Showing 12001 words to 15000 words out of 133887 words
Abdulazeez ko ba zai kula ta ba. Kullum sai ta tsaya ta ga sun shirya masa abinci sau uku a rana, mai rai da lafiya. In zai fita sai ta ce, ta raka shi da (basket) din karin kumallonsa, haka in ya dawo za ta ce ta fita ta kwaso kwanukan daga bayan motarsa, ta yi masa sannu da zuwa ko ranta ba ya so. Girki kawai ta sani, sai wanka da tsaftar jikinta, amma gyaran gida Harira ce. In ta ce ba za ta yi kewarta ba, ko ba ta ji dadin zama da ita ba, to tabbas ta yi karya ta kwana da yunwa.
Idanunta babu dalili ma kawo kwalla suke yi, balle yau ta yi dalili. Da hanzari ta mike ta bude (wardrove) dinta. Manyan turamen atamfofin (Vlisco) ta kwaso har guda biyar da sinkin sabulai guda goma ta watsa a katuwar leda ta bi ta da su da sauri.
Har ya tada motar ya yi reverse ya hango fitowarta da gudu-gudu ta madubi. Ya dan dakata har ta cimmasu. Bude kofar motar ta yi ta azawa Harira a cinya, sai ga hawayen sun zubo.
Harira kanta daurewa ta ke yi, amma idanunta sun kada sun yi jazir. Ta daure ta kama hannun Hafsat ta ce, To me ye na kuka Hansatu na? Ai ana tare, Baba Azumi ta riga ta hada mu. Na yi miki alkawarin in ki ka haihu ni zan zo in yi miki jego, ke dai ki yi kokari kafin shekara mai zuwa ki haiho min santalelen ango ko kawa mai kirki kamarki, kin ji?
Kokarin jan motarsa ya soma don sun soma ba shi haushi. Maganganun Harira sun yi masa wani iri, sai ya ji kamar da shi ta ke. Hafsat ta ja baya ta rufe mata kofar ya fizgi motar da gudu. La-shakka da cikin kasa ne da ya bule ta da kura, sai aka yi saa kananan fararen duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidayanta.
Ciki ta koma ta fada gadonta tana kuka riris, kuka mai dalilai da yawa. Mammah ta daina sonta ne? Ismaeel, Usman da Halim ma? Baba Azumi ma? Tunda Mammah ta yi mata aure kuma shi kenan ta rabu da ita? Auren da ta tabbatar ba dadinsa ta ke ji ba. Yar Harirar da ta bata tana debe mata kewa ta dauke abarta duk don a takura ta a nuna mata yanzu ba mai sonta? Ya ya za ta yi rayuwa a gidan nan daga ita sai Abdulazeez din da shara ta fita daraja a idonsa?
Ya Allah ka kawo min sauki ni Hafsatu, idan kuma mutuwa za ta fi min sauki ka gaggauta daukar raina in huta da zaman gidan nan.
****
Kusan kwanan da ta yi tana kuka shi ya sa washegari ta makara, don bayan ta idar da sallar asubah a nan kan sallayar barci ya sake yin awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai bakwai da rabi, kuma lokacin ne Abdulazeez ya ke tafiya aiki. Salati ta yi ta mike da ta dubi agogo ta fada toilet ta rage mararta ta wanko bakinta ta fio falo don wucewa kicin ta gani ko akwai abin da za ta iya ba shi na gaggawa duk da ta san da kyar ne in bai fice ba.
Amma ga mamakinta yana tsaye jikin dining yana daura agogo, ya shirya tsaf cikin suit bakake da farin tie a wuyansa kamar kullum yana kurbar tea din da ya hada cikin cup a gurguje.
Karfe tara daidai zai shiga kotu a kan case din wasu yara da kanin mahaifinsu ya cinye musu gado, tun daren jiya ya gama (compiling) duk wasu hujjoji da ya tara, amma ya manta da wani (recording) da ya yi saving dinsa a kan desktopdinsa ta ofis dole ya yi sauri ya je ya yi burning dinsa zuwa discyadda in ta kama zaa iya playing dinsa a kotun saboda haka kusan a gurguje ya kammala shirinsa yau ya fito. Ya samu ya hada shayin don ba ya jin yau yana bukatar abinci daga safe har dare, sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a kan wannan case din kamar yadda ya saba, musamman case na marayu ba ya daukarsa da sauki.
Jiya saboda wannan aikin bai samu ya kwanta da wuri ba don haka a dan makare ya tashi ya shirya ya fito falon. Sanyin A.C da ya ratsa shi a falon ya ba shi mamaki, don ya lura duk lokacin da ta fito da asuba sai ta kashe ta, amma yanzu ya tabbatar yadda ya barta jiya da daddare ya shiga daki ya kwanta haka ta kwana tana aiki. Talbijin a kunne, wutar falo a kunne, wadanda kullum sai ta kashe su ta ke kwanciya. Ya kafa wa kofar dakinta ido kamar hakan ne zai tabbatar masa tun shigarta daki jiya tana kukan tafiyar Harira ba ta kara fitowa ba.
