Showing 84001 words to 87000 words out of 133189 words
Chapter 29 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete
jin nawa, sai dai a yadda Abdull ya fada min yawancinsu suna jin turanci, duk da haka dai be amince min na leka gidan kowa ba kullum ina ciki gida kamar kifin gwangwani.
Ta wani bangaren kuma ai yana da gaskiya zaman aure na zo ba yawo ba, a yanzu kuma bana bukatar duk wani abu da zai daga hankalin mijina ko rayuwar aurena. A haka na cije na daure na yi zaman da ban tsammaci zan iya ba, a garin da ba ni da kowa sai Allah, sai mijina wanda nake gani a matsayin farincikina a yanzu.
Sai da na cika wata uku da sati biyu cif sannan ya yi min izinin tafiya gida domin duba yan'uwa da yan'uwansa. A tare da shi muka tafi ba saboda yanayin aikinsa ba su ba shi izinin tafiya, kuma na lura kamar baya son zuwan ma, zaman garin ya fi masa fadi fiye da Kano a yanzu.
Ticket din jirgi ya siya min daga Lagos to Kano, da kansa ya kai ni Airport ya tsaya har sai da jirginmu ya tashi, ina sauka na kira shi na fada masa sai ya turo kanensa ya dauke ni, gidan Safeena aka fara kai ni, wanda zan iya kira da gidan mijinmu a yanzu. Daman ya fada min gidan yake son na fara sauka saboda mu san juna ni da ita.
Abun da ya kamata yayi tun kamin mu bar garin be yi ba sai a yanzu. Gida ne mai fadi sosai bangare daya ne a gidan dayan bangaren kuma zallar fili ne da ba a gida komai ba, da alama a nan zai min nawa bangaren idan mun tashi dawowa garin gaba daya.
Kanensa ya wuce gaba ya shiga da sallama sai ta amsa masa da karfinta da far'ata.
Ina rangada tawa sallamar sai murmushin dake fuskarta ya gushe, waya sani ko be fada mata zan biyo ba, wata kila bata san da zuwan nawa a gidanta ba. Ko ma dai minene oho mata ni ma dai gidan nawa mijin ne bata fi ni iko da gidan ba.
Ban jira ta min izini ba na zauna ina kallon falon da aka kawata yayi kyau sosai kamar na sabuwar amarya, hotunan Abdull da yaransa ne suka yi ma falon ado, domin frame ne babba mai wadatar da mai kallonsa. Na fi maida hankali gurin hoton karamin danta da yake kama da Kareem, kuma yake kama da ita, shi kadai ya fita dabam da sauran yan'uwansa dukansu bakake ne kamar mahaifinsu, sai dai farinsa ba mamaki ba ne domin ita ma fara ce.
“Duk suna makaranta, Abulkhari kuma bachi yake”
Ta amsawa kanenta dake tambayar ina yara. Kamar dai yaron ya ji me ake fada sai ya fara ihu, ta tashi da sauri ta shiga wani daki dake fuskantar dayan ta dauko shi ta fito. Yaro ne dan wata biyar da kwanaki fari sol kamar dai ita, ta zauna a kujera tana rarrashinsa. Sosai nake ganin kamarsa da Kareem, wata kila dai saboda na san alakar da ta taba shiga tsakaninsu ne zuciya yake raya min abun da be dace ba kuma bana fatan ya faru.
“Amarya ya angon na ki?”
Na dago daga tsananin kallon da nake yi ma danta na kalleta.
“Lafiya kalau muke, ya muka same ku?”
“Muna cikin aminci da kwanciyar hankali”
Ta amsa min fuska babu annuri tana min kallon biri ina mata kallon bishiyar hawa.
“Dawood a kawo maka abinci?”
Ta tambaye shi kadai ba tare da ni ba.
“Aa ni wuce zan yi sai dai kanwarki idan zata ci”
“Kanwata tana gidanmu tana taya iyayena aiki, kanwata ai ba zata aure min miji ba, kuma ta ne mi daga min hankali”
“Idan har ni na daga miki hankali, to daman can cikin tashin hankalin kike na abun da yake boye a zuciyarki, ni kan aurena sai dai ya haifar muku da kwanciyar hankali ke da mijinki”
Na bata amsa daidai da furucinta. Dawood ya mike tsaye
“Miye wannan abun dan Allah? Ku da za ku hada kai ku kwantar masa da hankali, cewa fa yayi na kawo ta ku gaisa miye na wasu kananan magana dan Allah? Haba”
“Har a bada ba zan hada kai da macijiya ba, ki sare ni a gaba ki sare ni a baya kuma ki yi sammanin hada kai da ni, ai kin yi shuka ne a idon makurwa, shi dai da ya ji zai iya da yaje can yayi ta yi, ma san abun da maza suke gani a jikinki da suke rawar jiki, abu kamar daurawa muciya zane”
Na yi murmushi kai kace ban ji zafin maganar da ta jefa min ba.
