Showing 129001 words to 132000 words out of 133189 words

Chapter 44 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

271

na fara Umma kuma ta saka salati yana tabi da rike baki...





Pay 500 to
2451879008
Zenith Bank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.Ya rigata isa domin shi yake son magana da ita a yanzu, a yanzu ikon a gurinta yake hakan ya saka ta bata masa lokaci na tsawon mintuna arba'in sannan ta shigo gidan. Yana tsaye ta window falon yana kallonta har ta fito motarsa ta turo kofar falon ta shigo.

“Lafiya kake son ganina?”

“Me kike so Safeena”

Kamar jira take sai ta sauke gyalenta ta aje jakar a kujera ta nufo shi tana nuna shi.

“Kai Kareem kai nake so!”

“To miye matsalarki da Noor? Miyasa kike cusata a cikin matsalarmu?”

Ya tambaya ba tare da ua juyo ba hannayensa duka biyu suna zube a aljihunsa.

“Saboda Noor ce ta raba ni da kai, Noor ce macen da ta cike gurbina da ita, kuma ita ce ta kashe min auren da takardar kawai ya rage Abdull ya ba ni”

“Ban cike gurbinki da na noor ba, wani gurbi na gina mata mai kyau mai tsabta, mai cike da kauna da soyayya, dan Allah ki cireta a cikin matsalarki”

Har lokacin da yake maganar be juyo ya kalleta ba.

“Ita ce babbar matsalata a rayuwar nan Kareem, ta lalata min aure tun da mijina ya dauki yaran nan ya tafi da su ya auna jininsu be sake dawowa gidan nan ba, last week ya aiko kanensa ya dauki yaransa biyu aka bar karamin da na haifa da kai, yanzu haka mijina yana garin nan amman be tako kafarsa gidana ba, ya daina min aike ya daina kulani baya amsa wayata baya ba ni amsar sakona, na sani saki na zai yi bayaj ya gama kwance min zane a kasuwa, zai saka kowa ya tsane ni a danginmu saboda abun da na aikata Mijina cousin dina ne, kuma duk sanadin Noor ce ne domin ita kadai ta san sirrina ita kadai zata iya fallasa wannan”

Ya juyo ya kalleta.

“Ta aikata kuskure na fahimta, mu ma mun aikata dukanmu mutane ne, amman saboda me zaki lalata rayuwar kanwata me ya shigo da kanwarta ciki? Kina da tabbacin Abdull din ne ya aikata?”

Ta matsa kusa da shi tana masa wani kallo na tsana for the first time.

“To waya aikata kai? Ko kuma dai ita ta aikatawa kanta?”

“Baki da tabbacin Safeena karki jefa rayuwarki a matsala”

Ta yi wani shu'imin murmushi.

“Na san komai Kareem kai ka san wacece ni, ina da tabbaci mana, a gabana ka kira kawata ina jin muryarka lokacin da kake fada mata cewar wata yarinya kake son ta yi ma wankin ciki ka mata allura amman dai ka fi son a wanke saboda ka samu tabbacin komai ya zube, ka fada mata kaddara ce ta hau kan yarinyar fyade aka yi mata ko ba haka ba?”

“Ita Juwairiyya ce ta fada miki haka?”

“No Wallahi bata fada min komai ba, amman na ari wayarta na duba bangaren kira sai na ga number ka, daman kuma na ji muryarka domin wayarta ana ji duk abun da mutum ke fada sound din kiranta a karshe yake, lokacin da na duba zuciyata ta fada min Hana ce, there is no way da zai saki Noor da ciki ba tare da wani abu ba, kuma ya fadawa yan'uwansa wai ta tayar masa da fitina ne sai ya sake ta shi kuma ya sake ta saboda TA KI ZAMAN AURE, kana ganin hankalina zai dauka? Idan babu wani abu me zai saka Noor ta fada masa cewar dan da na haifa ba na shi ba ne? Mw zai saka yar'uwarta ya yanke karatunta da duk wani gata da yake musu ta dawo ita da kanwarta su zauna a gida? Daman ni ban yarda ba na san akwai wani abu a kasa, domin na san waye mijina ba kasafai yake iya rike kansa ba, a tsawon watanin da yake a Lagos da sunan aiki na san me yake aikatawa, kawai na zuba masa ido ne saboda babu yadda zan yi, kana tunanin namiji zai saka al'adar neman mata a gaba kamar yadda Abdull yake kuma ace matarsa bata sani ba?”

Ta share hawayen da suka zubo mata cikin daga murya ta cigaba da fadar.

