Showing 120001 words to 123000 words out of 133189 words

Chapter 41 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

255

son na fadawa kowa matsalarki, na miki alkawari babu wanda zai ji, dan Allah ki dawo na yafe miki kuma na fahimce a yanzu, Abdull ya sake ni, Hana kuma kin sani ina da ciki zan iya rayuwa zan iya mutuwa, idan baki dawo gida ba, ni ma zan koma ba, zan tafi na bar garin Kano ne, domin rashin izurin da na yi miki ya hana ni sukuni, ina kaunarki yar'uwata dan Allaj ki dawo, na miki alkawarin babu wanda zai ji”

Na saka number ya na dago na mika masa wayar ina kallonsa. Kwarjinsa da kirmarsa sun cika min ido, Kareem mutum har da rabin mutum, shi din mai tsayawa ne akan damuwata mai kokarin ganin bayan abun da ya hana ni farinciki.

“Na gode...”

Na furta ina hawaye.

“kwashe kudin ki tafi gida”

“Toh”

Na kwashe kudin na saka a jaka sai ya miko min wayar.

“Indai yar'uwarki tana sonki da gaske zata dawo ko ta kira ki tsakanin yau zuwa gobe, idan kuma bata kira ba, zamu yi amfani da line mu gano inda take, amman dai zata dawo na miki wannan alkawari ki kwantar da hankalinki”

Na daga mishi kai sannan ya karbi wayar na mike tsaye da cikina.

“Noor Zauna"

Na koma na zauna sai ya tashi ya nufi kitchen be dade ba ya fito rike sandwich da lemu ya janyo karamin lebur ya dora min a kai.

“Zaki iya cin wannan? Ko wani abun kike so a kawo miki? Jikina na rawa akwai yunwa a tare da ke”

Ban tsaya ba shi amsar zan iya ci ko aa ba na dauka na fara ci.

“Kar matarka ta dawo ta same mu a nan”

“Ba zata dawo ba. Yaushe rabonki da abinci?”

“Rabona da abinci tun jiya bana iya cin komai sai ruwa, gaba daya maza ba su da kirki, Zafeer be fahimce ni yanzu yana can yana cewa na ci amanarsa, na auri Hafiz ban jidadi ba, yanzu kuma wannan”

Ajiyar zuciya ya sauke ya bata rai sosai yana kallona.

“Wannan duk ya fi su zama dan iska, ni mana ban so aurenki da shi ba, kawai babu yadda zaka hana abun da Allah ya tsara faruwarsa ne, taya zai aikata duk wannan kuma ya sake ki? Ga cikin shi a jikinki”

“Ni na ce ya sake ni, ba zan iya zama da shi ba, ba zan iya zama da mazinaci ba”

Ina maganar ina kuka har na cinye duka sandwich din na shanye lemu na aje kofi, na mike tsaye Kareem be sake cewa komai ba. Ya dauki cups din ya kai kitchen ya kawo min tissue ma karba ina tsaka da goge hannuna ya jefa min tambaya.

“Noor ko da ya tuba?”

“Eh, ba zan taba iya zama da namiji mai neman mata ba”

“Kina da gaskiya, abu mai kyau na mai kyau ne, go ahead and live your life”

Na aje masa tissue a gurin na nufi kofar fita.

“Noor, kin san bana baki shawarar da zata cutar da ke ko?”

Na juyo na kalleshi.

“Daga gidan nan ki tafi gurin Mahaifiyarki kuma ki fada mata komai karki boye mata, ba zaki iya handle wannan ke kadai ba, you're too young for this”

Ban ji ina iya musa masa ba, saboda haka na amsa masa da kai sannan na juya na fice daga falon. Mai gadin ne ya bude min gate sai na nuna masa akwatina ya dauko ya ba ni na fara ja har na isa babbar titi na tari Napep na hau na fada masa umguwar da zai kai ni. A daidai gate din gidan Mama ya aje ni na ciro kudinsa na bashi ina jin marata na ciwo sosai.

