Showing 27001 words to 30000 words out of 133189 words
Chapter 10 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete
dakin da sauri sai ta bi bayansa kamar zata yi kuka. Kareem ya sauka kasa ya karasa gurin da Noor take kwance cikin jini.
“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, Me kika aikata haka Yusura? Baki san me ya kawo yarinyar nan gidan nan ba, ban san halin da take ciki ba kawai ki kara mata da wannan?”
“Ta mutu ne?”
Yusura da ta kasa karasa saukowa ta tambaya cikin kuka. Kareem ya saka hannunsa ya cire Hijab din Noor ya taba wuyanta ya cire dankwalin kanta ya daure mata kan dake zubar da jini sannan ya tashi ta sauri ya haura sama ya dauko keys dinsa ya fita ya janyo motarsa ya kawo kusa da entrance din ya shiga falon ya dauko Noor da bata san inda take ba ya saka ta bayan motar ya shiga driver side ya ja motar sai asibiti.
Gado aka bata shi yayi mata duk wani treatment da ya kamata, ya saka mata drip sannan ya lalaba aljihunsa ya sai a lokacin ya tuna be zo da wayarsa ba.
“Oh nikan matan nan son hada min wuta...”
Ya fada yana kallonta.
“Me ma ya sake fito da ke Noor?”
Tambayarta yake kamar ance masa zata iya amsawa. Dakin ya fita be bar asibitin ba sai da ya tsabtace kansa sannan ya shiga motarsa ya koma gida. Yana shiga falon Yusura ta mike tsaye tana kallonsa.
“Tana raye?”
Wani mugun kallo ya watsa mata.
“Kusan wannan ne karo na biyu da kike kokarin illata yarinyar nan, wannan ya zama na karshe, wacan karon kamin ta yi aure ne har ina fada mata kawai dai an samu akasi ne, ba wai dan kishi ba, yanzu kuma ban san me ya zo kanki ba...”
Ta matsa kusa da shi.
“Yanzu din ma akasi ne, gobe da jibi din ma akasi ne matukar bata dauke kafarta daga gidan nan ba, kusancinta da kai yana kusanto maka da mutuwa ne kai da ita”
“Idan kika kasheta zai ba ni mamaki, domin baki da wani dalili na aikata hakan. Kashe ni ba zai bada mamaki ba, tun da na san ba ki so na, ko akwai abun da ya canja?”
“Babu Kareem babu, babu abun da zai canja har gaban abada...!!! Ko a mafarki bana fatan ko a lokacin da kake da natsuwa balle yanzu da kake bibiyar matan aure ciki har da matar amininka...”
Ta fada da karfi sannan ta juya, fisgota yayi ya dawo da ita.
“Babu wata alaka tsakanina da Noor, idan har zan kulla wata alaka makamanciyar wadda kike zargina da ita, to da zan aureta ne na aje ta a gidan nan under the same roof mu rayu har abada ni da ita, sai dai kuma babu irin wannan sha'awar tsakanina da ita”
“An fada min ai, kun yi soyayya sai kuma ka saka abokinka ya aureta deal ne?”
Sakinta yayi yana murmushi.
“Haba ke kuwa taya Kareem zai yi soyayya da wata yarinya, yana da damar aurenta kuma sai ya ki aurenta ya saka abokinsa ya aure ta? Daga baya kuma ya zo yana bibiyarta? Wane irin ƙidahumi ne ni? Ai da abun da aka fada miki ne ya faru to sai dai na aurota na kawo nan mu sha soyayya”
Abu ta hade da karfi ta juya ta haura sama ta barshi a gurin tsaye. Ta wani bangaren baya ganin laifin abun ta aikata domin gidanta suka shigo kuma neman mijinta, ta gurin da abun zai daure masa kai ace tana kishinsa domin abun da ake so ake kishi, shi kuma be saka ran samun haka daga gurin Yusura. Isakar bakinsa ya busar ya nufi dakinsa ya wayarsa ya dauka ya kira Hafiz.