“Abun da baki da shi, shi suke hangowa”
Sannan na mike tsaye ina tabe baki.
“Ni ba fada ya kawo ni ba, mijina yace na biyo na gaishe da matar kuma na cika umarni, kin san ni ban iya cin amanar miji, Malama kin ga tafiyata”
Har na juya sai kuma na juyo na kalli yaron dake hannunta.
“Allah ya yara abulkhari yayi masa albarka, sauran yaran kuma idan sun dawo a ce new Momynsu tana gaishe su”
Ta aje yaron ta mike tsaye a lokacin da Dawoo ya kai kofa ya bude min yana fadin na zo mu wuce.
“Karya kike yi Wallahi har gobe yarana ba su da wata uwar sai Safeena, wato ku yan matan zamani yan matan titi da suka gama ganin duniya aka gama da su, shi ne kike son shigowa cikin gidana ki mallake gidan ko? To kin yi kadan”
Na yi murmushi mai sauti.
“Ashe dai kina son mijinki, to ki tana a hannu karki nemi daga min hankali domin kilu zata iya kan bau. And for your own information ni ba malleke gidan nake son yi ba, nawa ginin nake ginawa sabo fillll”
Zancen kilu ta ja bau ya saka ta saranda, bata sake yunkurin furta wani abu ba har na bar falon, a mota kanensa yake ta yi min nasiha wai sai na yi hakuri kishi ne yake damunta har yanzu, ya san halin matar yayanshi da tsananin kishi.
Har muka isa gidanmu ban daina jin zafin magangunta ba, musamman da tace min kamar an daurawa muciya zane.
#KhadeejaCandyhttps://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0
Can cikin bachi na ji ya taba an taba ni, hakan ya saka ni bude ido sai na ga wutar dakin a kunne.
“Taso mu yi magana”
Ya riko ni na tashi zaune ina sanye da kayan bachi wando ne da ya tsaya oya cinyata dai karamar riga marar hannu. Shi kuma yana sanye da pajamas dark green.
“Me ya faru?”
Na murza ido. Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannuna ya rike.
“Noor ina son ki fahimce ni please, ba wai bana son haihuwa ba ne kawa...”
“Indai maganar zubar da ciki ne, zai fi maka kyau ka tafi ka kwanta, ba zan zubar ba Abdull”
Ya kara sassauta muryarsa alamar rarrashi.
“Baki gane ba, ni gani nake ma kamar ba zaki iya haihuwa ba, kalli kunkurunki ma fa, karami ne sosai kuma be kamata ki fara haihuwa da kurciyarki kamar haka ba, Safeena ma sai da muka yi shekara biyu tukuna ta fara haihuwa...”
“Babu wasu kalamai da zaka iya daure ni da su Abdull, ni dai kawai abun da zan roke ka ka aje sirrin nan a tsakaninmu, bana son yar'uwata ta san mijina ya juya min baya, kuma bana son ta san baka son abun da zan haifa, mu kwana lafiya”
Na juya na kwanta na ja bargo na lulluba har kaina. Kwafa na ji yayi ya tashi ya fice ba tare da ya kashe min wutar dakin da ya tarar a kashe ba. Tashi na yi zaune na ina hawaye. Daren be mini dadi ba saboda haka ban runsa ba. Sai bayan na gama sallah na kishingida jikin gadon dake dakin sannan bachi ya dauke ni kadan, domin ban dade ba na farka saboda kiran da yake ta kwala min kamar zai tashi gidan.
Na zabura na fito falon ina kallonsa.
“Karfe Nawa ace baki hada abun karyawa ba? Ko salon na yi magana ki ce layi kike ke ga mai ciki”
“Zan shiga na hada yanzu”
Ita ce amsar da na bashi sannan na cire hijabina na aje akan kujera na shiga kitchen na fara dora ruwan zafi, ina tsaka da soya kwai amai ya taso min domin bana son karnin kwai a yanzu. Da gudu na fito na shiga bandaki na yi amai na wanke bakina da hannuna da fuska sannan na fito na shiga ba da aikina. Sai da na gama hada masa komai na kawo a dinning na aje sannan na koma kitchen din na gyara shi.
Na fito cike da gajiya sai na ganshi da shirinsa na fita. Kallon mamaki na yi masa kamin na yi magana ya ce.
“Ba zan iya cin wannan breakfast din na kazanta ba, sai ki zauna ki ci”
Wani bakincikin ne na ji ya ratsani, yanzu ya san ba zai ci ba kuma ya saka na girka? Ai ya sani dole zan yi amai me yasa be girka da kansa ba? Da kallo na bishi har sai da ya kai kofa sannan ya juyo ya kalleni ya ga har lokacin kallonsa nake na ma kasa motsawa daga inda nake tsaye.
