Showing 15001 words to 18000 words out of 133189 words
da kusan zan iya cewa tawainiyata ma muka sha hira muka koshi, ina ta sake saken yadda zan saci kafa na tafi na ga Mama babu hali, domin na san Baba zai yi fada idan ya dawo be tarar da ni ba, dole a wayar Yaya na gaisa da ita har nake tambayarta ance zata yi aure.
“Da yardar Allah kuwa Noor, idan lokaci yayi ai dole za a fada muku”
“Mama yaushe zaki zo?”
“Yaushe aka yi auren ma balle na kwashi kafafuwa na tafi Noor? Ni fa uwace ba zai yiyu na tafi gidanki ba sai da dalili”
“Amman Mama kin ji Baba yayi wuta?”
“Uhmmm Allah ya kyauta gaba, Noor ki rike aurenki da mutuncinki, idon mutane yana kanki kowa jiran yake wani abu ya faru da ke, kuma kin ga zaman gidanku nan ba shi da dadi, da alama kuma mijinki mai hankali ne da tunani, kishiyarki kuma ki rike ta da mutuncin kuma ki yi taka tsantsan da ita, ki rika kula da rayuwa na san halinki da sakarci, balle kuma an dauke ki an kai ki gurin babbar mace ina yarinya karama, ta fiki wayo ta fiki hankali kuma ta fiki sanin kan mijinku, ki bi a hankali kuma ki rike addu'a kar na ji kar na gaji wani abu ya faru, kuman ko da wasa bana son na ji kin bibiye Zafeer aure ya rabaki da kowa yanzu”
“Toh Mama, zan kiyaye, Zafeer ni ba zan taba yin magana da shi ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi masa magana”
“Toh sai ki kiyaye, ki zauna lafiya a gidanki kin ji?”
“Toh Mama”
Sallama muka yi sannan ta kashe wayar na mikawa Yaya.
“Mahaifiyar Kareem ta rasu ko Yaya?”
“Eh kwana uku aka yi ai ba a bude restaurant din ba, sai da aka yi sadakan uku duk mun je masa gaisuwa”
“Yayi kuka?”
“A gabanmu zai yi kuka? Sai dai a boye ko? Kin masa gaisuwa”
“Hafiz be bari na tafi ba matarsa kawai ta tafi, wata kila sai nan gaba idan na fara fita”
“Kila”
Saman sama muke taba hirar Yaya na fada min Kareem din ya rame sosai abun ya taba shi. Na yi zaton Hafiz zai dawo da rana ya dauke ni saboda yayi min zancen girki amnan shiru be zo ba sai bayan Isha'i a lokacin Baba har ya gaji da jiransa. Yana yin sallama Baba ya tarbeshi jiki na rawa suka gaisa sannan ya shiga nuna masa gidan yana fada masa yadda gobarar ta fara.
“In shaa Allah zan kira ka Baba sai mu yi magana na ga abun da ya dace ayi”
“Na gode Allah ya saka da alheri ya kara rufa asiri...”
Baki har kunne baba yake Fadar haka, sai dai ko kadan ban ga alamar sake fuska a gurin Hafiz ba, yadda yake rawar jiki da Baba ma wannan karon ban ga yayi haka ba. Ba Baba kadai ba ni kadai na yi tsammanin zai bawa Baba kudi ko kuma ya ce akai Hana asibiti amman ba ko daya har muka fito gidan. Na shiga motarsa shi ma ya zagaya ya shiga sai da yayi min wani kallo da ban fahimci ma'anarsa ba sannan ya tashi motar muka fara tafiya.
Ban kalleshi ba, sai dai na ji a jikina yana yawan kallon gefe da nake zaune.
“Noor na ga kin bata rai, ko kin yi marmarin gida ne?”
Na yi shiru bance komai ba, hannu na ga ya mika bayan motar ya dauko kwali ya dora min a cinya.
“Ya kamata ke ma ace kina da waya ko?”
