Showing 81001 words to 84000 words out of 133887 words

Chapter 28 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

575

sun hana ka. Sai ya ga in ya yi hakan bai kyautawa Babansa ba. A yadda ya fahimta auren ma ya dage sai ya yi masa ne don ya hukunta shi. A lokacin da suka riga suka koyawa zuciyarsa ta so matarsa. Fada ya shiga yi masa sosai kan abin da ya yi watoauren yarjejeniya ya ce.
Ko ba ka santa ba albarkacin rikon da mahaifiyarku ke mata ba za ka iya sanya ta a makaranta ka nemo mata danginta saboda Allah ba? Sai don ta amince ka sake ta bayan wani lokaci? Ka manta cewa yarinya ce karama bata da clearconscience. Abdulazeez ina iliminka? Yarjejeniya a cikin aure Haramun ne!!! Ni ma bana bayan a maida aurenka da Hafsat, ban yarda kana sonta ba. Idan kuma ta koma ka kara komawa wajen Muazatun fa?
Wannan karon ya kasa daurewa, duk da yadda yake kokarin yin hakan kuwa. Hawaye ya soma ya ce. Wallahi-wallahi Uncle idan Hafsat ta dawo ba ni ba Muazatu, ba ita kadai ba har duka sauran yaya mata ma. Ni kaina ina mamakin abubuwan da na dinga yi a kanta, bayan a can karkashin zuciyata ba wani damuwa na yi da lamarinta ba, my feeling on them is incomparable! Kawu Abdulkarim I believed im destined to be punished with her love for my misdeeds. Taimaka min in gyara komai; tsakanina da Ubangijina, tsakanina da mahaifina, tsakanina da mahaifiyata, tsakanina da matata. Taimakaminka fahimtar dasubabu wanda yake sama da aikata kuskure. Balle ni Dansu.
Ba abin da Abdulkarim bai yarda da shi ba a kalamansa, amma dole su kara ganar da shi kuskurensa don ya kiyaye a gaba, ya rike matarsa da daraja, ya daina daukar aure abin wasan yara.
Tashi ka je na ji, zan nemi Ambassadan.
Appealing look(kallon roko) Abdulazeez ke bin shi da shi, ya kauda kai saboda wani matsanancin tausayin yaron da ya shige shi. Abdulazeez bai da niyyar tashi, sake gyara zama yake. Ya dan juyo ya dube shi da nutsuwa ya ce. Everything will be alright (komai zai zama daidai da yardar Allah).Amma fa tsakanina da Babanka, shine abokin zance na. Tsakaninka da Maryam kai da ita ne, wannan babu ni a ciki.
A marairaice Abdulazeez ya ce. Ba dai za ka bari a daura auren ba ko? Yanayin muryarsa da helplessness din da ke cikinta ya baiwa Abdulkarim dariya. Amma sai ya gintse ya ce. Ai mun riga mun bada sadaki, ka ga babu dadi mu koma mu karbe ba tare da wani uzuri ba.
Da sauri ya ce, Uncle I dont want her in my life anymore(bana bukatar ta cikin rayuwata ko kankani). Ko kun daura zan saki.
Hararsa ya yi ya ce. Saboda ka zama auri-saki ko?
Sunkuyar da kai ya yi. Ni ma ba so na bane in zama hakan, shi ya sa nake rokon kada a fara, da muguwar rawa gwamma kin tashi.
Murmushi Abdulkarim ya yi ya cire hular kansa ya ajiye a gefensa, ga tsilli-tsillin furfura nan ta fara baibaye kan irin ta Dr Hamza. Shida Dr. Hamza saanni ne tare sukayi wasan kasa duk da shi Abdulkarim yana matsayin kani ga mahaifinsa,ya dube shi cikin sigar zolaya.
“How could a man forget his first love so easily haka? (Ta yaya namiji zai mance soyayyarsa ta farko haka da sauki?) Na dauka nan ka zo gabana kana fadin in ba ita ba sai rijiya? Hafsat din akai kasuwa baka so?Is my grandson loyal a cikin soyayyah? (Anya jikana amintacce ne a soyayyah)?