Sai ya matsa ya kashe A.Cn da sauran kayan wutar gabadaya ya tsaya nan jikin dining ya hada teadin da yake sha wanda ya dafa da butar ruwan zafi (kettle) yana sha daga tsayen da yake yana daura agogo.
A daidai lokacin Hafsat-Suhaana ta murdo kofar dakinta ta fito. Sanye ta ke cikin riga da wando na barci masu kauri, kanta cikin hular wanka (shower-cap), bai juyo ya dube ta ba da yake ya bata baya, tunda har ta fito to lafiya ta ke kenan. Ya karasa shanye shayinsa ya ajiye kofin a kan (table) ya dora (wig) dinsa a kansa ya suri rigar lauyoyinsa da (briefcase) ya fice zuwa harabar gidan. Ya bude motarsa ya shiga, ya ajiye kayan hannunsa a kujerar gefensa ya yi wa motarsa key Danfulani ya bude masa get ya murza kan motarsa ya nufi (office).
Barin Harira gidan maimakon ya kawo shakuwa kamar yadda Hajiya Maryam ta yi zato, sai ya kara lalata zaman gidan. Hafsat sai ta yi kwana biyu ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba. Da safe ya daina bi ta kan abincinta, da ma Harira ke cewa ta dauka ta bishi ta sanya mishi a mota, shi kuma ba ya musantawa in ta kawo ko in ta ce masa Ga breakfast yanzu kuwa da babu Harira ba ta da wannan kwarin gwiwar, shi ma ba ya nuna yana bukata, in ya fito zai hada tea ko coffee ya sha ya fice, ita kuma ta kama kanta sosai, ba ta yi masa shisshigi ta tsaya a matsayin da ya ajiye ta na mai yi masa gadin gida. Ya daina turo direbansa daukar abincin rana tun tafiyar Harira ko me ye dalili ba za ta iya cewa ba.
Da ya dawo karfe shida wanka yake yi ya shiga kicin ya kama girkinsa ya yi ta bare-barensa duk ya baba mata kicin ya tara mata kayan wanke-wanke. Tunda ta lura ya daina cin abincinta ta daina dafawa da shi, iya cikinta ta ke dafawa don duk ranar da ta ajiye masa na dare, a ganinta lokacin yana gida. To yadda ta ajiye shi haka za ta dawo ta samu abinta, ta dauka ta sa a firji washegari da safe ta yi steaming dinsa ta cinye don uwarta ba ta koya mata almubazzaranci da abinci ba, ko ta dumama ta mika wa maigadinsu.
Yana ganin abincinta wanda ya san don shi ta ajiye, amma tunda ta daina ce masa ga abinci zai tsallake shi ya yi abinsa. Girki ba bakonsa ba ne, don kuwa shi ya raini kansa ba wani ne ya raine shi ba.
Da ya gama ya zai zauna a dining din kicin din ya ci abinsa don ba ta wasa da tsaftar madafin nasu. Yana gamawa zai shige daki ya hau aiki, in kuma ba ta a falon to zai yi zamansa ne a nan ya baje takardunsa da systems dinsa ya yi aikinsa. Shi kadai ya san yaushe yake shiga daki ya kwanta.
Hafsat ba ta kara shiga shirginsa, wanka ta ke yi ta dauro alwala ta gurfana a side din da ta ware ta yi shimfida cikin dakin ya zama muhallin ibadarta, ta gurfana gaban mahaliccinta tana kai masa bukatunta.
****
Haka kwanakin ke mirgina musu har tsayin watanni ukku, rayuwar tasu ba wani abu mai dadi da za a dorar, connection dinsa da Muazatu ya yi rauni saboda ta samu tafiya (Law School) a jihar Adamawa (Yola) dole ta maida kai ta ajiye soyayyar a gefe, shi ma cikin lokacin nan fama yake da cases iri-iri masu zafi saboda a hankali fasaharsa da kwarewarsa a kan aikinsa ke fitowa sarari. Ya shiga sahun lauyoyi yan gaban-goshin gwamnati wadanda ake damkawa duk wani case na marassa galihu, (private individuals) sun fara son janye Abduazeez Dakata, amma ya tsaya a raayinsa na kasancewa lauyan gwamnatin tarayya mai rajin kare hakkin yan kasa. Wanda babban burinsa a gaba shi ne, barin Bar zuwa Bench. Wato daga lauya zuwa mai shariah (justice).