Na kalli kwalin wayar na kalleshi ina zaro ido.
“Tawa ce?”
Ya daga min kai, sai na rasa ina zan saka kaina tsabar farinciki domin taba rike wayar kaina ba. Yana faka mota harabar gidan na fita da sauri na shiga bangaren Aisha ina nuna mata wayar, sai ta fini farinciki da jindadi ma ita ta taimaka min na saka sim din ta nuna min yadda ake operating wayarsa.
#KhadeejaCandyPAID PAGE 6️⃣
©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024
Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar
And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....
You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153
_______•••_______
“Allah ya tsare ya sa albarka”
Ta yi min addu'a sai na amsa da amin sannan na karbi wayar bayan ya saka min number shi da number Baba da kuma na Aisha.
“Amman fa karki je ki kira Saurayinki da wayar nan na sa halinki”
Ta fada tana min wani kallo kamar na zolaya, ni kuwa na kalli Mijina na kalleta da mamaki.
“Ya za'ayi na kira sho kuma? Na fa yi aure yanzu na sani”
Ta sake fuskar zolaya tana min wani kallo na rashin yarda.
“Ke dai kin san yadda muke sirrinmu ko? Kawai dai ki kiyaye, ke matar aure ce a yanzu kin ji kanwata”
Na amsa mata da tohm domin kawai na takaita zancen sannan na mike tsaye rike da wayar da kuma jata na fice daga bangaren. Ina shiga bangarena na tare a kujera ina ta kallon wayar bude nan taba nan hotunan da na yi kuma sun fi a shirin a zama daya. Ima tsaya da daukar wani hoton sai hango Hafiz na yi ta cikin hoton ya leko kansa. Na juya na kalleshi ina dariya shi ma dariyar yayi ya matso kusa da ni ya zauna.
“Daukin wayar ne har yanzu”
“Eh na gode Hafiz”
“Ki daina cewa Hafiz Noor”
“Tohm Yallabai”
A bakin gaskiya ta na fada sai dai na lura kuma hakan dariya ya saka shi domin dariyar yake kamar na fadi wani joke.
“Ur Welcome..”
Ya kama hannuna na rike ya juyo da kafadata daya na fuskance shi da kyau.
“Noor, please karki ba ni kunya i trust you, kar na ji ko na ga abun da zai bata min rai wayar nan, ba ma waya kadai ba a komai ma, kin ga Aisha ta fada min abubuwa da kika fara fada mata akan zamantakewar duka duka kuma yaushe muka fara zaman auren? Sirrin dake tsakanina da ke na mu ne mu kadai kawaye iyeye ko abokiyar zama babu wanda zai sani, wanda ke tsakanina da ita kuma ita ma zata rike babu wanda zai sani, kin ga da farko na ji haushi amman daga baya na yi tunani hankalinki da tunaninki ba irin nata ba shi, saboda shekarun ba daya ba, amman ina son na ja kunnenki karki fadawa kowa sirrinmu kin ji? Kuma zancen baki so na kika aure ni na san wannan ita ma ta san wannan ba sai kin yi ta nanata mata ba kina fada mata yadda na raba ki da saurayinki, yan'uwana ba su san irin auren da muka yi ba, so bana bukatar su san cewar wai baki so na kika aureni kinji”
Na daga mishi kai.
“Me tace na ce”
Na tambaya ina mamaki, domin ban san na taba fada mata wani abu a game da Hafiz ba, yo ni da har yanzu ba mu taba hada shimfida ba ta ina zan fada sirrinsa? Kuma yaushe nake fada mata yadda ya raba ni da Zafeer.
“Cewa ta yi kin kura min ido kamar zaki cinye ni”
Ya ja hancina hana kallon cikin idona. Na sauke kai kasa.
“Baki jin yunwa ne? Ko kin ci abinci a gida?”
“Aa ban ci ba, kai baka ci ba?”
