Showing 60001 words to 63000 words out of 133189 words

Chapter 21 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

263

kila ita ma ta fahimci hakan shiyasa ta ce na tashi na tafi bayan ta gindaya min sharadin kar na jima saboda gyaran wankenta. To me ya zo yi kuma wannan karon? Biyo yayi ya duba ni ko kuma dai wata matsalar ce ta taso daga bangaren iyayen Hafiz da na tattara lamarinsu a gefe na aje.

Bakuwa mota ce da ban taba gani ba mai bakin gilashi baka ganin wanda ke ciki duk da kasancewar akwai hasken lantarki a lokacin. Tsaye na yi ina jiran Kareem ya bude motar ya fito, sai akasinsa ya fito, mutumen nan da na taba haduwa da shi a mall kuma shi ne dai wanda ya dauko ni daga gidan Mama ya kawo ni gida.

“Hajiya Nooriya kin yi mamakin ganina ko?”

Toh ko dai yayi arba da mamakin a fuskata ne shiyasa ya ke tambaya.

“Eh gaskiya na yi mamaki, ban yi tsammanin kai zan gani ba”

Na fada ina rumgume hannayena.

“Akwai wanda kike tsamanin zuwansa kenan, kar fa bazawarin ya tarar da mu ya dauka soyayya muke yi, yayi fushi”

Na yi murmushi feeling Speechless daman mi zan ce bayan shi ya zo shi ya kamata yayi magana ai.

“Well kawai hanya ce ta biyo da ni, sai na tuna i have a friend here na ce bari na biyo just to say, hope ban yi laifi ba?”

“Are we friends daman?”

Tambaya nake a bakin gaskiya ta domin ban san wata rana da muka zama kawaye ko abokai ni da shi ba. Da alama kuma tambayar tawa ta ba shi dariya har sai da ya bayyana hakoransa.

“Uhm ba ma bukatar request ai, idan ba mu zama abokai ba mun zama yan'uwa saboda Mama ko?”

“Maybe”

Na fada ina dan wara ido.

“Not maybe, pretty gal ban da jan aji, ko da yake kamata yayi na gabatar da kai ne, taya za ayi abota ba a san juna ba”

Ya miko min hannunsa.

“I'm Abdull by name, engineer ne ina zama a Lagos for now, ko da yake ni dan garin Kano ne haifaffen garin kano aiki ne ya kai ni Lagos kuma idan na tafi na kan yi wata biyar hudu uku har fi a can, am ina da mata da yara uku a yanzu”

Kallon hannuna nake wata kila dai ya manta da cewar ni da shi hausawa ne kuma musulmai, idan ba haka ba miye na miko min hannu mu gaisa. Kareem ne kadai ya taba yi min haka bayan shi kuma bana jin akwai wanda zai sake miko min hannu na karba.

“Nice to meet you Abdull”

Na amsa ba tare da na ba shi hannun nawa ba.

“Ba zaki gaisa da ni ba?”

“Ba ayi min wannan hallacin ba tukuna”

Yayi murmushi tare da maida hannun nasa.

“Daman dai na zo na gaishe ki ne, hallaci kuma za'ayi miki nan gaba kadan, abu na karshe bana bukatar ki fada min komai a kanki na tambayi Mama wacece ke ta fada min yadda kike da kafiya da rashin magana, ban yi mamaki ba kuma saboda kina da kyau kin san mata masu kyau suna da rashin magana sosai”

Na yi murmushi kadan, sai ya bude motarsa ya dauko leda ya mika min.

“Ga tsaraba ki shiga da shi gida”

“Aa na gode”

“Mu ai ba ma yin kyauta a mayar mana, ko dai ki karba ko na aje miki na tafi”

Jin haka ya saka na kai hannu na karba, na yi masa godiya na juya sai na ji ya kira sunana.

“Noo oor”

Na juyo.

“Yaushe zaki je ganin Mama?”

Sai da na yi nazari kamin na amsa masa.

“Friday”

“Okay see yeh✌”

Ya sara min da yatsu biyu sannan na yi masa murmushi as responsed sannan na juya na shiga gida. Gudun laifi ya saka na aje ma Umma ledar da ya ba ni ba tare da na bude ba.

“Shi ne abokin mijinki?”

Bana son dogon zance dan haka na amsa mata da eh ina kallon turaran da take fitarwa da man shafi masu kyau.

“Ko dai son ki yake?”

“Aa daman tun kamin na san Hafiz din na san Kareem”

“Toh bari a aje idan mahaifinki ya dawo sai a nuna masa”

Akan haka muka rabu, ban sake ganin ledar kayan ba sai washe gari bayan Baba ya fita ta miko min ledar wai ita ta dauki turare daya Baba ya dauki biyu sun dauki man shafi biyu suka bar min daya. Ban ce komai ba na karba na shiga da shi dakinmu na aje ma Hana man shafin da turare daya na dauki dayan da ya rage.