Na fita ina jan akwatin na shiga cikin gidan, hankali be tashi ba sai da na shiga falonta, Mama tana cikin jindadi da kwanciyar hankali, rayuwar da bata samu ba a gidan mahaifinmu gashi a nan ta same ta, anya zan iya zuwa mata da wannan tsarabar? Kaddara ta shafi Hana, yanzu kuma ta shafi Mama...!! Na juya na fara tafiya bana son na zama silar mutuwar auren Mama, ta fada min jikinta be dauki mace a baki komai ba, face rigar da zai iya sakawa ko ya cire.

“Subhanallahi”

Na juyo jiki babu karfi na kalleta da kumburarrin idanuwana, wani tsadadden green lace ne a jikinta har kyalli yake.

“Noor...”

Ta fada cike da mamakin ganina.

“Lafiya me ya same ki? Jini kike zubarwa”

Na sauke kaina kasa na kalli kafata zuwa tile din da jini ya bata gurin da na taka na juyo. Kamar jira ake na kalla sai jiri ya kwashe ni a gurin hudu ya rufe idona marata ta hau murdawa da wani irin radadi da ban taba jin irinsa ba, zafin har cikin bayana yake kai min. Bana iya ganin komai sai muryar Mama da nake ji tana rikona tana kiran sunan wata da ban san wacece ba, a gefe daya kuma ina jin wayar da Kareem ya saka min layi ya ba ni tana ringing...






KAREEM POV.


Sai da ta fice sannan ya nufi tissue da ta aje ya dauka ya kai hancinsa ya shinshina, yayi baya baya ya zauna ya jinke tissue din.

“I deserve this, i lost everything, babu wani abun da ya rage”

Ya aje tissue din, be yi addu'a ko fatan Noor ta fito ko wani abun ya sameta a aurenta ba. Shiyasa a lokacin da ta yi auren ya ayyana a ran cewar ya rasata, na tattara lamarinta gaba daya ya aje a gafe, not because of baya sonta but because of yana mata fatan samun farinciki da zaman lafiya, duk kuwa da ya san ba lallai ta samu hakan ba. Saboda Safeena da kuma mijinta.

But fada mishi cewar ba zata iya mazinaci ba ko da ya tuba it break him into piece, ya san ya rata ta kenan har bada.
Bayan ita kuma babu wata, bayan farincikita babu wani, bayan sonta babu wata, bayan burinta babu wani.

“That's okay, it alright Kareem...”

Ya furta yana encouraging kansa, ya mike tsaye kenan wayarsa ta yi ringing. Daukar wayar yayi ya duba wata bakuwar number ce da be santa.

“Hello..”

“Wallahi... Wallahi... Wallahi... Idan Noor ta kashe min aure, kuma ta zama silar tonuwar asirina sai na sai na shuka muku biyar bakinciki kai da ita, domin ba laifinta ba ne ita kadai, har da kai kai da ka fada mata sirrina saboda kana sonta, bata isa ta lalata min rayuwa kuma ita tace zata yi rayuwar jindadi ba”


“Excuse me”

Ya fada jin muryar Safeena da kuma kalamanta cikin kuka da bacin rai.

“Yes ,ina tabbatar maka wannan, domin idan bata fada masa wani abu ba babu yadda zai shigo, haka kurum ya kwashi yara da sunan yawo sai da suka dawo suke fada min asibiti ya kai su aka debi jininsu, kuma duk kai ne sila ai Kareem”

Ta kashe wayar tana kuka. Faduwa Kareem yayi zaune saman kujera hannuna rike da wayar ya rufe ido ya dafe kansa.

“Noorrrr...! Kai...! Meyasa na aikata ma to? Ita lu'u lu'u ce da na tsallake hanin da Allah yayi na aikata? Why from first plate?”

