Showing 9001 words to 12000 words out of 133887 words

Chapter 4 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

542

ya kara daga hankalin Muazatu wadda yadda ta ga rana haka ta ga dare, cikin matsanancin tashin hankali.
Sai karfe biyar da rabi alarm din da ya saita ya tashe shi, ya dauro alwala ya gabatar da (rakaatainil fajr), sannan ya bada farali. Haka kawai ya ji ya kamata ya tashe ta ta yi sallah in ba ta tashi ba, ko ransa na so ko ba ya so.
Dan karamin tsaki ya yi, sannan ya mike daga inda ya yi sallah. Haka kawai an dora masa nauyin mutum yana zaman-zaman sa.
Har zuwa lokacin wayarsa na ci gaba da ruri, jinjinawa naci irin na Muazatu ya yi, in ya tuno yadda suka yi sai haushinta ya sake kama shi, ya kasa amsa wayar. Da ya ga ba ta da niyyar daina kiran sai ya kashe wayar gabadaya ya mike ya nufi dakin Hafsat.
Kwankwasawa ya yi sau biyu ya saurara babu amsa, ya sake (knocking) har yanzu babu motsinta, sai kawai ya murda kofar ya shiga a sike, ba tare da tunanin komai ba.
Tana lullube cikin bargo bakidayanta, zazzabi, masassara da ciwon kai sun taru sun rufe ta tun daren jiya. Allah kadai ya san yadda ta yi ta kawo yanzu.
Gabadaya ta rufu ko don yatsanta babu a waje, sai karkarwa ta ke. Shi kansa bargon da filon da ta ke kai karkarwa suke. Ya lura da hakan, ya dan yamutsa fuska.
Ba ki da lafiya ne?
Daga cikin bargon ta daga kai, bai san ta yi ba, haushi ya soma kama shi, ba ya son shiga shirginta ko kankani, kuma ba ya son yana magana a kyale shi. To kuma ta dukunkune cikin bargo bai san halin da ta ke ciki ba, tana ta faman karkarwa wanda ke nuna bata da lafiya. What could he do? He actually dont know.
Yana wannan sake-saken ya jiyo motsin mutum a falo. Da sauri ya juya ya fito. Da farko har ya so ya tsorata don bai yi zaton akwai wani mahaluki a gidan bayan su ba, kawai sai ya ga mace a tsakiyar falo da tsintsiya a hannu. Gari ya dan soma haske wanda ya ratso daga fararen curtains din falon ya haska masa matar sosai.
Da mamaki ya ce.
Daga ina?
Harira ta zube tana gaishe shi da sakkwatancinta. Da sauri ya amsa, so yake ya ji daga ina ta billo.
Sunana Harira, yar Baba Azumi ce.
Ya yi ajiyar zuciya, a take ya ji kamar an yi masa rahama. Ya wuce dakinsa yana mata magana ciki-ciki.
Ki shiga ki duba ta, nake jin ba ta da lafiya idan akwai bukatar taimako na zan fito anjima ki sanar da ni.
A cikin ransa in ban da godewa Mammah ba abinda yake yi da ta samar da third party a tsakaninsa da Hafsat, da ina zai sa ransa? Zuciyarsa ba za ta juri shiga harkarta ba, sannan zai je koina hankalinsa kwance ya dawo sanda yake so ba tare da tunanin ya ajiye wani ba. Kowa ya ci gashin kansa.
Harira ta shiga da sallama, amma Hafsat ta kasa amsawa, ta daure dai ta yi motsi daga cikin bargonta. Harira ta isa gaban gadon ta yaye bargon, sai Hafsat ta kara dunkule jikinta. Karkarwa ta ke sosai, wadda ta bai wa Harira tsoro. Abinda tayi zato ba shi ta gani ba. Tun kayan data zo dasu ne a jikinta har sarka da dan kunne suna nan a muhalli su. Ta hau gadon ta ciccibo ta, ta taimaka mata ta shiga bayi ta yi fitsari, ita ta yi mata alwala ta ce, ko a zaune ne ta yi sallah sai ta gaya wa maigida su je asibiti, ya ce inda matsalar rashin lafiya a sanar da shi.
