Showing 117001 words to 120000 words out of 133189 words

Chapter 40 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

524

nake hango abun da Momy take guje min, na gode Allah da ban aure ki ba”

“Kai ka fara cutar da ni, kai ka fara yaudara da sunan zaka aure ni alhalin kansan mahaifiyarka ba zata bari ba, ina ji ina gani ka aje ni ka auri wata, na yi duk yadda zan iya saboda na cire a zuciya na amman na kasa, bayan na samu mai aurena na yi aure kuma ka sake sabunta min kaunarka har ta kai bana iya gane komai sai naka, na yi sha'awar haihuwa da kai ne saboda ina sonka, amman yanzu na gane na yi babban kuskure domin yaudarata kake a kullum, gashi yanzu na haifi jininka kuma aurena zai lalace bata sigar da nake so ba”

Hawaye na mata zuba ta matsa kusa da shi.

“All my plan was wata rana zaka aureni, saboda ka saba min da kanka, bana da buri sai na zama da kai, bana jin dadin mu'amala da mijina sai kai, a hakan ka budewa wata zuciyarka ta shiga, kuma ka kwashe sirrina duka ka fada mata, gashi yanzu ta yake ni da shi, igiyar aurena haka ya rage ta katse”

Ta muna mishi tazarar dake tsakanin babban yatsanta da mai binsa a yayin da ta kusa hade su. Ta goge hancinta

“Ya dauki yaran duka ya auna jininsu kuma na san ya gani, amman be ce min komai ba ya koma Lagos, the next thing da zai biyo na sani saki ne da tozarci a cikin dangi”

Ta share hawayenta.

“Kanwarsa ta fada min ya fada musu ya Saki Noor amman be fada musu dalilin rabuwar ba, ta dawo gida ta haifi bakwaini, kuma be zo da rai ba, are you planning all this? It's because you love her more then me?”

“I didn't plan this, but yes i love her more then you, i love her so much”

“And think zan tsaya ina kallonku ku auri junanku ne, bayan kun gama lalata tawa rayuwar? Taya? Ka ci amanata Kareem”

Ya daka mata tsawa.

“Babu wanda ya lalata rayuwarki, ke kika lalata rayuwarki da kanki, kuma karki zargi kowa a nan”

“Anyway na zo na na gargade ka, kuma na fada maka, idan har Abdull ya sake ni to ni ce zan maye gurbin Yusura, na san kai ma ba zaka so mutuncinka ya zube ba, ba zaka so a san ka haihu da matar aure ba, kuma na zo na gargade ka ne, ka fadawa Noor ta fita daga rayuwarka, kuma ta yi taka tsantsan da nata rayuwar domin Wallahi ba zan bar wannan ba”

Tsakanin rufe bakinta da kai hannunsa a wuyanta ba za a oya fadar wanda ya riga wani ba, shaketa yayi sosai har sai da idanuwanta suka fito.

“You're hurting me Kareem you're hurting me”

Baya baya take yana binta.

“Karki, taba yarinyar da bata miki komai ba saboda ni, kin cutar da ni that's enough, you have no idea what she's going though, because of your stupid husband, and yanzu kuma ke ki ce zaki saka ta gaba, kuma duk a kaina, ya ishe ki haka”

Ta fara bugun hannunsa da karfinta jin da gaske kokarin kasheta yake, she's fighting for her life. Sai da wayarsa ta fara ringing sannan ya sake ta fuska a hade, ita kanta bata taba ganinsa cikin bacin rai irin na yau ba. Tari ta fara tana hakki kamin ta juya da sauri ta fice daga falon.
Wayarsa dake ringing ya nufa ya dauka number Yusura ce, for the first time take kiransa bayan rabuwarsu, be haddace number duka ba but ya rike karshen numberta tun a lokacin da take gidan.

“Hello”

“Sallamu Alaikum”

“Wa'alaikumussalam, Lafiya?”