Sai da na dan kimtsa sannan na fito sanye da hijabina, kamshi kam kai kace gidanmu ake kamfanin turare na fesa wanda Abdull ya kawo min sosai saboda yana da dadi da saka sanyi zuciya.

Tsakar gidan na fito na dauki bokiti uku da nake deban ruwa da su na fice daga gidan domin yin abun da ya zame min wajibi. Fanfon da muke dibar ruwa irin wannan ne mai tuka tuka sai ka yi ta bugawa kamin ya cika, haka na yi ta wahala ni kadai ina jan karfen yana jana har na cika. Da kuduri biyu na fito daga gida, kudirin debo ruwa da kuma ziyarar gurin da na san Zafeer yana aiki, domin ban isa na tunkari gidansu da bukatar ganinsa ba.

Idanuwa kaikaiyin ganinsa suke, zuciyata tana ta muradin mai sakata farinciki, na san ba zai kalleni ba idan ma yana gurin ba lallai ya sake kaunata ba, amman ni zan ji sanyi idan na yi magana da shi ko da kuwa zagina yake. Tafiya ce mai dan nisa haka na kama hanya ina tafe ina ta sake saken yadda zan fara masa magana idan ma na sameshi a gurin.

Na tarar da Ogansa a gurin muka gaisa yayi min gaisuwar Hafiz, kana kuma ya sokeni da wata kalma mai daci.

“Noor kin guje mana ko? Duk soyayyar nan da muka nuna miki sai da kika butulci mana, gaskiya ban jidadi ba kuma na yi mamaki sosai, Wallahi ba karamin damuwa kika jefa Zafeer ba”

Na aje numfashi a muhallinsa ina jin yadda bakinciki ya fara yawo a zuciyata.

“Gurinsa na zo ko yana nan?”

“Kai ai Zafeer ya bar nan, tun a lokacin da kika yi aure yace ba zai iya zama garin nan ba, kwanan baya dai ya zo, amman ya koma gaba daya ya kwashe komai nasa a nan, shi ma kuma Allah yayi masa sakamako na alheri yar wani babban mutum zai aura karshen watan nan In Allah ya yarda”

Indai abun da nake ji a yanxu, irinsa Zafeer ya ji a lokacin da na yi aure na bar shi, tabbas ya shiga tashin hankali, kasa rike kaina na yi har sai da na fasa kuka sai kuma na yi hanzarin rufe bakina, hawaye suke Noor yau ma muna sha'awar yin ado a fuskarki.

“Haka daman abun Allah yake, lokacin da wani ya ƙi ka da wuni, wani zai ya so ka da kwana, yadda kika guje masa kika auri mai kudi, shi ma Allah ya ba shi yar masu hannu da shune, yar babban mutu kuma babbar ma'aikaciyar banki, an yi lokacin da take kawo gyara a nan, bata duba talaucinsa ko kaskancinsa ba ta aure shi”

“Baka san komai akaina ba oga Lawal dan Allah karka yanke min hukunci”

Na fada ina hawaye, na cira kafa daker ina tafiya kamar wata tsohuwa. Har na iso gurin bohol din hawaye nake, zuciyata zafi take wasu abubuwa nake ji a cikin kaina suna min yawo. Ban tarar da ruwan da bokitan da na kawo ba, daga ruwan har bokitin wanda ya fi ni so yayi awon gaba da su, wani mai dan hali mai son biya lahira.

Bana cikin yanayin da zan iya shiga gidajen da suke kusa da Bohol din balle na tambaya ko sun ga wanda ya dauka ko kuma sun dauko. Sai kawai na nufo gida ina tafe ina hawaye har na iso.

“Ina ruwan?”

Umma ta tambaya tana daura dankwalinta.

“An dauke kayan”

“Garin ya? Taya kika yi sake har aka dauke kayan? Sai kuma ki dawo min gida kina kuka, Wallahi ko kije ki nemo min kayana ko kuma na fadawa mahaifinki idan ya dawo wannan ai keta ce da sheri, kamar ya an dauke kayan kina aikin me aka dauke? Kukanki ba zai kwace ki ba”

A zatonta ina kuka ne saboda an dauke kayan, bata kukan bakinciki nake ba wanda ya fi na sata ciwo. Dakinmu na shiga na dauko dubu goma da Alhaji ya ba ni a lokacin da na tafi gurin Mama na cire 1k na mika mata saura.

