Showing 21001 words to 24000 words out of 133189 words

Chapter 8 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

250

da Zafeer ba?”

“Aa Wallahi ban sake ganinshi, kuma Baba yace idan na sake magana da shi be yafe min ba, ance ma ya tafi baya garin nan”

“Akwai mai shiga dakinki ko ya taba jakarki?”

Na girgiza kai alamar aa.

“Dole akwai yadda aka yi Noor magani ba zai kawo kanshi ba, dole akwai yadda aka yi”

“Ni dai na yi zargin Aisha amman tace ita bata saka ba, ban san ya zan wanke kaina ba Kareem, yanzu baya min magana kuma baya shigowa gurina fushi yake da ni”

“Me yasa kika zargeta?”

“Saboda tace wai na fada mata sirrinsa kuma ban taba fada mata ba, kuma a gabansa tace na ce zan kira saurayina a waya kuma Wallahi ban taba ce mata ba”

“To kin taba barin jakarki a bangarenta?”

“Aa, amman Wallahi ban san a ina aka samu maganin ba, ni ban taba ganin wannan ballom din ba ban san me ake yi da shi ba”

Yayi shiru alamar tunani ni ma shirun nake ina hawaye.

“Kawo?”

Ya miko min hannunsa na bashi maganin da  balloon din ya saka aljihu, sannan ya dago ya kalleni ido cikin ido ya sauke ajiyar zuciya.

“Noor ba zan iya miki komai ba, sai dai na baki hakuri, akwai dalilin da ya san ba zan shiga maganar ba”

“Wallahi ban san wanda ya saka ba Kareem ba nawa ba ne”

“Na yarda da ke Wallahi Noor i trust you, ko ma waye yana son yayi amfani da innocent you ya cutar da ke, Hafiz ya san abun da baki sani ba a game da ni, ba zan iya shiga maganar nan ba, wata kila shiga ciki zai iya janyo miki matsalar da ta fi wannan ba, iyaye ya kamata ki samu da wannan maganar iyayenki ko nasa”

“Baba ba zai yarda ba, Mama kuma bata ma saurare ni, ban san gidansu ba, kuma idan naje wata kila ba za su yarda ba”

Ya busar da iskar bakinsa damuwa ta bayyana a fuskarsa.

“Kawai ki yi hakuro Noor ki tafi gida kar ma ki fada masa kin zo nan”

“Tohm”

Na share hawayena wasu na sauko min na juya na fara tafiya, sai ya kira ni.

“Noor”

Na juyo.

“Kina da kudin Napep?”

Na girgiza kai, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi 2k ya ba ni, na karba ina kallon matarsa take tsaye jikin windows din sama tana kallonmu, shi ma daga kai yayi ya kalleta. Na juya sai kuma na sake juyowa a karo na biyu na kalleshi.

“Kareem ya keke?”

Yayi min kallon rashin fahimta.

“Rasuwar Mahaifiyarka ban samu yi maka gaisuwa ba, amman abun yana raina, na san kai ma kana cikin wata matsala kuma na zo maka da wata am sorry...”

Yayi min murmushi kawai. Ban sake cewa komai ba na kama hanya ina tafiya hawaye na sauko min har na fita cikin gidan. Ashe haka auren yake, ashe haka rayuwar auren take? Idan mutum yana cikin matsala babu wanda zai saurare shi, babu mai kawo masa dauki, shiyasa Baba yayi ta ganawa Mahaifiyarmu Azaba kala kala kuma ake ta ba shi gaskiya a duk lokacin da za a fadi matsalar.

A lokacin da na tari Napep na hau sai fargaba ta ta koma gurin hukuncin da zarar tarar a gida, domin be min izini ba na fita gashi kuma dare yayi ban dawoda wuri ba, kuma abun da naje nema ban same shi ba. Dubu daya na mikawa mai napep din da ya kawo ni gida, ban tsaya karbar canjin ba na shiga ciki, ina hango motar Hafiz wani irin faduwar gaba da tsoro suka mamayeni, a haka dai na daure na karasa bangare na taba kofar falon na murda sai na ji ta a rufe na sake murdawa na tura na jita a rufe gam da alama an saka mata key an rufe ne. A gurin na sulale kasa na zauna gaba daya na rasa me ke min dadi.