Ya rumtse ido sosai yana jin kamar ya hade zuciya ya mutu, ya san abun da zai biyo baya ba zai musu dadi ba.Na dauki awa hudu ina nakudar da ban san da zuwanta sai da muka tafi asibiti, na wahala iya wahala har na yi zaton rai zai yi bankwana da duniya ne.
Suka can na yi nishi na yunkura ina ta kokarina, amman kamar bana yi, ban yi zaton haka haihuwa take da da wahala da ciwon fa azaba ba sai da na kai matakin.

A lokacin da likitoci suka bada shawarar a shiga ni tiyata domin ceto rayuwata da rayuwar abun da yake ciki ganin na kasa haihuwar, na katse sosai na yi zaton idan ana shiga da ni ba zan fito da rai ba. Sun fada idan ba ayi haka ba zan iya samun matsala ko abun da ke ciki ya samu, domin haihuwar ce ta zo min babu abun da ya isa ya tare, ma'ana dai zan yi haihuwar bakwaini kamar yadda aka haife ni.

Cikin ikon Allah da rahamarsa kamin asuba wani karfin ya zo min, yunkuri daya biyu a uku kan yarinya ya fara fitowa, da na sake yunkurin ta kara fitowa, likitan da ya karbi haihuwata ya yanka gurin ya janyo babyn, azabar sai ta zame min kala biyu, ba ma kamar lokacin da ake dinkewa. Ko ba a fada min na sani yata bata so da rai ba, domin ban ji kukanta a lokacin da ta fado duniya ba. Sai dai ban tabbatar da sai bayan da aka min wanka aka gyara min jikina aka canja tufafina. Sannan Mama ta sake shigowa domin da taimakonta aka yi min komai. Ta shigo dakin da fuska a kumbure da alama ita ma ta yi kuka kamar ni.

“Sannu ya karfin jikin na ki?”

“Alhamdullahi”

Na amsa ina jin maganar ma kamar ba zan iya ba. Domin babu ragowar karfi a jikina kamar ba na da kashi haka nake ji.

“Mace kika haifa, amman bata zo da rai ba, na bada ita can gurin dangin mahaifinta, saboda Mahaifiyarki Abdull ta karba”

Abu ne da na riga na sani kuma na fahimtar da kaina. Amman da Mama ta fada min sai na ji wani irin babu dadi. Duk wahalar da na sha babyn bata zo da rai ba. Tea mai kauri Mama ta miko min na karba na sha rabin kofin sannan na aje sai ta miko min wayarta.

“Kin ganta nan”

Na karbi wayar na kalli hoton yarinyar mai kyau da jiki kamar ba yar wata bakwai ba, fara kyakkyawa kamar na kirata ta amsa amman babu rai, an lullube ta da zane gwanin sha'awa.

“Yi hakuri, Allah ya baki wata mai albarka, ita kuma Allah yasa mai ceto ce, na tsorata da nakudarki kin wahala har hankalina ya tashi”

Na share hawaye na mika mata wayarta.

“Mama baki ga waya a jakata ba?”

“Na gani, kuma na ga kira na amsa sai na ji muryar abokiyar zamanki wai zaki kashe mata aure Wallahi sai ta ga bayanki, da ta ji muryarta ina mayar mata da martani sai ta kashe bata sake cewa komai ba, fada kuka yi?”

Ta banbare magani ta miko min na karba na sha.

“Aa ba ni wayar na duba abu”

Ta bude jakarta ta dauko wayar ta miko min, sannan ta dauko ragowar tea da na aje ta ba ni.

“Daure ki shanye Noor kamin anjima sai ki ji jikinki ya sake, wata kila zuwa gobe su sallame ma idan ba wata matsalar ta biyo ba, yau dai sun ce zaki wuni a nan ki samu bachi”

Ba tare da na musa ba na karba na shanye na aje cup din sannan na duba wayata ko zan ga sakon Hana amman shiru.

