Ismael ya kawo wadda yake so kada ki kara zancen Khalisa, da Saima da Halima da Khalisa duka daya ne. Yaya Maryama mu da yayanmu naki ne ba sai kin roke mu ba. Iyakaci mu gaya wa iyayensu maza saboda hakkin haihuwa. Allah ya tabbatar mana da wannan abin alkhairin. Ya sa zumuncinki shi ne silar shigarki aljannah.
Adda ma albarka ta yi ta sa mata, ta ce, Maryam har gobe ina alfahari da haihuwarki, daya tamkar da goma. Allah ya albarkaci gabanki da bayanki.
Sun tsayar za a fara yin bikin Ismael da Wasila, Usman da Haleema in sun kammala hidimar kasar da suke yi. Zaa jinkirta na Haleem da Saima sai ya gama karatunsa nan da shekara biyu lokacin ita ma ta gama secondary watakila har ta fara tertiary. Hafsat na gefe tana jinsu tana shayar da danta Khalipha ita ma abin ya gamsar da ita. A ranta ta ce Fitinanne ya je ya nemo yar Abuja haka za ta zo ta fitine su kamar yadda ya fitine su.

Suna haka suka ji sallamar Abdulazeez, dare ya yi sosai don sun soma jin barci ma. Aunty Murja ce ta amsa masa Mariya sai harara. Kai kuma lafiya da tsohon daren nan? Kai da ke da tafiya a gabanka da asubahi ya kamata a ce yanzu ka kwanta.
Hafsat na ganin shigowarsa ta yi maza ta cire yaron ta gyara rigarta. Ya dubi Aunty Mariya cikin lallashi.
Wai don kawai na ce bai isa goyo ba ki ka dauki gaba da ni haka?
Ta ce, Au, wato haka ka ce ko? Wallahi sai in fallasa abinda idona ya gane min....
Da sauri ya ce, Mammah ki bata hakuri, kuma ni ba da wani nufi na ce Khalipha bai isa goyo ba, don kada ya samu gocewar kashi ne kasancewar kashinsa bai yi kwari ba.
Mariya ta ce. Ita Addar har a bakwaininta mun goya ta a Saudiyyah, nata kashin ya goce? Balle wannan shekararre a ciki?
Wani irin bata fuska ya yi. Ni Dana bai shekara a ciki ba.
Mammah ta kalle shi, sai da ya ji kunyar da yake jin ba shi da ita yanzu. Ya hau shafa kai ya ce. Wai sallama na zo muku.
Mariya ta ce. Ka zo mana ko ka zo musu?
Dukkanku.
Ta ce To, mun karbi tamu. Allah ya kiyaye hanya. Ke Addah ku je daga falo ku yi sallamar mu muna magana.
Ya kuwa juya ya fita yana ce da Anty Mariya. Dadina da ke zuma ce, ga zaki ga harbi.
Ta ce, Ka ce min kunama ma duk daidai da kai ne.
Ci gaba suka yi da maganganunsu, Murja ta lura Hafsat ba ta da niyyar tashi ta dube ta ta ce Addah ba jiranki yake yi ba ne?
Anty Mariya ta ce, Bar munafuka jira ta ke sai an maimaita don a ce mata saliha, ni yau a tafin hannuna suke.
Da sauri Hafsat ta zura hijab ta sauko daga gadon ta doshi kofa saura kadan su yi dariya amma ban da Mammah, magana suke ita da Adda Hafsatu.
A falo ta tadda shi a zaune da alama a kagare yake da zaman jiran da ta sa shi. Yana ganinta ita daya ta ce. Koma ki dauko shi.
Kamar za ta yi kuka ta ce Ni wallahi ba zan iya dauko shi a gabansu ba.
Mikewa ya yi ya koma dakin, sai ga shi ya dawo da yaron a hannunsa ya zauna yana ta aikin kallonsa. Can ya lura har yanzu a tsaye ta ke kamar a ce Kyat ta arta a na kare. Ya ce, Kin min kerere a ka!.
Ta dosana can nesa da shi ta zaune a dofane. Wani haushi ya kama shi ya zube shanyayyun idanunshi a kanta.
Is that the kind of farewell you choose for Us(wannan ce irin bankwanar da ki ka zabar mana)?
Ya yi maganar ne cikin kwantaccen sauti yana danne bacin ransa.
To wace iri za mu yi? Ita ma ta tambaya cikin irin yanayin da ya yi tasa tambayar.
Au tambaya ta ma ki ke yi?
Ta mirgina kai, Yaya Azeez we are not alone. Muna tsakiyar iyayenmu ne, please ka tuna wannan.
Su suka ce ba za mu yi sallama ba saboda suna nan?