Ta ba ta katon mayafi ta yafa, ta shimfida mata darduma. Daga zaune ta yi sallar. Harira ta taimaka mata tana daga zaune ta canza su zuwa doguwar riga yellow da mayafinta ta kamo ta suka fito falo, ta zaunar da ita a (three seater), tana dunkule jikinta cikin karkarwar jiki kanta cikin cinyoyinta.
Tun Harira tana kallon kofar dakinsa da tunanin zai fito, har ta hakura da kallon kofar tasa ta mayar kan baiwar Allah wadda ke cikin wani hali na neman taimako na masassara da zazzabi mai zafi da matsanancin ciwon kai. Ita ba abun ta je ta buga masa kofa ba tunda bai ba ta umarnin hakan ba. Haka ta zauna shiru, ta tallafo Hafsat jikinta.
A daidai lokacin ya murdo kofar dakin nasa ya fito, lokacin gari ya idasa wayewa sosai.
Kallo daya ya yi musu ya dauke kansa wayar da ke hannunsa ta fara ruri.
Ba ta da lafiya ne? Ya tambayi Harira.
Zazzabi ne ya rufe ta, ina ga gajiyar biki ne.
Ya wuce gaba yana amsa wayarsa, bayan ya ce da ita, Ku biyo ni mu je asibiti.
Harira ta kamata, ta taimaka mata suka bi bayansa.
Baya suka shiga duk su biyun. Ya tada motar a ransa yana fadin, Lallai direba ya samu. Ya ja dan karamin tsaki. Yarinyar ta faya langwai, shes not strong anymore kamar lagwanin risho. How could he be the husband of such a fragile and delicate woman? Hes bold and energetic,yana son jarumar mace kamarsa ba dangin ta-kitse-ta-narke ba.
Asibitin da file din gidansu yake ya kai ta wato DIFF. Nan da nan likitoci suka karbe ta, ashe tana ma da file da su bai sani ba. Yadda Mama ba ta sakaci da lafiyarta tun dawowarsu Abuja ta ke kawo ta check up lokaci zuwa lokaci na nimoniyarta. Kulawa ta musamman suka shiga ba ta a daki na musamman. Ya nuna wa Harira inda za ta zauna ya yi tafiyarsa gida, ya manta da su. Wanka ya yi, tare da yin shirin (office) don shi ba wani hutu da ya dauka don bai dauki kansa ango ko sabon aure ba. Yana nan a (single Abdulazeez) dinsa, he will never answer the namemarried sai ranar da Muazatu ta zamo matarsa.
A office ya tadda sabon case mai tsauri, don haka ya zama (occupied) bai kara tunawa da wata Suhaana ba. Aiki ya dukufa yi kain da nain kamar yadda ya saba a kullum.
Sai da Suhaana ta samu barci zazzabin da ciwon kan suka sauka, likitocin suka fito suka kyale ta. Suka ba wa Harira izinin shiga da umarnin kada ta yi wani kwakkwaran motsin da zai tashe ta, sai ta tashi don kanta.
Tun Harira na kallon kofa tana tsammanin shigowar Abdulazeez har ta gaji ita ma barci ya yi awon gaba da ita a kan kujerar da ta ke zaun a gaban Hafsat. Ba ita ta farka ba sai ana kiran sallar azahar. Ta bude ido ta kalli Hafsat da ke barci ta ga ta tashi itama tana kwance ne kawai lamo a kan filo.
Ta ce, Hafsatu kin tashi?
Kai ta daga mata.
Nurse ta turo kofa ta shigo da keken magunguna, ta dubi Hafsat ta yi mata murmushi, Kin tashi?
Ita ma kai aka gyada mata.
Ta dubi Harira ta ce, Ki hada tea ki bata mai kauri, sannan in ba ta magungunanta.