“Neman matansa ya taimaka min gurin bibiyarka da kokarin kulla alaka da kai Kareem, na san yana neman mata tun kamin na aure shi, na aure shi ne saboda an matsa min a gidanmu na yi aure, kai kumaka guje ni, duniya ta min zafi, shi kadai ne mutumen da ya zo zai share min hawaye a lokacin, bayan mun yi aure ya zama bana burge shi saboda ya saba da matan waje, mijina ba shi da lokacina, baya ganin kyauna, ba ya ganin ado na, kullum idonsa akan matan waje ne, mijina baya iya gamsar da ni yadda kake min Kareem, gaba daya ban yi dacen rayuwa ba, amman a haka nake zaune kullum burina idan har na bar Abdull kai ne”

Wannan karon da cinyar hannu ta goge hawaye idonta na dama.

“Na san na yi kuskure na haihuwar ba ta sunna ba, dukanmu yin yi kuskure amman sai mu rumgumi wannan kaddarar, nan gaba kadan Abdull sakina zai yi, to sai ka aure ni mana Kareem”

Ya juyo da kyau ya fuskance ta.

“Ba zan taba aurenki ba, amman zan tabbatar maki da abu daya, Noor ba zata aure ni ba, saboda bana cikin mazan da take so, please ki cireta a cikin matsalarki”

“I don't care ka auri Noor ko karka aureta ba matsalata ba ce, abun da kawai na damu da shi, shi ne idan Abdull ya sake ni zaka aure ni”

“Har abada ba zan taba aurenki ba, aure ya haramta a tsakaninmu”

Ta rausayar da kai tana murmushi.

“Na fahimci hakan ai, shiyasa na bullowa ubanta ta wannan sigar na fada masa gaskiya kuma na kwadaita masa dukiyar da zai samu idan ya Abdull ko mahaifinsa suka bukaci a sirrinta abun, na samu wata kawata muka je a zuwan ita ce nurse din da ta cire ciki, kuma na samu kudi mai kauri na ba shi. Ka ga yanzu hankalin Abdull zai koma gurin abun da ya aikata ne ba wanda zai aikata a gareni ba, kuma idan ya fallasa sirrina duniya zata zage mu a gaba dayanmu mu uku, kai ni da kuma shi”

Kareem ya sasauta fuskarsa ba dan tsoron furucinta ba sai dan yana son ta fahimcin illar fa hakan zai mata ba mijinta kadai ba. Ya busar da iskar bakinsa ya jin kirjinsa na ciwo sosai.

“Ki rika yin tunani kamin ki aikata abu, kina da yaya Safeena, tun farko baki rike aurenki kika biyewa shaidan muka aikata alfasha, hakan be wadatar da ke ba sai da kika ga mun haihuwa, yanzu gashi abun ya dawo yana bibiyarmu, kuma duk yadda wannan abun zai taba ni be kai yadda ke zai miki illa ba Safeena, saboda ke mace ce ni kuma namiji ne, shiyasa da Allah zai ambacin mazinata a kur'ane sai ya fara da mace, domin ita ce mai rauni kuma ita ce mai shiga kaso 90 na matsala sama da namiji”

“Zaka aure ni Kareem? Ka min alkawari kawai zaka aure ni Wallahi zan yi duk yadda zan iya mahaifinta ya janye shari'ar nan”

Ya cire hannunsa daya a aljihu yana nuna mata.

“Let me make this clear to you, idan har zan sake wani aure a rayuwata, to mace daya ce zan aura Noor, idan har ba zan auri ba ba zan sake aure ba, so ki saka a ranki ni da ke ba mu taba sanin juna ba, ba zan taba aurenki ba Safeena!!”

Wani mugun kallo take masa zuciyarta na bugawa da karfi. Cikin ihu da takiya ta ce

“Ba zan saka ya janye shari'a ba Kareem kuma zan daukar masa lauya, domin ina bukatar abun da zai daga hankalin Noor ya zubar da mutuncinta da na iyayenta ya kashe auren uwarta ya jafata a matsala, ba ni da makiyaya a duniya irin Noor yarinyar da saboda ita igiyar aurena take rawa? Saboda ita juya min baya, yar sikar yarinya shashasha mahaukaciya, yarinya da bata kai ta goge talkamin kafata ba, yarinyar da bata kai ka rika hannunta ba, amman ita kake so? Yarinyar da ubanta baya jin wani yare sai na kudi? Yarinyar da ubanta be san wani mutuncin ba sai na kudi? Yarinyar da babu komai akanta sai hauka da gidadanci, fasika da bata iya komai ba sai bibiyar mazan mutane yarinyar da...”

Tassssss ta ji saukar lafiyayyen mari a fuskarta daga hannun masoyinta Kareem, Wani irin numfashi taja da karfi ta kai hannu ta dafe kuncin hawaye masu zafi na sauko mata. Cikin wani irin bacin rai da Kareem be san yana da shi ba ya nuna ta da yatsa ya ce.

