Showing 78001 words to 81000 words out of 133189 words
Chapter 27 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete
jin sautin hade yawunsa.
“Amman kin taba ganin matarsa?”
Na dan kawar da ido daga kallonsa sannan na amsa.
“Eh na taba ganinta ya nuna min hotonta”
Ya langwashe halshensa.
“Kin san sunanta?”
“Safeena your ex-”
Murmushi yayi ya jinjina kai yana juya idanuwansa like na bashi mamaki sosai, kamin ya kalleni.
“Kin san duk wannan kuma kika yarda zaki auri Abdull?”
“Ba mutumen kirki ba ne?”
“Ban san komai a kansa ba, amman na san komai akan Safeena, ba zaki iya kishi da yarinyar nan ba, she's criminal”
Na dan tabe baki.
“Bana jin zata yi kishina, ai kai take so kuma kai take kishi, me zai saka ta yi kishin mutumen da bata so indai har da gaske bata son shi”
“Mijinta ne uban yayanta taya ba zata ji kishi ba, kuma ni ban taba fada miki cewar bata son shi ba, taya zata ki mutumen da shi ya tsamota daga ruwa a lokacin da na jefata?”
Na daga kafaduna not knowing what to say yanzu kuma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da murya ya ce.
“Noor me kika fadawa Safeena?”
Na kalleshi da sauri daman na san za a zo gurin.
“Me tace na fada mata?”
“Sirrin da na yi dake ta zo ta fada min duk abun da kuka yi, saboda me zaki nuna mata cewar kin san abun da yake tsakaninmu”
Na ciro wayata daga aljihun rigata na nuna masa sakon da ta turo min, kamin wani abu ya tsikare ni kamar zan yi fada na fara magana.
“Ganin na yi tana neman daga min hankali tun kamin na shiga, ni kuma ba na yi aure ne saboda na je na fito ba, bana son aurena ya sake rabuwa sai idan mutuwa ta raba”
“Amman sai ki yi amfani da wata hanyar ba wannan ba, ke yarinya ce, baki gama fahimtar duniya ta mutanen cikinta ba, ba ki san illar abun da kika ba sai bayan ki aikata”
“Ba ni da wani weapon na yakarta sai wannan”
“Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?”
Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa.
“Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!”
Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni.
“I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba ”
“Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa”
Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa.
“Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor”
Na share hawayena.
“Ta je ta bata ni gurinka ko?”
Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali.
“Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ƴaƴana abun kunya”
“Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji”
Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau.
“Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri”
“Ameen”
Ya sake Bude motarsa zai shiga.
“Shikenan tafiya zaka yi?”
Ya juyo
“Ko kina da bukatar wani abun ne?”
Na girgiza kai.
“I will miss you alot”
Yayi murmushi ya sauka kansa.
“Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?”
Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci.
“An yi komai”
Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba.
“Sai wata rana”
Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi.
Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba.
Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni.
A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni.
Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai.
“Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta”
“Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma”
Cewar Baba Garba.
“Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota”
Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba.
“Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?”
“Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata”
Anty Larai ta ce
“Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girma, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji”
“To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai”
“Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango”
“Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai”
“Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...”
Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta.
“Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi”
Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa.
“Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?”
Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su.
“Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba”
Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce.
“Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa”
“Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor”
Duk yadda zata karfafa min guiwa sai da ta yi har ta yi nasarar kwantar min da hankali na dan sake raina. A napep muke ta labarin Zafeer da sabon auren da aka ce yayi a gurinta nake jin labarin irin hidimar da aka yi na bikin auren domin Zainab tana abota da kanwar Zafeer sosai, shi ma kuma yana good time da ita ko a lokacin da muka samu matsala ita yake aikowa gurina.
“Amman kin ga yana dariya?”
Na tambaya ina jin bakinciki marar misaltuwa kamar ba ni na fara guje masa.
“To zai ki dariya ne Noor? Ai dole yayi farinciki ko yaya ne, wata kila ma yanzu ya manta da soyayyarki, domin yar masu kudi ya aura ance mahaifinsa ma shi zai sama masa aiki, daman ita yarinyar tana aikinta, ance ta girme shi da shekara uku”
“Allah ya saka masa tun ba ayi nisa ba, ya samu wadda ta fi ni komai”
Na fada hawaye na sauko min, Zainab ta dube ni.
“Noor har yanzu kina son Zafeer wai?”
“Unconditionally, har abada zuciyata ba zata daina son Zafeer ba, ba zan taba son kowa kamar yadda na so shi ba”
Shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa Uffan daga ni har su. Har muka isa gida hawaye nake, haka na shiga gida rai babu dadi zuciya na kuna, kiran da Abdull yayi ta min ma kasa dagwa na yi saboda damuwar data haifar min da ciwon kai.
Washe gari ya Friday gidanmu ya cika da makota da yan'uwa na kusa da nesa maza da mata, kusan wannan bikin ma kamar ya fi wacan yawan jama'a.
Bayan saukowa daga Massallaci na fita waje na yi alwala na shigo dakinmu kenan wayata ta yi kara, dubarwa da zan yi sai na yi arba da number Abdull, a take na amsa kiran na kara wayar a kunnena.
