Showing 24001 words to 27000 words out of 133189 words

Chapter 9 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

498

hakan a zaman da na yi da Safeena da Yusura, baka iya ganewa kansu, yanzu idan ka ga yadda Yusura take min a gaban mutane ba zaka tana tunanin akwai wani abu na rashin so ko zaman lafiya a tsakaninmu ba, yanzu kuma har wani hali ta kirkira saboda Safeena ta zo gidan har dakina take kawo min abinci idan zan fita tace Allah ya tsare idan na dawo tace min sannu da zuwa, na fara tsorata da lamarin matar nan”

Hafiz yayi murmushi.

“Safeena ta zo gidan fa ka ce Kareem? Amman ban taba ganin mutumen da ya raina matarsa ba irinka”

“Ba zuwa na yi da ita ba, kuma na gayyato ta na yi ba saboda na daina daukar wayarta ne ya saka ta zo da sunan ta zo min gaisuwa, amman dai na taka mata burki. So ni ina ganin ya kamata ka yi bincike ko kuma ka yafe mata ka rufe maganar kawai ba wai ka dauke mata kafa ba, kuma ka daina magana da ita a halin da take karkashin kulawarka. Ka ga duk yadda nake da Yusura bata so na bana sonta ba ma zaman dadi amman a haka idan na ga ta wuni bata fito shiryawa yara abu ba, ko kuma ban ji motsinta ba na kan leka na duba lafiyarta domin hakkinta ne da ya rataya a wuyana, please ka gyara”

“Zan gyara, amman kamar yadda baka yarda Noor bata san komai akan samun maganin a jakarta ba ni ma ban yarda Aisha ta saka mata ba, na san wacece Aisha shekara nawa muna tare da ita, mace ce mai kirki mai mutunci”

Kareem be sake cewa komai ba, domin baya son ya zafafa kasancewar ba shi da hujja kuma baya son Hafiz ya dauki abun ta wata sigar. Sai dai abun da be sani ba Hafiz ya gama fahimtar har yanzu akwai Soyayyar Noor a zuciyarsa hakan kuma ya saka shi jin kamar aurenta ba shi da amfani a gareshi. Sai bayan Sallah Magariba suka rabu da juna Hafiz ya nufi gidan Kareem kuma ya fito ya zauna a harabar kamar yadda ya saba domin baya shiga gida sai bayan Isha'i lokacin da yake tare da Safeena gidansa da suke badala yake tafiya sai kusan 11 ko 10pm suke rabuwa...
A hanya yayi sallah Isha'i sannan ya shiga gidansa, yana faka mota yaransa suka fito da gudu suka tarbe shi sai ya daga su sama yana ajewa yana dariya.

“Baku yi bachi ba”

“Eh Daddy me ka siyo mana”

“Ban siyo komai ba amman dai akwai chocolate a daki muje na baku”

Ya kama hannunsu suka shiga ciki babbar ta rufe kofar falon, Yusura ta mike tsaye daga zaune da take.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa Sannu”

Yana rike da hannun yaransa ya haura sama suka shiga dakin, gaban maduni ya tsaya ya fara cire agogonsa akan Areef ya hau gado yayi tsalle ya haye masa baya yana dariya, shi ko yana juyowa ya fara masa chakulkuli sai dariya suke har shi gogan. Gurin da yake aje kayan dadin ya bude ya dauko ya mika musu. Yusura ce ta shigo dakin hannayenta a baya tana kallonsu.

“Tine ku je falo zan yi magana da Daddy”

Ya juyo ya kalleta, su suka sauka daga kan gadon suka fice daga dakin. Karasa ta yi kusa da shi ta dora masa abun da ta samu a aljihunsa kan gado. Ya kalli maganin da sabuwar robar ya kalleta irin kallon nan na me aka yi? Ita ma ta yi masa irin kallon ya aka yi suka zo aljihunka. Ya dan tabe baki

“Ba nawa ba ne”

“Su suka kawo kansu?”

“Ni ban taba amfani da condom ba a rayuwata, da maganin da cdm din ba nawa ba ne, dalili ya kawo su”

“Dalilin nake son ji”

“Miye matsalarki da shiga hurumi har kina bincikar kayana? Ki tsaya matsayinki kar ki sake yi min haka”

“Okay so kake na zuba maka ido ka lalace? Matan auren har gida suke zuwa nemanka? Ka ba su fuska na nuna musu ba ni da muhimmanci a gurinka?”

“Babu wata alaka tsakanina da su, can you excuse me please...”

“No idan wani abu ya faru yanzu ai ni za a zaga saboda Momy bata raye ni za a dorawa laifi”

Da mamaki yake kallonta wato gata uwarsa.