Harira ta ware ido tana kallon dakin, babu komai na ci a dakin. Ta rausayar da kai ta ce da Nos din,
Don Allah ko za ki taimako da shayin? Maigidan nata bai dawo ba tunda ya kawo mu.
Nos din cikin mamaki ta ce, Ya zai kawo matarsa ba lafiya ya tafi bai ajiye muku komai ba?
Harira ta yi shiru, don ita ma abin ya ba ta mamaki. Amarya ce fa, amarya guda! Da aka kai masa jiya-jiya? Za ta iya tunawa ko sallama bai yi mata ba da zai tafi. Ta ce da Nos din, Wattakila uzziri yarrike shi, kiddai taimakko mata da shayin.
Nos din ta fita a harzuke, can ta dawo da shayin a kofin. A wajen wasu marasa lafiyan ta karbo. Harira za ta kama Hafsat ta tashi, ta dakatar da ita ta tashi da kanta. Nos ta ba ta shayin ta karba tana sha a hankali, kamar ba ta so.
Sai da ta shanye ta ba ta magungunan da ruwa, ta ce ta koma ta huta. Ta sa hannu a wuyanta da goshinta, zazzabin ya sauka sai zufa ta ke.
Ta ce, Good, ki kara hutawa zuwa yamma in Doctor ya zo ya kara ganinki za ku iya tafiya gida.
Ta amsa daga can kasan makoshinta, Toh.
Karfe shidda na yamma Abdulazeez ya tashi aiki. A matukar gajiye ga yunwa, coffee kawai ya sha tun safe. Ya harhada komatsansa da system zuwa black robe dinsa da wig ya zuba a kujerar gaban motarsa. A hankali yake tuki idanunsa na lumshe sabida gajiya, a kan hanyarsa ya gifta ta asibitin da ya zube su Hafsat. A take ta fado masa a rai, ya tuno da su.
Da hanzari ya yi reverseya shiga asibitin yana fadi a zuciyarsa. Haka kawai an dora wa mutum nauyi, yana fama da kansa. Ni kaina kulawar nake bukata. A yadda na kwaso gajiyar nan kulawar mace nake bukata, ba ni in yi ta fama da ita ba.
Sosai ya yi dogon tsaki, amma a take ya yi istigfari cikin zuciyarsa a lokacin da zuciyarsa ta tambaye shi, Wa ka ke wa tsakin?
Daga shi sai bakaken suit din jikinsa ya fito kansa babu hula. Cikin takunsa na nutsuwa ya nufi cikin asibitin. Ya murda kofar dakin ya shiga da sallamarsa can kasan makoshi. Doctor da Nos din nan ya tarar a dakin suna kan Hafsat. A fusace Nos Hindatu ta dago ta dube shi don ta kudure a zuciyarta sai ta kare wa mijin yarinyar nan Hafsat tanadi idan ya zo, don hatta abincin rana ita ta ba su. Amma me? Kwarjini da kamalar Abdulazeez Hamzah Dakata sai ya disashe ganinta ya kashe kuzarinta, ya warware mata duk wasu kalami da ta shirya na cin mutuncinsa.
Fuskarsa a daure ta ke tamau, ya ba wa likitan hannu suka yi musabiha. Likitan ya ce, za su iya tafiya gida ya rubuta musu sallama yanzun nan, don ta warware, stressne kawai wanda ba ta saba da shi ba. Ba sai ya biya bill ba, yana cikin billdin gidansu.
A takaice ya yi masa godiya ya juya zai fita, sai kuma ya kalli Harira a fizge, Ina jiranku a mota.
Da sauri ta mike tana yafa mayafi, sosai ta ke jin shakkarsa ba ta san me ya sa ba. Yana da tsare gida sosai kuma da alama ba ya son wargi. Hafsat da kanta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigarta ta sauko daga gadon ta zura takalminta suka bi shi a baya.
Tunda ya shigo idanunta suka sauka a kansa sau daya, ta ga yadda ya yi murtuk da fuskar nan ba ta kara marmarin kallon inda yake ba, kuma da ma ita ba gwana ba ce a kan kallon nasa ba, ba tun yau ba. Abu ne da ta horu da shi tun tana karama; ta ganshi ta sunkuyar da kai.