“Ban ci na so ki dawo ki girka, ni ma ban samu dawowa ba sai daren nan”
“Girki cikin dare akwai wahala kamin ka fada na yi bachi”
“Wa zai dafa?”
Na dan saci kallonsa na sauke ido, ba dai yana nufin ni na girka ba? Ganin na yi ya mike tsaye.
“Taso muje mu siyo wani abu a waje”
Na mike tsaye ina rike da wayata, a nan na bar jakar da na dawo da ita daga gida. Hannuna ya kama muka fita daga falon be sake ba har gurin motarsa ya bude min na shiga sannan ya zagaya ya shigo ya kunna motar sai kuma ya kalleni.
“Bari na tambaya Madam ko za a siyo mata wani abu”
“Tohm”
Yana fita na fara daukar kaina hoto a motar, be jima ba ya dawo ya ja motar muka kama hanya. Na yi zaton zamu tafi Kareem Restaurant ne sai na ga ya faka a wani restaurant da ban sani ba, ko'ina na gurin wuta ce mai calar blue da ja daga waje. Ciki kuma farin haske ne irin wanda ko allurarka ta fadi zaka iya gani. Sai da ya fara fita sannan ni ma na fito muka jera a tare muka shiga.
“Me kike son ki ci?”
“Ice Cream”
“Ice Cream ai ba abinci ba ne”
“Ni idan na ci shi ya ishe ni, sai kuma nama”
Muna tafiya ina fada ina rabon ido, katon guri ne aka yi kowa bangare abu dabam ne, idan zaba sai ka tafi gurin biya ka biya sannan ka fice. Gurin masu pizza ya fara zuwa ya daukar mana daya, ya nufi shawarma ya dauki biyu, sannan muka nufi gurin masu kaza dake cikin gilashin tana juyawa kawar wata karuwa.
“Ba mu daya”
Ya fada sannan ya kalleni ya ciro wayarsa aljihu da hannu daya ya matsa can gefe yana amsawa. Mutumem ya gama yanka kazar ya saka a leda sai ya miko min, na waiga na kalli saitin da yake tsaye yana wayar da murmushi a fuskarsa da alama da Madam yake waya domin ita ce kadai zata iya saka shi irin wannan murmushi kuma ta dauke masa hankali. Ban bi ta kansa ba na nufi gurin masu ice cream ina duba wanda ya fi girma a jikin hoton dake gaban box din, domin sai ka zaba sannan za a dauko maka.
“Wane ya fi dadi?”
“Kowane ne yana da dadi yan mata, amman dai ki dauki vanilla ice cream mata sun fi son shi”
Na ji an fada daga gefena, na juyo na kalleshi sai ya sakar min murmushi.
“Can i pay”
Na girgiza masa kai alamar no, sai ya bata fuska kamar mai magana da yarinya.
“Why? Baki son na samu lada?”
“Kai Malam Lafiya”
Hafiz ya fada tun kamin ya karaso ni da shi muka juya kallon Hafiz din da ya daso gurin da saurinsa.
“Waye wannan? Yayanki ne?”
“Mijina ne”
Ya matsa nesa da ni ya kalli daga sama zuwa kasa.
“Duk kyaun nan naki, wannan ne mijinki”
Ban ce masa komai ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba ya nufi gurin biya ya bar shi a gurin tsaye.
“Waye wannan?”
“Ban san shi ba, yau na fara ganinshi ni ma”
“Amman ai magana na ga kina yi da shi”
“Tambaya yayi zai iya biya na ce aa ni matar aure ce”
Hafiz ya kalli gurin da mutumen nan yake tsaye, shi ma kallonmu yake kamin ya karbi katinsa a fara saka masa kayan a babbar leda.
“Mu tafi...”
Na wuce gaba yana bayana muna isa gurin Mutumen ya karbi kayansa ya fara tafiya.
“Oga Abdull ga canjinka”
Daya daga cikin masu karbar kudi a gurin ya fada yana mika masa canjin 750.