“Hello...”
“Barrister kana gida?”
“Ina gida lafiya?”
“Zaka iya fita waje mu yi magana”
“Okay....”
Shiru na 2 minutes ne ya shiga tsakani kamin Hafiz ya amsa daga dayan bangaren.
“Ina jinka”
“Kun sake yin fada da Noor ne?”
“Daman ba fada muke ba, kawai dai na turata gidansu ne yau?”
“Saboda me?”
“Tana bukatar a koyar da ita zamantakewar aure Kareem, ba zan Boye maka ba na fara nadamar auren yarinyar nan!”
“Subhanallahi, to maybe wani abun ya faru a gidansu ko kuma bata tafi gidan ba, ta zo gidana by mistake Yusura ta fasa mata kai yanzu haka dai tana asibiti”
Hafiz yayi shiru kamar ba zai ce komai ba.
“Dan Allah kaje ka sameta kuma ko miye a tsakaninku ka yi hakuri mana Hafiz, hankalin Namiji baya zama daya da mace, kuma san halin mahaifin yarinyar yana daga cikin dalilin da ya saka ka aureta saboda ka tsamota daga kunci, to miyasa ba zaka jure ba kana lurar da ita har ta fahimta, ba mamaki mahaifinta korarta yayi ta rasa gurin zuwa ta zo nan, ni kuma ban ma sani ba sai fitowa na yi na samu Yusura ta yi mata aika aika, kuma kai ya kamata na kira domin responsibility dinta yana kanka as her husband don't misunderstand the issue please”
“Tana ina yanzu?”
“Tana asibitinmu, emergency room 44, please ka sassautawa yarinyar nan Hafiz duk yadda kake tunanin hankalinta be kai can ba, a yanayin yadda na fahimta ta tashi a wani yanayi ne na rashin dace da iyaye shi ne musabbabin komai, idan ka hada mata zafi iyayenta suka hada ma za ku iya sakawa ta kamu da depression domin bata da mai rarrashinta bata san gurin da zata tafi ta ji sanyi ba, ta yi kankanta ace ta fara samun matsalar aure tun a yanzu, and idan bata samu kwanciyar hankali a gidan ka ina zata samu? Already ta rabu da wanda take so, idan ta rabu da kai iyayenta za su iya juya mata baya, idan a gidanka bata jin sanyi kashe kanta kuke son ta yi? Kai da kanka ka ce za a iya koya mata son wani, to ka koya mata mana, ka nuna nata gurin da illar abu yake da sannu zata gyara”
Hafiz ya ki ce komai ba, sai wani cika zuciyarsa take duk abun da Kareem yake fada shi wani abun yake hangowa can dabam.
“Good Night”
Kareem ya kashe wayar ya jefar kan gado ya sauke dogon numfashi.
“Poor girl”
Ya furta, ya zauna bakin gadon yana jinjina kai.
NOOR POV.
“Good Morning...”
Na ji wata matar da ban taba arba da kalar fuskarta ba ta fada tana yi min murmushi. Yunkurin tashi na yi zaune sai ta rika ni na zauna na sake dubanta da idanuwa da ba su gama budewa ba.
“How are you feeling now?”
Na daga mata kai ina jin kamar an dora min wani dutse a gefen kaina saboda nauyin da yayi min. Hannu na kai na taba sai na ji an daure gurin, gefen wuyana ma an saka min wani abu a gurin sai ciwo yake min.
“Ya jikin na ki?”
“Da sauki”
Na amsa ina kallon dakin da ban san lokacin da aka kawo ni ba. Gashi babu kowa a kusa da ni sai wannan nurse din da ba musulma ba domin sakar cross ce a wuyanta sai gashin doki da ta dora. Ta taba jikina ya cire robar ruwan da be kare ba sannan ta yi rubutu akan files din dake hannunta tana min tambayoyi, sunana umguwata ina da aure ko babu sai kuma number wayar Mijina ko ta mahaifina, da alama dai sabon file take bude min a yanzu. Sai da ta gama sannan ta saka hannunta aljihu ta ciro wata takarda ta miko min.