“Barakallah Maa Shaa Allah, babu abun da zaki iya yi da ni, idonki ko mugun nufinki a zuciya ba zai min komai ba, na sha tabara na sha yasin nan gani nan bari Abdullahi kam, duk wani nufin da kike da shi akaina sai dai ya koma kanki lafiya zan tafi lafiya zan dawo kuma lafiya zan cigaba da rayuwata”
Ban san lokacin da hawaye ya zubo daga idona ba. Shi kuma ya bude kofar ya fita ya bar ni rumgume da bakinciki. A gurin na zauna ina tambayar rayuwa me yasa take min haka? Ina tunanin kamar na dace sai kuma wannan ya bullo min? Kamar an karfafa min guiwa haka na ji sai na mike ina fadawa kaina cewar zan iya jure wannan ma kara bakincikin gidan miji da wanda zan fuskanta a gidanmu ko unguwarmu.
Dakina na shiga ina gyarawa ina mamakin wai haka Safeena take rayuwa da shi idan yana kusa da ita ko kuma dai ni yake yi ma haka saboda baya son haihuwa? Wata kila shiyasa take son Kareem sosai take ta rufe ido tana aikata abun da zuciyarta take so. Waya sani ko ita ma bata jindadin zama da shi.
Na yi zaton shi zai aika mata da kudin mota ko ya siya mata ticket din jirgi ta zo ta jirgi amman be yi ko daya ba. Dan kudin da nake samun gunsa ne lokacin da yake so na na hada na bawa Mai gadi ya saka mata a pos ta account din mai pos din unguwarmu. Sannan na fada mata ta rubuta number wayata a takardar saboda idan ta iso ta ari wayar wani ta kira sai a na fada mata inda za a kawo ta.
Sanin dakuna biyu ne a gidan ya saka na kwshe kayan Abdull da suke dayan dakin na dawo da su dakina kamar yadda suke a da, domin ba zan kwana da ita a dakina ba shi kuma ya kwana a daki daya dabam, hakan ma be dace ba, kuma zata iya fahimtar kamar ba ma zaman lafiya tsakaninmu.
Ana gobe zata taso sai gashi ta kira ni da bakuwar number ta fada min karamar waya ce Mama ta bata tare da layi a ciki, kuma ta kara mata wani kudin da zata rike saboda expensive na hanya. Na jidadi sosai hakan zai taimaka mu rika communication kamin ta iso. Washe gari misalin 6am na kirata domin ta fada min tun asuba zata tafi ta sha. Duk bayan awa daya sai na kira ta fada min yanzu suna guri kaza da haka dai har suka sauka Lagos.
Na fada mata sunan unguwarmu ta tari okada ta hau, a nan sai da aka kara bata lokaci saboda yamma ta yi, akwai cinkoson mutane sosai. Ina jin an taba gate na fito daga falon da sauri na, a lokacin da muka hango juna ni da ita sai murna ta bare na je gurinta a guje ita ma ta yo kaina a guje ta bar jakar kayanta a gurin tana murna. Tsalle nake ina direwa tsabar murna da jindadi na ga yar'uwata, domin na san abubuwa za su zo min da sauki.
Mai gadinmu ne ya riko jakarta ya shigo da ita cikin falo, sannan mu ma muka shiga ina tambayarta ina Mama ina Baba. Sai da ta huta na kawo mata indomie da na dafa ta ci sannan take ba ni labarin yadda aka yi ta rigima kamin Umma ta amince mata ta zo saboda ganin take idan Hana ta zo sana'ar da take zata gurgunta babu mai fitar mata da awara.
Abdull be dawo gidan ba sai misalin 10 na dare, ina zaune falo ina kallo ya shigo fuska babu annuri, a lokacin Hana ta yi bachi a dakin da na nuna mata zata rika kwana.
“Sannu da zuwa”
Yayi kamar be ji ba ya nufi dakin.
“Hana tana ciki na maida kayanka a dakina tare zamu rika kwana har sai ta tafi”
Ya juyo ya kalleni.
“Saboda kin raina ni ko saboda me? Vabu sanarwa babu komai zaki kwashe kayana ki kai can, kuma ki aje ta nan?”
“Amman dai ai ba falo zata kwana ba? Kuma zai yiyu na kwana da ita daki daya ba alhalin kana mijina, na fada maka bana son kowa ya san zaman da muke yi, amman idan haka ya bata maka rai ka yi hakuri”
Guntun tsaki yaja ya wuce dakina ba dan ransa ya so ba.
