Showing 48001 words to 51000 words out of 133887 words

Chapter 17 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

553

fizgar zuciyarta irin wanda ba ta taba ji a kan kowa ba. Ci gaba ta yi da kallonsa, wannan feeling na kara cika kowanne sako na zuciyarta. Shin ko wannan shi ne abin da kowanne Da ya ke ji a kan mahaifansa, su ma mahaifan suke ji a kan yayansu wanda Daddy ya kasa ji a kanta a baya???
Mammah ta lura da jikin Hafsat rawa yake yi, kuma ta bude idonta daga lullubin dolen da ta saka ta tana ta kallon Dr. Bashar Mai-jamaa Numan. Jawo ta jikinta ta yi, ta kwantar da kanta a cinyoyinta. Hafsat ta rufe idanunta hawayen farin ciki suka shiga kwaranyo mata. Farfesa Bashar ya ci gaba da bada labarinsa bayan ya tsane hawayen idanunsa da hannun babbar rigarsa.
Cuta ta karshe Hajara ta yi min, ba ni kadai ba, har iyayen da suka tsugunna suka haifi Habiba. Tunda duk son da nake mata ban kai su ba. A lokacin na damka ta hannun iyayenta na sake ta saki uku. Ni da su, (Malam Babba da Dada) da sauran yan uwanta na ciki daya da yayan da ta haifa muka rungumi kaddara. Domin a shekarar farko in Malam ya yi istikhara yana gaya mana ya ganta lafiya cikin kwanciyar hankali a duk inda ta ke. Amma a shekaru na gaba sai ya ce ba ya ganin komai a kanta sai duhu. Allah ya rufe masa alamarinta.
Yaya Tijjani babban Yayansu, kasancewar maaikacin gidan talabijin ne na jihar Yola, ya yi hobbasa iri-iri wajen neman Habiba a kafafen yada labarai har yau ba amo ba labari, babu ko wanda ya ce ya taba ganinta sai a wannan shekarar da dan wajenku, abokin Sagir ya zo daurin auren Modibbo ya ce mana yana da labarinta, ya san inda ta ke, zai dawo mana da cikakken bayani a kanta bayan watanni hudu.
Ya gaya musu cewa, shekaru takwas ya kwashe bai kara aure ba, kasancewar matan bakidaya tsoro suke ba shi, kuma yana sanya ran zai ga Habiba komai daren dadewa bai taba fidda rai ba.
Kuka Hafsat ta fara yi cikin mayafinta lokacin da Dr. Bashar ya dasa ayah. Mammah ma kukan ne ya ci karfinta. Da fari tausayin iyayen Habiba ta ke ji, amma yanzu Dr. Bashar yafi bata tausayi. Da ace Habiba ta yi tsawon rai zai fi kowa bukatarta a yanzu ko mata ukku gare shi. A hankali ta ke jijjiga Hafsat da ke kuka a kan cinyarta. Daddy da Abdulazeez hankalinsu na kan Mammah da Addah wadanda kukansu ya soma fitowa fili har aka soma maida hankali gare su duk da dai fuskar Hafsat na rufe cikin mayafinta. Wani iri Abdulazeez ke ji a ransa da kukan Hafsat, yadda shi kansa ba zai iya fassarawa ba. Mammah ta share hawayenta cikin murya mai sanyi ta soma ba su labari.
Tun daga sanda aminiyarta Hajiya Halima matar Controller ta kawo mata Habiba da kuma bayanin da Haliman ta yi mata a kan Habiban na yadda ta same ta, zuwa yi mata fasfo da visa da tafiyarsu Jeddah, yadda ta gane Habiba na da ciki bayan tsautsayi ya sameta sun je asibitihaihuwar gaggawa ta sameta. A nan ne ta dago ido ta dubi ahalin Habiba sun zubo mata na mujiya caaa! Kamar idanunsu sa fado.
Russunar da kwayar idonta ta yi kasa, muryarta cike da alhini ta ce.
Im sorry, ina mai baku hakurin sanar da ku cewa, Habibah ta rasu a wurin haihuwar diyarta Hafsat-Suhaanah...!!!