“Tine ce bata da lafiya, tun shekaran jiya, an bata magani amman abun be yi ba, jikinta ya tsanani yanzu”

“Ganin nan zuwa”

Ya sauke wayar ya dauki wayoyin duka biyu ya nufi stairs keys dinsa ya dauko ya sauko ya fita daga falon. 30m ya isa family house dinsu be faka ko'ina ba sai a bangaren da Yusura take tare da kanensa da yaransa. A falo ya same su daga Yusura har Tine din da aka yi ma shimfida a falon. Tun da ya shigo Yusura take kallonsa har ya karaso falon da babu kowa sai yarsa da tsohuwar matarsa dake sanye da katon Hijab domin a yanzu shi din ba muharraminta ba ne.
Ya kai hannu ya taba jikin Tine sai ya ji shi da zafi sai dai ba sosai ba, domin bachi ma take.

“Me yake damunta?”

“Zazzabi ne kawai sai ciwon kai da take cewa ta yawan tari da ciwon ciki”

Ya saka hannayensa ya tallafota ya maidata jikinsa yana taba cikin nata, a nan ta bude ido ta kalleshi.

“Dady ka zo?”

“Eh baki da lafiya”

“Eh amman da sauki”

“Fada min abun da kike ji”

Ta nuna masa gun da ke mata ciwo ta fada masa.

“Okay zan siyo miki magani yanzu, idan baki ji sauki ba daga nan zuwa gobe sai mu auna ki mu gani kin ji?”

Ta daga mishi kai tana kwantar da kanta jikinsa.

“Dady i miss you i miss our home, yaushe zamu koma?”

Ya kama hannunta ya rike yana wasa da shi.

“Tine akwai abun da ya kamata ku sani, the thing is...”

“Yara ne ba za su fahimta ba”

Yusura ta tari numfashinsa sai ya daka mata tsawa.

“We have to make them understand...”

“Are you Okay?”

“I'm Not...”

Nan ma ya amsa mata a tsawace, Tine ta dago daga jikinsa ta kalleshi

“Dady why are you shouting?”

“Am... Uhm..”

Ya rasa me zai ce, sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume. Kamin ya kwantar da ita ya mike tsaye ya fice daga falon.




**** **** ****

Ta faka a harabar gidanta misalin karfe goma daidai na dare. Kanta ta jinginar a kujerar dake bayanta tana kuka.

“So cuta ne Allah ka cire min son bawan Allah nan, shi baya ganina ba ni ce a gabansa ba, ina kaunarsa amman baya gani”

Ta fada tana kuka sosai, ta bugi gambun motar.

“Ba zan kyale mutanen ba, taya za su lalata rayuwata su kuma su zauna a free? Ni na rayuwa a bakinciki shi kuma ya auri wacce yake so ya rayuwa cikin farinciki? Na san duk shi ya shirya wannan ai daman yana cire ciki, ta kashe aurenta ta fito yanzu ya aureta ko? Tun fa ya rabu da matarsa, bayan ni tawa rayuwar ta gama lalacewa, shiyasa ya fada mata sirrina, to ba ni kadai zai shafa ba har da kai Kareem, ganin yake idan yayi haka zai wanke kansa zai tsira ko? Okay zamu ga ni ai”

Ta bude motar ta fita sannan ta share hawayenta ta nufi cikin gidan cikin zafin zuciya tana taba wuyanta da dayan hannunta, dayan kuma yana rike da key din mota.“Lafiya Hajiya Lafiya?”

Ban kula mai gadin ba na dago da guduna na dawo cikin gidan na nufi jakata na bude na kira number wayarta. Na yi sa'a ta shiga kamin ta amsa har wani jiri nake ganin tsabar bugun da zuciyata yake yi. Ringing tayi ta katse bata daga ba, ina sake kira sai na ji wayar a kashe. Faduwa na yi zaune kan kujerar, ban san abun da zan yi ba, ban san ta ina zan fara nemanta ba. Ban san kowa cikin kawayenta ba. Hana bata da kawaye a garin nan sai yan makaranta kuma ban san waye zan fara bincika ba, ni ban ma san ina makarantarsu yake ba.