“Allah ka ga halin da nake ciki, Allah ka shirya min mijina ka karkato da shi ya fuskance ni”
Na yi addu'a na shafa sannan na mike tsaye na bi bayansa. Washe gari ma be ci abun da na girka na breakfast ba saboda ni na girka, Hana tana daki tana ta bachin gajiya bata farka ba sai 11am a lokacin Abdull ya dade da barin gidan. Tsintsiyar dake hannuna ta karba.
“Kawo na share miki ba dan halinki ba”
Na kai mata dudu a baya daman ta fini naman jiki, ni babu komai a jikina sai kashi ba kamar ita ba da take da cikar gaba da jiki, wasu har cewa suke ma ni ce kanwa ita ce Yaya. Ta share gidan tass ta gyara ko'ina sannan ta dora mana girkin rana bayan ta gama cin nata breakfast din. A nan ma mun sha hira har Mama ta kira a waya muka gaisa, na kira Baba muka gaisa sannan ya fada min Hana ba zata dade a gidanmu ba, da zarar na fara jin sauki zata dawo, a haka din ma na yi masa godiya domin yayi kokari da ya barta ta zo ma.
A ranar ma Hana bata ga Abdull ba, washe gari ma ko da ta tashi ya tafi aiki, har take tambayar su basa samun sukuni ne tun safe suke fita kuma basa dawowa sai dare yayi sosai, na yi mata karya da cewar yanayin aikin ne yanxu a haka. Sai da ta kwashe kwana biyu a gidan sai a rana ta uku suka hadu kasancewar weekend ne, babu aiki kuma ita take girma mana abun karyawa a yanzu, na jidadin ganinta da yayi burina ya fahimci ba ni nake girkin ba a yanzu ya rika ci saboda kar yar'uwata ta zargi wani abu.
Sun gaisa cikin mutunci yayi mata ya gida ya mutanen gidan duk ta amsa da lafiyarsu kalau. A ranar ni da ita da shi duk a dinning muka yi breakfast ina ta Jefa masa hira sai ya ga dama yake amsawa, arziki na daya be fadi wata maganar marar dadi ba, har muka gama. Sai da zai tashi yake tambayar wa zai girka abinci a yau.
“Hana zata girka ai ita take girkawa a kullum yanzu”
“Me za a girka?”
“Me kake so?”
Na tambaye shi sai ya kalleta.
“Kin iya dambu?”
“Babu abincin da Hana bata iya ba, ta fi ni kokari ita bata jin wahalar aiki da girki ma”
“Sai na ci na ji zan tabbatar”
Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamar dai bakar magana kuma kamar a bakin gaskiyarsa kenan. Na yi murmushi
“Shikenan sai ta baka mamaki kuwa”
Ya kalleta kadan ya dauke kai.
“Za mu gani”
Na yi dariya ita kuma ta yi murmushi. Sai da ya bar dinning sannan take fada min next time zata zuba nata abincin ta ci a dakinta.
“Why?”
“Ni dai kawai na fi jin sakewa, ki bar ni na ci a dakina ku kuma ku ci a falo”
“Shikenan ba dole ai sai rai na so”
Na fada mata ina dariya. Ya ci abun da ya girka da rana saboda a gida ya wuni, be yaba ba amman kuma be isa yace be yi dadi ba domin kowa ya ci dambu a ranar ya san yayi dadi. Da haka dai har ya gaji ya fara yabawa idan ta yi girki, wani lokacin har cewa yake a sake yin jiyar jiya. Sannu a hankali ya fara sakewa da ita ita ta dan sake da shi har sukan zauna su yi hira a falo. A gaba ranar yake tambayar makaranta ta fada masa ta kare amman bata cigaba gaba ba saboda tana jin Baba ba zai aminta ba.
“Indai haka ne sai mu rike ki a nan a saka ki a makaranta, ga makarantu masu kyau a nan, kuma da ganinki zaki yi kokari ba kamar Noor ba”
Na kalleshi da sauri ina hade rai irin na wasa, jin yana shigar mata a yau, domin idan yana wasa da ita nuna yake na fita iya komai alhalin ya san kuma ta fi ni.
“Yau kuma?”
Yayi saurin kai hannu ya taba ni.
“Ke wasa nake, ta ina zata fi Mamata kokari, kawai ina dan zuga ta ne kar ta ji babu dadi”
Muka yi dariya dukanmu. After magariba ya fita titi zagayawa, ni kuma na yi dawo falon na zauna inda Hana take cin abinci.
“Noor gaskiya yanzu kam kin dace, yadda kuke rayuwa da Abdull abun ya burgeni Allah yasa hakan ya dore”
“Ameen”
Na amsa ina hamma, domin tun da na shiga wata na hudu nake ta yawan bachin dare, da zarar an yi magariba zan