Juyar da kansa ya yi wani barin daban, yana tuno tarin wautar da yayi, wai har Ishma ya bi yana roka ya auri Hafsat, ba don yaron mai hankali bane da tuni ya dade da daina gaisheshi, Uncle Abdulkarim kuwa bai san da me zai saka masa ba don ya tabbata ba don shi ba da rashin arzikin da zai yi wa iyayensa akan auren Hafsat yanada yawa duk akan mace, macen ma da ko asalin iyayenta bai sani ba, haduwar bariki kawai, babu wani abu na burgewa a tarbiyya da dabiun ta. A hankalikamar mai yin rada, kamar baiso zancen ya fito ba ya ce.
Uncle it is not love!
Mene ne to tsakaninka da ita in ba soyayyar gani kashe ni ba?Cikin hikimar bugun ciki Kawu Abdulkarim ya tambaya.
Wannan karon kallon Uncle din nasa yake kamar amininsa, aminin da ba shi da shi a tsayin rayuwarsa, bai taba tattauna sirrikan zuciyarsa irin wadannan da kowa ba, amma yadda Minister Abdulkarim ya saki jiki da shi yau yana jansa a jiki kamar saansa cikin hikima da son sanin hakikanin matsalolinsa na aure, sai ya samu kansa da son gaya masa komai, watakila hakan yasa ya kara taimaka masa ya dawo da Hafsat cikin rayuwarsa da ta damalmale ta wargajeyanzu. Ya yarda sonta yake ba don Mammah ba, ko don ta shirya da shi. So ne mai zaman kansa, mai cin gashin kansa, wanda baa gina shi bisa kowanne tubali ba sai kauna zallah saboda Allah. Cikin kankanuwar murya ya ce.
It is lust!
A matsayinsa na wanda ya karanta Forensic Psychology ya yarda Abdulazeez gaskiyar zuciyarsa ya gaya masa. Jinjina kai ya yi, ya dube shi cike da kauna. Na fahimci komai. Ka kwantar da hankalinka, yanzu zan je wajen Ambassadan ka tafi gida ka huta. Amma ka ci gaba da lallaba Maryama ka santa da wuya ta yi fushi, amma idan ta yin ba ta iya yinsa ba. Ka jure dukkan punishments dinta ta fika son auren nan, amma ka bada mata kasa a ido.
Sosai ya yarda da shawarwarin Kawun nasa, kuma dama ya dade da sawa ransa ko tsire shi Mammah zata yi zai jure, indai watarana zata huce ta dawo masa da Hafsat,suka yi sallama ya tafi bayan su Farhan sun rako shi jikin motarsa..
Sun-city ya wuce, hankalinsa ya dan kwanta; ya san dai ya kashe maganar auren Muazatu wajen madaurin auren.Sai da ya zo barci ne ya gagara, kewar Hafsat ta hana shi ko da runtsawa, how he wish zai iya jin muryarta ko da bai ganta ba? How he wish suna kwance ne tare a gadon nan nasa suna rigimar duvetkoda kwanciyar ta kai da kafa ce yadda take cewa? Abubuwa da yawa yake tunowa na zamantakewarsu, masu dadin da marassa dadin. Marassa dadin su ne watannin farko na auren, halin ko in kulan da ya nuna mata, musamman ranar da aka kawo ta gidansa, ranar tarihin kowadanne maaurata. Amma ita Hafsat ba ta karar da komai a cikinta ba ban da bacin rai, ciwo, da kwanciya a asibiti. Ya tuno yadda ya kai ta asibitin ya watsar bai kara sanya ta cikin lissafinsa ba balle ya ciyar da ita. Wani kunci ya ziyarci zuciyarsa, ya kai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa, ya ja duvet dinta ya rufe rabin jikinsa. Abubuwa da yawa ya cigaba da tunawa a wannan lokacin, yadda ta dinga wahalar shirya masa abinci yana barinta da shi, duk wai don kada ya saba da ita. Shin ashe mutum ya isa gujewa kaddararsa? Ya isa tsara wa kansa rayuwa? Ya tuno watannin farin cikin wadanda ba su yi nisa ba ya bi duk wata hanya ya tottoshe su don ya tsira da Muazatu! Wace irin makauniyar soyayya ya yi wa Muazatu wadda ta rufe idonsa har ya rasa clear conscience? Mene ne amfanin irin wannan soyayyar ta a cutar da wani don a faranta wa wani? Sosai ya yi wa Mammansu uzurin matakin da ta ke dauka a kansa. Ya rufe fuska da tafukansa zuciyarsa na masa wani irin zugi.