Da ma ya tula shirginsa a kan kujerar gaban motar don haka baya suka shiga dukkansu, kuma ko kujerar (empty) ce babu fuskar zamanta kusa da shi. Ko da wasa ita ma ba za ta fara ba.
Ko da suka iso gida ya kwashi shirginsa ya kule a dakinsa, ba su kara ganinsa ba. Zama suka yi zugum-zugum a falo daga ita har Harira, kowacce ta yi tagumi cikinta na kugi. Zuwa yanzu Harira ta fahimci wannan auren da matsala, ba auren SO ba ne. Don ta lura ita ma amaryar ba ya gabanta. Amma dai ko ya ya ne a shekarunsa ya kamata a ce ya san cewa, akwai hakkin ciyarwa a kansa.
Ta dubi hafsat sai ta ji tausayinta ya kamata. A ganinta wannan salihar yarinyar mai kyau da kamala ta wuce auren RASHIN SO! To ba ta san wace irin kaddara ke tare da ita ba. Mikewa ta yi ta nufi kicin don ta ga ko za su samu abin da za su ci.
A daidai wannan lokacin Abdulazeez ya fito. Ya yi wanka ya sauya kayan jikinsa zuwa kananan kaya. Rike yake da mukullin motarsa da wayarsa ya wuce Hafsat a falon ba tare da ya ce mata uffan ba. Ba ta tsammanin ma ya kalle ta ya fice. Wata irin ajiyar zuciya ta saki ta sauke tagumin da ta yi ta mike ta nufi dakinta, ta ajiye mayafinta ta fada toilet ta sakar wa kanta showerna ruwa mai dumi. Ruwan na sauka a jikinta a hankali, sai ta ke ji kamar yana wanke mata zuciya, yana tafiya da yar damuwar da ta samu kanta a ciki tun shigowarta gidan. Rashin kulawar Abdulazeez gare ta bai dame ta ba ko kadan, tunda ta fi kowa sanin wane irin aure ke tsakaninsu. Horon yunwa da ta soma cin karo da shi a cikin auren shi ya so ya taba zuciyarta, musamman da yake ga mutum a tsakaninsu ko don ita ai ya rufa asirin rashin son nasa gare ta.
Tana zaune a gaban madubi tana shafa ta ji ana dan kwankwasa mata kofa. Rigar wanka ce a jikinta ta tawul ta kame gashin kanta a tsakiya da katon (hair-bound).
Shigo. Kawai ta ce, don ta san Harira ce.
Murda kofar ya yi ya shiga, ya tsaya daga jikin kofa hannayensa duka biyu rike da fararen ledoji guda biyu. Ta cikin madubi ta ga wanda ya shigo din, sai ta kasa juyowa ta yi kasa da kwayar idanunta. Ajiye ledojin ya yi ya juya ya fita tare da rufo mata kofar. Sun kusa gwabza karo da Harira wadda ta taho rike da plate shake da jallop din taliya, ta ja gefe da sauri ta ba shi hanya ya wuce. A ransa yana fadin, Abincin ma sai an dafa mata, gata mugun abu. To da babu wannan matar ni zan dafa kenan? Ko kuwa ana nufin kullum in je restaurant in sayo abinci sau uku a rana? Mtsew!
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Yau yana (office) da laasar ya samu wayar Mammah, ta ce da ya dawo ya dauko Harira da kayanta ya kawo mata ita za ta koma Sokoto. Mijinta yayi waya ta koma. Muryarsa ta nuna damuwa a sailin da yake cewa. Mammah da kin bashi hakuri zuwa gaba kadan, na ga alama suna jin dadin zama da junansu, kin ga ni in na fita tun safe sai karfe shida nake komawa gidan, tana debe mata kewa.
Mammah a dan hasale ta ce, Sanda na kawo ta kai ka ba ni shawara? Ko kuwa mace da aurenta sai ta dawo gidanku da zama?
