Showing 54001 words to 57000 words out of 133887 words
ya sonta! Ba ya bukatar hada rayuwa da ita, dole ita da Mammah su dau dangana su hakurkurtar da zukantansu. Allah ya sa hakan ya zama alkhairi ga rayuwar kowannensu. Ta sa gefen mayafinta a fakaice ta share hawayenta.
Mammah na tsaye aka fito da kayanta na boot ta kasa jiranta ta karaso inda ta ke ta tako ta iso jikin motar ta bude mata kofa. Salisu ya roke ta ta bar masa kayan zai shiga da su. Ta kama hannun Hafsat abinda ta lura da shi jikin Hafsat a matukar sanyaye yake tamkar wadda aka yiwa duka. Idanunta sun kode da alamun ta jima bata sanya musu kwalli ba. Kai in ba ta yi kuskure ba, za ta iya cewa Hafsat ta rame. Ta dai bar komai a cikinta Hafsat din ta samu ta huta.
Dakinta na yammatanci aka shigar da komai nata, a can ta yi wanka ta yi sallah kuma har can Baba Azumi ta kai mata abincinta ba su ce ta zo ta ci a dining ba kamar yadda yake a aladar gidan duk don ta samu nutsuwa.
Ta nemi wata doguwar riga mara nauyi cikin kayanta ta sanya, ta zauna da zummar ta ci abincin, amma duk yadda ta kai da kokarin ganin ta ci din abin ya faskara. Zuciyarta ta yi nisa wajen tunanin yadda za ta nunawa Mammah takardar sakinta! Haka ta saka abincin a gabanta tana kallo kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta. Sau biyu Mammah na shigowa jin shirun nata ya yi yawa tana ganinta cikin wannan halin. Azumi ma shigowarta biyu, har suka fita ba ta san sun shigo ba balle fitarsu.
Mammah dakinta ta koma ta yi shiru, daga bisani ta yi kiran Baba Azumi, ta shigo ta zauna gefen uwargijiyarta a kan center carpet, Mammah na gefen gadonta.
Ba ki fahimci Adda na cikin damuwa ba?
Azumi ta gyara zama ta ce, Ni kuwa na fahimci hakan. Har magana na yi mata sau uku ba ta san ina yi ba.
To a ganinki me ke damunta? Ko a da Hafsat da ta san ba ta da kowa sai mu ba ta sanya kanta cikin damuwa ba sai yanzu?
Ba kya tunanin tafiyar mijin ce? Inji Baba Azumi.
Ba ta magana da shi a waya. Ya gaya min rabon da ya yi magana da ita tun a Jimeta. Ta kashe wayarta kwata-kwata tsayin kwanakin nan data yi acan. Da na yi mata fadan kashe wayar cewa ta yi ba ta samun zama, kuma ta je kauye. Shin a wannan zamanin duk inda ka je za ka kasa yin muamala da waya? Balle ka kasa magana da mijin aurenka tsayin sati biyu?
Duk sai suka yi shiru. Daga bisani Azumi ta ce
Ina tunanin matsala ce suka samu a tsakaninsu.
Mammah ta runtse ido kadan ba ta ce komai ba, amma ta yarda da abin da ta ce din.
Ki zuba musu ido Maman Haleem, kada ki tambaya, kada ki bi baasi. Tsakanin mace da miji sai Allah. Sanda za su shirya kansu ba za ki sani ba.
Zuciyar Hajiya Maryam babu dadi, ta ce, Haka ne. Amma can a karkashin zuciyarta tana jin ba dadi, sanin cewa auren Abdulazeez da Suhaana ba normal auren so ba ne. Sai dai ya taho da nasara fiye da yadda ta tsammatar masa. Tana tsoron duk wata matsala da ka iya tasowa a cikinsa.
“Ya Rabbi Sallim!
Ta furta a fili bayan fitar Azumi daga dakinta.