******
Kamar yadda Minister Abdulkarim ya yi alkawari ga jikansa Abdulazeez ya je ya samu Yayansa da Mammah a kan zancen. Sun tattauna sosai, ya gaya musu duk abin da Abdulazeez ya gaya masa bai rage komai ba. Ya ce Saboda tausayin da ya ba ni na so in gaya masa ba ya bukatar kaffara a kan yar Attorney, sai kuma na yi tunanin tunda ba ka fada masa ba may be ba ka so ya sani ne a halin yanzu shi yasa na bishi a haka. Don Allah ku yi hakuri ku maida masa matarsa, he really repented, regretted, and wanted his wife back. Kada garin punishment ku koma daukar hakki, ita ma yarinyar tana son mijinta biyayya ta ke miki.
Sai wannan lokacin Mammah ta san an hana Abdulazeez auren Muazatu bonono Daddy yake musu ita da shi. Wani dan relief ta samu a zuciyarta ba don ta daina jin haushinsa ba, ga kuma labarin auren kwangila wanda a zahiri ba ta san hukuncinsa a addini ba da ya shiga kunnuwanta. Ta tabbata abinda ya fi wannan ma Hafsat za ta iya in aka sanya ta in dai a kan a barta ta yi karatu mai zurfi ne. Tausayin Hafsat ya kara kamata. Ta kudure a zuciyarta in har tana raye sai Hafsat ta zama Farfesa. Abdulazeez kuwa tunda a kan budurwarsa ya saki Hafsat(wai ba don ba ya sonta ba)she will make sure she made him understand the worth of what heabandoned negligently (sai ta tabbatar ta sa shi ya fahimci darajar abin da ya yi wa rikon sakainar kashi).
Da wannan zaman nasu ya tashi, babu wata kakkwarar amsa daga bakinta. Daddy ya ce shi dama bai dauka da nisa ba, zai nemi Baffa Atiku a yi wa auren duba na addini sannan su gyara, kawai yana ganar da shi kuskurensa ne kafin ya bada goyon bayan maida auren ba tare da ma yan Jimeta sun ji ba. Kuma dama ya gaya wa Maryam ta cire kanta daga shaaninsu bakinsu daya ta ki ji. Sai dai har Abdulkarim ya tafi ba wanda ya ji ta bakinta a cikinsu.
A daren ranar kwana Daddy ya yi yana lallashin matarsa ta amince ya maida auren yaran, amma ta yi bakam ta ki ba shi amsa, har sai da ranshi ya yi mummunan baci, ya ce Maryama saboda ba ni na dauki rikon Hafsatu ba shi ne za ki nuna min iyakata? To ai ni ma ina da iko a kanta tunda a gidana ta rayu karkashin kulawa ta kuma sunana ta ke bearing. Don haka ko ta ina aka je aka dawo nima ubanta ne ina da iko da ita. Don haka ba zan zuba ido yaran nan su ci gaba da zaman haramci ba. Da idanunki kin gani yana shiga dakinta ba da saninki ba yana bibiyar matarsa. Abdulazeez ya yi kuskure, kuma ya yarda ya yi, in ya yi istigfari ba ki isa ki shiga tsakanin bawa da Ubangijinsa ba. Laifin da ya yi miki shi ne wanda ki ke da ikon yafewa ko kin yin hakan, amma ba wanda ya yi wa Ubangijinsa ba.
