Showing 78001 words to 81000 words out of 133887 words

Chapter 27 - Auren Kwangila Book 2 & 3 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

567

Maryam in yayi dubu to ya kai kololuwar baci da reaction din Hafsat, mai nuna babu jin zafin Abdulazeez a ranta, bata ji zafin komai da Abdulazeez yayi gareta ba. Kada dai tana can wajen miji tana shan AC ta yi sakacin da dare daya kacal Abdulazeez ya juye mata kwanya? Da salon yaudararsa dacontracts din da ya kware akai? Tsawa ta daka mata, Answer me I said...!. (Nace ki bani amsa).
Hafsat ta soma kuka, cikin rishin kukan ta ce, She has to forget him and move forward... (sai ta manta da shi ta fuskanci gaba),
Ta gyada kai cikin gamsuwa da abin da ta furta da bakinta, sannan ta nunata da dan yatsa(abinda bata taba yi ba).
Kin fadi amsa daidai da abin da ya kamace ki. Forget him... move forward...thinkbig for your future!Ki je ki karkade takardunki gobe ki koma makaranta. Ni da kaina zan dinga kai ki ina dauko ki ba direba ba.
Hafsat ta gyada kai. Umartarta ta yi da ta tashi ta ba ta wuri, mai nuna har yanzu ranta a bace yake. Sum-sum-sum ta mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, har ta kai bakin kofa ta tsinto muryar Mammah a tsakiyar kanta. Ina wayar da ya baki? Bani ita nan!
Saura kadan Hafsat ta saki fitsari a wando don kaduwa da mamaki hadi da tsoro. Amma ba ta ce komai ba, a sanyaye ta murda kofar ta fita, ba ta yi mintuna biyu ba ta dawo da galleliyar wayar Abdulazeez ta russuna ta mika mata. Mammah ta jinjina kai sannan ta karba ta yi jifa da wayar can karshen gadonta.
Ko da Hafsat ta koma daki toilet ta shige ta kulle kanta, guilty conscienceya bi ya dabaibaye ta, ta shiga tunanin da wane ido zata kara kallon idanun Mammah, ga kuma son mijin da tausayinsawanda shi yafi komai yawa a daidai wannan lokacin. Da ta san Mammah za ta kwace wayar da jiya ba ta kashe ta ba, da ta barta sun yi sallama da juna, da ta gaya masa how much she love and missed him, da ta gaya masa ta yafe masa baki da baki. Da ta yi masa goodnight kiss din da ya nema ta ki yi masa ta kore shi dole.Yanzu kam ta san da wuya su kara kadaicewa nan kusa tunda Mammah ta gano me ya faru jiya. Kuka ta dinga yi wanda ba ya mata wahala. Ita yanzu wane karatu za ta iya? Ta dade da tsanar karatun. Babu komai a zuciya da kwakwalwarta sai Abdulazeez Hamzah Atiku!!!
Aiki yake a office Barrister Surayyah ta shigo, ransa ya yi mummunan baci, ta zo ne kawai ta kara masa damuwa kan wacce yake ciki. Da surutanta na banza na rashin kamun kai. Ya tattare girar sama da ta kasa ya maida fuskar kamar hadarin gabas. Wani irin kwarjini ya yi mata, hakan yasa ta hau inda-inda na abin da ya kawo ta, wai photocopy za ta yi a ofishinsa nasu injin ya samu matsala. Nuni kawai ya yi mata da machine din ya mike ya soma tattare takardunsa da systemdinsa ya cire wayarsa daga caji ya bar mata ofishin. Ya bawa masinjansa umarnin in ta fito ya rufe masa ofishin.
Ba tun yau ba hakan ta sha faruwa, Barrister Surayyah Saidu ya kwana da sanin sonsa ta ke yi a matsayinta na matar aure kuma. Rashin samun fuska ya hana ta fitowa gaba da gaba ta gaya masa. Tafe yake a kan hanyar Asokoro yana tunanin abin yana Allah wadai da wannan rikitaccen zamani da Allah ya kawo mu. Saboda takurar Surayya da ire-irenta cikin Abuja ya soma tunanin komawa karo karatunsa (L.LM) ya fara gajiya da Federal High Court. Bai samu wannan matsalar a Ibadan ba zamanin karatunsa. Bari dai ya gama da kalubalen da ke fuskantarsa yanzu. He wanted to move forward...
