Showing 9001 words to 12000 words out of 133189 words
bata jindadin yadda kike fadar sunanta, ko ba komai ta girme ki ya kamata ki ce mata Yaya ko maman wane”
“Ba ni da tarbiya Hafiz, ai kasan wacece ni ka san gidanmu miyasa ka yarda ka auro ni? Ko an maka dole ne? Ka raba ni da wanda yake so na ka kawo ni cikin gidanka kuma kana son ka kuntata min, zafin rabuwa da masoyina zan ji ko bakinciki zama da kai”
Tsayawa yayi kallona irin kallon nan na mamaki.
“Baki da tarbiya Noor, ba a fada miki muhimmancin aure da zama da miji ba, shiyasa kike kallona kai tsaye ki fada min maganar da duk ta zo bakinki, to ni ba irin Kareem ba ne, iskancin da matarsa take masa kwatarsa ba zan dauka ba, ba zan taimake ki na tsamoki daga wannan gidan da unguwar ta ku ba ki zo nan ki hana ni kwanciyar hankali, shiyasa ana kusan auren nan sai da na ce a fasa kika ce a a mahaifinki zai iya fushi da ke, saboda Mahaifinki.... ”
Sai kuma yayi shiru, idona cike da kwalla na ce.
“Ka karasa mana ka ce mahaifina mai kwadayi ne, saboda ya siyar da mutuncinsa ya siyar da nawa, kana da hujja na siye shi da kudi, amman ni har abada ba zaka taba iya siye ba Hafiz ba zan taba sonka ba”
Na wuce shi na shige dakina ina kuka, na bakinciki da Baba ya janyo min daman na san Hafiz ba zai taba ganin kimata ba, duk mace da ta samu uba irin nawa bata dace ba. Na bata minti talati akan gadona ina kuka sannan ya shigo dakin rike da plate din taliyar da na dafa yana nuna min.
“Wane irin abinci ne haka? Gishiri yayi yawa kamar zaki yanka halshen mutane? Kuma kin bar kitchen kacha kacha ke baki san ki gyara guri ba? Idan baki canja rayuwa ba Noor Wallahi zaman gidan nan sai ya miki wahala, tashi ki tafi ki girka min wani abincin”
Na tashi zaune ina kuka.
“Ni ban iya kalar girkin da kake so”
Kamar abun arziki sai na ga ya aje plate din hannunsa ya zauna kusa da ni yana sauke ajiyar zuciya ya fara rarrashina.
“Shikenan ya isa, yi hakuri na taba amarya hmmm a yafe min kin ji yar Amaryata”
Ya kwantar da ni jikinsa sannan ya ce min na tashi mu yi wanka, na san manufar hakan domin ya gwada min ba sau daya ba. Na yi saurin naje jikina daga na shi na tashi daga jikinsa na matsa. Sai ya tashi ya dauki plate din ya fice daga dakin. Ya dade kamin ya sake shigowa ina kallon yadda ya sakawa kofar dakin key hankalina ya tashi na mike tsaye kan gadon ina kallonsa...
#KhadeejaCandyPAID PAGE 4️⃣
©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024
Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar
And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....
You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153
_______•••_______
Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona.
“Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you”
Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi.
“Zo mana Noor...”
Na matsa can nesa ganin ya mike tsaye, ina ganin ya doso inda nake ya rikona na fara masa ihu iyakar karfina irin da na tsira yi masa a duk lokacin da ya nuna zai yi forcing kansa a gareni, sai dai a duk lokacin da na fara ihun yana saurin saki na ya kyale ni ba kamar wannan karon ba, da ya rike sai ya rikide min kamar ba shi ba ya sakar min karfinsa na kasa motsa hannuna ma ihun kawai nake iya yi, kamin mu ji ana dukan kofa da karfi kamar za a ballata, can kuma aka dawo gurin windows din ana bugawa da karfi. Sakina yayi dan dole ba dan ya samu abun da yake so ba, ya sauka daga kan gadon ya dauki rigarsa ya saka ya bude kofar dakin ya fita, ni kuma na tashi zaune na gyara rigata na ina jan numfashi da karfi. Aisha ce ta shigo dakin da gudunta
“Noor Lafiya?”
Na rumgume jikina ina hawaye sai ta juya ta kalleshi.
“Barristers miye haka? Da yamma haka? Wane irin rashin hakuri ne? Sati daya da aka yi a bangarenta be wadatar da kai ba sai ka nuna mata fin karfi da ido na ganin ido? Kowa ya san halin da kuke ciki? Mai gadi ne fa ya fada min ihun da yake ji a nan yayi yawa naje na duba? Yanzu wannan ba abun kunya ba ne? Kuma duk zaman da ka yi be wadatar ba sai ka shiga hakkina? Yau fa zaka bar nan, daga yin auren kuma sai ka fara abu kamar karamin yaro ko wanda ya fita hayyacinsa? Me kake haka Barristers kanka farau auren budurwa?”