******
Kwanan Hafsat biyu kenan da dawowa daga Jimeta. Mammah na lure da ita, ba abin da ya canza cikin yanayin da ta dawo da shi, sannan ko sau daya ba ta ga ta jona wayarta a caji ba balle ta kunna. Washegarin ranar suka koma makaranta. Hafsat ta sani, amma ko alama ba ta yi wa Mammah zancen ba. Ji ta yi karatun kansa ya fita a ranta, duk wani buri da ta ci masa ya zagwanye. Ashe karatu ba shi ne farin cikin rayuwa ba? Ashe akwai abin da yamace ta fi bukata a rayuwarta fiye da karatun boko? Ashe ba abin da ya fi muni ga rayuwar diya mace fiye da sakin da ada ta ke ganin ba komai ba ne? Ashe tsakanin zuciyarta da Abdulazeez soyayyah ce kuma kauna ce mai tsananin da zuciyarta ta kasa karbar rabuwa da shi da sauki???
Duka a bandaki (toilet) ta ke wannan tunanin, ta shiga da zummar wanka, amma sai ta bige da zama a kan (soak-away) ta shiga shesshekar kuka, kukan da a baya ba ta yi ba tun ganin takardar sakinta. Koyaushe cikin mutane ta ke a Jimeta ko gaban kakanninta, suna yi mata hirarrakin uwarta da ke debe mata kaso 80% na tunanin Abdulazeez da karewar KWANGILARsu. Yanzu ne komai ya rufto mata take jin kanta cikin wata irin kewa mara misaltuwa. Tamkar ta rasa komai na jin dadin duniya, tamkar ta rasa komai data taba mallaka a rayuwarta.Zamanta cikin gidansu da kasancewarta kusa da wadda ta fi kowa kusanci da shi a duniya ya maido komai sabo kuma danye a zuciyarta, ya maido mata komai baya na rayuwarda ta yi da shi ta shekara da watanni.Yadda shekarar ta kasance dalla-dalla a kan tafin hannunta....... Daga rayuwar DUHU zuwa rayuwa mai HASKE kafin ta karkare ta koma DUHU dudum a halin yanzu kenan da wannan rayuwar taduhu da haske ta kare bakidaya. Sai dai duk ta inda zuciyarta ta karkata don baiwa Abdulazeez laifi Hafsat ta ki karba, zuciyar mai so da kaunar Abdulazeez kare shi ta ke yi. A bisa dalili da dama da hujjojinta kwarara!
Muhimmi cikin hujjojinta shine;Abdulazeez bai taba yaudararta da cewa za su dore da rayuwar aurensu ba! Bai taba yaudararta da kalmar SO ba. Zuciyarta ce ta zarme zuwa ga son abinda yafi karfinta.... ta zamo out of her controlta jefa ta cikin matsananciyar soyayya da kaunar Abdulazeez din data ke da tabbacin baya son ta. Ba ta yarda da hakan ba sai yau da suka rabu, auren kwangilar ya kare! A yau ta yarda cewa ta dauki lokaci mai tsawo cikin soyayyar Abdulazeez Dakata ba tare da saninta ba. Wani kwantaccen so mai bin jiki da jijiya. Ba ta fahimci hakan ba sai a kurarren lokaci, lokacin da ya zamo haramiyarta...!!!
Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta dinga kuka wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta.
Shigowar Hajiya Maryam na uku kenan dakin tana komawa ta fita da sauri, saboda zuciyarta da ta kasa jure sauraron irin kukan da Hafsat din ke yi. Ta koma dakinta jikinta har rawa yake yi. Babu wanda zai tada hankalin Hafsat, ya jefa ta cikin wannan halin in ba mijinta Abdulazeez ba, tunda wa ta ke da shi bayan iyayenta da su in ba shi ba? Babu wanda zai bata mata rai a Jimeta! Zuciyarta na son daukar waya ta kira shi, wata zuciyar na hana ta.So ta ke ta ce da shi da ka bata min ran marainiyar Allah Addah yar amana ta, gara ni ka bata nawa ran. Ta tuna shawarar da Baba Azumi ta bata; Kada ta shiga, kada tatambaya, kada ta bi baasi. Baba Azumi ba yar aiki ce kawai agareta ba yanzu, uwa ce a gareta, kuma wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Bataso ta yarda da kaso mafi rinjaye na zuciyarta da ke cewa, Abdulazeez ba ya son Hafsat har yanzu....... damuwar Hafsat kenan.