Ina zaune a gurin na hango Aisha ta fito da saurinta ta nufo inda nake babu jimawa Barrister ya biyo bayanta, ina ganin haka na mike tsaye ina kallonsa fargaba ta saka ni gaba kamar ance ga mutuwarki nan zuwa.

“Ba magana make miki ba?”

“Wallahi Barrister ba zan yarda ba, ko dai ka bude mata ta shiga ko kuma na kaita bangarena ta kwana ko kuma ni ma na bar maka gidan, cikin uku dole ayi daya, yanzu duk abun da ya faru mutane ni za su dorawa laifi, ace na hana muku zama lafiya, babu wanda zai iya wanke ni, Wallahi sai na yi ma Walida tsinanen duka a gidan nan, sai da na gargade ta karta fada maka amman saboda kunnen kashe ne da ita sai da ta fada”

“Karki kuskura ki taba min yarinya, kuma ki cire bakinki ki cire idonki akan zamantakewarmu, ba ke kike aurenta ba ni nake aurenta”

Yana fada ya jefo min keys din, sannan ya nuna mata bangarenta.

“Wuce mu je”

Ta share hawayenta, ta dora hannunta a cikinta da be gama girma ba.

“Dan Allah Noor ki natsu, ko da baka son auren mutum ba haka ake rayuwar aure ba, be kamata ki fita baki fada masa ba, ki sani yanzu baki da ikon kanki ikonki yana gurin mijinkin ne, kuma idan ba ki yi dan Allah ba baki yi dan shi ba ki yi dan ni mana, Wallahi idan wani abu ya faru tsakaninku ni za a zaga, kuma a zarge ni”

Cikin kuka take maganar sannan ya juya ta nufi bangarenta. Tsaye yayi yana kallona irin kallon na tsana da jin haushin mutum, sannan ya juya ya shige bangaren nata. Ni kuma na sunkuya jiki babu karfi na dauki keys din na saka na bude kofar na shiga, na rufe na jingina da kofar falon suuuu na tafi kasa na zauna ina kuka...




KAREEM POV.

Tsaye yayi yana kallonta har ta fice sannan ya juya ya nufi hanyar shiga cikin gidan. Murda kofar ya shiga.

“Sannu da zuwa...”

Yusura ta fada masa, sai ya kalleta fuska ya yabo ba fallasa ya amsa.

“Yauwa”

Ta sabuntawa kanta wasu dabi'u da hallaya da bata masa a baya, kamar kaima masa abinci a dakinsa yi masa sannu da zuwa ko a dawo lafiya idan zai fita. Tun a wacan ranar da Safeena ta leko gidan duk wasu hallaya da dabi'u nata sai suka sauya. Ya wuceta zai haura sama sai ta juyo tana kallonsa.

“Ina tunanin a matsayina na matarka ina da hakkin tsare mutunci da martaba ta”

Ya juyo.

“Akwai wani furuci ko wani aiki da nake yi da ke zubar da kimarki?”

“Kamar zuwan yan matanka, ya kamata ka san ina da girma a matsayina na matarka”

“Noor Matar Hafiz ce, amaryarsa Safeena matar aure ce miye baki sani ba a ciki?”

Ta masa wani kallo sannan ta ce.

“Ga abinci can a dakinka”

Ba tare da ya sake cewa komai ba ya haura saman ya shiga dakinsa. ko'ina kamshin sinasir yake da miyar da ta ji nama da manshanu. Amman ko kadan be kula abincin ba ya cire tufafinsa ya shiga yayi wanka kmar yadda ya saba ya fito ya saka kayan bachi, daman baya dawowa gidan sai ya cika cikinsa.

(Idan kika karanta min littafi baki biya ban yafe ba.)