Ba su ce ba,we are to make use of our senses, mu yi abinda ba zaa ga rashin kawaicinmu ba.
Muryarsa a sanyaye ya ce.
Madame! Yanzu ni me na yi na rashin kawaici? Ko dakin da nake ban ce ki je ba, ko soro ban ce ki je ba. Im going thausand miles away, amma ko kusa da ni ba za ki zauna ba. Ba za ki zo mu kalli Khalipha tare ba. Ba za ki gaya min abin da zan ji dadi ba in dinga tuna shi yana debe min kewarku ba. Guduna ki ke yi kamar zan sace ki, in wannan ita ce kunya, toh Allah wadaranta! Wuce ki ba ni waje, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi.
Kasa tafiyar ta yi duk da kafin a yi hakan ita ce abin da ta fi so ta yi, sai hawaye da ta soma sharewa. Bai kara bi ta kanta ba ya ci gaba da kallon Dansa yana sumbatarsa. Daga karshe ya mike ya shiga da shi ciki ya kwantar ya zo ya wuce ta ya fice.
Ji ta ke kamar ta bi bayansa ta bashi hakuri, amma ta san ba za ta iya ba. Hawayenta ta share da gefen hijabinta, sannan ta shiga dakin. Daga ita sai Mammah suka kwana a dakin, tana daga kasa kan carpet. Dukkansu a daya bedroom din suka kwana, Addah Hafsatu da ma (kwana sallah) ce kaman Dadanta.
Washegari gida ya watse kowa ya koma inda ya fito. An nemi wayarta kafin a gano Abuja aka baro ta, Mammah ta ce za ta bayar a kawo mata ko za ta sayi sabuwa? Ta ce a barta, yanzu kam ba ta da bukatarta, in za ta yi kira za ta yi amfani da ta Adda. In za a kira ta a kira Addan ta ba ta.
Ta fadi hakan ne sanin halin kayanta, in ya yi fushi da ita punishment dinta a yi barring dinta zuwa sanda aka ga dama.

******
Alhamdulillah! Yau Abubakar (Khalipha) ya cika kwana arbain a duniya. Sun yada wanka. A washegarin ranar gidajen yan uwa suka wuni. Uncle Ibrahim ya kakkaisu har AKTH gidan Dr. Idris Dakata. Mammah ta ce da Adda Hafsatu Hafsat ta shirya ta wuce Jimeta daga Kano ta yi sati daya sannan ta koma Abuja.
Ibrahim autan Addah shi ya kai su filin jirgi ya yankar musu tickets ita da Zulai mai sa mata ruwan wanka wadda tsohuwar mai aikin gidan Malam Abdullahi Dakata ce. Ita Adda ta sa ta rakata Jimeta don ta taimaka mata da hidimar Khalipha. Sun samu Imamu na jiran saukarsu ya dauke su zuwa Demsawo.
Dangi sun ga Khalipha sun more. Haka ake kwantar da shi a gefen buzun Mallam a kan yar katifarsa mai laushi wai ya je taya shi hira. Su ne har Numan, daga karshe a gidan Abbanta ta kwana biyu. Suka dawo babban gida Daada ta soma yi musu shirin komawa. Gyaran haihuwa ta ke mata bana wasa ba irin na fulanin usli da nono da madara da tukudi da hakukuwansu na gado. Ta kuma yo mata guzurinsu. Ranar Lahdi Abba da kansa ya kai su filin jirgi shida su Modibbo. Aka sa Zulai a jirgin Kano, Hafsat da danta a jirgin AZMAN mai zuwa Abuja.
8/13/20, 8:13 PM - Mmn Nasreem: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
*****
Hafsat ta iso Abuja lafiya ta tadda dalleliyar kankanuwar motarta tana jiranta. Tafiyayya tun daga General Motors din Amurka, sakon Baban Khalipha matsayin gift dinsa na haifa masa Abubakar Sadik. Usman ne mai wannan bayanin ganin ta tsaya tana shafa motar tana tambaya ko Daddy ya yi sabuwar mota ne?
Maimakon ta yi murna, kunya ta yi ta ji ba ta kara zancen motar ba. Ismael ya ce, in ba ta so ta ba shi ya samu ta kai Wasila shopping. Harara ta dalla masa, Mammah na bada baya ta sassauta murya ta ce da shi.
Ashe ba sonta ka ke ba, tunda ba za ka iya saya mata mota ba.
Tafi ya yi har sau uku. Cikin ransa yace haihuwa ta bude idon Addar su. A fili kuma a yace Sannu matar so! Ki bari in samu aiki ki sha kallo, Wasila ta fi karfin mota wallahi, private jet zan gwangwaje ta da shi in ta haihu. Ki ma daina murna wai SO ne ya sa aka siya miki, wallahi arzikin Sadik ki ka ci, da can me ya hana a saya miki aka bar mu muna jigilar kai ki makaranta da dauko ki?.