“Ga wannan mijinki yace idan kika tashi a baki”
Na mika hannu na karba, a gabanta na fara warware takardar har na bude.
“A yau 2 ga watan 6 ni Hafiz Abdullahi na saki Matata Noor saki daya”
Shi ne a rubuce, gashi sunana da nasa ne a rubuce balle na ce kuskuren fahimta aka yi aka ba ni abin da ba nawa ba.
“Wayyo Allah.. Na shiga uku na lalace, wayyo ni Allah me yasa Hafiz zai sake ni yanzu na shiga uku, yanzu ina zan je? Wayyo Allah... Baba kashe ni zai yi, yanzu korata za su yi, na shiga uku”
Na kalli matar ina kuka mai taba zuciya.
“Dan Allah ki kira min shi”
“Ya riga ya tafi, but bari na kira Doc abokinsa ne ai sosai”
Ta fita dakin, sai na sauko daga kan gadon i don't even care about the pain haka na zube kasa kaina ya sake buga da gadon asibitin ina wani irin kuka, domin na san karshena ya zo, matar bata dade ba ta dawo ta miko min waya.
“Ga Doctor zai yi magana da ke”
Na karbi wayar da sauri na kara a kunne na saka hannu na dafe.
“Noor sakinki yayi?”
“Ya sake ni Kareem, rayuwata ta kare Baba zai iya tsine min ma, ba za su fahimta ba, dan Allah ka taimaka min ka ba shi hakuri, ka ce yayi hakuri ya maida ni gidansa ya yafe min, ka ce masa zan zauna a haka ba zan sake kai kararsa wani gurin ba, Kareem ka ba shi hakuri dan Allah ya hakura ya maida ni...”
Ina maganar ina kara matse wayar a kunnena ji nake kamar yana tsaye a gabana ne na kama kafafuwansa na bashi hakuri, domin ni kadai na san halin da zan shiga a sakin nan da yayi min.
“Ba zan ba shi hakurin ba”
Ta cikin wayar Kareem ya daka min tsawa ya kashe wayar. Na kalli matar da bana iya ganin fuskarta a yanzu saboda hawaye ya tare ko'ina na idona.
“Ya kashe... Ya kashe... Sun ruguza min rayuwa, sun raba ni da mai so na tsakani da Allah mai kaunata mai fahimtata mai tausayina, yanzu kuma sun hada ni da mahaifina shikenan rayuwata ta kare wayyo Allah na ni Khadija, Allah ba ni da gata sai na ka...”
Nurse din ta dafa ni.
“I'm sorry... Please take heart”
Na kwanta jikinta ina kuka sosai kamar zan mutu, ni kadai na san waye mahaifina ni kadai na san halin da zan shiga. Da sauri na dago daga jikin matar mai sanyin hali na fara share hawaye, so nake na tafi na samu Hafiz a duk inda yake na ba shi hakuri ya maida ni gidansa...
#KhadeejaCandyPAID PAGE 1️⃣1️⃣
©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024
Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar
And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....
You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153
_______•••_______
KAREEM POV
Fuskarsa a hade yana tsaye gaban madubi yana kokarin saka agogonsa Yusura ta turo kofar dakin ta shigo. Be dago ya kalli kofar ba amman hakan be hana shi fahimtar ita dince ta shigo dakin ba. Tsayawa ta yi nesa da shi ita dai fuska babu annuri ta ce.
“Ina kwana?”
“Lafiya Kalau”
Ya amsa a taikaice sannan ya fuskanci madubin da kyau ya dauki turare ya fara fesawa.
“Ka ce zaka yi shawara, zaka duba lokacin da ya dace ka aiwatar da abun da zai bawa kowa yanci a tsakaninmu, har zuwa yaushe ne Kareem”
“Abokiyar shawarata wadda ta bani shawarar aurenki ko na ce umarni bata duniya, amman zan yi shawara da Daddy tukuna”
Ya danna abun da ta ji yana taso mata a zuciya.