“Ina kika bar Hana ya aka yi kika zo a tare da ita ba? Na kira wayarta kashe mijinki kuma na yi ta kira be daga ba, shiyasa na kira kanwarsa da uwargidanmu na fada musu, su suka kira mahaifiyarsa suka fada mata, kanensa ma jiya duk suna nan mahaifiyarsa kuma a nan ta kwana, ita ta tafi da jaririyar ma, shi din ne dai be kira ba”

Wata zuciyar tace na yi mata karyar cewar Hana tana makaranta shiyasa ban zo tare da ita ba. Sai dai tunawa da shawarar da Kareem ya ba ni ya saka na yanke shawarar fada mata gaskiya.

“Daman kin ji alamar haihuwar ne kika dawo? Ai kara da kika yi haka a can babu kida kowa sai Hana ita kuma yarinya ce ba sani komai kuka yi ba, ko da yake likitoci ne suke yin komai, amman dai hankali ba zai kwanta ba kara da kika haihu a gida”

Na daga kai a hankali na kalli fuskarta, wani tea take kokarin hada min.

“Mama”

“Na'am”

Ta kalleni.

“Hana bata tare da ni”

Ta kalleni da sauri.

“Kamar ya?”

“Wani abu ne ya faru, shiyasa na dawo gida ba haihuwa na dawo ba, kuma na dawo ne da takardar saki, Abdull ya sake ni”

Ta dauke hannayenta daga tea da take hadawa na biyu tana kallona.

“Ya sake ki? Me ya faru? Me kika masa?”

“Ban masa komai ba...”

Bata bari na karasa ba ta fara min fada.

“Karya ne, ba zai sake ki ki dawo gida da ciki wata bakwai haka kawai domin jindadi ba, akwai abun da kika yi?”

Na kalleta idanuwana na cika da kwalla.

“Me yasa kullum ni ce mai laifi Mama?”

“Saboda baki jin magana, ba ki tunani kamin ki aikata abu, gaba daya ke ba rayuwar aure ce a gabanki ba, shiririta kawai kika saka a gaba, wacan auren na farko ma be dade ba ya sake ki, yanzu kuma wannan da ciki ki dawo ki haihu ina murna ki ce min wai ya sake ki? Kin san farincikin da uwa take ji idan ta aurar da yarta Noor? Zaman aure nake son ki ji ba jeka ka dawo ba, yanzu mutane za su fara magana, ba ki gudun abun fada, daman an raya cewar ba zaman aure zaki yi ba, ke dai kin ki zaman aure Noor kin ki zauna”

Ta karasa tana kuka, ni ma kukan nake marar sauti.

“Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min liyi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zan bi...”

Na lumshe idanuwa.

“Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna a yanzu, gashi har kaddarata ta shafi yar'uwata”

A take ta daina kukan da take.

“Me ya faru me ya samu Hana?”

“Abdull ya keta mutuncinta, har ciki ya shiga....”

Faduwa Mama ta yi kasa zaune a lokacin da na labarta mata abun da ya faru, ba kuka take ba tagumi ta yi tana kallon kasa.

“Yanzu tana ina?”

“Ban sani ba”

Ya cije baki ta rumtse ido sosai tana girgiza kai. Tashi ta yi ta fice daga dakin ban sake ganin kowa ba sai misalin bakwai wata nurse ta shigo ta yi min allura ta ba ni magani na sha, sannan ta ce anjima likita zai zo ya duba ni, wata kila a sallame ni yau.

Haka kuwa aka yi likitan ya zo ya duba na fada masa bana jin komai a yanzu sai rashin karfi sai kuma gurin da aka min dinki ne kawai ke zafi. Magani ya rubuta da allurai masu yawa sannan ya bani takardar sallama misalin karfe biyu na rana. A lokacin Gwaggo Saude da Anty Larai suna asibitin sai kuma kanen Mama biyu. Kai tsaye gidan Baba aka wuce da ni a can ko da muka je mun samu Umma ta dora ruwan zafi, babu bata lokaci ta zuba min a zuba na shiga bandaki na xauna a cikin ruwan da ta zuba shirina na zauna, ga azabar dinki ga na zuwan dake taba gurin ga kuma na zuciya da tunanin yar'uwata.