Har ya iso gidansu tunani yake yi, tunanin abin da ya sa Hafsat kin yarda ta yi amfani da wayar da ya bata jiya. Wane irin lallashi ko ban baki ko ban hakuri kuma zai yi mata bayan wanda ya kwashe awanni biyar cur yana yi mata jiya ta fahimce shi? Ita ce kadai hope dinsa a gidan nan.
Kusan tare suka shigo gidan shi da Daddy da ke kwance a bayan mota hyundai Salisu ya dawo da shi daga ofis. Shi ya karba ma Daddyn tarkacen hannunshi, ya bude sliding doorta shiga falon farko, Ismael ya fara hanga yana kallon tashar Sunnah T.V, babu Mammah da Hafsat suna kitchen suna aikin abincin dare. Ismael ya yi musu sannu da zuwa suka wuce shi zuwa sassan Daddy.
Har gaban Daddy ya isa ya mika mishi kayan, sannan ya samu waje ya zauna ya tankwashe kafafunsa yadda ya saba in yana gabansu cikin tsantsan ladabi. Daddy ya ajiye hularsa ya ce, Yanzu da ma zan kira ka, kakanka ya dawo daga Lagos.
Wani irin bugawa kirjinsa ya yi ya sunkuyar da kansa kasa. Daidai lokacin da Mammah ta shigo dauke da Jug da cups da bowldata shako da dambun naman kaza ta jero a kan karamin tray zuwa gaban Daddyn.
Dambun naman ya soma ci wanda ya zame masa alada, Abdulazeez ya gaida Mammah ta kauda kai kafin ta amsa kamar ba ta so, zuciyarsa ta yi masa ba dadi jikinsa ya kara yin laasar. Daddy ya yi kamar bai ga halin da yake ciki ba ya dora bayani.
Sun ba ka aure. Sati mai zuwa kakan naka ya tsayar za su koma a daura aure. Na bada sadaki dubu dari biyu amma kawun yaki karba ya dawo min da su ya biya daga aljihunsa. Sai ka je ka fara shirin daurin aure da abokanka da gyaran gida ko fenti ne ka sake, ke kuma Maryama ku shirya ku wuce Kano a can zaa yi komai.
Da sauri ta ce. Ai ba sai na je ba, auren dan fari? Inna Hafsatu da su Zuwaira zasu yi duk abin da ya kamata, ga iyayensa su Furairah duk sun isa gabatar da komai. In an kawo amarya na je in ga dakin yar masu kudi da mulki. Allah ya sanya alkhairi.
Tsam ta mike ta bar musu falon. Zuciyarta na wani irin zafi. Kafin ta kai kicin ta share hawaye sau uku. Saboda ita bata san minister Abdulkarim yazo da bayanin baza su bawa Abdulazeez Muazatu ba, sun mata miji. Bata san duk bayanin Daddy ne ya shirya abinsa ba. Tanashiga ta tadda Hafsat ta takarkare tana ta suyar dankali, tun jiya ta lura saboda fadan da ta yi mata ta daina walwala kwata-kwata, yau ta kai ta shoppinga Sahad na komawa makaranta da laasar har suka zo gida uffan ba ta ce mata ba. Ita ma sai ta basar da ita. A ranta mamaki ta ke yi tana fadin ta yaro kyau ta ke......Yau ni Hafsat kewa fushi sabida da namiji. Amma mu zuba ni da ku. Yadda na hada wannan auren cikin mutunci kuka hada baki kuka tozarta ni ya kare har abada! Zan ga karshen soyayyah.
Ta ce. Yi a hankali kada ki kone hannu.