“Kul bakinki ya sake kiran Noor dita da wata kalma marar kyau, iyakar kiyayar da kike mata saboda tana da alaka da ni ne, ni kuma ba aurena zata yi ba, ki fadawa mahaifinta karya kike ya janye shari'ar nan idan ba haka ba...”

Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya duba farincikinsa ce take kira wato Noor, ya amsa wayar ya kara a kunne shi ma dai sound din kiransa a karshe yake kamar yadda na mutane da yawa yake a manyan wayoyin yanzu.

“Kareem ka yi magana da Baba? Me ya fada maka?”

Sai da yayi iya yadda zai ya danne yakin dake zuciyarsa ya amsawa Noor da murya mai sanyi.

“Na yi magana da shi be yarda ba, amman zan sake samun shi gida mu yi magana karki daga hankalinki”

“Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...”

Safeena ta fada da karfi, Kareem yayi hanzarin kashe wayar, fuska a hade ya jefawa Safeena mugun kallo da idanuwansa da suka gama canjawa. Wani marin ya sake kai wata, ya saka kafarsa ya kwashe nata kafafuwan sai da ta fadi kasa, ya daga kafarsa ya daki bayanta sai da ya amsa, sannan ya cire belt din jikinsa ya fara zuba mata ba ji ba gani...
Duka yayi mata sosai kamar wani ubanta sannan ya fice ya barta a gurin tana ihu tana kuka. Motarsa ya shiga ya kama hanyar tafiya ganin yarsa domin ya san a yanzu su kadai suke rage masa, aikin ma baya jin zai iya tafiya a yau tun tashinsa baya jin lafiya balle kuma yanzu da abubuwa suke juye masa. Sai da ya shiga unguwa ya ji ba zai iya karasa family house dinsu ba, nesa da gidan ya faka mota ya kwantar da kujerarsa ya jinke hannunsa ya rufe ido yana nadamar dukan da yayi ma Safeena, domin be tana kai hannunsa yayi ma mace duka irin wanda yayi mata a yau.

Yana cikin motar ya aka kira sallah azahar sannan yaja motar daker yana jin kansa na ciwo kamar zai tsage gida biyu ya isa masallacin unguwar yayi sallah ya sake komawa motarsa, sannan ya karasa gidansu. A harabar gidan ya faka motar ya kashe yana kallon flowers din da suke gabansa amman zuciyarsa tana can wata duniyar. Wayarsa ya ciro ya duba number Noor ya sauke ajiya zuciya ya kai sau takwas sannan ya danna na aika mata kira cikin tsoro jikinsa har rawa yake.

Shiru yayi bayan ta daga kiran, sai kuma ya rasa me zai fada mata, ya zai fara mata bayanin komai ya zai wanke kansa, ta ina zai fara fahimtar da ita, be ma yi tsammanin zata amsa kiran ba.

“Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!”

“Noor”

Zai yi magana ta yanke kiran, runtse ido yayi sosai, ne bude ba sai da ya ji an bude gate din gidan, direban dake dauko yaransa daga makaranta ne ya dauko su ya faka a inda ya saba faka motar. A yake Kareem ya nemo kwarin guiwa da juriya ya sakawa zuciyarsa ya bude motar ya fito cikin karfi hali yake takawa yana murmushi ya nufi yaransa da suka nufo shi suna.

“Oyoyo Dady Dady Dady”

Kamin ya karasa gurinsu su ma su karaso gurinsa ya yanke jiki ya fadi kasa ribbbb.

“Dady.....!”

Tine ta saka ihu ta saki bag dinta da lunch box din dake hannunta ta kama mahaifinta tana kiran.

“Momy Hajiya... Anty Khadija... Yaya Aaryam... Dady na ya fadi... Dady...”





NOOR POV.

Sai da na zabura a lokacin da yayi hanzarin yanke wayar, kenan yana tare da Safeena har yanzu? Kuma yake fadar yana so na? Yake fadar ya tuba? Yake fadar yayi nadama? Me ya kai shi gurinta? Me yasa ma zai amsa wayata a gabanta.

“Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...”

Maganar Safeena ta sake nanata kanta a kunnena, zai iya zama gaskiya shiyasa dazun ya daure ni da kalamansa, namiji zai iya aikata komai domin ya samu biyan bukatar kansa. Na mike tsaye zuciyata na raya min Safeena ce matar da Baba yace ta same shi da maganar, ita kuma ta ji ne ta gurin Kareem.
Ya fada mata sirrina kamar yadda ya fada min nata, me yasa yake haka? So yake ta jefa ni a matsala ta yadda zan rasa kowa sai shi kadai shiyasa yake taimako na a ko da yaushe? So yake na rasa kowa na zama tare da shi shi kadai, shi kuma sai ya juya ni a yadda yake so? Yanzu na gane dalilin duka taimakonsa na gane manufarsa, na gane buri da bukatunsa.