Ta yaye lullubin kan Hafsat ta ce,
Je ki ga mahaifinki Hafsat!.
Hawaye ne suke bulbula daga idanunsu bakidaya, in ka dauke yara-yaran matasa da aka haifa a bayan batan Habiban. Hatta Yaya Tijjani kuka yake yi, Fusam, Saade mai binta da Haladu, sun ko kasa kallon Hafsat din.
Fuskar Dr. Bashar cikin tafukansa yana ta gunjin kuka, amma hakan bai hana shi dagowa ya mikowa Hafsat hannu ba. Wadda ita ma nata kukan ya tsananta, kanta ko kallabi babu. Wani ignition Abdulazeez ya samu zuciyarsa na yi da kallon Hafsat cikin wannan hali. Shi ba abun ya je ya mikar da ita tsaye ya rungume ta ba, komai ya kare a tsakaninsu. Ya riga ya yanke hukuncin da tun baa je koina ba ya soma shiga halin haulai akan ingancinsa.
Kasa jure ganin wannan abin tausayin ya yi, ya tashi ya fice zuciyarsa na wani irin zabalbala. Ga shi ya riga ya aiwatar da komai, tun a Abuja ya sanyawa Hafsat takardar sakin cikin handbag dinta a lokacin da ya sanyata ta koma daki wai ta canzo mayafi, tsabar shikansa yana jin kunyar bata takardar sakin a hannunta. Saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai iya fuskantarta ido cikin ido ya ba ta wannan takardar sakin ba, duk da abu ne da ta kwana da sanin kasancewarsa, to amma akwai KARAMCI da KYAUTATAWA a cikin zamansu, wanda ba zai taba gogewa daga tarihin rayuwarsa ba, kuma ba zai gushe yana kallon Hafsatu da su ba. Da sassarfa ya isa ga motarsu ya bude ya shige ya maida kofar ya rufe, ya kwantar da kai a kan sitiyarin ya kai hannu ya dafe kirjinsa daidai saitin da ke azabtar da shi. ME NA AIKATA??? Yake fadi a fili.

*****
Da rarrafe Hafsat ta rarrafa ta isa ga Dr. Bashar kafin ta karaso ya taso ya cimmata, ya sanya ta tsakiyar hannayensa ya rungume. Yanayin da Hafsat ta samu kanta a wannan lokacin ba ta taba tsintar kanta a kololuwar dadin irinsa ba. A tsaye suke tsakiyar taron nan kusan minti goma kafin Dada ta mike ta rabo ta da uban ta kamo hannunta.
War hadosabajoam Hafsatu (Zo nan kawata Hafsatu). In ji tsohuwa Dada.
“Sobirawo na malla launirawo? (Kawalli ce ko kishiya ce?) Daada ta sake fadi tana hawaye.
Duk da Hafsat ba ta san me ta ke fadi ba ta isa gare ta, ta rungume ta don ta fahimci ita ce mahaifiya ga Habiban, wato Kaka a gare ta.
Malam Hashim Babbah ya share nasa hawayen ya shiga baiwa kowa baki. Ya ce, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhadulillahi har sau uku. Sannan ya cigaba da cewa Allah bai yi lamunin za mu sake ganawa da Habiba ba, amma bai barmu da kewarta mai yawa ba tunda ta ajiye Hafsu. Zuciyoyinmu yanzu sun samu nutsuwa daga taraddadin da kullum suke ciki.
Baiwar Allah!Ya dubi Hajiya Maryam.
Alkhairinki ya bi ki har yaya da jikokinki. Ba mu da kalaman da za mu furta godiya a gare ki. Muna rokon Ubangiji Ya fi mu godewa. Ba sai kin fadi irin rikon da ki ka yi wa yarinyar nan ba, ido ba mudu ba amma ya san kima, kowa ya dube ta ya san ta fi karfin komai na rayuwa. Allah ya zama gatanku ke da mijinki da zuriarku bakidaya.
Kowa ya amsa da, Amin-amin.
Hafsatu matso kusa da ni, ko ba kya aure da tsoho? Dube ni sosai, gemuna bai gama kodewa ba.
Murmushi ta yi ta matsa kusa da shi. Ya kama hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Adda Hafsatu babar Hajiya maryam ta ce da shi.