Ismaeel ya kunnata yadda yake so, ya tashi ya bar gidan yana mata dariyar keta.

Hafsat sai ta koma gefe ta zama yar kallo tana kallon yadda ake soyayyar jika da kaka tsakanin Daddy da Mammah da jikansu Khalipha Abubakar As-siddiq. Ita dai ta san ta haifi Abubakar ne, amma wadannan bayin Allah sun fi ta kaunarsa. Daddy in ya dawo kafin ya ci abinci sai ya ga Khalipha cikin gadonsa a gefensa, yana wutsilniya da kyawawan kafafu da hannayensa cikin koshin lafiya. Mammah kuwa goyo, ko umh ya ce za a jefa shi a baya a daure. Ita da shi tsakaninsu shan nono, ko Jummai ba ta taba musu jika sai dai ta yi wankin kayansa.
A wannan lokacin sai ta ga ba abin da ya kamace ta irin ta ba da kaimi wajen ibadah da gode wa Mahaliccinta. Ya yi mata komai a rayuwa, burinta a yanzu shi ne cikawa da imani da ganin dawowar mijinta kasar haihuwarsa lafiya.
A wannan satin suka koma makaranta, bayan dogon hutu da suka sha na gama zangon farko na shekara ta uku. Sun fara (second semester) na level three Usman ya soma koya mata driving. Dole ta ajiye tsoron don tana so ta koya din ko don ta ragewa Abdulazeez hidima, ta lura da yadda yake takura kansa sosai wajen kaita makaranta da dauko ta sanda suke gidansu. Cikin sati biyu da farawarsu ta soma ganewa, shi kuma zai koma Edo inda yake hidimar kasa. Don haka ya makala mata katuwar L ta ke tuka kanta. A gida ta ke barin Khalipha kasancewar ya fara shan madara. Cikin satin nan suke sa ran dawowar Abdulazeez gida bakidaya.
Daddy ya sa an fidda komai na gidansu an zuba sabo na yayi, hatta fenti an sake. Gida ya koma kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Mammah ta yi wa Daada magana a nema wa Hafsat rikon ya a dangi, wadda ba ta haura shekara goma ba saboda ta taya ta da Khalipha, Daada ta ce gara babba wadda ba sai ta bi su makarantar ba, akwai Lantana kanwarta da ke aure a Girei mijin ya mutu shekarar baya, kuma ba ta taba haihuwa ba, za ta yi mata magana in ta amince za ta koma wajensu. Sosai Hafsat ta ji dadi, don kuwa mammah ta sangartata da rainon Khalipha ba wani iyawa ta yi ba. Ta fara tunanin yadda za su karke in sun koma gidan nasu da wannan kukan daren nasa da goyo kadai ke rufe bakinsa, ita ba ma iyawa ta yi ba, ji ta ke kamar zai fado ko kafarsa ta goce kamar yadda Abdulazeez ya ce.
Saura kwana biyu Abdulazeez ya dawo Lamtana ta iso Abuja.
A washegari Daddy da kansa tare da maidakinsa suka zuba su a mota suka maida su gidansu. Salisu ya biyo su da motarta. Sun dade suna tofe gidan da adduoi. Mammah ta jaddadawa Baba Lamtana yadda za ta dinga kula da Khalipha sannan suka shake musu store da kayan garar Hafsat da aka kawo daga Jimeta. Na freezer ma ba abin da Mammah ba ta ajiye musu ba. Danfulani dan amana, har yanzu shi ke kula da gidan bai je koina ba don Abdulazeez ba ya wasa da hakkinsa.
Daga Mammah har Daddy sun kasa sakin Abubakar su tafi, shi kuma kamar ya gane sai kuka yake yi. Sai da Mammah ta goya shi ta yi ta jijjigawa ya yi bacci, sannan ta je ta shimfidar da shi a gadonsa suka bar gidan kamar kar su tafi. Ina ruwan abin cikin kwai ya fi kwai dadi!. Haka Lamtana ta ce bayan fitarsu.
Hafsat ta ce. Ai sauri zan yi in yaye shi in kai musu abinsu.

