Showing 81001 words to 84000 words out of 133189 words
Chapter 28 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete
Mama ta cika min ciki da wasu kayan mata har sai da kaina ya fara ciwo. Haka na kwashe kwana biyu ana ba ni abubuwan nan da bana bukata, ban kuma isa na ce aa sai a rufe ni fada.
A cikin kwanakin da na yi a gida bayan daura auren, babu ranar da Abdull baya zuwa da dare a kowa dare kuma sai yayi kokarin taba ni har ya wuce gona da iri. Baba yayi min nasiha da kuma jan kunne, ranar Lahadi Mama ta aiko da mota aka dauki zuwa gidanta ta yi nata nasihar, acan na kwana sai washe gari na dawo. Na dawo gidan na tarar Hana ta gyara min kayana ta kintsa komai, a take na fara jin kewar gidanmu duk kuwa da kasancewar ba wani dadin zaman gidan nake ji na.
Ranar Monday da misalin karfe 2pm Abdull ya iso gidanmu tare da wani abokinsa da kanensa mata biyu da sunan za su dauke ni. Sai Baba ya tsayar da shi jege suka tattauna, ban san me suka tattauna a kai ba, bayan sun gama na fito ina sanye da green abaya da mayafinta sai mask da na saka na rufe fuskata. Handbag dina tana hannuna tare da wayata da karamin akwaitin da yace da shi kadai zamu tafi a yanzu saboda jirgi zamu shiga.
Yace daga baya zai aiko da mota a dauki saura kayan nawa da kuma yan'uwana domin su ga gurin da muke rayuwa. Da ace ina da iko da tun a yanzu zan tafi da Hana domin ta rage min kewar gida da kuma bakuntar gurin da ban sani ba. Na yi kuka sosai ina jin kamar wata kasar zan tafi ba iya Lagos ba. Har gurin mota Baba ya rako mu tare da Hana da Umma, na shiga gidan baya tare da kanensa shi kuma yayi ma Baba sallama ya shiga front seat kanensa kuma yaja motar sai airport....
Ban taba ganin airport a fili ba sai a ranar da muka isa gurin, ashe babban guri ne mai hada hadar jama'a mun zauna a wani guri jiran jirgin bayan an gama yi mana check-in. Id card din dake hannuna nake ta kallo, sai dai zuciyar da tunanin yana can wani guri. Hannun Abdull na ji cikin nawa yana kokarin saka yatsunsa cikin nawa.
“Amarya are you Okay”
Na kalleshi sai na ji hannunsa a fuskata yana share min hawayen da ban san taya suka zubo ba.
“Har kin fara missing din gida ne?”
Ban yi magana ba na kalli kanensa dake can gefe zaune suna ta hirarsu, jira suke har sai jirginmu ya tashi sannan su koma gida.
“Ka yi min wani alkawari”
“Cewar ba zaka taba cutar da ni ba”
“Me yasa kika fadi haka Noor”
“Ba komai ni dai ka yi min alkwarin rike ni amana, ina fatan wannan auren da muka yi mutuwa ce kadai zata raba”
“In Shaa Allahu, na miki alkawari ba zan taba cutar da ke ba Noor”
Ya ba ni tabbacin da nake bukata sannan ya amsa kiran dake shigowa wayarsa ban san da wa yake magana amman na ji yana fada masa lokacin da zamu sauka. Ni kuma na juyar da kaina ina kallon wani gafen.
Kalamansa sun saka na ji hankalina ya kwanta, na samu natsuwar da na rasa.
Na sani mutum ba zai taba samun abun da yake so dari kan dari ba, shiyasa na yarda da wannan kaddarar kuma na shiryawa wannan zaman aure da dadi babu dadi zan zauna, ko da Abdul zai rika yanka naman jikina ya siyarwa ne. Zan jure ko wace kalar azaba da ukuba ko da kuwa ita ce zata yi silar ajalina...
An samu delaying gurin tashin jirgin, karfe biyu da mintuna goma sha biyar ya kamata mu tashi amman ba mu tashi ba sai misalin Karfe uku daidai muka tashi daga filin jirkin saman Aminu Kano, bayan mun yi bankwana da yan'uwan Abdull, har na ji ina ma ace ni ma nawa yan'uwan sun rakoni kamar yadda na shi suka yi. Abdull ne ya saka min belt ya sakawa kasa ya rike hannuna ganin yadda nake jin tsoro sosai lokacin da na yi arba da jirgin for the first time.
Sai da muka yi nisa da kasa sosai jirgin ya fara tafiya sannan ya cire min belt din shi ma yhttps://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0
PAID PAGE...
©️KhadeejaCandy
©️®️Copyright
2024
Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar
And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....