Anya takwara tana auren nan da kai Malam? Dubi sardidin mijinta a gefe, gara ka rike Dadanka kada ka yi ba-wan-ba-kanin.
Ido ya koma ga inda Adda Hafsatu ta nuna, kowa na son ganin wane ne mijin dalleliyar baturiya Hafsat? Wayam! Babu kowa, babu wanda ya ankara da fitarsa saboda a lokacin sun rude da koke-koke.
Modibbo ya fiddo ido cikin mamaki ya tambayi Adda Hafsatu, Ba dai Barrister abokin Kawu Sagir ba?
Shi kuwa. Jiya aurensu shekara guda da watanni uku. Aunty Luba ta ba da amsa.
Kuma Da yake a gare su, shi ne babba dansu. Aunty Mariya ta kara bayani.
Allahu akbar! Allahu Akbar!! Abinda Malam Babba da iyalinsa ke fadi kenan cikin jinjina halin GIRMA da karamci irin na Hajiya Maryam da mijinta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daddy ya ciro waya yana kiran Abdulazeez. Yana dagawa ya ce da shi, Ina ka tafi? Ka shigo yanzun nan. Ba tare da ya saurari amsa daga gare shi ba ya kashe wayarsa ya maida aljihu.
Falon ya rikice da tofin albarka da fatan alkhairi ga Hajiya Maryam Hamza Atiku. Sai da kowa ya gaji ya bari sannan ta gyara zama, ta ce.
Na yi zama da Habiba zama na amana, domin ta so yarana ta kaunace su, ta kula da su tsakani da Allah, musamman Abdulazeez na hannun damanta. A kan idonsa aka haifi Hafsat a asibiti can Jeddah. A tasowarsu kuma sai na fahimci yana shiri da uwa ba ya shiri da yarta, tun a wannan lokacin nake nazarinsu na fahimci sam ba sa ga maciji. Ni kuma na sa a raina tun a lokacin Abdulazeez ba shi da mata sai Suhaana. Mun yi musu aure ba tare da son ran kowannensu ba, su suka san yadda sukai suka shirya kansu.
Kalaman da ya tsinta kenan a shigowarsa falon wadanda suka kara tsinka masa zuciya. Wata juwa-juwa ya ji tana kwasarshi tana neman fyada shi da kasa jin kowa a falon na kiran sunansa cike da kauna da tsananinbegensa a zukata da fuskokinsu, Angon Hansatu!.Shine mijin nata? Wasucikinsu suka ceAbdulazeez na Hafsu. Allah ya yi albarka!. Kowanne da abin da yake cewa na nuna kauna da kulawa a gare shi.
Kusa da mahaifinsa ya lallaba ya zauna, amma sai Malam Babba ya ce ya taso ya zo kusa da shi. Da rarrafe ya yi hakan, sabida gwiwoyinsa sun kasa daukar sa. Malam ya yafito Addah da hannayensa. Cikin matsananciyar kunya ta tashi daga kusa da Dada ta tafi ta zube a gabansa. Hannun Abdulazeez ya dauka ya sanya cikin na Hafsat ya cure wuri guda. Daga Abdulazeez har Hafsat bugun zuciyarsu ya tsananta a wannan lokacin, sun kuma kasa duban junansu idanun kowannensu na kan kyawawan yatsun da Malam Hashim ya cure ya dunkule wuri guda,siraran zobunan danyen gold na hannunta guda biyu sun kawata yatsun. Yatsun kawai suke kallo sarke cikin najunansu da tunanuka masu nauyi a zukatansu. Abdulazeez na ji a ransa sallama yake yi da Hafsat, sallama irin ta SAI WATARANA...... Hafsat na tunani a zuciyarta, mene ne muhimmin aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta???