Takardar na dauka na saka a jakata na koma dakin na dauko babban akwatina na zuba iya kayan da nake iya gani na rufe na janyo akwati na fito ina kuka. Bana son na kira Mama na fada mata domin bana son su san abun da yake faruwa da Hana, musamman Baba da ba fahimta zai yi ba. Idan kuma na koma me zan fada musu? Miye silar mutuwar aurena? Kuma ina zan ce na bar Hana. Ban amsa tambaya ko daya da mai gadin date din yake min ba. Na mike hanya na fara tafiya ina hawaye har na isa babban titi na tari okada na fada masa tashar da zan hau motar Kano zai kai ni.

Ya charje ni dubu biyu daga unguwar da nake zuwa unguwar da ya kai na hau mota. Na taki sa'a na isar tashar a lokacin da ake neman mutum daya motar Kano ta tashi na mika duka kudin da nake da su na shiga motar na zauna bayan sun karbi information dina. Tafiyar ta min nisa sosai wata kila saboda mota na hau, domin ban tana zuwa ko dawowa a mota ba sai wannan karon, wata kila kuma saboda abubuwan da suka saka ni gaba ne. Dan carjin da ya rage min na siye ruwa da shi su nayi ta sha, har muka isa Kano.

Karfe shida muka sauka garin Kano, domin Tafiyar awa tara ne daga Kano to Lagos a babbar mota. Na fito motar aka cire min akwatina na karba na fara ja zuwa gate din tashar. Napep na shiga na fada masa kasuwar da zai ni, wato kasuwar yan waya.

“Dan Allah ka dan jira ni sako kawai zai karbo”

“Okay amman Karki dade”

“Ba zan dade ba”

Na bar akwatina a ciki na shiga cikin kasuwar a lokacin da wasu suke ta hada hadar tashi saboda yamma ta yi. Wani shagon na nufa na nuna masa wayar hannuna.

“Malam kuna siyen irin wannan wayar?”

Ya kalleni irin duban nan na rashin yarda. Sannan ya karbi wayar ya duba waje da ciki.

“Wayar waye?”

“Tawa ce siyarwa zan yi”

“Saboda me zaki siyar?”

“Ina cikin matsalane ina bukatar kudi”

“Ina receipt da kwalin wayar”

“Suna gida”

“To kije ki dauko waya a hannuna haka ai ta sata ce”

“Wallahi tawa ce, ka duba ciki akwai hotuna na a ciki, kawai ina cikin matsala ne ina bukatar kudi”

Na fada hawaye na jika fuskata. Dayan dake gefensa ya taso ya karbi wayar ya duba.

“Nawa zaki siyar”

“Ni ban san kudinta ba ku siya kawai”

“Iphone 14pro max mu baki 305k kin ga ta dan ji jiki”

Na zaro ido ashe babbar waya nake riko ban sani ba. A zatona wayar ba zata wuce 50k ba idan ma ta yi tsada.

“Ka dai kara, dan Allah matsala ce ta saka zan siyar Wallahi”

Sai ya miko min wayar.

“Ba zan iya siyenta fiye da haka ba, siyen waya haka ma ai it's risk kawai dan na ga kina cikin damuwa ne zan siya, kin ga ma yanzu tashi zamu yi”

“To kawo kudi”

Ya cire min layina ya miko min sannan ya kirgo kudin ya miko min ba tare da na kirga ba na karba ina masa godiya. Na fito da sauri na samu mai napep din nan a inda na bar shi ina shiga ciki ya rufe ni da fada wai na bar shi yana ta jira.

“Yi hakuri”

“Ina zan kaiki?”

“Hotel”

Na fada kai tsaye domin kudirin da ya saka na siyar da wayar kenan domin babu sauran kudi a hannuna.

“Wace hotel”

“Ko wace ma wacce dai mutane ba su cika yawan cikawa ba”

Ya fara lissafa min sunayen hotel yana tambayar wacce za zai kai ni. Zuciyata kuma taya raya me kamata na tafi can ba, gida ya kamata na tafi, amman idan na tafi gida me zan fada.