“Keep the change”
Ya fada ba tare da ya juyo ba. Hafiz ya ciri Atm dinsa ya biya kudin aka fara saka mana a babbar leda, a nan na samu damar satar kallon mijin na wa, ni ban taba lura da yanayinsa kyau ko muni ba dress ko yanayinsa, gaba daya babu ko daya a gabana sai yau da mutumen nan yake mamakin ni din matarsa ce. Kuma gaskiya ya fada Hafiz ba shi da wani kyau na azo a gani, ba laifi dress dinsa na zamani riga da wando, kuma yana ta kamshi ba laifi ba zaka kira shi baki ba haka kuma ba fari bane.
“Muje”
Ya rika duka ledodin gaba ya saka ni sai da na fara fita sannan ya fito. Kamin mu isa motar na hango yarinyar nan da Zafeer yake yi ma gyaran mota tana doso gurin, ita ma kallona take kamar yadda nake kallonsa da alama ita ma dai ta gane ni kamar yadda na wayance ta.
“Noor ko?”
Ta fada yana nuna ni a lokacin da ta karaso kusa da ni. Na daga mata kai ina murmushi Hafiz ya kalleta.
“Wacece wannan?”
“Waye wannan Yayanki ne?”
Ita da shi kusan a lokaci daya suka yi tambayar kowanensu yana kokarin sanin abun da ke tsakanina da daya.
“Mijina ne”
Na fara amsa mata jiki a sanyeye ina jin babu dadi domin ta san alakata da Zafeer. A take na ga yanayinta ya sauya kamar mai mamaki kamar kuma bata jidadin amsar tawa ba.
“Zafeer...”
Sai kuma ta yi shiru...
“Allah be yi da shi ba, Noor shiga mota mu tafi”
Hafiz ya fada rai a bace yana ba ni umarni. Na nufi motar ina jin wani abu marar dadi ya tokare min zuciya. Kamin na isa gurin motar hawaye ya cika idona har ya fara zubo domin ta tuna da abun da nake kokarin mantawa da shi a kankanen lokaci, mutumen da ba ya kunyar nuna soyayyata a gaban kowa. Tsaye ta yi tana kallonmu har sai da muka bace mata. Kaina a kasa yake har muka isa gida na ki yarda na dago dan kar Hafiz ya ga hawayen dake min zuba, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuncin dake zuciyata ba, domin yanayina ya sauka ba kamar yadda muka fita ba.
“Mutumen nan kamata yayi ki fada masa kina da miji tun farkon da yayi miki magana, kin san kina burge maza for no reason me ya ba zaki kama kanki ba? Ke komai sai an fada miki sannan zaki yi? Aisha tana da gaskiya be kamata na baki wayar nan a yanzu”
Ban ce masa komai fadansa sai kara min zafin hawaye yake.
“Ba ni wayar...”
Ya miko min hannunsa yana kashe motar. Sai da na hade yawu sannan na mika masa wayar.
“Zan baki amman sai nan gaba idan kin yi hankali, yanzu ko na barki da ita hankali ba zai kwanta ba, ai na ga darasi gurin abokina mata ba ku da amana if not taya kina tare da ni zaki zubar da hawaye saboda da wani da ba zai iya zaman aure da ke ba, ba zai iya miki rabin abun da na yi miki ba”
Na kalleshi.
“Amman zai ba ni farinciki, irin wanda ba zan taba samu a gidanka ba, da baka bar ni tsaye ba ka je kana waya da munafukar matarka ta ya wani zai min magana? Ko kuma an rubuta a goshina na ne cewar ni matar aure ce? Wayarka kuma ka aje bana so ko da nan da tsufa ne, idan ba ka yarda da ni a yanzu ba ba zaka taba yarda da ni ba har abada”
Na bude motar na fita a fusace na bar masa kofar a bude ba tare da na rufe ba. Falon na shiga na zauna kan kujera gaba daya na rasa me ke min dadi. A kan kujerar da nake zaune ya watsar siyayyar da muka yi.