Sai bayan Sallah azahar sannan kiran Kareem ya shigo wayata, na sani daman zai kira ko ya zo domin kare kansa, kuma na shiryawa duk wata karyarsa sai na ga iya gudun ruwansa. Na amsa kira sai yayi shiru ba tare da ya ce komai ba.

“Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!”

Na fada masa kai tsaye hawaye na zubo min zuciyata na zafi because this is the most hardest words i had ever said to someone, who's there for me in every Situations, rabuwa ce irin wanda rai be so ba amman dole na yi.

“Noor...”

Zai yi magana na yanke kiran ba tare da na tsaya na saurari abun da zai fada ba. Na dafe zuciyata ina kuka he's someone who's  always been a good friend to me, but the fact that i know yana da manufa na yin haka ya yanke duk wani hanzari, ya ture duk wani uzuri nasa, ba zan iya yarda na lalata rayuwa saboda namiji ba.
Karfin hali na yi na fita na siyowa Hana maganin zazzabi domin jikinta yayi zafi sosai fever ya rufe ta.

Ana gama sallah la'asar ban tsaya cin abincin rana da Umma ta sauke ba na yi mata karya cewar Zainab ta kira waya na kaiwa mahaifiyarta su yi magana saboda wayar mahaifiyarta ta lalace.

“Ki dawo da wuri, domin Babanki tun da ya fita be dawo ba har yanzu kin san kuwa yana hanya a yanzu, idan ya dawo be same ki ba, ke ce a ruwa”

“Ba zan dade ba In Shaa Allahu”

Na saka talkamina ina kara sirranta jakata dake boye a hijab dina na fice daga gidan, kai tsaye titi na nufa daman manufar ta samu dalilin fitar ne. Ina kokarin taron Napep na muka yi ido hudu da Zafeer zai karya kwanar gidanmu da wata kafirar mota mai kyau da kyalli. Wuce ni yayi ya shiga kwanar ni kuma na shiga Napep din na fada masa inda zai kai ni, yana tafe ina mamakin mi ya kawo Zafeer a nan ya domin tuni ya dauke iyayensa daga unguwar saboda likkafa ta yi gaba a wata unguwa mai kyau suke zaune a yanzu.

A kofar gidan Abdull kuma gidan Safeena mai napep din ya sauke ni na bashi kudinsa na shiga gidan bayan mun gaisa da mai gadin, har yake fada min bata dade da shigowa gidan ba. Da manifa biyu na zo gidan an roketa alfarma ta saka mahaifina ya janye ko kuma na yi mata ta karfi.
A bakin kofar falon na tsaya na bude jakata na dauko wayata na sakata a airplane mode sannan na kunna recording na shiga falon ina sallama, wayar na rike a hannuna.

“Wa'alaikumussalam, bakar macijiya me kuma ya kawo ki?”

Ta amsa min tana tsaye rike da maganin da ban san na miye ba a hannunta, fuskarta ta kumbura daga bakin inda yake ina kallo a jikin, fuskarta da kafadarta zuwa kafafuwanta da hannunta sun yi ja, alamar an mata duka.

“Magana na zo mu yi dan Allah ki saurare ni Safeena”

“Ina jinki”

Na matsa kusa da ita na fara mata magiya da raunaniyar murya.

“Idan kina tunanin wani abu ne a tsakanina da Kareem, Wallahi babu dan Allah dan girman Allah ki yi hakuri da abun da na yi miki, ina rokonki alfarma ki saka Baba ya janye shari'ar nan”

“Ashe kin san kin cutar da ni, wato yanzu kina son mu sasanta dan kar auren uwarki ya mutu kuma asirin kawarki ya tonu ku kunyata ko? Amman ke kika son kunyata ni, ki bara ni da abun da nake so, kin yi iya yadda kika iya har sai da kika fitar da ni a zuciyar Kareem, hakan be miki ba sai da kika auri mijina, hankalinki be kwanta ba sai da kika fada masa cewar dan da na haifa ba jininsa ba ne”

“Cikin fushi na fada masa hakan, kuma ba dan ya sake ko ya juya miki baya ba, kawai na fada ne saboda a lokacin raina yana bace ne, na bakinciki abun da yayi ma kanwata”

“Ai kin ci riba idan bibiyar mazan mutane yana da kyau kin gani ai, kin gaji kwadayi gurin ubanki, gaba daya kin firgita min tunani, kin saka Kareem ya tsane ni mijina ya tsane ni, mijina yana garin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login