Kowa tambayar yake ina Hana take, sai karya na yi nace jarabawa suke shiyasa ba zai yiyu ta zo ba, kuma na fada musu a hostel take zama ba a gidan ba gudun zargi. Makota suka fara shigowa suna duba ni tare da addu'ar Allah ya ba ni wani mai albarka. Bakinciki be kara min yawa ba sai da dare yayi na gwada number Hana har lokacin a rufe ga kuma bakinciki na haihu amman abun da na haifa babu rai. Kofin ruwan zafin dake hannuna na je na lalabo wayar da Kareem ya ba ni na kira Mama.

“Mama”

“Noor kina lafiya?”

“Ba lafiya ba Mama, na san ke ma kina cikin damuwa”

“Ina ciki Noor Kaddara ta riga fata, ni daman ban so tafiyarta, kawai saboda kun matsa ne ke da shi, kuma da san hakan zai kasance da ban bari an yi auren nan ba, ina masa kallon mutumen kirki ne mai sanin ya kamata, jindadi nake hango miki shiyasa na goya masa aka yi auren ina farinciki”

Hawaye na zubo ido.

“Hana ta kira ki?”

“Aa, tashin hankalin kenan, ban san wane hali take ciki ba”

“Kareem yace min zai iya kokarinsa ta dawo, amman har yanzu shiru”

“Alhaji ma yace zai yi iya kokarinsa za a samota”

“Kin fada masa ne?”

“Na fada masa cewar daga tafiya makaranta ta bata, ban fada masa abun da dansa ya aikata ba, idan maganar nan ta fita Noor Hana ba zata taba aure ba, babu wanda zai aureta abun yayi muni, fyade kuma har ta yi ciki? Babu wanda zai karbi wannan kadarar, kuma zata kunyata a unguwa zata zama abar kwatance”

“Shiyasa ni ma ban fadawa Baba ba, na masa karyar cewar tana hostel din makaranta, saboda bana son Umma ta ji ta yada, amman kuma Mama haka zamu bar Abdull ya tafi a free?”

“To ya zamu yi? Sai hakuri, ni dai Allah ya kawo min Yata”

“Ameen”

Kiran Mama na fita wayata kiran Hana ya shigo, jiki na rawa na daga.

“Hana”

“Noor”

Na daga sai na ji muryar Kareem, fashewa na yi da kuka.

“Dan Allah karka ce wani abu ya same ta, dan Allah karka ce ta mutu ka, na haihuwa yata bata zo da rai ba, i lost my baby, bana son sake jin bad news, ya isa haka yanzu”

Ina maganar ina kuka sosai sai ya kashe wayar hakan ya tashi hankalina sosai, domin na fahimce ba ya tafe da labari mai dadi, idan ba haka ba me ya kai wayar Hana hannunsa? Me yasa ita ba zata min magana ba? Na dafe zuciyata ina numfashi daker.

“Ke Lafiya me ya faru?”

Na kasa magana sai kuka nake...





KAREEM POV.


Yayi ending call din ya nufi wani motarsa ya dafa kamar wanda ya rasa abun yi. Kamin ya dago ya kalli gate din da aka bude motar Safeena ta doso harabar gidan, yana tsaye yana kallonta har ta karaso ta faka motar ta fito sanye da atamfa sai mayafin da be gama rufe jikinta.

“I thought i warning you karki sake na yanke duk wata alaka da ke”

“Alakata da kai ba zata taba yankewa ba, do you want us to talk about it a nan ko mu shiga ciki?”

Ya kalli Mai gadinsa da ya gama rufe gate ya kira shi, ya zo da sauri yana sassarfa.

“Ga ni ranka ya dade”

“Kalli wannan matar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login