Shigowar Daddy dakin nata yana tambayar wasu mukullansa ya sa ta farfadowa daga zazzafan tunanin da ta fada, wanda zuwa yanzu ya fara tafarfasa zuciyarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi idanunta jazir. Da sauri Dr. Hamza ya karasa shigowa dakin, Lafiya Maryama? Me ya faru? Mutuwa aka yi? Ya kama dukkan hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Ganin yadda hankalinsa ya tashi da ganin yanayinta ya sa ta nemo wa kanta murmushi wanda bai wuce iya fatar bakinta ba.
Bai kamata ta ce masa komai ba, tunda itama ba ta san me ke faruwa din ba. Ga shi Baba Azumi ta ce ta ba su lokaci, watakila da ya dawo sun koma gidansu komai zai wuce, ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ita da ta yi auren soyayya da Prof. Hamza wane irin bacin rai ne bai jefa ta a ciki ba, kuma ta jure sun zauna a haka har aka zo gejin da bacin ran nata shi ne abu na karshe da yake guje mawa?
Hafsat ce ba ta jin dadi. Ta fada a hankali yadda zai kwantar da hankalinsa.
Ya ce, Ai sai ku je asibiti a duba ta, ba ki zauna kina tagumi da jan ido ba.
Ya dauki mukullayensa a kan lokar gadonta, ya juya. Har ya kai bakin kofa ya kama marikin kofar sai ya juyo da murmushi a kan fuskarsa.
Ko amarya zan samu ne kwanan nan aka gaya min indirectly?
Duk yanayin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, a zuciyarta ta ce, Ina ma hakan ne!
Sai dai a matsayinta na mace, kuma babba ba ta ga wani alamu na juna biyu a tare da Hafsan ba. Jin ba ta ce komai ba ya lura kuma ba ta son magana sai ya fita, zuciyarsa na gaya masa kamar ta sakaya masa wani abu, amma ko ma mene ne in ta yi wari da bakinta za ta fada mishi.
Haka suka zauna a gidan su uku tsayin sati biyun, ba sa ummm ba sa umm-umm. Baba Azumi ce kadai ke yi musu hira. Ita ma idan tayi-tayi ta rasa mai tayata sai ta yi shiru. Ana i-gobe Abdulazeez da su Ismael za su dawo Hajiya Maryam ta ce wa Hafsat ta shirya ta koma gidanta, su tafi da Baba Azumi don ta taya ta su yi tiding gidan ta kwana, za ta turo Salisu ya dauke ta in Abdulazeez ya sauka a Abuja.
Hajiya Maryam na ganin yadda Hafsat ta kidime ta rikice, ta gigice, a karshe ma kasa zaman wurin ta yi ganin yadda ita da Azumi suka zubo mata ido. Mikewa ta yi ta nufi daki, kafin ta isa da gudu-gudu ta karasa ta shige, kuka ya kufce mata, karshen tika-tika-tik! Me kuma za ta ce wa uwar tasu? Za ta ci gaba da boye sakin ne kuma? A dauke ta a maida ita gidanta bayan kuma auren babu shi, ya mutu?
Tambayoyin da ta ke ta jero wa kanta kenan ta rasa amsar ko daya.
Bayan tashinta da kulewarta Hajiya Maryam da Baba Azumi suka bi bayanta da kallo sannan suka dubi juna, an rasa mai magana a cikinsu.