In a da rashin asali ne, yanzu fa? Zai dubi Allah da girman UWA ya kaunace ta su ci gaba da kyakkyawar rayuwarsu ko kuwa? Ko kuwa zai rufe ido a karo na biyu ya zabi Muazatu a kan su su biyu ita da mahaifiyarsa? Yau ta tsayar da zuciyarta wuri guda ta fahimci kauna ce sak! Mai lullube da soyayya ta ke yi wa mijinta Abdulazeez Dakata ba wani abu daban ba. Ba za ta taba sonsa da abin Allah wadai ba. Fushin iyaye kuwa abin Allah wadai ne, tana rokon Allah ko ba zai so ta ba ya ci gaba da zama da ita don tsira daga fushin UWA-MAHAIFIYA, ta amince ya auro Muazatu ya karo cikin gidan za ta zauna lafiya da ita, koda kuwa bazai iya adalci a tsakanin su ba zata jure ta zauna. Ta sa a ranta muddin ta samu damar kebewa da shi kafin barinsu Jimeta za ta shawarce shi a kan wannan hangen na zuciyarta. Za ta iya jure komai ban da rasa shi a yanzu. Yana da matsayi iri-iri cikin rayuwarta. Ya cika mata dukkan burirrikanta. Ya kawo dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali gare ta. Za ta so shi da makamancin hakan shi ma (Allah sarki Hafsat).
Kawunansu Malam Babba ya kama ya shiga kwararo musu addua. A karshe ya ce, Miji ake baiwa amanar matarshi, amma ni Hashim Babba Jimeta, ke Hafsu na baima amanar jikana Abdulazeez, ki kula min da shi, ki rike shi amana, Allah ya yi muku albarka bakidaya.
Abdulazeez ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla. A haka ya dago su ya kalli Hafsat wadda kanta ke sunkuye, mayafinta ya zame ta baya. Manyan kitson kanta sai kyalli suke suna daukar idonsa. Da a ce bai yi azarbabin kuskuren sanya takardar nan a jakarta ba ya bari sai za su koma Kano ya bata hannu da hannu kamar yadda zuciyarsa ta shawarce shi da farko, da yayyagawa zai yi yanzu ba wanda ya ji ba wanda ya gani, ya yi fatali da wasu alkawurruka da ya san ya daukarwa Muazatu tunda ita ba Allah ba ce. In ya so ya yi kaffara ya ci gaba da zama da Hafsat har karshen rayuwarsa.
An ce ana barin halas ko don kunya! Ya tabbata zai iya mantawa da Muazatu cikin rayuwarsa, amma ba zai taba iya mantawa da Hafsat ba. Alamarinsa da ita ya fi gaban a kira shi soyayya irin tashi da Muazatu. Wani alamari ne daban beyondhis expectations. Wasu igiyoyi ties sun bi sun daddaure zuciyarsa tamau sun hanashi sukuni da jin dadin rayuwar ko ta yaya, daga jiya zuwa yau da bai kwana wuri guda da Hafsat ba.
Ya tabbata za su ci gaba da bibiyarsa suna kassara shi har karshen rayuwarsa in bai yi gaggawa ya gyara kuskurensa ba.
Kamar an ce da Hafsat dago. A hankali ta cira idonta suka sauka cikin na Abdulazeez. Sababbin alamura masu ban mamaki ta gani a cikinsu wadanda bata taba gani ba. Ji ta yi ba za ta iya jure kallon tsakiyar idanunsa ba domin sosai ta fahimci yana cikin wani hali da ta kasa ganewa. Sunkuyar da kanta ta yi ta zame hannunta daga cikin nasa ta koma jikin Dada ta zauna. A kusa da Malam ya ci gaba da zama ya kasa tashi. Don ya san muddin ya mike kafafunsa ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba. Ya tafka gundumemen kuskure wanda bai san ya ya zai yi ya gyara shi ba.
Hotunansu da Habiba a Jeddah Mammah ta fiddo kala-kala a ke ta gani. Duk cikin bakar abaya ta ke irin ta matan Saudiyya amma fuskarta a waje ta ke ta dage himar din sama dauke da murmushi mai keta zuciya da hakorin makkah na gwal a bakinta, yawanci duk tare ta ke da su Ismael a wuraren wasan yarababu Abdulazeez yana Nigeria a lokacin. Adduoi na musamman aka yi aka rufe taron, sannan jamaar gidan suka shiga fiddo da garar abinci kala-kala wanda aka tanada musamman dominsu. Rago guda aka kyafe aka gashe musu ko daddatsa shi baa yi ba. Abinciccikan na fulanin Jimeta ne irin su tuwon Alabo (nyiri gurka)da miyar kubewa, tuwon masara da miyar yakuwa da gyada wato (hako lauto), tuwon dawa da miyar zogale (hako kabije) tuwon shinkafa da miyar karkashi (hako gubudo). A fannin abin sha kunu ne guda uku; ga kunun shinkafa (garibasise), kunun gyada (gari biriji), kunun tsamiya (garijabberi) sannan ga soyayyar rama (saande). Kowa yaci abincin nan da matukar marmari yayi hanian hade da gasashshen naman rago.