Yau yana zaune a office wata abokiyar aikinsa Barrister Surayyah Tanko ta isko shi rike da wasu files a hannunta. Tana zuwa ta dire masa su. Aiki yake yi, amma ya dago ya dube ta, Taimaka ka duba min su Barrister Abdulazeez ka gani ko akwai abin da ya kamata mu kara ni da Adebayo. Zan je (Jamb Office) na dawo yanzu, zan sayo wa Suhaima jamb form, saura kwana uku a rufe. In aka rufe kuma sai wata shekarar.
Idonsa ya dan kafa mata, matar aure ce amma tana son shiga shaaninsa da yawa bai san dalili ba. Sai kuma ya ji kamar ta yi masa tuni game da wani nauyi da ke kansa.
Hafsat!. Sunan ya fado masa a rai (with a low tune).
Surayyah ta gyara tsayuwa ganin sai kallonta yake yi, amma in ka dubi tsakiyar idonsa za ka lura ba ita yake kallo ba, tunani yake yi. Ta kada masa yatsunta a fuska, ya dauke kai daga kallonta ya mayar bisa (computer).
Tunanin me ka ke ta yi haka Barrister ina ta magana ba ka jina?
Ina jinki.
To amma ka yi shiru?
Ki yi hakuri ba zan iya duba miki files din nan ba, amma zan bai wa Abdallah. Ni ma in zan samu mai rage min nawa ayyukan zan so.
Surayyah ta dan bata rai, Ka ce dai kana tunanin budurwarka, amma ba ka da ayyuka da yawa, tunda jiya ku ka gama shariar da ka ke yi.
Murmushi ya yi har dimple dinsa ya lotsa gashin saman idonsa ya kwanta sosai a kan lumsassun idanunsa. Ba tare da ya dube ta ba, hannunsa a kan (system) dinsa ya ce, Budurwa kuma? Ai an dade da wuce wurin Surayyah. Im married. Sai bayan ya fada zuciyarsa ta jefo masa tambaya.
Are you really married?
Ya girgiza kai da sauri, a fili ya ce.
No, not really.
Ita dai Barrister Surayyah ta saki ido da baki da kunne duka tana kallonsa tana saurarensa, shaidaniyar zuciyarta na kara kawata mata shi ta kowacce fuska, shikadai ke burgeta duk fadin kotun, akan sa mantawa take ita matar aure ce, ba ta ma fahimci me yake fada ba. Ya kashe system din ya dube ta.
Ki wuce gaba a motarki zan bi ki a baya, sai dai bana gudu a titi ni kada ki bace mini. Ni ma zan sayi Jamb form.
To mu yi amfani da mota ta mana?
Haram, in shiga motar matar mutane.
Ni zan shiga taka.
Allah ya kiyashe ni daukar mace a gaban mota ba Muazatu ba.
Sosai abin da ya fada din ya yi mata ciwo, ta ce. Ai sai ka tafi kai kadai, ni ban iya tafiya a hankali ba.
Ta juya, ya bi bayanta yana fadin, Ga shi kuma bana niyyar yin abu in fasa.
Ta zumburo baki suka fice tare, kowa ya shiga tasa motar a haka suka tafi. Da gayya Surayyah ke sharara gudu shi kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen binta, har suka isa. Suka nemi wuri suka yi parking ita ta shige gaba suka sayi forms din, babbar yarta ta sayawa, shi kuma ya saya da sunan Hafsat Hamza Atiku Dakata.
A hanyarsu ta dawowa ya yi mata signal ya dauke kan motarsa ya nufi gida, bai koma (office) ba duk da lokacin tashinsa bai yi ba. Yana so ya cike mata da sauri tunda ya ji cewa babu isasshen lokaci.
Yaushe rabon duniya da ayyaraye!
Suhaana ta ce a ranta, lokacin da ta tsinkayi muryar mijinta Abdulazeez na yi mata sallama a kofar kicin, ta bada baya tana soya miya a kan gass wadda za ta sanya a firji ta yi mata kwana biyu tana amfani da ita, don kayan abincin da ke cike da firji da freezer da nama da kifi duk sun kamo hanyar karewa, girke-girken da ta saba dole ta hakura ta koma cin fara da miya. Su kansu kayan miyar daga wadannan da ta ke soyawa babu wasu, cancana abinta za ta yi tunda ba ta san ina za ta nemo wasu ba. Kayan abinci kam suna nan a shake a buhunhuna da katon-katon ta san har gaba da shekara ba za su kare ba.
Yau kwananta hudu ba ta sanya Abdulazeez a idonta ba, ta kan dai jiyo bare-barensa a kicin in ya dawo kafin magriba, lokacin kam ita ta kammala abin da ta ke yi ta shige daki don ta lura yana jin dadin yin aiki a falon in tana nan kuma sai ya kuke a daki, shi ya sa ta haramta wa kanta zaman falon don ya sake a gidansa.