******
ABDULAZEEZ DAKATA
Shi kadai ya san yadda rayuwar ta kasance masa a tsayin sati biyun nan da Hafsat tayi a Jimeta. Zai iya kiransu kwana goma sha hudu mafiya tsayi da fadi a renakun rayuwarsa. Abin da ya sani kawai shi ne; ba ya iya zaman gidan, barci kadai ke kawo shi cikinsa. Da safe zai yi wanka ya tafi office babu tunanin karin kumallo, sai ya je can dinhanjin cikinsa ya hana shi sukuni yake samu ya sha coffee ya cika wa kansa aiki duk don ya hana kansa tunanin komai. Haka zai zauna babu ko tunanin abinci sai lodawa kansa aiki, sallah kadai ke tayar da shi.Ba shi zai baro office ba sai karfe shidda na yamma. Daga nan kuma kai tsaye gidansu zai wuce, a can zai yi sallar maghriba da isha tare da Daddy, su ci abinci tare har Mammah ya zauna ya ki tashi har sai Daddy ya ce da shi dare ya yi, watarana har ya tsokane shi ko zai koma Jimeta ne a yi sati biyun tare da shi?
Daga Daddy har Hajiya Maryam sun fahimci yana cikin damuwa wadda cikinsu babu wanda tunaninsa bai ce da shi ta rashin maidakinsa a kusa ba ce. Don haka babu wanda ya bashi hankalinsa. Babu daren da zai zo ya wuce a tsayin kwanaki goma sha hudun nan da bai gwada kiran wayar Hafsat ba sama da sau hamsin a rana, amsar dai a kullum iri daya ce; wayar a kashe ta ke. Ya kasa amsa wayar Muazatu ko guda daya daga ranar da ya saki Hafsat! Abinda shi kansa bai san dalili ba; wadda ke can gidan su a birnin Lagos hakan ya dugunzuma nata hankalin. A ganinta yanzu lokacin farin cikinsu ne, lokacin cikar burinsu, me yake nufi da kin amsa wayarta idan shi ya kasa kiranta?
Kwanansa bakwai da baro Hafsat a Jimeta ya yanke wa zuciyarsa komawa. Wannan ne kadai mafita a gare shi, ya koma ya samu Hafsat ya gyara dingimemen kuskurensa ko rayuwarshi ta koma daidai, zai lallaba ta ya karbe takardar... ya yayyagata kafin kowa ya gani, zai maida ita dakinta kafin kowa ya ji. Ya godewa Allah ya yi sakin da addini ke so zuciya bata kaishi ta baro bakidaya ba! Idan ya samu ya dawo da Hafsat sai kuma ya san ya zai yi da Muazatu. A wannan gejin yana jin zai iya karya alkadarinsa ya zauna da su su biyun. Ya fahimci abin da yake kin fahimta da gangan; Hafsat ba ta shigo rayuwarsa don ta fita ba, ba ta shigo zuciyarsa don ta yi KWANGILA ta wuce ba... Ba mata irinta ne ake aura a saki a lokacin da ake so ba. Ba mata irinta ake saki don a samo wasu ba. Ba mata irinta ke barin gidan auren su na farko zuwa wani, ba tareda kwakkwaran dalili ba. Irin Hafsat saidai wata kaddararta daban mai karfi ta raba su da gidansu na farko (mutuwa) amma ba common saki irin wannan ba. Ya yarda ya amince a cikin mata akwai virtuousones;Their prices is per above rubies! Baa amfani da su don cimma wata manufa sai don biyan bukatar rai kadai! Ya yarda ya amince zuciyarsa SOYAYYAh ta ke wa Hafsat ba irin wadda ta ke yi wa Muazatu ba... Idan abinda yake ji a kan Hafsat shi ne soyayyah zai so wani masanin ilmin zuciya ya taimaka mishi, ya fada mishi wanda yake ji a kan Muazatu kuma mene ne shi???
Ya tsaya, ya nutsu, ya kintata, ya yi estimating, sai ya samu cewa the feeling is totally different....Ba soyayyah kadai yake yi wa Hafsat-Suhaanah ba, har da wata boyayyar kauna yar usuli mai yawan kintace. Yana begen sake ganinta ko da sau daya ne, yana kewarta cikin gidansa... Har ila yau yana nadamar yin AUREN KWANGILA da ita... yana nadamar yin amfani da halitta mafi soyuwa a zuciyar mahaifiyarsa don son cimma wata manufa. Watakila Ubangiji ya canza zuciyarsa a kanta ne don Ya ganar da shi kuskurensa.