Ta ce a hankali ba tareda ta juyo ba. Ai na gama, kwashewa nake sai in je in yi sallah. Ta ce, To jira ni in kwashe abincin duka, mu je sallar tare.
Hafsat ta ce, Toh.
Ta jingina da kitchen cabinet tana jiranta bayan ta gama nata.
Sai ga Abdulazeez har cikin kitchen din. Suna hada ido gaban Hafsat ya yi mummunan faduwa. Wata irin rama ta gano a jikinsa da fuskarsa, idanunsa sun kada yadda suke yi in yana tsananin jin yunwa ya dawo daga ofis. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, tana karbar sakon bugun zuciyarta. Mammah ta juyo ta dube shi ta ci gaba da kwashe abincinta a warmers, a cikin ranta mamaki ta ke yau Abdulazeez ne a kitchen? Ba ta yi zaton ko hanyar kitchen din ya sani ba komai saidai yace a dauko masa kafin ya bar gidan. Ita ma zuciyarta ta tabu da ganin yadda ya sauya, ta ce. Ko lafiya?
Hafsat ya dan kalla ya russunar da idanunsa. Ajiya na bata zan karba. Kai tsaye Mammah ta ce, Wayarka?
Ya yi shiru.
Ta ce. To in ita ce tana hannun Usman na bashi tun safe ya baka.
A sanyaye ya juya ya fita daga corridor din kitchen din ya dakata yana kallon Hafsat daga nesa wadda ke fuskantar kofar shiga kitchen din. Ta dago suka hada ido, kallonta yake kallon Me ya sa ki ka yi min haka? Ita kuma ta rausayar da kai, kallonI have no idea. Ta ke yi masa.
Sai ji ta yi Mammah ta buga mata ludayin miya a tsakar kanta tana fadin. Za ki wuce mu je ko sai na tsokale miki idanun munafurcin? Shashasha. Wawuya kawai! Wadda ba ta san ciwon kanta ba.
Da sauri Abdulazeez ya bar wajen, yana jin sababin da ake matan har kokon ransa.
Maitama ya nufa kai tsaye gidan tsohon Minister Abdulkarim Dakata, he has to cancel it all. Daddy na shirin kashe shi da ransa! Shi bai ce musu yana bukatar Muazatu yanzu ba. Ya dage sai ya aura masa harda biya masa sadaki na makudan kudi. Ko auren Hafsat da kansa aka ce ya biya, amma wannan da yake na mugunta ne an ce fenti kawai ake bukata yayi. He have a lot to tackle a gabansa ba karin aure ba. Shi ina zai kai mata biyu? Idan har igiyoyin aure uku ne daya ya ce ya saki, kuma ya ce ya mayar tun abun bai je koina ba.
Ya same su complete happy familykamar yadda suke koyaushe. Tare da samarin yayansu; Shaaban da Farhan saannin Ismael da Usman ne. Ramadan ne saansa. Nan ya yi sallahr Isha, sai ya zauna a kan sajjadar ya yi shiru ya rasa abin da zai fara roka ma kansa. Wargajewar zancen aurensa da Muazatu ko dawowar Hafsat gidansa? Daga karshe sai ya daga hannu ya ce.
Na bar maKa alamarina Ya Ubangiji, Ka zaba min abin da ya fi alkhairi, Ka sassauto da zuciyar Mammanah, Ka sanyaya mata, Ka sa ta afuwanta min. Abin da yake ta fada cikin adduar sa ta yau kenan.
Uncle Abdulkarim ya aiko Farhan ya kira shi jin shirunsa ya yi yawa, ga shi ya ce wajensa ya zo. Sai da Farhan ya jira shi ya kammala adduoinsa, sannan ya gaya masa Daddy na jiransa.
Kallo daya ya yi masa ya dubi Aunty Zuwaira ya ce. Je ki hado mindinner.