“Ga kudi ki siya wasu”

Sai da ta gama kallon kudin baki sake sannan ta karba bata ce min komai ba ta shige dakin Mama wanda ya zama dakinta a yanzu. Ni kuma na sa kai na fice daga gidan, bana iya daga kai saboda bana son kowa ya ga idanuwa. Ina isa titi na tari Napep na hau na fada masa inda zai kai ni, domin ba ni da gurin zuwa yanzu da ya wuce can.

Ko da yake idan ma na tafi ban san me zan fada mata ba, ba lallai ne ta ji yadda nake ji ba, ni kadai nake iya fahimtar kaina.
Bayan na sauka na ba shi dubu daya ya ba ni canji na nufi gate din dake bude na shiga, a lokacin ne wata motar ta iso kusa da gate din zata fice. Daidai saitin da nake tafiya mai motar ya tsayar ya sauke gilashin kasa.

“Noor kika ce min sai friday?”

Na kalleshi Abdull ne a cikin motar yana sanye da facing cap. Ban ce masa komai ba na nufi bangaren da Mama take. Ina tana kofar na jita a rufe na fara kwankwasawa.

“Bata nan fa ta fita”

Na juyo na kalleshi sai ya saka hannayensa aljihu ya cire hular kansa yana kallona.

“Sai dai ki shiga bangaren Hajiya”

“Aa ba sai na shiga ba, zan koma gida kawai”

Na fada ina mamakin Hajiyar mahaifiyarsa ce ta Safeena tsakanin shi da Safeena gidansu waye ne? Ko kuma shi da ita Yaya da kanwa ne oho.

“Okay Let me drop you off Girly”

Ban masa musu ba ya wuce gaba na bi bayansa har muka isa gurin motar na bude na shiga, shi ma ya shiga yaja motar muka fice daga gidan. Tafiyar kamar ta kurame haka ta zama bana cewa komai sai tunanin Zafeer nake da irin rayuwar da yake ta fada min zamu yi. Ban ankaro ba na ji hannunsa a cinyata yana shafa ni.

“Kin yi shiru baki cewa komai Noor”

Na yi saurin buge masa hannu.

“Miye haka?”

Sai yayi murmushi.

“I'm sorry daman ina gwadaki ne kawai”

“Gwada ni kamar yaya to see what?”

Asking with little bit of confuse.

“To see if you're wife material...”

“Sauke ni a nan”

Ya dube ni da sauri.

“A nan?”

“Eh a nan zan sauka”

“Ba gidanku ba ne ai”

“Na ce ka sauke ni a nan zan sauka”

Wata kila bakin hadarin da na hada a fuskata ya firgita, domin na daure fuskar sosai babu alamar wasa. A dole ya faka gefen titi ni kuma na bude na fita na bar masa motar a bude.

“Kin ga ni fa gwadaki ne kawai nake ba wani abu ba...”

Ban kula shi ba na cigaba da tafiya a kafa, ya so gwada bina a motar yana min magana da ya lura ba zan saurare shi ba kuma ba ni da niyar shiga motar sai ya motarsa yayi gaba. Tsaye nake ina jin kamar na fasa ihu na fadi na yi birgima a guri. Kusa da ni wata motar ta tsaya wannan karon ina ganin wanda ya fito motar sai na ji sabon kuka ya taso ni gaba, wani irin shagwaba da narkewa na fara yi kamar wata yar baby.

“Me ya faru? Me kike yi a nan?”

Ya tambaya tun kamin ya karasa fitowa daga motar, matsawa na yi kusa da inda ya faka motar ina kuka har da shessheka.

“Kareem...”

Ya kalleni hankali a tashe.

“Me ya kawo ki nan Noor waya taba ki?”

“Kowa ma taba ni yake...”

Ya kama hannuna ya ratsa da ni ta cikin wasu itatuwa da ke gurin muka shiga ta can ciki gurin da ke da sanyi da iska mai dadi, sakin hannuna yayi.

“Fada min me ya faru?”

Na daga kai na kalleshi kawai hawaye na sauko min. Cikin kwantar da murya da lallabawa ya ce

“Can i be your best friend?”

Na daga mishi kai.

“Okay daga yanzu na zama best friend dinki, yanzu fada min damuwarki”

I don't know why, how and when, i just find myself laying on his chest idanuwa na zubar da kwalla.

“Zafeer zai yi aure Kareem...”

Mun dauki 12-seconds a haka, ni da shi babu mai motsi kamar mun mutu, but zuciyata na bugawa da wani irin karfi kamar yadda nake jin tasa ma tana bugawa, sannan ya matsa baya hakan ya saka dole na dago daga jikinsa, he look straight into my eye ball ya ce.

“Noor ki daina saka turare mai yawa haka idan zaki fita, Haramun ne”

“Kai turaren ne damuwarka?”