“Noor For the very last time karki sake kiran Aisha munafuka, ko ba komai ta girme ki, ta cancanci girmama daga gurinki, balle kuma tana matata, ba zan yarda ki shigo gidana ki rainata ba, babu kalar soyayyar da bata nuna miki ba, idan baki gode ba karki zage ta ba zan yarda a raina min uwargidana ba uwar yayana, ki tsaya matsayinki...”
Uffan ban ce masa ba na tashi na shiga daki na kwanta kan gadona ina kallon OPO dake dakin hawaye na zubo, haduwata da matar a nan ya tuna min da waye Zafeer a gurina, abu da duk wanda ya san alakarmu zai yi mamakin ace ba shi na aura ba.
“Miye wannan?”
Ya tambaya a tsawace dagowar da zan yi ya watso min wani abu mai kamar magani a fuska da wata roba. Na tashi zaune na dauki maganin mai kananan yaya na duba, sai wata roba da ban gama sanin ta miye ba guda biyu, roba na fi duba domin ta yi min kama da balloon sai dai ta banbanta da ballon sosai, ba kuma zan iya fadar ko ta miye ba domin ban san amfaninta ba. Na sake duba maganin shi ma wani kalar magani ne mai 2 colors da ban taba ganin irinsa ba.
“Miye wannan.?”
Ya daka min tsawa har sai da hankalina ya tashi, gaba daya fuskarsa da hallitarsa sun canja jikinsa har rawa yake kamar zai doke ni.
“Ban san ko miye ba...”
“Karya kike munafuka, a jakarki na ganshi yanzu waya baki ina kika siya?”
Na girgiza kai amman na kasa magana domin tsoron fushinsa da nakr gani a yanzu ya cika zuciyata. Furta cewar a jakata ya gani ya saka na sauka da sauri da zimmar na tafi na duba jakar tawa da na bari a falon sai na ji ya fisgoni iyakar karfinsa na wulgar da ni kan gadon.
“Ina zaki je? Ba zaki fada min ba? Uban waye ya baki wannan maganin? Ina kika siya? Mi ya kawo condoms a jakarki?”
“Wallahi ban sani ba... Ba.. Ba.. Ban saka.. Magani ba... Ni ban...”
Na kasa magana tsoro da kuka suka ci karfina, ban san me yake fada ba maganin ne condoms ko kuma robar, ko ma duka? To miye illarsu? Miye kawo su a jakata? Taya? Ya hauro saman gadon da talkaminsa ya riko ni da duka karfinsa.
“Ina kika siye Noor? Saboda me kika siya?”
“Ban saya ba, ban san amfaninsa ba, ni ban saka komai a jaka na ba, ban san maganin miye ba, ban san robar ta miye ba, ba nawa ba ne Wallahi”
“To ina aka samu ya aka yi na ganshi a jakarki?”
Na rike hannunsa daya jikina na rawa.
“Wallahi Wallahi ba nawa ba ne, ban san miye ba”
“Da na aje ki gidanku ina kika je?”
“Ban tafi ko'ina ba Wallahi”
“Amman kin yi magana da Zafeer?”
“Ban yi ba, Wallahi ban ga Zafeer ba”
“To wannan abun su suka kawo kansu a jakarki kenan?”
“Wallahi ban san na miye ba, Hafiz sai idan saka min shi aka yi a jaka..”
Fwauuu ya buge min baki.
“Ban ce ki daina fadar sunana ba? Ke gaba daya kanki babu tunani babu tarbiya babu hankali? Gaba daya baki da lissafi? Waya saka miki maganin to? Waye? Ko ki fada min ko na ci ubanki da duka Wallahi”
“daga gida ban je ko'ina ba, kanwata kuma ba zata saka min wannan abun ba, ni da