Ko ba ta daraja dangin mijinta ban da iyalin Dr. Hamza Atiku.Dinner mai rai da motsi ta hado har da zazzafan black tea. Sanya shi ya yi a gaba ya ce ya cinye abincin nan a gabansa in yana so ya saurare shi. Haka ya zauna ya yi ta turawa kamar yana cin dusa. Ya bude masa gwangwanin coke yasan yana sonta sosai tun yana yaro ya bashi ya shanye, ya zuba masa ruwa ya sha. Abdulazeez ya samu ya soma regaining consciousnessdinsa. Idanun karamin Kakan na kansa ya san dai ba zai wuce damuwar auren nan da aka hana shi a Lagos ba.
Sanda uban ya kira shi da maganar auren ya yi mamaki, ya ce duka-duka yaushe aka yi aurensa, how could he cope with two wives a shekarunsa? Daddy ya ce rabu da Abdulazeez, ka je ka nemo masa auren nan shi ne kawai maganinsa, ba ka sanin muhimmancin abunka sai ranar da ya kubuce maka. Ya saki mai sunan Addah, bayan ya nemo mata iyayenta. Musabbabin sakin ne har yau ba mu sani ba, ta ki fada, ya ki fada.
A lokacin ne Minister Abdulkarim ya tuno yadda suka yi da Abdulazeez a kan auren Hafsat. Idan a da ya ce rashin asali ne, to ba ga shi ya bi shawarar da ya bashi a baya ya nemo mata asalin ba? Dole akwai abin da suke boyewa dukkansu,wanda ya tabbatar ya zu ba rashin asali bane, ya kuma sa a ransa yau sai ya ji shi. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa ya ce da shi.
“Whats wrong my grandson? (Me ya faru jika na)
Sunkuyar da kai ya yi, ya kara tankwashe kafafunsa cikin matsanancin ladabi, cikin damuwa ya ce Uncle ba da yawuna Daddy yake nema min aure ba. In factwannan tsohuwar magana ce tsakanina da yarinyar na kuma dade rabona da ita. Alkawarin da na yi mata na cika shi, daya alkawarin zan yi masa rafkanuwa (wato na aurenta). Koda kuwa na azumi dari (100) ne Uncle. Alamarin ba daga ni ba ne daga Allah ne,alamari ne irin na zuciya da mutum baida iko a kanta. Ka taimake ni ka bashi hakuri ya mayar min da matata, ban san wani hakikanin so ba sai a kanta. Kuskure ne na yi,ina neman afuwa da yafiyarsu, don Allah Uncle ka taimaka mini.
Cikin idanu Abdulkarim Dakata ke kallon jikan nasa, yana karanto zahirin abin da ke zuciyarshi ne zallah yake amayarwa. Ya amince gaskiyar zuciyarsa kawai yake gaya masa kuma Dr. Hamza bai gaya masa gaskiyar yadda ta kaya zuwansa Lagos wajen Attorney General ba. A matsayinsa na babba, tuni ya gano dalilin Dr. Hamza.
Ya ce. A kan me ka saki matarka?
Abdulazeez bai zaci wannan tambayar ba, don haka sosai ta ruda shi, ya hau kame-kame, abin da Abdulkarim Dakata ya tsinta cikin kame-kamen nasa kawai shi ne;
......Wallahi ba don bana sonta ba ne!!!
Ya tausasa murya ya ce.
Abdulazeez, sai na san matsalarka gabadaya zan iya dosar mahaifinka. Ka tuna ba ni na haifar masa kai ba balle in tursasa shi kan duk hukuncin da ya yiwa rayuwarka.Feel free to discuss your problem with your junior grandpa. Im at a door to help.