Kowa ya sani yin yarjejeniya a cikin aure sharia ba ta so, ta yi hani, amma ba kowa ne ya san hakan ba ko ya dauke shi da muhimmanci. Yau ko kisan kai Abdulazeez ya aikata ba marriage contract ba, danki ne, ba ki da yadda za ki canza wannan. Ki gode wa Allah da bai yi saki uku ba, sannan bayan sakin alamarin ya rikide zuwa yadda ki ke mafarkinsa. In ba ki gode wa Allah ba kada ki butulce wa niimarsa gare ki. A gobe za mu je Kano da su Kawu Abdulkarim gun Baffa a maida aurensu idan har shariah ta amince da hakan. Ki je ki yi ta fama da muguwar zuciyarki. Ina rokon Allah idan wannan shi ne gata na karshe da zan yi wa Abdulazeez ya sa in cika shi da sauran numfashina.
Sai da ta ji zuciyarta ta raunana da wannan furucin nasa na karshe, sai kawai ta sa kuka. Juya mata baya ya yi ya kwanta, ta ci gaba da kukanta har ta yi ya ishe ta. Sannan ta share hawayen, ta ce cikin kuka.
Na yarda a mayar da auren, amma wallahi sai na ga dama za ta tare.
Dariya abin ya so ya baiwa Daddyn, wani zubin kamar ba ita ta haifi wadannan zaratan samarin ba, musamman idan tana gabansa, yajanyo ta gareshi yana fadin.
Hakan ma mun gode, kwanciyar hankalinmu auren ya dawo dai-dai, kiyi ta rike yar ki har ta fara furfura agabanki. Kuma ni ban ce mutuwa zan yi ba a hanyar Kano sai in kwana na ne ya kare, kin ji Maryamata?

******
Washegari ta maida Hafsat makaranta da kanta, za ta zo ta dauke ta karfe hudu na yamma a gaban department dinsu. Hafsat ba ta sha wahalar ganin Rabia Sada ba (Mami). Mami ta yi farin cikin ganinta sosai, ta gaya mata ta shiga damuwar rashin dawowarta ga shi ba ta san gidanta ba, wayarta ta buga har ta gaji. An wuce ta da karatu ba laifi, duk ta samu notes, handouts da courses outline a wajen Mami, ta gaya mata ta yi mata assignment har uku. Kuma tana yi mata attandences don jikinta ya bata ba zata watsar da karatun ta gabadaya haka kawai ba. Hafsat don farin ciki sai ta rungume Mami, ta yarda yanzu aboki rahma ne, sai dai zama da mutane ne da wuya, amma in ka yi katari da na kirki mai kaunarka da gaskiya amfaninsa yawa ne da shi. Mami ta mannewa tana highlighting dinta abubuwan da ba ta gane ba. Sun wuni tare ba abin da suke sai karatu. Ta kwafi time-table, sai dai cikin duk abubuwan da ta ke yi yana fado mata a rai, sai ta tambayi kanta ko me yake ciki? Ko ya ci abinci? Ko yana ina yanzun? Idan ta lura tunanin zai tafi da walwalarta da dan kwarin gwiwar da ta samu na son farantawa Mammah sai ta yi maza ta kira sunan Allah Al-Lateef, ta roke shi Ya karfafe ta da yin biyayyah ga uwarta, uwar da jinin haihuwa ne kawai bata diga mata ba a duniya. Ta tabbata duk son da Abdulazeez ke ikirarin yana yi mata a yanzu, bai kai rabin wanda ta samu daga mahaifiyarsa ba.
Yana son nata ya zabi wata akanta? Yana son nata ya sake ta? Wannan kalma ta saki na yi mata mugun ciwo kamar ba da amincewarta aka yi ta ba. A ranta sai ta ce, Na amince ne a wani QARNI (centuary) na rashinsanin ciwon kai (period of barbarism). Ban san darajar miji a gun matarsa ba. Ban san waye Abdulazeez Dakata ba, idan yanzu ne zan iya rasa komai in koma matarsa!
To ai ya ce aurenmu yana nan, ya yi sakin kamar yadda ya yi alkawarin yinsa, kuma ya maida auren tun a lokacin. Wani gwauron numfashi ta sauke wanda ya sa Mami Sada juyowa ta dube ta. A sign of relief sunan numfashin nata. Murmushi ta yi wa Rabia Sadan ta ci gaba da rubutu.