You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153
_______•••_______
Abdull ya miko min hannunsa na rika na fita, na yi zaton Zafeer zai wuce ne sai gashi ya fito daga motar ya rufe yana kallon gidan.
“Wannan ai zai wadace ku kai da kake ta complain yayi muku karami”
Abdull ma ya fara kallon ko'ina.
“Ni kam yayi min karami, na fi sha'awar baban gida wannan ai ba zai wuce daukar mota biyu ba”
“Haya ce fa, ba gidanka ba ku biyu ne kawai”
“Haka zan daure dole mu yi maneji ai, shigo ka ga cikin mana”
Kamar zai ce aa sai kuma ya kalleni sai ya fara takawa Abdull ya ja hannuna muna wuce cikin karamin gidan zaman mutum daya. set din kujeru ne falon sai kayan kallo da firjin, kitchen din ma ba wani mai girma ba ne sosai dakin kuma two bedroom ne kawai ko wane da toilet dayan dakin ne kadai yake da gado dayan kuma babu komai a ciki.
“Gidan nan yayi datti”
Cewar Abdull yana kallon yadda kura ta bata ko'ina.
“Sai ku gyara ai”
Zafeer ya amsa masa.
“Wane irin mu gyara na fa fadawa mai gadin cewar ya gyara mana gidan, bari na dubo shi”
Ya saki hannuna ya fice daga falon, sai ya rage daga ni sai Zafeer, hakan ya saka na ji falon ya mana kadan domin har yanzu ina jin kunyarsa, bana son hada ido da shi saboda haka na sauke kaina kasa ina wasa da yatsuna.
“Wannan ne aure na biyu ko?”
Na dago na kalleshi da sauri. Ashe ya gane ni kuma ya san ni din ce, to me ya fi wannan kunya? Na yi shiru na kasa amsawa.
“Haka zaki yi ta yi Noor, har sai kin ji aure ya fita ranki, a lokacin ne zaki gane kin yi ma kanki babbar illa na rabawa zuciyarki da ni saboda kwadayin abun duniya, yanzu ma mai kudin kika sake aure ke dai kokarinki ki gujewa talauci”
“Ina ta kokarin na samu damar yi maka bayani Zafeer Wallahi babu..”
Be bari na karasa maganar da nake da in'in'in kuka ba ya katse ni.
“Damar me? Wane irin roko ne ban miki ba? Wace kalar bibiya ban miki ba? Kin sani son ki jinin jikina ne Noor kin san halin da na shiga da kika juya min baya? Ke da mahaifinki kuka biyewa son zuciya da kudi, kika rufe ido daga ganina Noor, ba ki amsa maganata saboda wasu mutane sun zo daga sama sun nuna miki kudi sai kika ga kamar sun fini daraja, suka raba ni da ke kuma su ba za su iya rikonki ba, haka kuma zaki yi ta aure saboda babu wanda zai iya dake sai ni, babu wanda ya san ki a yadda na sanki Noor... Ni kuma din sun lalata mana komai bana ma son ganin fuskarki”
Na share hawayen dake min zuba.
“Na san yanzu ka daina so na, amman kana fahimta idan ina maka magana Zafeer..”
Nan ma dai be bari na karasa ba.
“Da kenan Noor, yanzu kin fado daga zuciya da hannayen da suka rike ki, ko sunanki bana son ji”
Na runtse ido ina jin zuciyata na min zafi, yau ni Zafeer yake cewa baya son jin sunana ma. Ina jin takun tafiyarsa ya nufi kofa ya bude ya fita. Bude idanuwana na nufi kujera na zauna na dafe kaina ina kuka, a haka Abdull ya shigo ya same ni sai ya zauna kusa da ni da sauri yana tambayar me ya faru.
“Na yi kewar gida, na yi kewar kowa da kowa, na fara jin kadaici tun a yanzu”
Ya kwantar da ni jikinsa.
“Kukan ya isa haka Noor ko dazun da zaki fito mota da hawaye kika fito, nan da kwanan biyu zaki saba”
Na daga mishi kai ina kuka a jikinsa. Sai Magariba muka yi wanka na huce gajiya, ya fita ya nemo wani abun ci, da kuma kaji manya da fura mai dadi irin ta gorar nan da ta sha Nono, sai ice cream da zallar madara mai sanyi. A tare muka ci abincin sai dai ban wani ci sosai ba saboda tunani da damuwa dake kokarin hana ni farinciki a daren farko a gidan sabon mijina.
Bayan mun gama na kira Mama muka gaisa ta yi mana maraba da sauka, sannan na kira Baba shi ma muka gaisa. Shi ma ya kira nasa familyn suka gaisa. Safeena ce kira ta karshe da yayi har yayi ya gaji ya aje wayar bata amsa ba. A tare muka yi sallah Isha'i sannan ya saka kayan bachi ni ma na saka muka fito falon muka zauna muna kallo.