“Har zuwa yaushe kenan? Tsawon shekarun da muka yi da kai ina numfashi ne cikin matsuwa, ina ta jiran ranar samun yanci”
Kwalbar turaren ya aje ya juyo ya kalleta.
“Na fiki shiga kangin na takura da kunci, da kin san matsalolin da aurenki ya janyo min wata kila, kin shiga daki kin rufe kanki kin yi kuka, Yusura na rasa natsuwata, na rasa farinciki, rayuwar da nake buri ko mafarkin yi aurenki ya ruguza ta, ba ke kadai ba ce a dakin damuwa, ni ma yancin nake nema, i deserved happiness too ba kullum bakin ciki ba, so please karki matsa komai a sannu yake zuwa, kuma zan fi jindadi idan kika daina shigowa dakina kamar yadda kike yi tun farkon zamanmu, bincikar kayana ko bibiyar rayuwata ba na ki ba ne. And ki daina biyo ni har daki da abinci, a dinning ma ya isa idan ina ra'ayi zan ci a can... Please excuse me... ”
Ya zagayeta ya fice daga dakin, binsa ta yi da kallon ita kadai ta san yadda take danne zuciyarta take rayuwa da a gidan, amman yau ya kalli idonta ya fada mata magana son ransa.
“You got to be kidding me... I'm doing all this saboda na sauke hakkina da Allah ya dora min, waya fada maka a cikin dadin rai ko neman kauna nake? I need space...”
Ita kadai take magana da kanta a lokacin da ya dade da fice daga dakin, so take ta kyautata masa kamin ta bar gidan, tun a wacan daren da Safeena ta zo gidan, wani bangare na zuciyarta ke raya mata wata kila saboda rashin samuwa kulawar da ya dace ne ya saka shi tunanin aron hannu ko kuma ma aron gaba daya, tana jin kamar idan ta mutu Allah zai tambaye ta ko da kuwa bayan ta bar gidan ne. But what happened yesterday ya canja tunaninta idan rashin samun kulawa ne ya kai shi ga kula Safeena a yadda take zargi, to ita wannan Noor din fa? Bayan abun da ta kama a aljihunsa wadda ta hango Noor din tana hannanta masa ga kuma abun da Aisha ta fada mata.
Now ta ji kamar ba zata iya tarar yakin ba, ba zata iya rumgumar wani dacin ba bayan wanda take ciki.
Takowa ta yi ta fito daga dakin ta shiga nata dakin, arba da ta yi da hoton yaranta biyu like a bango ya tsumata.
“Rabuwar ita kadaice mafita, ita kadai ce maslaha a gurina, nesanta da Kareem shi ne burin da na dade ina binnewa a zuciyata, dakun mutuwar Momy da nake a baya duk saboda samun yanci ne...”
Ya zauna kan gadonta tana kallon hoton hawaye na sauko mata.
“Yanci irin na ya mace mai burin auren wanda take so, yanci na rayuwa a karkashin inuwar wani namijin dabam da zuciyata zata yi na'am da shi ba Kareem ba, Wallahi kullum da wannan bakinciki nake kwana da shi nake tashi. Momy ta hada wuta da ruwa ne ba tare da tunani ba, bama haduwa da juna, ba mu dace da juna ba, dan Allah ku yafe mini”
Ta kwanta saman gadon tana hawaye, tana jin kaunar yayanta domin babu ruwansu a cikin matsalarsu, sai dai kuma Kiyayyar Kareem ta fi soyayyar yaransa karfi a zuciyarta.
*** *** ***
Tuki yake da hannu daya a lokacin da wayarsa ta yi ringing. Sai da ya kalli mai kiran sannan ya daga ya sakata a speaker.
“Hello”
“Doctor Ka fito gida?”
“Eh ya aka yi?”
“Wani dan abu na aikata”
“Na me?”
Barrister ya sauke ajiyar zuciya ta ciki wayar sannan ya ce.