Har dare suna gidan sai magriba maza suka fita sallah, suma matan suka yi a cikin gida. Bayan sallar ishai suka yi sallama da kowa za su wuce masauki. Mammah ta dubi Hafsat wadda ita ma ta mike tana son ta bi su saboda rashin sabo, ta ce ta zauna da Dada, gobe kafin su wuce Kano za su biyo su yi sallama, kuma ta sanya wayarta a caji za ta kira ta anjima.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

HAFSAT DAKATA
Bayan shigewarta daki, Mammah ta mike don ta bi bayanta. Da sauri Baba Azumi ta kamota ta maidata ta zaunar.
Kada ki bi ta. Bari sai ya dawo sai su tafi tare. Mu je yanzu ni da Salisu ni kadai in gyara gidan.
Hajiya Maryam jiki a sanyaye ta koma ta zauna. Damuwarta ta fito sarari akan kyakkyawar fuskarta, amma Azumi ta shiga nuna mata cewa samun sabani tsakanin miji da mata wani abu ne wanda yake normal ba yau aka fara shi a doron duniya ba. Ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ba irin tunanin da ba ta yi ba na abin da ya shiga tsakanin Abdulazeez da Hafsan, sai dai ko kusa koda da taki daya tunaninta bai kawo saki ba. Wannan ko a mafarkinta bai taba zuwa ba.
Da daddare Hafsat takardar Abdulazeez ta dauko daga jakarta, kwanciya ta yi a tsakiyar gadonta idanunta sun yi luhu-luhu sun kankance sabida kukan da ta ci a yau. Da Mammah ta ce ta tashi ta koma gidanta wani miki ne ya taso mata na kaunar gidan, maigidan da duk abin da ya shafe shi. Warware takardar ta yi tana so ta yi mata duba na tsanaki, ta fahimci hakikanin me Abdulazeez ke nufi da kalamansa?Don kuwa a Jimeta daga sanda taji kalmar saki cikin wasikar bata kara fahimtar sauran bayanan dake cikinta ba.
Abinda ta fahimto a karo na biyu da karanta takardar cikin nutsuwa da tsaida hankali shine;kalaman duka na yabo ne da rashin kushe a gare ta. Ya kare da cewa, ita din abar so ce (a darling) a zuciyarsa. Halayenta ababen yabo ne. A zamansa da ita ba ta zalunce shi ba. Rauninsa guda daya ne yana sonMuazatu, kuma muddin yana aurenta iyayensa ba za su taba bari ya auri Muazatu ba, da ya kasance kuma son da yake yi wa Muazatun ya rinjayi wanda yake yi mata sai ya zabi ya samu Muazatun ita ya rasa ta... Wannan ya isa ya nuna in har ita mai tsinkaye ce ta yarda ta amince da cewa Abdulazeez ya fi son Muazatu a kanta. Koda yana sonta a yanzu bayan aurensu, son bai kai koda taki daya na wanda yake yi wa Muazatu ba...... Wani kuka ne ya taho mata da karfinsa, ta kai hannu ta toshe bakin don hana masa fitowaamma hakan ya gagara saboda karfin sa, daya hannun rike da takardar ta rufe ido ta soma sakin kukan sosai mai cakude da wani irin kishin Muazatu da tausayin kanta.
Ji ta yi an sanya hannu an zare takardar daga hannunta. A razane ta bude idanunta da suka yi jajawur sai bulbular hawaye suke yi. MAMMAH ce!
Ba tare da ta ce da ita komai ba ta juya ta fita da takardar a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login