A daren ya kwanta da tausayin Noor da kuma tunanin yadda zai bullowa lamarin, ta ko wane bangare idan ya hango sai ya ga kamar shiga maganar zai iya zama matsala. Sai dai ya yarda da wani abu daya, Noor bata aje maganin a jakarta domin idan har ajewa ta yi ba zata bari ya gani ba, wata kila dai tsakanin Aisha da Zafeer akwai mai shirya mata wani abun bata fahimta ba. Washe gari misalin 7am ya bar gidan saboda operation da za su a 8am a asibiti. Be wuce 10 -15 Min da fita ba Yusura ta shigo dakin kamar yadda ta saba ta fara bude kayan abincin da ta kawo ta ga be ci, daman kuma ta san ba zai ci ba domin yar kullum ce be cin abincinta ita ma kuma bata fasa girkawa. Sai da ta fitar da kayan sannan ta dawo dakin ta nufi gurin da yake aje kayan dauda ta bude ta dauko green shaddarsa ta jiya ta zauna gefen gadon tana lalaben aljihun kowane bangaren. Domin zuciyarta bata natsu da abun da ta hango Kareem ya karba a hannun yarinyar da ta taba fasawa goshi ba jiya...







#KhadeejaCandyPAID PAGE 8️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______

Wani irin faduwa gabanta yayi a lokacin da ta yi arba da abun da ke cikin rigar aljihun Kareem. Me hakan yake nufi Kareem yana tare da yarinyar nan kenan? Ba ita kadai ba wata kila har da Safeena, matan aure yake bi kenan? Shiyasa yake takura mata a lokacin da take fita gani yake kamar ita ma gurin wani zata tafi? Anya ma wannan Amaryar Hafiz ce? Idan har gaskiya ne me zai saka yayi tarayya da ita?
Ta mike tsaye da sauri ta fice daga dakin rike da maganin da robar ta shiga dakinta sai da ta dauki wayarta sannan ta tuna bata da number matar Hafiz domin ba kowa take hulda da shi ba a cikin matan abokan Kareem, iyakar ta da wasu gaisuwa. Number wayar Samira ta nema ta kirata suka gaisa cikin mutunci sannan ta bukaci Samira ta turo mata da number Aisha matar Hafiz.

“Wai daman baki da number ta”

“Ban taba karba ba”

“Kai kawata baki da kirki, bari na turo miki yanzu”

“Yauwa na gode, Ai na san kuma good time da ita ba zaki rasa number ta”

“Okay”

Ta sauke wayar kamin Samira da ta kasance cousin dinta ta turo mata mumber Aisha har ta matsu. Sakon mumber na shigowa ta bude da sauri ta taba Number ta kira sai daf da zata yanke Aisha ta daga.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikusalam Aisha ya gida?”

“Lafiya kalau ya yaran?”

“Alhamdullahi kin gane mai magana?”

“Na so dai na gane, amman ban gane ba”

Yusura ta yi murmushin karfin hali.

“Yusura ce Maman Tine”

“Kawai ki ce min Mrs Kareem zan fi ganewa, uwargida ran gida”

“Oh oh toh ke ma ai uwargidance, ko da yake yanzu nake jin cewar Hafiz ya kara aure”

“Wallahi haka ne, kika ji ko dai Kareem ya fada miki, ai ke ma auna arziki kika yi da yanzu ke za a kawowa ita”

“Ban gane ba”

Yusura ta fada daman abun da take nema kenan. Aisha ta sauke numfashi.

“Hmmm ai mijinki ya so aurenta shi yayi sonta sosai, sai dai ban san miya hana shi aurenta ba, kwatsam Hafiz ya zo min da zancen auren, wai zai rufa mata asiri ya aureta saboda wanda zata aura an fasa auren sanadin Kareem shi kuma Kareem din yace ba zai aure ta ba, kin san mazajen na mu da hadin kai ko ma dai miye Allah kadai ya sani”

“Amman kika yarda Aisha?”