“Kai ni ko wace ma”

“Okay”

Na share hawaye ina jin bakinciki a zuciyata, yau ga ni a garin Kano amman ba damar tafiya gidanmu. Ina yar'uwata take a wane hali take yanzu? Me ye makomar cikin dake jikinta? Me yasa ban saurareta ba wata kila da bata gudu ba. Ya sauke ni a gaban wata katafariyar hotel mai girma da haske ko'ina.

“Mu shiga ciki ko na sauke ki a nan?”

“Nan ma ya isa”

Na fito na dauko akwaiti na bude jakata na dauko 3k cikin kudin wayar na mika masa, sai ya karba yana min godiya. Na juya na hotel din sai kuma na ji bana ra'ayin shiga ciki. Dan haka na tari wata Napep din na shiga domin aiwatar da kudirina.
A kofar gidan Kareem mai napep din ya sauke ni, na sallame shi na nufi flowers din da suke gefen gidan na daga akwaitina na jefa a ciki sannan na nufi gate din. Na kwankwasa na san by that time yana gida ko hanyar gida, domin muna hanya aka yi sallah Magariba.
Mai gadin ya bude ya leko.

“Mai gidan yana nan?”

Ina magana numfashi daker domin karfina ya gama karewa ga bakina ya bushe, har lokacin kuma ban ji ina sha'awar komai ba duk da kasancewar ina jin yunwa.

“Eh yana nan”

“Dan Allah ka ce mishi yana da bako a waje dan Allah ya fito abu ne mai muhimmanci”

“Wa zan ce masa?”

“Kawai ka fadi haka dai”

“Tohm”

Ya juya ya koma ya rufe gate din. Ni kuma na kai hannuna na dafa ginin ina jin zuciyata kamar zata fashe. Tun a lagos na kudurtawa zuciyata zuwa na fada masa damuwa ba, da na yi nufin na fara sauka hotel ne washe gari na je na same shi a restaurant ko asibitinsa na fada masa, amman burin ceton yar'uwata ya saka na ji kamar idan ta kai gobe zan iya rasa rayuwarta. Na kwashe minti talatin tsaye a gurin sannan ya sake bude gate din.

“Yace a shigo da bakon”

Na cira kafa na shiga cikin gidan na fara takawa sai na hango shi tsaye a entrance yana kallona har na karaso. Ya kalli daga kasa har zuwa sama.

“Noor”

Na kalleshi ba tare da na amsa ba.

“Minene kuma wannan karon?”

“Kareem na san ina damunka ina shiga rayuwarka da yawa, amman dan Allah karka ce min aa na maka alkawari daga wannan ba za sake ba, dan Allah ka taimaka min dan girman Allah”

Na kai kasa ina rokonsa sai kallona yake ya kasa cewa komai. Na nufo shi ne saboda ina jin yana karfi na dukiya wata kila har da hanyar da zai taimaka min.

“Shigo ciki”

Ya juya.

“Matarka za....”

“Bata nan”

Na mike tsaye na bi bayansa na shiga cikin falon sai na zauna a kujera shi ma ya zauna nesa da ni yana kallona.

“Me ya faru?”

Na bude jakata na dauko takardar sakin zan tashi na kai masa sai ya taso ya karba ya zauna a dayar kujerar dake kusa da tawa. Yana gama karanta takardar ya kalleni

“Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Saki Noor mi ya faru?”

Na ciro dayar takardar da Hana ta aje min na mika masa ina hawaye. Ya karba ya fara karantawa mikewa yayi tsaye ya girgiza kai ya runtse ido, can kuma ya bude idon ya kalleni.

“Da gaske?”

Na daga mishi kai har sau uku, ya koma ya zauna na dafe kansa.