Karfe hudu Mammah ta zo daukanta. Har gaisawa suka yi da Rabia, Hafsat ta gaya mata dimbin taimakon da Rabian ta yi mata. Sosai Mammah ta gode, suna tafe a kan hanya suna hirar makarantar har suka zo gida. Mammah ta gane Hafsat ta fara sakin ranta, ta daina yi mata fushi, watakila ta fara shiga karatun ta nutsu ne kamar yadda ta ke ankarar da ita. Watakila kuma don ba ta ganinsa ne. Koma dai mene ne daidai ta ke da kowannensu.
Da asubah ya nemi layin Abdulazeez cikin saa ya samu, ya ce ya shirya yanzu ya fito su tafi Kano. Tun daga lokacin ya tabbatar Kakansa mai kaunarsa wato Abdulkarim Dakata ya yi kokarin da ya ce zai yi. Wata irin kaunar Uncle din ta sake mamaye shi. A gurguje ya yi wanka ya fiddo wata sabuwar shadda (filtex) ya saka, ya dora hula wadda ta dace da kalar shaddar wato coffee color, agogon hannunshi swatch-blustery kalarshi kenan, ya feshe jikinsa da turaren da yazame masa jiki sannan ya dauko duk abin da zai bukata ya fito. Gidan ya rufe gabadaya maigadinsa Dan fulani ya bude mishi kofa ya fita.
Duk mutanen gidan ba su fito ba sanda ya isa, a falon farko ya jira Daddyn ya sauko ya karbi jakar hannunsa. Bai wani sake masa fuska ba ya wuce shi yayi gaba, mukullin babbar motarsa kawai ya ba shi yana nufin shi zai tuka su. Ya soma gaishe shi da safiya wadda a da baya irin ta duk don ya samu Daddyn ya sake masa ne, maimakon haka sai Daddy ya harzuko. A fusace yace Ba za ka rabu da ni ba Abdulazeez? Na ce ina bukatar gaisuwarka? Gaisuwar dole ce? Nace dole ce?
A yi hakuri Daddy. Ya ce yana shafa kai.
Sai da maigadi ya rufe gate bayan fitarsu suka hau titi sosai, sannan Daddy ya ce a gajarce, Ka biya mu dauki Kakanka.
O.k Daddy.
Hararsa ya yi, Abdulazeez na hangowa ta madubi ya nutsu ya kara shiga taitayinsa. Da alama yau a Ambasadansa yake baya son wargi.
A maadanar motocin sa suka tadda shi(tsohon Minista Abdulkarim Dakata) ana goge masa motar da ya yi niyyar yin tafiyar a ciki. Aka wangale musu tafkeken (gate) din suka shigo. Ya iso motar tun kafin Abdulazeez ya gama parking ya mikawa dan sa Hamza hannu, Abdulazeez ya gaishe shi, shi ma ba sakin fuska ya amsa masa. Daddy ya ce, ya hutar da direbansa kawai ya zo su hadu su yi maneji a mota daya tunda a yau za su dawo. Ya amince da hakan.
Tafiyar nutsuwa da kwarewar tuki ta awanni hudu cur ta kawo su Kanon Dabo. Tushensu, usulinsu. Yaro ko da me ka zo an fi ka. Suka shigo cikin birni, sannan sannu a hankali Abdulazeez ya karya kan motar suka shiga unguwarsu mai tsohon tarihi a Kanon Dabo, wato Dakata.
Adda Hafsatu na aikin abincin ranar gidan sanda suka iso. Yau gidan akwai rangwamen mutane kasancewar ranar aiki ce, kuma ranar makaranta ga jikoki. Sun samu Baffa Atiku na baccin rana don haka dakin Adda suka yada zango, ta cika su da ruwa da lemuka kasancewar ba ta gama abinci ba. Sai da ta ji lafiyar jikokinta na Daddy da yayan kaninta Abdulkarim su ma suka ji lafiyar yan uwa, sannan suka shiga hira, tana tsokanar Abdulazeez wai ko takwararta ba ta iya tuwo ba ne ta ga duk ya yi dan wuya bayan da ma can ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login