“Na saki Noor..!! Na san ba abu ne mai dadi ba, but ina ganin kamar hakan zai fi zame mana mafita, saboda akwai abubuwanta da ban gamsu da su ba, kuma ina ganin kamar ba zata iya canjawa ba”
Doctor ya tabe baki ya kalli ne mirror sannan yayi overtake yana tabe baki.
“Okay.. Daman aure rai ne da shi, na wasu ya kan dade na wasu kuma be dade ba, Allah yasa hakan shi ne mafita alheri, ya baka zaman lafiya da matarka, ita kuma Allah ya bata wanda ya fika ya dace da ita..”
Hafiz yayi shiru ya kasa amsa da Ameen kuma ya kasa sake wani furucin, all what he expected Kareem ya fada hakan da ka yi ka yi daidai or no baka yi daidai ba. Sai dai kam be ji haka daga gurin abokin shawararsa ba. Kareem ya kashe wayar jin Hafiz be ce komai ba kuma be yanke kiran ba. Tuki yake cikin natsuwa har ya ratso cikin unguwarsu Noor, a gaban gidansu ya faka ya bude motar ya fito rike da wayarsa. Nabil ya kira yana dagawa ya ce.
“Ranka ya dade”
“Kana gida?”
“Eh ina gida ranka ya dade”
“Fito ina waje”
Before Kareem yayi blink Nabil ya fito ya fito da saurinsa. At that time ne Kareem ya daga kai yana kallon kofar gidanta data kone kana ganin gidan zaka san an yi gobara.
“Oga Allah yasa ba wani laifi na yi ba”
Kareem ya mika masa hannu da suna gaisawa amman Nabil ya ki ya karba saboda yana jin kamar kuskuren gaisawa da mai gidansa a lokacin da yake karkashinsa, shi kuma yake samansa sosai.
“Ka yi laifi zan biyo ka har gida? Me yasa kullum tunaninka ka yi laifi ne ko dai akwai laifin da kake min ne a restaurant ban sani ba?”
Nabil ya shafa kansa yana dariya.
“Aa Wallahi oga, na ga yanzu Noor bata nan balle ace ita ta janyo min wani abun a gurinka”
Kareem be biye mishi da maganar ba sai ya tambaye shi yaushe aka yi gobara a gidan.
“An yi sati uku yanzu”
“Subhanallahi, Allah maida alheri na zo gurin mahaifinku ne yana ciki?”
“Eh yana ciki kasan safiya ce yanzu, be isa fita ba”
“Good ka yi masa sallama, amman kamin nan me yasa kullum nake samunka a gida baka karatu ne?”
“Na fara kuma abun ya zo da dan nauyi sai na aje sai nan gaba kuma”
Nabil ya fada yana sosa kansa cike da kunya.
“Allah ya taimaka, sallamo shi”
“Ameen ranka ya dade”
Nabil ya juya ya shiga cikin gidan, nan ma babu jimawa Baba ya fito yana gyaran hula ganin Kareem ya saka shi washe hakora ya mika masa hannu biyu suka gaisa.
“Baraba da zuwa, baka shigo ba kake zaune a waje”
“Ba sai na shiga ba, magana ce kawai na zo da ita zamu iya yi a waje ma Baba”
“Toh Allah yasa dai lafiya”
“Lafiya Kalau, Irin na amsu lafiya ba irin na masu matsala ba, Baba na zo da magana ne mai nauyi kuma daci sai ka jure”
“Kar ka ji komai fada min ko minene kai tsaye”
Kareem ya sauke ajiyar zuciya.
“Baba jiya, ko kuma ma na ce kamin jiyan Noor ta samu matsala da mijinta wanda amini ne a gurina, kusan ma ni ne dalilin auren domin sanadina ya san ta ni kuma na san ta sanadin danka Nabil”
“Haka ne, ai ta zo nan na korata bana son sauraren komai daga gareta, domin na fahimce take takenta so take ta kashe auren, yaushe aka yi auren ma? Fisabillilahi, a yau ma nake da niyar tafiyar gidan shi