“Me ya same ki ne? Why are you behaving like this? Ba ma shiga hurumin juna, me ya canja yanzu”

“Babu abun da ya canja, kawai duk abun da nake ina yi ne saboda yarana, kuma ba zan sake daukar wata karuwa ta shigo cikin gidan nan nemanka, ka tsaya can waje ka yi tun da ka lalata rayuwarka, ka dauki hakkina ga hakkin yara ga hakkin Momy ga hakkin Daddy ga hakkin Allah ga hakkin matan da kake lalatawa ga hakkin mazansu da yayansu kana zuwa lahira wuta a a saka ka kai tsaye...”

Shi dai kallonta kawai yake har ta gama balbalin bala'in ta fice daga dakin. Because he's not a fan of argue. Juyawa yayi yana kallon kofar be taba aikata wani abu da ya shafi rayuwarsa ya ga Yusura ta fusata haka ba irin wannan, kuma ta nuna a fili sai wannan karon, and the most funniest part is yadda ta jero masa hakkin kowa a kai kamar ita zata kai shi wutar. Kai ya girgiza sannan ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya shirya cikin Pajamas.




NOOR POV.

Yadda nake kwana sati biyu da suka wuce haka na kwana a yau ma. Wato kwanan bakinciki da damuwa da kuka da kuma kadaici. Da safe na fito na gyara falon da be yi dattin komai ba na shiga kitchen na hada tea na fito falon na zauna ina sha. Muryar Aisha na ji tana yi ma Hafiz Allah ya tsare. Hakan ya saka ni mikewa tsaye na isa gurin windows din na bude sai na hango shi zai shiga mota ita kuma tana tsaye da murmushi a fuskarta sai hannu take daga masa. Har ga Allah bana son Hafiz kuma bana jin zan iya son sa ba shi kadai ba har zuciyata ba zata taba kaunar wani namijin ba bayan Zafeer amman tabbas ina jin zafi sosai yadda ya aje ni a karkashinsa amman ya kasa yi min inuwa kuma yana min ba ni muhimmanci a gurinsa.

Ina kallonsa ya tuka mota ya fice daga gidan ba tare da ya shigo bangarena ba, na yi tunanin zai shigo ko da fada ne yayi min ya tambayi ina na tafi ba tare da izininsa ba.
Kuka na yi har sai da numfashina ya fara sakerwa na kasa cin komai a wunin sai kuka. Sallah ma daker na yi saboda jikin babu karfi, I'm so hopeless babu mai taimakona, ko da zan mutu a wannan halin na kunci da nake ciki babu wanda zai kawo min dauki.
A falo na yi sallah magariba ina sanye da hijab dina milk color na ji tsayawar motar Hafiz, sanin ba zai leko bangarena ba ya saka ban leka waje ba, kar na yi arba da bakinciki. Sai dai abun da ban yi zato ba ne ya faru, ganinsa na yi a falon kamar an jefoshi gabana ya shiga bugawa da mugun karfi ganin yayi tsaye a kaina yana kallona ni kuma na gagara cewa komai.

“Ina kika je jiya?”

Gabana ya fadi na gagara cewa komai sai hade yawu nake.

“Gurin Kareem? Office kika same shi ko gida.?”

Na sauke kaina kasa nan ma bana iya fadar komai.

“Ke wai sai yaushe zaki yi hankali?”

Na ji sanyi hawaye ya jika fuskata.

“Ta so muje”

Na dube shi da sauri. Kamin na yi wani yunkuri har ya mike tsaye, a dole ni ma na yi tsayen na bi bayansa sai ya juyo ya kalleni.

“Je ki saka talkaminki”


Na nufi gurin da talkamin suke na saka shi kam tuni ya fice daga falon ma. Ko da na fito ya tashi motarsa da kansa ya bude min front na shiga na zauna ya rufe sannan yaja motar muka fara tafiya, be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba sai sake saken nake a zuciyata ina zai kai ni? Me Kareem ya fada masa? Ina son na tambaya amman na kasa saboda bakinnya rufe min gam. Unguwarmu ya nufa yana ratsa gidajen dake ciki har ya isa kofar gidanmu, a nan na fahimci so yake ya hada ni da iyayena. Na kalleshi hawaye na min zuba.

“Fita ki shiga gida, ki zauna sai na neme ki...”

Ya fada ba tare da ya kalleni ba, na juyar da kaina dake rawa na bude motar na fita sai na yi tsaye na kasa daina kallonsa na kasa juyawa na shiga cikin gidan. Mun dauki mintuna a haka sannan ya miko hannu yaja gambun motar ya rufe yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin ruwan hawaye. Me kuma aka ce na ce? Yanzu kuma wane kalar laifin na aikata? Na zauna sai ya neme ni ya sake ni kenan ko kuma yaya?