“Ko da yaushe idan ina cikin damuwa, na kan zo gareka saboda ina samun mafita kuma kana taimaka min, dan Allah ka taimaka min ta dawo, bana son Mama ta sani ko Baba domin idan Baba ya ji zai Fadawa Umma ita kuma zata yada a cikin unguwa, Mama kuma idan ta ji wata kila ba zata iya hakuri zata janyo mutuwar aurenta, bana son daya daga ciki ya faru?”

“Na ji zan taimaka miki amman dole ne iyayenki su sani Noor, me zaki fada musu a mutuwar aurenki? Kuma yanzu kamin a gano yar'uwarki me zaki fada? And idan ma an ganta amman ba a cikin hali mai kyau ba dole za su ji ba zaki iya boye wannan ba, yanzu idan kin tafi gida me zaki fada?”

“Ba gida zan tafi ba Hotel zan zauna, har sai an gane Hana sai mu tafi gida tare, na Fadawa Baba kawai mun yi fada ne ya sake ni”

“Noor yanzu kurciyata tana damunki, matsala irin wannan iyaye kadai suke iya tsayawa mutum, dole ne ki fada musu gaskiya, gidan ba zaki iya Fadawa Baba ba, to ki fadawa Mahaifiyarki, kaddara ce babu wanda ya wuce kaddara”

“Kaddarar ita ce kullum a biye da ni, aure na biyu kenan ina yi babu dadi, gashi yanzu har na janyo Hana ta gudu ta shiga duniya”

Na fada ina kuka. Mikewa yayi tsaye ya haura sama ya bar ni a falon ina ta kuka ni kadai gaba daya ma duniyar ta isheni. Be dade ba ya sauko da waya a kunnensa.

“Yeah let me ask her”

Ya kalleni.

“Ina kika saka ran zata tafi?”

“Ni da ita ba mu san kowa a Lagos ba, ban san inda zata tafi ba, bata da kawaye sai yan karantarsu ban san gurin waye zata tafi ba”

“Wai bata san kowa a lagos ba”

Can kuma na ji ya amsa da

“Okay Thank you”

Ya zauna sannan ya amsa kiran da ya shigo.

“Aaryam na kira baka daga ba”

Ya kalli agogo.

“Okay, daman wani taimako nake so dan Allah, wata yarinya ce ta gudu a Lagos nale son a nemo ta, na san kana da friends yan Lagos sosai maybe you can help”

Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya turo kofar, bana jin komai da yake fada har sai da ya gama wayar ya dawo ya zauna.

“Ina wayarki dole sai an tura hotonta”

“Na siyar na siyar da ita yanzu, suka ba ni 305”

“Wayar?”

“Eh”

“Saboda me?”

“Ba ni da kudi ne, kudin sun kare a hawan mota, shi ne na siyar da wayar saboda na yi amfani da kudin, irin wayarka ne”

Ya kalli wayar ya kalleni.

“15 pro max suka baki 305k?”

“Aa taka ta tsufe tawa da shekara daya, tawa 14pro max ce”

Na ciro kudin na zube duka a gurin.

“Wane barayo ya siye wayar?”

“Ba barawo ba ne shago ne”

“Saboda kawai sun ga baki san kan waya ba sai su siye a 305k? Dole sai an nemo hotonta da Yanzu ina layinki yake? Dole sai an nemo hotonta da sunan makaranta su”

Na yi shiru ina tunanin gurin da zamu hotonta domin ban zan tafi gida babu ita ba.

“A dp dinta na whatsapp akwai hotonta kuma sunan makarantar su Victory College Of Health”

“Yanzu ina line ki?”

Na saka hannu jaka na dauko layi na mika masa, sai ya karba ya haura sama sai gashi ya sauko rike da wata wayar touching amman ba iPhone ba. Ya saka line da na bashi ya dade yana taba wayar ban sa me yake dubawa ba kamin ya miko min wayar.

“Saka number ta”

Na karba sakon karta kwane ya rubuta a messager wayar.

“Dan Allah Hana ki dawo, tafiyarki ta haifar min da matsaloli da yawa, na bar Lagos na dawo Kano, amman na kasa tafiya gidanmu saboda ban san me zan fada musu ba, bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login