“Saboda yana dagawa mutane irina hankali turare is my weakness, my weak point”

Ban gama fahimtar abun da yake fada ba, na ganshi slowly yayi kasa ya zauna akan turbaya ya nade kafafuwansa ya dago yana kallona.

“Zauna karanta min damuwarki, maybe zamu iya solving matsalar...”

Na zauna a gurin ina fuskantarsa da irin zaman da yayi.....Kareem ya sauke numfashi mai nauyi.

“Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni”

Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa.

“Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce”

Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce.

“Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba”

“Okay yanzu da bata raye mu ne abokan wasarka? Kai da ita? Ni ba zan ma yarda ba ku son junanku ba. Kareem zan baka shawara karka yarda ka rasa Yusura, na yi aure tun kurciya har yanzu na zauna da mata biyu a lokacin da mahaifiyarka take raye, mu kan samu tsabani mu yi dadi, wani lokacin har iyaye su sani, amman ban taba ganin matar aure da bata taba kuka da mijinta ba sai Yusura, bata fadin sherinka, bata kawo kararka, kai a gurinka ba abun kunya ba ne aji ka saki matarka? Kuna da yara biyu me kake fada musu? Idan aure kake son karawa you're free to do so ba sai ka saki matarka ko ka wulakanta ta ba, idan har kana fadar saboda Mahaifiyarka ka aureta to miye amfanin sakin a lokacin da mahaifiyarka bata raye? Ke nan ganin idonta kake yi ma biyayya ba saboda Allah ba? Yanzu da ban yi magana ba haka zaka zuba ido ta cika idda? Ko saki uku ka yi mata? Domin bata fada mana ko saki nawa ka yi mata ba, kuma ita bata zauna kamar kai ta kalli kwayar idonmu ta fada mana bata son dan mu ba, Kareem idan ka sake ka rasa Yusura ka rasa matar kirki kenan har abada”

Kareem yayi shiru be ce komai ba, domin ya fahimci Daddy ba zai yarda da duk wani zancensa ba.

“Saki nawa ka yi mata?”

“Daya”

Sai a lokacin Daddy ya sassauta muryarsa ya daina yi ma Kareem fada.

“Ka yi hakuri, shi zaman aure dan hakuri ne, duk can talkaminmu suka tsinke, dole sai an kai zuciya nesa, bana son na sake jin wata matsala a tsakaninku, ka maida matarka dakinta ku zauna lafiya dan Allah”

Kareem kamar zai fasa kuka ya ce.

“Daddy mai daki shi ya san inda yake masa yoyo...”

Be rufe baki ba Daddy ya rufe shi da fada yana masa tsawa.

“Get out Kareem, tashi ka dauki matarka ka aje ta gida sannan ka wuce aiki, wato Momy kake tsoro kana gudun zuciyarta mu kuma ka raina mu ko? Toh ka bari har bayan raina sannan ka saketa idan ka ga dama ka hada har da yayanka ka koresu gaba daya”

Da sauri Kareem ya sauko daga kan kujera yana bawa Daddynsa hakuri, domin idan akwai abun da yake gudu da tsoro a rayuwarsa to fushin iyayensa ne.

“Ka yi hakuri Daddy, na maida aurena saboda kai, kuma zan dauke ta mu tafi gida yanzu kamar yadda ka ce ka yafe min dan Allah”

Daddy ya dauke kai ya kai hannu ya dauki gilshinsa ya mike tsaye ya shige bedroom dinsa. Kareem ya dafe kansa ya rumtse ido, ya fi karfin minti talatin a haka sannan ya dago ya fito daga bangaren ya dawo bangaren Hajiya Hassana ya zauna a falon ya kasa yin komai har sai da Step mother dinsa ta fito sannan ya gabatar mata da abun da ya maido da shi bangaren nata.

“Na maida aurena Hajiya, a fada mata ta fito mu tafi”

Hajiya Hassana ta yi murmushin jindadi.

“Haba yanzu na ji magana, ko kai ba haka ake so, kuma dan Allah ayi ta hakuri karka ce zaka biyewa mace ita mai rauni ce, kuma duk matsala da za a samu a daina saurin saki, muna raye idan ya kamata mu ji sai ka sanar mana mu tsawatar mata yafi ayi ta saki ga yara”

“Tohm Hajiya”

Ya amsa irin amsawar nan na wanda ya rasa interes da mafaka da kuma gata a lokaci daya, daman tun farko yayi tsammanin haka shi ya hana shi sakinta a lokacin da Momy bata dade da barin duniya ba, da ace kuma ya sake a lokacin da take raye Allah kadai ya san irin fushin da Momy zata yi da shi. Ya mike tsaye yana jin wani fever na rufe shi ya nufi motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna yana jiranta bakinciki cike fal a zuciyarsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login