Dan karkatowa na yi kadan na kalleshi.
“A ina ka san mutumen da ya kawo mu dazun?”
Ya sosa hancinsa da da hannunsa dake rike da remote.
“Zafeer wai?”
“Eh”
“Ba dade da zuwa gurin da muke aiki ba, matar da ya aura mahaifinta shi ne mai kamfanin, so shi ya turo shi a koya masa wasu abubuwan kuma a nuna masa yadda gurin da ma'aikatan suke, kamin su tashi wuce New York, kuma da ya zo sai ya zama jinina ya fi dahuwa da na shi, cikin kankanen lokaci muka shaku, har baya son na yi tafiya”
“Yana da kirki”
Na fada ina kwantar da kaina jikinsa.
“Yana da shi gaskiya, akwai mutunta mutane, kin ga ai shi ya dauko mu, ko wacan zuwan da na yi shi ya dauko ni Airport, ko na ce ya bar shi sai yace Aa ba komai ba ne, ba wani abun yake yi da na hau taxi kara ya dauko ni”
“Amman be taba zuwa gidan nan ba?”
“Eh sai yau, ina dai ba shi labari ne a lokacin da na so n samu wani gidan nan canja saboda yanzu mun zama mu biyu ba kamar can da da nake zaune ni kadai ba sai baki idan sun kawo ziyara, wannan kuma ai zaman aure zamu ko?”
“Wannan gidan ma ya wadatar, babu matsuwa ai tun da Mu kadai ne”
“Haka ne Amaryata”
Ya sumbanci hannuna ni kuma na yi murmushin karfin hali. Ina sauraren yadda yake ta aika min sakwannin har sai da ya ji kamar falon ya mana kadan sannan ya kama hannuna muka koma daki.
A daren ne na karbi bakuncin Abdull ban hana shi hakkinsa ba saboda ina tsoron kar na sake afkawa a cikin halaka irin na wacan karon.
Hakika na ji azaba na ji wani yanayi na dabam, sai dai be kai yadda Aisha ta yi ta koda min a wacan karon da nake farko aure ba. Da gari ya waye sai na rasa ya zan yi domin ni bakuwa ce a lamari na rasa ya zan yi na kula da kaina, bandaki na shiga an rufe na zauna a gurin ina hawayen da a yanzu ban san na minene ba, gaba daya jikina ya mutu.
Shi kuma be farka ba sai karfe bakwai na safe. Ina zaune a kasa har zaman ya gundire ina tunanin tashi ya turo kofar dakin yana mika da hamma da alama bachin be wadace shi ba.
“My soul me kike yi a nan? Na dauka kina falo ma”
“Babu ruwa a bandakin kuma gurin zafi yake min ban san ya zan yi ba”
Na fada ba tare da na kalleshi ba.
Ya taba fanfo ya murda ruwa be kawo ba.
“I'm sorry ina jin sai an tada gen, bari na dora miki ruwa zafi”
Sai da ya tada gen din ya dora min ruwan zafi sannan na iya gasa jikina na yi wanka na fito cike da karfin hali. Ganin karfe tara saura na safe ya saka ni cira kafa na dauko hijabina a akwati na gabatar da sallah asuba, a zato ya shiga dayan bandakin ne dake dayan dakin yayi wanka yayi alwala har ya gama sallarsa, ashe yana can kitchen yana hada mana abun karyawa.
Ina sallamewa ya shigo dakin, ta madubi nake kallon murmushinsa har ya karaso inda nake zaune, ya rumgume ni ta baya.
“My Soul my joy... Shi ne kika yi sallah baki jira ni ba?”
“Na yi zaton ka yo sallah ne”
“Aa ke nake jiran ki fito ai na shiga bandakin na yi wanka da alwala, ina tsoron na ce zan shiga ki ce zaki ji kunya domin na lura baki son hada ido da ni ma”
Ya sake ni ya nufi wayarsa ya duba sannan ya aje ya shiga bandaki yayi wanka ya fito yayi sallah, sai na gaishe shi.
“Ina kwana”
Ya taso daga inda yake zaune ya dawo kusa da ni ya zauna ya kama hannuna ya rike yana sumbanta.
“You drive me crazy my soul, na yi mamakin yadda na same ki kamar baki taba aure ba”
Na kara jin kunya ta rufe ni. Ya leki fuskata.
“Ko dai baki taba sanin komai ba sai akaina? Ko kuma tsananin gyara ne?”
Nan ma ban amsa ba.
“Ba zaki amsa min ba?”
“Ban taba ba”
Ya bude ido sosai irin na mamakin nan.
“Mijin da kika aura ba?”