Duk ilmin addinin da yake da shi bai yi amfani da shi ba, ya sa kafa ya take saninsa saboda soyayyar Muazatu data rufe masa idanu. Sanin kansa ne babu wani aure na kwangila a cikin addini, kai duk wani aure da za a kafa shi a kan wasu sharudda ko a deba masa waadi bai inganta ba a addinin musulunci. Duk wani aure da za a yi shi ba ka kusanci iyalinka ba har tsayin watanni ukku ba tare da dalili ba, shi ma ba cikakken aure ba ne! Ya zauna ya cutar da Hafsat watanni goma sha biyar bai taba sauke nauyin auratayya da Allah ya dora a wuyansa ba ba tare da hujja wadda addini ne ya tsara ta ba. Babu mamaki don Allah ya hukunta shi da soyayyar Hafsat da ta hana shi nutsuwa a lokacin da ya haramtawa kansa ita. Ta tsayar da duk wasu daily activities na rayuwar cikakken mutum a gare shi. A tsayin kwanakin nan bakidaya a dakin Hafsat yake kwana a kan gadonta. Barci gwanin iya sata kadai shi ke sace shi, shi ma duk inda assalatun fari ta ke zai bar idanunshi. Zuciyarshi ta dora daga inda ta tsaya na tunanin hanyar da zai bi ya maido Hafsat cikin rayuwarsa ba tare da kowa ya ji ya gani ba. Babu mafita ban da komawa ya cimmata a Jimeta.
Bai kara fahimtar cewa ya fita daga saiti ba, sai da ESQ Ahmad Kutama ya kawo wasu manyan files ya ajiye a gabansa. Da mamaki yake dubansa kafin ya janyo kujera ya zauna a gabansa.
“Check these files for me properly,please.
Janyo su ya yi gabansa yana dubawa, shi ya rubuta clues na shariar da za su yi sati uku masu zuwa, amma me? Clues din ba su da alaka da wannan shariar na wadda za su yi kafin waccan ce. Lumshe idonsa ya yi ya bude a hankali, Im so sorry. Kawai ya iya cewa.
Ahmad ya bi shi da kallon tsaf! Ga shi dai ya yi shigarsa tsaf cikin suit kalar grey da ratsin fari ta ciki kamar yadda ya saba,but its obvious that he is definitely upset... alamu ma sun nuna kwana biyun nan he didnt shave his face, sannan gashin kan ya cukurkude alamar ba ya samun extra kulawar da yake samu a baya duk da shi ba maabocin yawan askin bane amma kula yake da sumar sa sosai. Ya san yana da aure don har da shi aka raka shi dakin matarsa balle ya ce rikicin soyayyah ya fada. To me aure ba ya iya fadawa soyayya for the second time? Ahmad ya tambayi kansa.
Bayan wannan shi dai ya san Abdulazeez bai da matsala, dan gata ne na karshe, gatan da ya sa duk ya riga su aure. Saboda Babansa ne ya gina masa gida. Su kuwa sai haya suka kama cikin Abuja. Shi nasa wata biyu kenan, na Abdallah wata hudu. To ko kuma ta gidan ce ta ke birkita shi haka? Duk zai iya yiwuwa. Ya san Abdulazeez da shegen zurfin ciki a kan abin da ya shafi matarsa. Bai taba zama yayi hirarta da wani a cikin su ba. Ko suna hirar yammatansu kafin suyi aure shi baya magana. Haka bayan sunyi aure suna zancen amaren nasu a gabansa irin sun makarar dasu ko makamancin haka ko kai baya dagawa balle ya tofa. Amma duk da haka ya samu kansa da son taimaka masa koda da shawara ne don bai