“au hanawa zan yi? Kin ji Yusura da wata magana, namiji da zai yi aure zaka iya hana shi ne? Ai idan namiji zai kara aure baya ji baya gani, shiyasa na nuna masa na fi shi tausayinta, na san waye Hafiz na gama karantar mijina daman kuma idan ka fahimci waye mijinki zaman aure ba zai yi ma mace wahala ba, shiyasa na goya masa baya dari bisa dubu aka yi komai aka gama cikin mutunci lefen ma ni na hadawa kaina na hada mata, yadda na san Hafiz ina daga hankalin na daga na shi zuciya zata iya dibarsa ya sallame ni gidanmu, amman hakan da na yi sai na siye zuciyarsa da ta yan'uwansa gashi muna zaune lafiya ni gani nake kamar ma ya fi so na yanzu sama da lokacin da be auri yarinyar ba, domin na kara value a idonsa”

“Toh Allah yasa yar gidan mutunci aka dauko miki kin san yan matan yanzu”

“Waya sani ance dai ubanta dai shegen kwadayi ne da shi ko kashe rai zai iya yi akan kudi, ita kuma gaskiya ance bata tsayawa kanta ba, kawai dai maza ne mace daya bata isarsu sun maida karin aure rayuwa, kuma basa tsayawa su duba yar gidan mutunci daukowa kawai suke, saboda tana da kyau”

“Oh Allah ya kyauta, matan zamanin nan sai a hankali”

“Ameen kedai ina nan ina lallabawa karta kashe min aure, ga yara ga ciki na tafi ina? Samun miji irin Hafiz a wannan mazanin ai sai an tona is rare gaskiya”

“Allah ya tsare miki aurenki, ni ai be fada min ba sai yanzu, na ce dole na kira na miki jaje”

“Hmmm na gode, zan yi saving number ki ai a rika gaisawa”

“Toh sai anjima”

Yusura ta kashe wayar gabanta na bugawa da karfi. What her husband got into? Ko shiyasa ta zo nemansa har cikin gidan kamar yadda Safeena ta zo? Me yake kokarin zama ne? Matan aure yake nema? Ta mike tsaye ta fara tafiya tana daga kanta. Amman ita miye nata a ciki idan ma neman matan yake yi? Kabarinsa dabam nata dabam, kuma bata fatan zama da shi har abada.

“Saboda yaranki...”

Wata zuciyar ta fada mata. domin saboda su ta dawo tana kokarin kyautata masa tun daga lokacin da Safeena ta leko gidan. Ji take indai tana raye ba zata iya bari Kareem ya auri Safeena ba ko da kuwa bata da aure domin Momy bata son Safeena ko kadan, mutuwarta kuma zai iya saka Safeena ta yi tunanin sake kulla alaka da Kareem. Gashi yanzu babu Momy babu mai masa fada idan yayi ba daidai ba.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Gaba daya ta rasa me ke mata dadi, ta rasa ina zata kama abun ya daure mata kai, wai saboda be sonta yake bin mata ko kuma dai wani sabon hali ne ya kirkirarwa kansa? Tunaninta ya kasa tsayawa guri daya.



KAREEM POV.

@4:11pm suka fito daga massalacin dake cikin restaurant din, Kareem na gyara hannun rigarsa ya ce.

“Ni dai da zaka dauki shawarata Barrister karka karbi case din nan, case ne mai matukar hadari kasan yadda yan siyasa suke”

“Amman za a samu kudi mai kyau fa Doctor”

“Rayuwa ta fi kudi muhimmanci, duk kudin da zaka samu idan ba zaka samu rayuwa ba ba su da amfani”

“Kusan kowane aiki akwai risk ciki, kawai dai ka taya ni da addu'a”

“Allah ya tsare, amman ni ban yarda ka karba ba gaskiya”

Hafiz ya tura kofar office din ya fara shiga yana fadin.

“Su suka neme ni fa, kuma saboda cancanta suka neme ni, ba zan oya watsa musu kasa a ido ba, abu na biyu ba a nan za'ayi ba a Kaduna ne”

Kareem ya daga kafadunsa.