Hakan ne ya sanya wata irin nutsuwa da aminci cikin zuciyarsa. Ya samu kansa da warware wa Abdulkarim Dakata komai tun haduwarsa da Muazatu, fitinannen son da ya samu zuciyarsa da yi mata rana daya bayan da in the first place mutuncin Babanta ya sa yake kula ta. Amma shi a a ransa ya san da farko ba son ta yake ba. Yanada buri mai yawa akan karatu da ya shafe masa tunanin soyayya ko yin aure a lokacin.Kuma ya sanar da Muazatu hakan amma rana daya ya samu kansa in ba aurenta yayi ba bazai taba nutsuwa ba. Kawo zancen Hafsat da Mammah ta yi masa rana daya, tunanin hanyoyin gujewa auren da ya yi ta yi ya rasa, don tsira da Muazatu. A karshe ya ga babu mafita (don Mammah ba da wasa ta dauki alamarin ba) ban da ya nemi Hafsat su yi auren a kan yarjejeniya na zaman auren shekara daya da watanni daidai da lokacin da Muazatu zata gama law-school. Ya gaya masa tubalan da aka gina yarjejeniyar akai daidai da burin kowannensu. Ya dan yi shiru, kansa na kasa (feeling guilty). Tsohonminista Abdulkarim ya saki baki, hanci da ido yana jin wauta da kuruciya zallarta hadi da shiga hurumin Ubangiji duk saboda soyayyah. Ya ce a ransato ita Muazatun da diamond aka kerata da dole sai an aure ta ko ta halin kaka? Abdulazeez ya kara sunkuyar da kansa cikin jin nauyin abin da zai fada.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Uncle a cikin watanni na shidda da auren ne muka fara gane shayi ruwa ne daga ni har ita, don ita ma Hafsat na fara gane ta fara yi min soyayya irin ta kowacce mace ga mijinta, na ki ba ta dama ne ta nuna min don a ganina ta yi kankata da yin hakan. Ba a dade ba ni ma na soma experiencing sauyuka masu yawa a zuciyata a kanta. Na fara mancewa da Muazatu, muka zama kamar abokan juna, haka alamarin ya ci gaba da rikidewa and this is where it landed me today.
Uncle kafin na saki Hafsat na yi nazari mai yawa, na tuna girman alkawari, amma ba don soyayyar Muazatu ta yi min yawan da ba zan iya hakura da ita ba. I just want to be out of hypocrates masu baki biyu. Ina so in cika alkawarin da na dauka ga Muazatu. Sai da na riga na sanya takardar a jakarta na soma regrettingcewa abin da ya kamata in yi shi ne, in nemi fatawar malamai ba sakin ba.
A garin iyayenta na yi niyyar karbe takardar ban samu ganinta ba, not even by phone, wanda ya nuna ta ga sakon sakin. Da na dawo Abuja na yi niyyar komawa Jimeta in same ta mu kashe zancen a tsakaninmu, Daddy ya katse min hanzari da tafiya U.S kammala karatun su Ishma. Na sa a raina da na dawo zan je in dauko ta mu kashe zancen in karbe takardar. Lokaci bai ba ni dama ba! Komai ya bayyana ga Mammah, ta yi min mummunar fassara, ta yi fushi da ni mai tsanani. Uncle ko ganina ba ta son yi, ta hadu da hawan jini duk a kaina, na san ko yanzu na mutu wuta zan je a kan fushinta. But I dont have the guts to explain sannan ta ki ta bani dama. Jiya na je na bai wa Hafsat hakuri, mun shirya kanmu. Amma yau sai maganar aure kawai Daddy ke min, wane irin aure ka ke ganin zan iya yi a halin da nake ciki yanzu? Wane dadi ne Muazatu za ta ji a taredani alhalin zuciyata, tunanina da farin cikina duka suna ga Hafsat da tunanin hanyar da zan bi in shawo kan mahaifiyata? Daddy na tunanin auren son raina ne da kwanciyar hankali a gare ni while it is absolutely not! Wannan wani abu ne da ya zama past (bygone)a wajena. Im now after my present and future. Please Uncle ka taimake ni a fasa auren nan. Ba abinda zai kara min sai damuwa da rudani. Zan yi rafkanuwa (kaffara) ta rashin auren Muazatu. Ya karasa muryarsa na son nuna karewar karfin zuciyar da yake amfani da ita wajen yin bayanin.
Kawu Abdulkarim tausayi ya kama shi, kamar ya ce da shi ba ka bukatar yin watarafkanuwa, iyayenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login