Showing 132001 words to 133189 words out of 133189 words

Chapter 45 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

517

amman ya ki ya zo gidana, yau kuma Kareem yayi min abun da be taba ba, kin saka masa wani banzan hali da ba na shi ba, na tsane ki Noor”

Na risina kasa ina rokonta.

“Dan Allah ki taimaka min Safeena, Wallahi ba zan fadawa kowa cewar kin haihu a waje ba, dan Allah ki fadawa Baba karya kike ya janye shari'ar nan”

“Fadi na nawa kuma, ai kin gama fada tun da kika fadawa mai gayya mai aiki, kin fadawa Abdull ya sani to miya rage? Wato Kareem fada miki ni na fadawa mahaifinki haka ko? To be yi karya ba ni na fada, ni kuma shi ya fada min, ki daina biye masa kina yaudarar kanki ni dai na riga na harbo jirginsa, kuma babu abun da za a fasa idan kina son ubanki ya fasa shari'a to ki fadawa Kareem ya aure ni, ya kyale ki shikenan nake bukata sai ki samu salama idan ba haka ba kin fara ganin matsala kenan a rayuwarki tafi ki bar min gidana”

Ta fara turani, sai na tashi na share hawaye na fice daga falon, ban yi nisa da gidan ba na shiga contact list din na whatsapp na tura mata recording din da na yi saving sannan na buga mata warning.

“Ko dai ki fadawa Baba karya kike ki karyata kanki, ko kuma na tura audio nan a gurin surukarki da mahaifin mijinki da kanensa kuma da gaske nake na baki daga yau zuwa gobe”

Ina fitowa na cire airplane mode din na kunna data da domin sakon ya samu isa, sannan na tari Napep na shiga, gidan Mama na nufa domin labarta mata halin da ake ciki na tabbatar bata san wainar da ake soyawa ba, idan har ta sani zata kira ta fada min ko ta tambayi wani abu, wata kila ita ma idan ta saka baki Baba zai aminta ya sauko. Sai dai na yi rashin sa'a ban same ta a gidan ba, sai mai aikinta na samu tana kallo a falo.

Ruwa kawai na sha na kira wayar Mama, ta amsa ni ta fada min bata gidan tana gurin gaisuwa wata kanwar mijinta mahaifin Abdull ce ta rasu.

“Mama idan kin dawo ki kira ni akwai maganar da zamu”

“Ki jira na dawo, lafiya na ji yanayinki haka?”

“Mama bari sai kin dawo”

Kiran Mama na yankewa, sai ga kiran Baba ya shigo wayata ina dauka ya fara zagina yana tambayar ina na tafi.

“Ina gidan Mama”

“Maza maza ki dawo gida yanzu nan”

Na mike tsaye babu shiri na yi ma mai aikin sallama na fice. Tare muka fito gidan da Abdull yana cikin motarsa ni kuma ina tafiya a kafa, ban yi mamakin ganinsa ba domin gidan ubansa ne, kuma Safeena ta fada cewar yana gari. Sai dai abun da ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni a lokaci daya tsayar da ni da yayi yana son magana da ni, ashe karfin halin maza har ya kai haka.

“Magana ce kawai zamu yi Noor dan Allah ki shigo”

Na yi kamar ban san da wanzuwarsa a duniya ba domin babu wanda na tsana irinsa kallonsa ma idan na yi bakinciki nake ji.

“Zamu yi magana ne akan karar da mahaifinki ya shigar, ina nan ya kawo sammaci, magana ce da zata sama mana masalaha gaba dayanmu”

Na tsaya wata idea na zo min, sai na saka wayata a recording kamar yadda na yi dazun idan na samu yadda nake so, zan iya mixing abubuwa su tafi yadda nake so. A gurin da na tsaya ya faka motar ya bude min front seat.

“I know you hate me but please ki shigo mu yi magana magana ce ta sirri”

Na kalli gurin sannan na shiga na zauna.

“Na ga shigowarki, na so na miki magana amman na san ba zaki saurare ni a lokacin ba, shiyasa na jira har kika fito”

“Ka ce zamu yi magana akan abun da ya shafi Shari'a ne ba wani abu ba, idan baka ka abun fada zan fita”

Na fada a tsawace jikina har bari yake ji nake kamar ace akwai wuka kusa da ni na caka masa.

“Akan shari'ar da mahaifin ya shigar ne, baki tunanin hakan zai iya shafar ki ya shafi kanwarki? Ni fa ban aikata komai ba? Wane tabbaci kike da shi cewar ni na yi mata fyade?”

Na dube shi.

“Baka aikata ba karya ake maka?”

Sai yayi saurin dauke idonsa.

“Na ji na aikata, amman ai kaddara ce da bata wuce kowa ba, kuma ke kin san ba zan amsa wannan a kotu ba, kuma baku da wata shaida, na san ubanki ya shirya haka ne saboda kwadayi irin nasa, zan bashi kudi enough, ya janye karar nan karya bata min suna ni da mahaifina, abun da zai biyo baya ba zai muku dadi ba”

Kalaman da suke fitowa bakinsa sun karfafa min guiwar aje wayata a cinyata fa yadda sautin zai samu daukuwa da kyau.

“Sannu namiji wato har kana da baki da karfin halin da zaka min bazarana kuma ka cilasta ni ko mahaifina, bayan duk abun da ka yi? Ka keta haddin kanwata har ka yi mata ciki sannan ka kalli kwayar idona ka yi min barazana Abdull...!”

“Baku da wata hujja akan hakan, kuma fitar wannan zancen zai zubar mata da mutunci ne kawai, dan haka ki natsu ki tattauna da mahaifinki mu taru mu rufawa juna asiri, idan wani abu yake so zan ba shi”

Kiran mahaifina da kwadayayyen da suke ya fi komai kona min rai sai dai babu yadda zan yi domin Baba ne ya budewa kowa kofa. Sam na manta da ban saka wayata a airplane mode ba, sai da kira ya shigo wayar. Wayar ta kawo haske kiran yayi appearing saman screen recording din kuma daga tsayaki daman wayar ba a key take ba, tun da Kareem ya ba ni ita ban saka mata password ba. Na yi hanzarin daukar wayar amman hakan be hana shi gani ba, daga Safeena da take kira har zuwa Recording din da nake.

“Recording kike? Ina kika dosa Noor”

Na bude motar na fita da sauri sai ya bude ya zagayo kamin na yi wani yunkuri ya kamani da kokawa ya murde min hannu ya karbe wayar.

“Ka ba ni wayata Abdull”

Be kula ni ya rufe gefen da nake tsaye ya zagaya zai shiga motarsa na bishi ina fadin ya ba ni wayar.

“Ka goge recording din ka ba ni wayata”

Be kula ni ba ya rufe motar yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin bakinciki da nadama. Why I'm such a fool and idiot me yasa ma na yarda na yi magana da shi, no wait me yasa ban saka wayar a airplane mode ba kamar yadda na yi dazun.
Da kafa na taka na isa Family house din su Mama, a gidan na kwana gaba daya na rasa ya zan yi kuma na san idan na koma gida Baba zai rufe ni da fada ne wata kila har da duka. Abun da ban sani ba, ashe bachin da na yi a gidansu Mama na tsira ne, bachin na chanji ne daga wata kaddarar zuwa wata, ashe na bude wani sabon babin ne na kaddara, domin na wayi gari da mummunan labari...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login