Ba tare da tunani ko fargabar komai ba na fada masa irin zaman da na yi a gidan, sai ya cika da mamaki yana ta yaba hakurin Hafiz.
“Wannan shi ne garabasa, amman duk da haka gaskiya mutumen da kika aura mai hakuri ne, ni ba zan iya hakuri da wannan ba ko kadan, bana iya daukar wannan”
Na masa murmushi kadan ina mamakin idan baya iya hakuri taya yake iya wata hudu, uku a nan kamar yadda ya fada ba tare da matarsa ba. Ko da yake irin wannan hakurin kamawa take na dole ne. Shiyasa ya damu ya kara aure.
Akan ce aure dace ne, a yanzu kam ina ganin kamar na dace domin Abdull yana mutunta yana nuna min so da kauna, idan zai fita zan raka shi har gurin motarsa idan ya dawo kuma na tarboshi zai dawo min da tsaraba a kullum haka yake. Girkin ma da ke babu dadi ko ya chabe wani lokacin haka zai ci ko ya siyo wani abu be taba nuna min ransa ya bace ba ko kuma ya rufe ni da fada.
Abu daya ne zuwa biyu illar Abdull, shi ne an rashin son ibada, da azuba sai dai na yi sallah na bar shi idan ya farka misalin 8 ko 7 yayi duk yadda zan tashe shi ba zai tashi ba. Na kam lura idan ya dawo daga aiki yana rama sallah azahar kamin yayi La'asar wani lokacin ma sai ya kai magariba yake hadawa yayi, a tsawon zamana da shi ban taba ganin ya bude kur'ane ko da a wayarsa ne ya karanta ba. Sai kuma rashin kishi domin baya son ina saka hijab idan zamu fita shakatawa ko siyen wani abu ko kuma idan abokansa suka zo, yana yawan fada min wai shi yana son abokansa su san wayayin mata yake aure, ya nuna min rayuwar Lagos rayuwa ce da babu ruwan kowa da kowa.
Kuma na lura haka din ne, domin idan muka fita ina gani mata da wando ko guntun skirt, ni kuma ina dora hakan ne a mu'auni na banbancin yare, addinin da kuma al'adarmu ba su zama daya ba. Dole hakan ya haifar da banbancin abubuwa dama, amman shi ya kasa gane haka ya dauki rayuwar Lagos ya sakawa kansa kamar ba bahaushe ba.
Ba mamaki ta kan iya yiyuwa saboda yawan abokai mata da yake da su ne, yana da females friends da yawa, kuma suna saka kananan kaya wanda kusan ita ce 70% na suturar mutanen garin.
Ba illa ba ne idan ya bukaci na saka masa a gida, idan zamu fita sai na saka after dress a sama ko gown. Duk yakin duniyar nan da zan yi ba zai taba yarda na fita da hijab ba, sai dai guntun mayafi kamar wata budurwa. Ko da yake abayar ta kan rufe min jiki, gashi ni kuma din ba mai kiba bace balle na ce ta bayyana surata.
Mun sha ziyara har mun gode Allah bokansa sun yi ta kawo mana ziyara sosai, musamman na gurin aikinsu maza da mata, idan za su zo hotel yake tafiya ya siyo abinci, kamar kala biyu ya kawo na zuba a kulolin da ya siya min sabbi domin ban zo da komai ba, sai tufafi su ma atamfa ne sai laces kananan kayan a garin ya siya min su.
Ba ni da wata matsala da Abdull sai ta rashin sallah kamar yadda na lura tun farkon zuwana gidan.
Ina jin nauyin fada masa kuskurensa gudun kar ya fahimci a abun abaibai, har sai da na fahimci ba shi da niyar gyarawa sannan na fara nuna masa masa muhimmancin sallah da illar da barinta yake kawowa, cikin hikima da dan gutun ilmina.
Idan na fadi hadisi ko karatun wasu malamai akan sallah sai na ji ya karasa min, da alama ya san komai ba zahili ba ne, kawai dai shedan yayi nasara a kansa ne ta wannan bangaren. Na kara jajircewa ina tunatar da shi a duk lokacin Sallah ko da kuwa baya gidan. Ya kan dan motsa yayi Sallah a cikin lokacinta wani sa'in, musamman idan weekend ne yana gida tare da ni a tare muke yi. Sai dai a yadda na lura kamar takurawar da nake masa bata masa dadi kawai dai yana min kawaici ne yana yi saboda yana son farincikina.
A kwana a tashi hausawa suka ce hasarar mai rai, a haka mu ka kwashe wata uku a gidan, ni kam kadaici ya hana ni na saba da gidan har yanzu, gashi ta inda muke makota na duk yarbawa ne babu wasu kuma ibo ne bana jin yarensu basa