#KhadeejaCandyPAID PAGE 9️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______

Na kusan minti talati tsaye kofar gidanmu kamar wanda aka cewa shiga ki tararda hisabinki haka tsoron shiga gidan ya kamani, domin na san waye mahaifina. Amman ba ni da wani gurin da ya fi gidan ina zan je? Ai ba ni na kawo kaina ba shi ya kawo ni. Cikin kasala da fargaba irin na wanda ya rasa makoma na saka kafata a gidan, duk yadda nake son hana hawayena zuba kasawa na yi. Sai kuma na yi rashin sa'a Baba na tsakar gidan yana alwala, ban yi sallama ba domin bakin har lokacin a rufe yake. Baba ya hasko ni da fitilarsa mai haske.

“Wa nake gani kamar Norriya?”

Tafiya kawai nake cikin gidan na kasa Cewa komai.

“Lafiya?”

Na durkusa a gabansa.

“Wani abu ne ya samu Hafizun?”

Na girgiza kai.

“Toh me ya faru?”

Hana ta fito daga daki tana kallona cikin tashin hankali.

“Cewa na zauna sai ya neme ni”

Fitilar dake hannun Baba ta subuce ta fadi kasa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, daman ai sai ba ke ba Noor, yanzu duk irin abubuwan da mutunen nan yayi min yayi miki sai da kika kai shi makura? Tafiya kika yi kina masa shashanci da sakarcin na ki ko? Har ya gaji yanzu ya koroki gida”

Na matsa baya da sauri jikina na rawa domin fadan da Baba yake min irin na son duka ne.

“Yaushe aka yi auren da zaki biyo dare yanzu ki ce wai yace ki zo gida?”

Na bude baki zan yi magana ya daka min tsawa ya cire talkaminsa ya jefani da shi.

“Ban son jin komai daga bakinki, marar mutunci daman ai na san sai kin masa shashanci, kina kallon yadda rayuwa take a gidan nan kin samu mai rufa miki asiri ne shi ne kika fara masa rashin kunya ko? Saboda ya sake ki ki auri Zafeer ke ga ki shim mai ruwa uku shashasha, sakinki yayi?”

Na girgiza kai.

“To tashi maza ki koma dakinki, ina nan ina jindadi na samu suruki mai dauke mana komai shi ne zaki fara watsa mana kasa a ido? Ni daman sai da zuciyata ta raya min anya ba kina masa rashin mutunci ba ne, in ba haka ba da yanzu ya gyara mana gidan nan amman shiru, ashe kina can kina nuna masa rashin tarbiya, mai kashin tsiya so kike mu koma rayuwarmu ta baya ko? Ke yar zamani, minti biyar ban yarda ki kara yi a gidan nan ba, koma dakinki gobe zan zo na ji me ke faruwa amman Wallahi ba zaki kwana gidan nan ba, wato halin uwarki zaki dauka na rashin hakuri ko? Ko kuma so kike ya sake ki ki dawo ki sake zaunawa ke da kanwarki a daki daya? Wawuya marar hankali, wato ki zaki nunawa wai ba zaki yi zaman aure ba ko? To na fiki zama dan tasha... ”

Ya karasa yana daukar butar da yake alwalar da ita ya jefa min. Na tashi da sauri na fice daga gidan ina kuka, Baba be saurari izurina ba ya koroni daman na san hakan zai faru, da na fito sai tashin hankalin yayi min yawa na rasa ina zan je, na koma gidan Hafiz din da ya kawo ni gida yace na zauna sai na neme ni ko kuma na tafi gidan Mama? Ita ma koroni zata yi. Haka na bi hanya ina tafe ina hawaye har na isa titi, wata zuciyar na ce min na tafi gidansu kawata Zainab na kwana, domin ba ni da kudin abun hawa ma balle na koma gidan na san kuma ba zai ba ni ba, wata kila ma na samu ya fadawa mai gadinsa cewar kar a bar ni na shiga cikin gidan. Juyowa na yi na dawo cikin unguwarmu na shiga gidansu Zainab, Umma na ganina ta san ba lafiya ba, kamin Zainab tace min komai Umma ta fara tambayata lafiya.

“Umma Hafiz ne yace na zauna a gida sai ya neme ni, na zo kuma Baba ya kore ni, na san idan na tafi ma Mama ba zata saurare ni ba, ban san inda zan je ba”

“Wani abun kika masa?”

“Ban masa komai ba Wallahi ban masa komai ba”

“Aa Noor ba zai yiyu haka nan kawai yace ki tafi ki zauna a gidanku ba, sai kin masa laifi, Allah yasa dai ba Zafeer kika saka a zuciyarki ba, kar soyayyarshi ta hana ki zaman aure, ki kama kanki Noor ki natsu, yaushe aka miki auren da har za ace an fara samun matsala irin wannan?”

Na yi shiru domin ba kowa zai yarda da ni ba.