“Hello...”
“Congratulations an daura aurenmu, Alhamdullahi”
Gabana ya fadi har sai da kaina ya sara, kai kace ban tsammaci zuwan wannan ranar ba.
“Allah ya ba mu zama lafiya”
“Ameen”
Ya amsa sannan ya kashe wayar, shi ne mutum na farko da ya fara min albishir, kamin gidan mu ya dauki guda har Hana ta shigo dakin tana rangwada guda tana farinciki, sabanin wacan auren na farko da bata yi farinciki ba. Madadin na yi murna sai na fashe da kuka na zube a gurin an rufe idona ina ta rutsar kuka kamar wanda aka sake yi ma auren dole.
Haka na wuni ban iya cin komai ba, sai da Anty Larai ta siyo fura ta dama min ta saka kankara sannan na iya sha shi ma ba da yawa ba, yan'uwan Abdull sun leko mana wuni, daga bangaren mahaifiyarsa da kuma na mahaifina. Angon kuma be duro gidan ba sai isalin karfe takwas na dare. A lokacin da na kira a waya ya sanar min yana waje, sai na jin kunyar fita a dole na yi masa karyar Gwaggonta tace ba zan fito ba.
Ban san da wa yayi magana ba, sai ga Baba ya shigo yana fadin na tashi na leka waje mijina ya zo tare da abokinsa yana son magana da ni. Jin cewar yana tare da wani ya karfafa min guiwa kuma ya rage min kunyar da nake ji ta mutane. Hana ta dauko turare ta kara fesa min, Anty Larai kuma ta saka na cire lace din dake jikina na saka farar lafaya sannan na fita gashin kaina na yawo domin ban saka ribbon ba.
Nesa da gidanmu ya faka ta inda mutane ba za su ganshi ba, ni ma ba dan na kira shi a waya ba ba zan iya gane shi ba. Kamar ana daure min kafafuwa haka na karasa gurin motar sai ya sauke gilashin ya kunna hasken wayarsa ya haska fuskata.
“Amarya ba kya laifi, kyakkyawar amarya mai tsaye siririya duk ni kadai”
Kunya ta saka ni sauke kai kasa ina murmushi.
“Shigo motar mana, kar na gajiyar da matata”
“zan iya tsayuwa a nan”
Bude motar yayi ya fito ina kallonsa ya kama hannuna ya zagaya da ni ta baya ya saka ni a back seat sannan shi ma ya shiga. Rabon nake ko zan ga abokinsa amman ban ga kowa ba.
“Ka ce kana tare da abokinka...”
“Na fadi haka ne saboda na rage miki kunyar dake kanki”
Ya yana maganar kallon bakina zuwa kirjina.
“Ko ban kyauta ba?”
Kamin na amsa na ji na kara matsowa kusa da ni sosai har ina jin numfashinsa, ta dama da ni ya lakamo hannunsa yana lasa cikina a hankali.
“Ya gajiyar biki?”
“Alhamdullahi”
Ina kokarin cire hannunsa sai ya juyo da fuskata zai sumbance ni, na dauke kai na dauke numfashi ina jin wani iri. Murmushi yayi ya saka dayan hannunsa ya juyo da kaina.
“Da alama dai kunyar nan zata cutar da ni”
Ya sumbanci goshina ya shinshina hancina kamar mai kokarin tantance wani abu. Rufe ido na yi jikina ya hau bari ina jin wani bakon al'amari. Hakan kuma be hana shi kai bakinsa cikin nawa, sai da na ji yana kokarin wuce gona da iri tukuna an matsa baya na rike hannunsa.
“Abdull za a iya ganinmu fa”
“Babu wanda zai gani bakin gilashi ne”
Ya sake kai hannunsa a jikina sai na tare.
“Baba zai ga na dade”
“Me yasa kike ta guje min ne Noor? Kin san how long nake ta jiran wannan ranar? Ni fa yanxu halalinki ne”
“Na sani amman ban tare ba, kuma na fito gida ne da sunan zaka yi magana da ni”
“An riga an daura ko da sadakin da na biya kin zama mallakina balle kuma an daura, sadaki shi ne aure ai wasu da zarar an biya sadaki ma suke sakewa juna balle mu da har an daura mana aure”
“Auren dai shi ne gaskiya, amman biyan sadaki ba aure ba ne, tun da har ana daura mana ai ya kamata mu yi hakuri har zuwa lokacin da za mu tare babu dadewa”
“Allah yasa zan iya jira, sai monday zamu bar garin nan Noor, kuma ba wani abu zan aikata da ke ba a yanzu, it's just a kiss, ina kokarin wayar da ke kamin mu tare domin na lura kamar baki gama fahimtar rayuwa ba”
Na yi murmushi karfin ina mamakin yadda yake da rawar jiki haka, kuma ina yaba kokarin Hafiz na jurewa da yayi ashe shi din jarumi ne sosai. Na matsa ta gefen da kofar take na bude na fita.
“Sai da safe”
“Sai da safe my shy Bride, an hana ni kiss ko? Zan rama”
Murmushi na kawai abun da na yi na fara takawa ina tafiya har na isa cikin gidanmu. A dare wata kanwar