Ya yi murmushi, Aah, ba ni ba ne, kuma ai dama ba nufina ta dawo kwatakwata ba kamar two months haka, lokacin ta saba.
To yanzu ma ban nemi shawararka ba, ka dauko ta ka kawo min ita na ce, in ka ga dama ka kwana ba ka koma gidan ba, ai zaman aure ne mu ma da haka muka saba a namu gidajen.
Za a yi yadda ki ka ce Mammah.
Ta kashe wayarta, ya ajiye tashi a gefe cikin zuciyarsa yana jinjina rigima kala-kala irin ta mahaifiyarsu.
A nata bangaren Hajiya Maryam Hamza Dakata murmushi ta yi tana rike da wayar a hannunta, ta dubi Daddy da ke gefenta ta gaya masa yadda suka yi da Abdulazeez. Ya ajiye takardun dalibansa da yake (marking) ya dube ta sosai.
To ke me ya sa za ki raba su da mai aikin?Na san ba wata waya da mijinta yayi don naji Azumin na gaya miki ya tafi fatauci ne Shagamu
Ta gyara zamanta tana fuskantarsa ta ce, Daddy, daga baya ne na fahimci na yi kuskure da na tura ta. Ba aure irin na Adda da Abdulazeez ake sanyawa third-party ba, in hakan ta kasance ba za su yi irin shakuwar da nake so su yi ba. Miji na tausaya wa matarsa in ya ga hidimar gida da ta abincinsa ta yi mata yawa, har ya yi marmarin dauke mata wasu hidindimun idan ya san cewa ya barta a gida tun safe har yamma ita kadai, zai fi damuwa da komawa gida cikin lokaci ya ga halin da ta ke ciki, ko ya dinga kiranta a waya sabanin in ya san akwai wani tare da ita.
Jinjina kai Daddy ya yi, ya ci gaba marking dinsa yana mamakin Maryam, ya ce, To sai yaushe kuma za ki barmu mu je mu gansu, nace in bazaki ba ni zani kin hana, ko ki kira ta a waya ki ji lafiyarta? Allah kadai ya san yadda ta ke cikin damuwa da wannan takunkumin naki.
A nan kuma dariya ta yi, ta kafe shi da kyawawan idanunta, Manta da su Daddy. Sai ranar da Abdulazeez a kan karan-karansa ya ga ya dace ya saya wa Suhaana waya. Mu kuwa sai ta shekara zamuje.

*****
Zaune ta ke a kan sallayarta bayan idar da sallar isha tana jan cazbaharta cikin istigfari, ta jiyo sallamar Harira daga bakin kofa. Juyawa ta yi suka hada ido, ta ganta ta sha lullubi dauke da katuwar (Ghana must go) dinta. Da sauri ta karashe lazimin ta shafa adduar cikin kulawa ta ce,
Aunty Harira ya ya dai? Tana mata kallon mamaki.
Harira ta rausayar da kai, Hansatu Allah ya sada mu da alkhairi, zan koma gidan Mammanku ta turo a dauke ni.
Gaban Hafsat ne ya bada wani irin damm! Zuciyarta wadda da ma a karye ta ke kullum ta sake karyewa. Rasa me za ta ce ta yi, Harira na ta yi mata adduar fatan alheri, da zaman lafiya ita da mijinta ba ta iya ta amsa ba, sai jin (horn) din Abdulazeez suka yi, wanda ya sa Harira sungumar jakarta ta wuce. Wani kuzari ya shige ta da ta tuna watakila rabuwarsu kenan har abada ya kamata ta yi mata alheri ko ya ya ne, domin hakika ta ji dadin zama da Harira, mace mai saukin kai da sanin yakamata, mara shisshigi da saido.
Ta dade da fahimtar zaman da ta ke yi da mijinta ba zama ne na soyayya ba, amma ko da wasa ba ta taba tambayarta wani abu a kai ba. Kokari ta ke ta sanya ta a hanyar yadda za ta kyautatawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login