“Kin ga ni ba zan baki mafaka ba, mahaifinki ya koreki wace ni na baki gurin zama? Ai zai ma iya ci min mutunci ko kuma a ce saboda ni ba uwarki bace yasa na yi haka, ki yi hakuri ki koma dakinki ki bawa mijinki hakuri ku zauna, shiyasa ma na hana Zainab tafiya gidanki kar wani abu ya faru ace ita take hure miki kunne, ki yi hakuri ki koma dakinki Noor”

“Tohm...”

Na amsa kana na juya domin bata bar ni na zauna ba ma, haka na fito daga gidan ina hanya Zainab ta tarar da ni ta ba ni 500.

“Mama tace ki hau Napep, kuma Noor idan ba zaki iya komawa gidan kai tsaye ba, ki tafi gidan iyayensa ko kuma wani dan'uwansa wanda kika san yana jin maganarsa, sai a kira shi a yi masa magana kinji”

“Ban san gidansu ba, be taba kai ni ba”

“Ko gidan wani abokinsa ba kisa ni ba?”

“Na sani amman hakan zai iya bata masa rai, jiya naje can na fada masa amman be yi komai ba, wata kila shiya saka yau na ce na dawo gida na zauna”

“Idan kin tafi kice ya fada miki gidan iyayensa ki tafi, ba wai dole shi zai masa magana ba, kuma Noor na san halinki da rashin jin magana dan Allah ki zauna lafiya”

Na yi murmushi ina jin ina ma ace ni ce a matsayinta.

“Na gode Zainab”

Ta tsaya a gurin har sai da na samu Napep na hau sannan ta juya. Kuka ne abun da nake yi har mai napep din ya isa kofar gidan Kareem.

“Allah yasa lafiya kike wannan kuka ko mutuwa aka yi?”

Ban ce masa komai ba na mika masa dari biyar din na fita Napep din ina kallon gate din gidan ban san me zan sake ce masa ba. Ina ta zuwa masa da matsalata, waya sani ma ko hakan ya zama sanadin mutuwar auren nawa gaba daya. Sai dai ba ni da wata mafitar bayan wannan, a gaban gate din na duka ina kuka sosai. Da rarrafe na isa gate din na kwankwasa, babu jimawa mai gadin ya bude ya leko.

“Waye?”

Na share hawayena na mike tsaye.

“Ni ce wadda na zo jiya, Kareem yana nan?”

“Eh yana ciki”

Ya bude na shiga ido a kumbure hancina n yaji saboda majina da gugar da ya sha, fuskata ta yi ja sosai. Kai tsaye na nufi cikin gidan cikin rashin sakewa da tunani kala kala a raina, damuwa ta saka na manta waye matar Kareem, na manta cewar huruminta na shigo domin mijinta. Na kwankwasa kofar falon ta bude min ni da ita muka tsaya kallon juna.

“Ke ce?”

Na daga mata kai.

“Kareem yana nan?”

“Eh yana nan shigo”

Na goge gudun hawayena na shiga falon na tsaya daga gurin kofar ina kallonta.

“Ina son magana da shi ne dan Allah”

“Okay ina zuwa bari na kira shi”

Ta juya ta nufi wani gurin da nake kyautata zaton kitchen ne. Bata ji ba ta fito nufo gurin da nake tsaye.

“Ki shigo ki zauna mana bari na kira shi”

Ba tare da tunanin komai ba na shigo kamin na zauna ta ware hannunta ta buga wani abu mai mugun karfi a kai, ban gama tantance miye ba na sake jin saukarsa a wuyana, wani irin jiri ya dauke ni na soma ganin ta zame min biyu kamin idon ya rufe...




*** *** ***

Babu ihu babu kokarin kare kai Noor ta yi kasa idon suka rufe, gefen da ta buga mata mociyar kuma jini ya fara jika hijabin har ya zubo kasa. Da sauri Yusura ta saki muciyar ta matsa baya jikinta ya fara rawa, me ya kaita? Me yasa ta aikata? Ina tunaninta ya tafi haka? Sai kuma ta matsa ta taba Noor ta ji bata motsi ta sake matsawa baya ta zauna kan kujera hankalinta a tashe jikinta na rawa. Kaminnta tashi da sauri ta haura sama. Dakin Kareem ta shiga yana sanye da multicolours din Pajamas dinsa hannunsa rike da books din Rules of the Journey. Daga kishingiden da yake ya dago kai ya kalleta ko'ina na jikknta rawa yake tashin hankali a fuskarta karara.

“Ya.. Yarinyar da ta zo jiya ce ta dawo yau”

Kareem ya rufe littafin yana kallonta hankalinsa kwance.

“An samu akasi na buga mata abu ta fadi”

Wani irin tsalle ya daka ya sauko daga kan gadon.

“What.... Me yake damunki? Why?”

Ya fice daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login