Ta fashe da kuka ta fice daga dakin, sai ya juyo ya watso min wani mugun kallo.
“Kin ga abun da kika ja ko?”
Na sauke kaina kasa.
“Ke wai wace irin yarinya ce? Wawuya kawai sakarya, marar hankali marar tarbiya”
Uffan ban ce masa ba, ba dan kuma bana jin zafin kalaman nasa ba, sai dan na san nice marar gaskiya a nan, be kamata na yi ihu ba amman kuma kiyayyarsa da tsoron da matarsa ta ba ni ba zai bari na zame masa yadda yake so ba. A fusace ya fice daga dakin, ni kuma na kwanta a gurin ban tashi ba sai da aka yi kiran sallah Magariba bayan na yi sallah na fito daga dakin na sai na samu plate din abincin da ya zuba a dazun aje a gurin, kadan na ci na ji gishiri kamar zai yanka halshena da sauri na zubar kasa na kasa hadewa na nufi kitchen da sauri ina taba kofar na ji ta a rufe da makulli a dole na dawo dakina na shiga bandaki na wanke bakina ina mamakin yadda gishiri yayi yawa haka domin na dandana abinci a lokacin da na gama girkin ban ji gishiri haka ba. Dawowa na yi na zauna a dakina domin zuciyata bata raya min cewar Aisha zata iya kara min gishiri a abinci ba balle na zarge ta, da ma dai ace bama zaman lafiya ne, wata kila kuma jika yayi a yanzu shiyasa yayi yawa.
Bayan sallah Isha'i na sake fita na taba kofar kitchen din sai na same ta a rufe da alama da Hafiz ya rufe kitchen yayi tafiyarsa ya bar ni da yunwar cikina. Ni nake kamar zan iya jurewa na dan lokaci ne zai hakura ya dawo min da keys din ko kuma ya shigo ya bude min idan ya gaji. Saboda haka na shiga dakina na kwanta cikin tsoro domin wannan ne karo na biyu da na kwanta ni kadai a bangaren bayan kwanan da na yi na daren farko a gidan. Washe Gari na farka da tunanin yadda za'ayi ni ma kanwata Hana ta zo ta rika taya ni bachi idan baya bangarena saboda na rage kadaici kamar yadda ita ma kanwarta Ni'ima take tayata kwana, na yi ta jiran tsammanin ko ko Hafiz zai leko bangare ya duba lafiya kamar yadda yake duba lafiyar Aisha kullum amman shiru ko da yake ni idan yana nawa bangaren yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa.
“Kanwata ya kike?”
“Lafiya kalau”
Ta yi fuskar tausayi.
“Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?”
Na daga mata kai.
“Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa”
“Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa”
Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta.
“Aisha ki ce yayi hakuri”
“Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci”
Na zaro ido da sauri gabana na faduwa.
“Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba”
“To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi”
Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai.
“Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji”
“Taya zai ji? Ba zan fada masa ba”
Na girgiza kai na lake kafada.
“Ni dai ba zan je ba”
“Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin”
“Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min”
“Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister”
“Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min”
“Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri”
Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare giďa. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji.
“Lafiya Amarya?”
“Hafiz yana nan?”
Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye.
“Eh yana nan? A kira Miki shi?”
“Eh ina son na yi magana da shi”
“Toh”
Ta aje plate din giďar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min.
“Yace ki jira shi zai yi wanka”
“Tohm”
Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi....
Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai...
**** **** ****
Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi.
“Wa'alaikusalam”
“Sannu da gida”
“Yauwa sannu dai”
Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera.
“Kin gane ni kuwa?”
Yusura ta yi murmushi yake.
“Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right”
Safeena ta yi murmushi.
“Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne”
“Gaisuwa...? Ko dai murna?”
Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta.
“Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura”
“Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?”
“Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara”
Yusura ta yi murmushi.
“Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa”
Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin.
KAREEM POV.
A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa.
“Sannu da zuwa...”
Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali.
“Ga Safeena ta zo gaisuwa”
Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa.
“Safeena? Me kika zo yi nan?”
“Gaisuwa...”
Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena
“Ashe Momy lokaci yayi”
“Haka Allah ya so”
“Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi”
Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice.
“Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka”
Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira.
“Okay...”
Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa.
“Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba”
“Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona”
“Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba”
“Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?”
“Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....”
Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki.
“Aurenta ya mutu ne?”
Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki.
“Me