“Indai ka nace sai ka yi ai babu mai hanaka, haka shi ne kawai matsalata da kai”

Yayi murmushi yana gyara zamansa a kujerar da ya zauna. Kareem yayi shiru na yan mintuna sannan ya kalli Hafiz cikin karfin hali ya ce.

“Hafiz ya iyalinka?”

Wani kallo Hafiz yayi masa a cikin kallon da yake masa idan yana tuhumarsa da wani abun.

“Lafiya?”

“Ka tabbata?”

Hafiz ya gyara zamansa.

“Akwai abun da kake son mu tattauna?”

Kareem yayi murmushi domin shi da abokinsa kowa ya san halin kowa, da zarar dayan ya fuskaci wani canja ko da na magana ne zai fahimci akwai manufar aikata hakan.

“Amm... Ban san ya zaka dauki abun ba, na so na bar maganar sai kuma nake ganin kamar zaka kone kanka ka cutar da iyalinka, be kamata na shiga cikin maganar ba amman dole ce ta saka”

Hafiz ya mika masa duka hankalinsa yana kallonsa.

“Lokuta da yawa idan ka ga In aikata wani abu da be dace ba kana yawan jan hankali kuma ka lurar da ni gurin da illar abun take”

“Ka wuce duk wannan Kareem fada min kawai”

Kareem ya zauna da kyau.

“Hafiz akwai wata matsala tsakaninka da Noor ne?”

Hafiz ya kalli wani gafen alamar tunani sannan ya kalli Kareem.

“Ta zo nan ne?”

A madadin Kareem ya amsa masa sai ya dora da abun da yake jin kamar shi ne matsalar.

“Hafiz ka rika bincike kamin ka yi fushi ko yanke hukunci”

“Kareem ta fada maka abun da ta yi?”

“I don't think Noor zata yi abun da kake tunani, she's very innocent, Hafiz bata ma san amfanin abun da ka gani a jakarta ba bata san me ake yi da shi ba, kuma abun mamaki ne ace ta san wannan a yanda take da kananan shekaru, she's too young for that ita ba karuwa ba ba matar da ta shekara hudu gidan miji ba”

Hafiz ya nade hannayensa.

“Idan bata sani ba taya suka zo a jakarta? Kasan dai ba za su kawo kansu ba ko? Idan ba ta siya ba maybe wani ya bata wani like Zafeer amman ta ki yarda ta fada wanda ya bata, ko kuma ya fada mata ta siya, ranar da na kaita gidansu ta wuni a ranar da ta dawo ne na karbi wayar da na bata kawai wata zuciyar ta raya min na bude jakarta and i did na ga abun a ciki”

“Taya zata amsa laifin da ba nata ba, bata san ya aka yi ya zo jakanta ba”

“Kai kuma ka yarda da ita?”

Kareem ya kasa cewa komai wannan babin saboda baya son ya janyo mata laifi gurin Hafiz.

“Ya kamata dai ka yi bincike, ta rantse bayan aurenta bata hadu da Zafeer ba ko ta yi magana da shi”

Hafiz ya kwanta jikin kujerar.

“Wa kake zargi? Aisha saboda ta fada maka Aisha, shiyasa na kirata ai lokacin da ta zarge ta kuma ta rantse a gaban Noor ba ta saka ba, sai me?”

“Maybe the way you confront her zai iya sakawa ta rantse ko da akan karya ne saboda ta wanke kanta”

“Me yasa ka yarda zata aikata amman baka yarda Noor zata aikata ba?”

“Saboda Noor bata waye duniya, da zaka ce min ta shiga gidan mutane ta yi arba da nama ta sata ko ta dauki wani abun dadi ta boye a jakarta zan fi yarda, amman ko kudi bana saka ran Noor zata dauka a dan fahimtar da na yi mata na kankanen lokaci Noor ba zata san miye abun da ke jakarta ba, kuma mace makira ce Hafiz na ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login