******
A zaton Hafsat da aka ce washageri Abdulazeez zai dawo ta sa a ranta irin da yamma ko da rana ko da daddare. Tunda dai ita ba waya suke yi ba. Karfe biyar da rabi na Asubahi ta idar da sallah, tana so ta yi lazimi amma wani irin mayataccen barci ke cin idanunta, kasancewar Khalipha bai barta ta runtsa ba daren jiya saboda kuka, ba ya bude jiniyarsa sai tsakiyar dare, Lamtana ta zo ta buga mata kofa don ta taimaka mata ta ce ta je ta kwanta ba komai za ta iya da shi. Goya shi ta yi, ta yi ta yawo da shi a dakin ba dama ta zauna. Ta ba shi ruwa, ta ba shi nono duk a banza kuma ta san lafiyarshi kalau. Haka yake yi a gidan Mammah ba ta san yana yi ba baccinta ta ke shaka komai a kan Mammah yake karewa. Sai jiya ta san yaya Mammah ke shan wannan hidima. Ba ta samu ya yi bacci ba sai goshin asubahi, ita ma da ta idar da sallar a nan kan dardumar ta bingire tana bacci. Wani bacci mai tsananin nauyi da ta dade rabonta da irinsa.
Har Abdulazeez ya shigo ya shiga toilet dinta ya yi alwala ya fito, ya yi sallah a gefenta ba ta sani ba. Ya dade yana addua yana gode wa Allah da ya dawo da shi cikin iyalinsa lafiya. Zuwa ya yi ya ciro Khalipha daga gadonsa ya maida shi tsakiyar gadonta. A ransa yana fadin.This is punishment. Ta jefa yaro a gado shikadai tana can tana bacci ba ta san me yake ciki ba. Kamar ya tashe ta sai ya lura tana jin dadin baccinta.
A hankali ya dauke ta ya maida ita gadon ya sanya Khalipha a tsakiyarsu ya ja quilt din ya rufe su iya wuya. Shi ma da gajiyar zaman jirgi ya dawo, don haka bai dade yana kallonsu admiringlyba shi ma ya yi bacci.
Yunwa ce ta tashe ta, kasancewar ba ta ci abincin dare ba ta yi baccin. Ta sha mamaki da ta ji ta a kan gadonta, ba ta fita daga wannan mamakin ba ta yi arba da danta a gefenta. Kusa da shi mahaifinsa ne Barrister Abdulazeez Hamzah Attikou, yana ta barcinsa freely irin baccin warware gajiyar zaman jirgi. Wani dakace (INAMA A CE!) Da ta taba yi a can a baya... Ita da Abdulazeez matsayin maaurata na din-din-din da BABY (in between) yana kicking kwance a tsakaninsu. Yau Allah ya cika mata wannan dakace da ba ta taba mafarkin zamansa reality ba.
Ci gaba ta yi da kwanciya a yadda take a kan pillow tana kallonsu; her heartSWELLING with love and pride (zuciyarta na kumburi da soyayyah da alfahari). Ba ta jin in za su shekara a haka za ta gajiya da kallonsu. Wani naushi da Khalipha ya sa kafa ya kirba wa ubanshi ba shiri ya soma bude idonshi a hankali. A kanta ya sauke su, suka yi wa juna kuriiii da ido. Babu wanka, ko kwalliya,ko wani special artificial abu a tare da ita sai kayan barci masu tsananin taushi, amma a haka ta kawatu a zuciya da idanunsa fiye da duk matan duniya da ya taba cin karo da su a rayuwarsa.
Sannu da zuwa!. Ta fada cikin nutsuwa da farin cikin da ya gaza boyuwa a cikin muryarta.
He is kicking me.
Ya yi complaining.Ba tareda ya amsa sannu da zuwan nata ba.
Me ya sa ka rabo shi da gadonsa toh?
Because I want him to do so. (Saboda ina son shi da yin hakan).
Murmushi ta yi.Then why are you complaining? (Me yasa kuma kake korafi?)
Because Im appreciating (Sabida ina jin dadin hakan). Ya ba ta amsa.
To Allah ya raya maka shi rayuwa mai tsayi da albarka.
Ke ban da ke? Ke ba kya son shi ko Hafsat?
Murmushi ta yi. Ta ya ya zan ki son dan Abdulazeez dina?
Lumshe ido ya yi kalmar karshe ta yi masa dadi.
Ban ga alamar hakan ko daya daga gare ki ba. In fact a gabana sai an roke ki ki yi breast-feeding dinshi. Wannan abu ya dade yana mun ciwo.
Ka yi hakuri, lokacin ban saba ba ne, ina jin zafi sosai.
To ba za ki daure saboda shi ba? Na san dai duk zafin bai kai na labour ba, horon yunwa ga Dana Hafsah!
Girgiza kai ta yi, ta san Abdulazeez da mita akan hakkin sa. Ta dade da sawa a ranta zancen nan bai wuce ba idan ya tuna sai ya dawo dashi sabo. Ka bar abin da ya wuce ya wuce don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login