Amma abin mamaki yau ga shi a gidan karfe hudu na yamma, wai yana yi mata sallama. Amsawa ta yi ciki-ciki ba tare da ta juyo ba. Sosai ta ke jin kiyayyarsa a ranta don ta lura bayan rashin so ba shi da imani ko kankani, ba shi da kirki, ba shi da adalci.
Wasu tawagar hawaye suka shimfido a kan kundukukinta, ba ta yi wani hobbasa na hana su zuba ko share su ba. Zubar tasu ne kawai zai sa ta ji sanyi a zuciyarta. Ko da ya ce za su yi AUREN KWANGILA, auren cin gashin kai ba ta zaci har da rashin sanin halin da junansu ke ciki ba, yanzu in mutuwa ta yi haka gawarta za ta rube ta lalace a daki sai ta fara doyi zai sani. In ciwo ta ke sai ya ci ya cinye ta zai sa ni.
Tun tana tunanin Mammah da mutanen gidansu, har ta hakura ta daina, ta yarda Mammah ta aurar da ita ga azzalumin danta ne don ta gaji da ita, ya kashe ta da bakin cikinsa duk su huta. Hawayen suka fara gudu suna sauka a kan kirjinta, hakoranta na karkarwa suna haduwa da junansu saboda kuka mai cin rai, amma ta sa hannu ta toshe bakinta ba ta son amon kukan nata ya fito fili.
Abdulazeez ransa ya so ya baci da yadda ta yi watsin Allah-tsine da shi a bakin kofa, ta kuma amsa sallamarsa kamar ba ta so. Sannan ta ki juyowa. Kwafa ya yi ya zuro jikinsa ya idasa shigowa cikin kicin din yana kallon abin da ta ke yi. A matsayinsa na wanda rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai miyansa ya tsinke da wannan hadaddiyar miyar wadda ta ji naman saniya zuku-zuku sai tashin kamshin spices da mushroom curryta ke yi. Ya hadiye miyau mukut! Ya bi ta da harara duk kuwa da ance aikin banza harara cikin duhu don kuwa bayanta kawai yake iya gani.
Sallama fa nake yi amma ki ka yi banza da ni?
Haushi ya ba ta sosai, kamar ta juyo ta dalla masa mari amma ina! Ko tsakiyar idanunsa ba za ta iya kalla ba balle mummunar magana ta hada su har akai ga abin da zuciyarta ke kissima mata.
Na amsa ai. Ta sake amsawa ciki-cikin. Cikin hadiye kukanta gabadaya. Kwafa ya sake yi ya juya ya fice yana fadin, In kin ga dama ki zo ki yi min bayani in cike form dinki ne na jamb.
Ai ba ta san lokacin da ta saki ludayin miyar a kasa ba ta biyo bayansa. Jin karar faduwar ludayin ne ya sa Abdulazeez ya juyo sai ganinta ya yi har ta kusa cimmasa, fuskarta jage-jage da hawaye. Wani abu mai kama da tausayi ya so ya tsirga masa, yana mamakin son karatu irin nata, wato fushi ta ke da shi sosai a kan laifin da bai sani ba, amma jin zancen jamb ta manta komai ta biyo shi har ta manta ta bar wuta a kunne.
Dakatawa ya yi, ta zo ta shige shi ta yi falo ya dawo ya kashe gass cooker din da kansa, ya rufe mata miyar sannan ya bar kicin din.
A falon ya same ta a tsaye, zama ya yi cikin (3 seater) ya jawo briefcase dinsa ya fito da scratch card din da receipt ya daga lumsassun idanunsa ya dube ta, Kawo takardunki, sai ki zauna mu cike.
Zan iya cikewa da kaina.
Kina da system ne?
Akwai tawa ta gida, amma babu internet connection.
Ga mamakinta sai ya tura mata jakar laptop dinsa.
Dauki wannan ki yi da ita, ki hanzarta ki gama zuwa gobe sun kusa rufewa.
Dauka ta yi ta matsa gabansa ta karbi scratch din da sauran takardun ta tsugunna a gabansa ta yi shiru. Tunanin me ya tsayar da ita yake yi, sai ji ya yi can a tsakar kansa tana fadin, Na gode sosai.
Ya bude idanunsa sosai a kanta daga lumshewar da suke yi da kansu, You dont need to thank me. Its part of our contract, kin manta ne?
Girgiza kai ta yi, a sanyaye ta ce, Ban manta ba, duk da haka na gode.
Sai ya kasa ba ta amsa ya bi ta da ido har ta mike ta shige daki dauke da system din cikin nutsuwa.
8SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ta dago ta dube shi kamar za ta ce, aah, ya tsare gida sosai. Ya sanya layin etisalat a ciki ya yi charging wayar sosai. Kamar yadda ta haddace karatun sallahr farillarta haka ta haddace lambobin uwarta da na Baba Azumi. Da sauri ta shigar da lambobin ta