Showing 66001 words to 69000 words out of 133189 words

Chapter 23 - Taki Zaman Aure Book 2 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

264

ba, ki kirashi da suna Alhaji kamar yadda kowa yake kiransa a gidan nan, wato ke dai sakarcin ki ba zai canja ba ko?”

Na yi shiru ina kallon Yaya dake cin taliyar, sannan na soma cin tawa. Rabin abincin kawai Yaya ya ci ya sha ruwa yace zai tafi.

“Da wuri Nabil na yi zaton sai dare, saboda Alhaji ya dawo ku gaisa, yana ta fadar ban taba gabatar masa da sauran yarana ba, be san kowa a cikinku ba sai Hana da ke yawana zuwa”

“Bana son na kai dare Mama, akwai guraren da ya kamata na tafi kamin ba bar garin nan, kuma kin ga kwana biyu ya rage min”

“To sai dai kai ka tafi Noor kuma zata tsaya sai ya dawo kun gaisa tukuna ta wuce”

Mama ta shiga dakinta ta dauko masa babbar leda cike da kaya sannan ta danka masa 20k tana ta sakawa Kareem albarka wai daman a yanzu tana ta tunanin wace makaranta zata nemawa tarin kudin da take shi take yi ma, amman gashi ya dauke mata nauyi. Bayan Ya Nabil ya wuce muka zauna da Mama muna hira take tambaya ko Zafeer ya ji rayuwar Mijina.

“Zai iya ji tun da iyayensa suna cikin unguwar, ko basa nan ma ai yan gulma suna nan, fitowar nan ma cewa suke ta yi hakkinsa ne”

“Zafeer yana sonki sosai, zai iya dawowa yanzu ma, wata kila kuma iyayensa su hana shi, ko da yake a can baya ma sun yi ta kokarin hana amman ya nace sai ke, gashi kuma an watsa masa a ido, Wallahi mahaifinku be kyauta ba”

“Baba ma da yace be yafe ba idan na sake masa magana, shi ne abun da ya fi damuna”

“Wai har yanzu? Toh ai Hafiz din baya raye kuma, yanzu idan Zafeer ya dawo ba zai bari ya aureki ba?”

“Ban sani ba, amman da kamar wahala saboda yana ganin Zafeer talaka ne”

“Haka ne, ubanki be ji wani yare sai na kudi, gashi babu mai iya ja masa liyi a dangi komai yayi daidai ne a idonsu”

Na daga kai ina kallon POP din falon.

“Taso mu tafi ki gaisa da mutanen gidan, suna ta tambayar, da kika fita wanka ma sai da matarsa tace zata tafi ta duba ki kuma Allah be yi ba”

“Ita bata kishi ne Mama?”

“Ana tabawa mana ayi mace babu kishi, amman boyewa ake na ciki na ciki, ita dai tana da kirki ba kamar wasu ba”

“Ko dai irin na Aisha take miki ba, haka take nuna min ba komai ashe wayo take min”

“Ke dai da halinki Noor, na san ki ba, kuma zamanmu a nan Alhaji ya fada mace kamar riga take a wuyansa duk wanda ta daga masa hankali cire ta kawai zai yi ya aje, duk tarin yaransa babu wanda uwarsu take cikin gidan nan, sai wannan matar da yaranta uku, sauran duk iyayensu sun fita, ni ma sai bayan auren nake ji, wata kila shiyasa ta kama kanta”

Ina jin haka na san an gudu ba a tsira ba ne, kenan ita ma idan ta yi masa ba daidai ba zai iya sakinta. Daga bangaren Mama muka fito muka shiga bangaren matar da take gidan a yanzu. A cike muka samu falon da mata da maza, Mama ta yi sallama suka amsa suna gaisheta da mutunci.

“Noor Ya hakuri?”

Wata budurwar da ban waye ta ba ta fada sai na amsa da Alhamdullahi na gaishe da Hajiyar.

“Lafiya Kalau Noor, an fita wanka ko? Tohm Allah ya bada hakuri ya kawo na gari”

Mama ta amsa da Ameen.

“Alhaji ne be santa ba sai mita yake ina boye masa yara, tare da yayanta take jibi zai wuce Sudan gurin karatu, ya zo bankwana amman be tsaya ba, ita kuma ba ce ya tsaya ta gaisa da yan gida”

“Ta kyauta gaskiya, da ma dai kin maido nan kila zata fi jin sanyi kin san gidan na mu cike yake da mutane”

“Mahaifinta ne ai be yarda ba, ko takaba a nan ya so ta yi amman uban yace ba zata yi ba”

“Kin san wasu mazan akwai kishi”

Haka dai suke ta hirarsu ni dai kaina na kasa ban dago har sai da na ji an bude kofar falo alamar mutum ya shigo. Dagowar da na yi sai muka yi ido hudu da Safeena tana dauke da cikinta da be gama girma ba. Bata kallon kowa sai ni ni ma kuma bana kallon kowa sai ita muka rika kallon kallo wata kila ita ma tana mamakin ganina ne kamar yadda nake mamakin ganinta. Gidansu ne? Ko kuma zuwa ta yi? Ko kuma dai tana da wata alaka ce da mutanen gidan?

“Kin dawo Safeena?”

Hajiyar ta fada sai Safeena ta amsa mata ba tare da ta kalleni ba, har lokacin ni take kallo.

“Na dawo Hajiya, na karbo files din gobe zan tafi asibitin na kai”

“Toh Allah ya taimaka ya raba lafiya”

“Ameen”

Ta amsa sannan ta dauke idonta ta zauna a kujerar dake facing dina, sai kuma ta sake dasawa daga inda ta tsaya.

“Anty Safeena kin santa ne?”

Na kalli mai tambayar wata kila su ma sun lura da kallon da take min yayi yawa. Ga mamakina sai ta amsa da cewar

“Aa ban san ta ba, wacece hala? Ta yi min kama da wata kawata ce ta yarinya”

“Noor ce yar wajen Anty Amarya, wanda mijinta ya rasu”

“Allah sarki Allah ya masa rahama”

Ya juya tana kallon Mama dake amsawa da Ameen sannan ta sake kallona. Har muka baro bangaren babu abun da take sai kallona kamar wata bakuwarta. Ban kuma san dalilinta na boye cewar ta san ni ba. A bangaren Mama na koma na zauna har dare ina jiran dawowar mijinta saboda mu gaisa, be shigo ba sai bayan Magariba a lokacin da ake hada hadar Sallah Isha'i.

Na yi mamakin yadda yayi murna da farinciki ganina babu wata kyama, har na na yi sha'awar ina ma ace shi ne mahaifina ba Baba ba, zaunawa yayi a falon yana ta min nasiha akan hakuri da rayuwa na halin da na samu kaina da kananan shekaru, na yi masa godiya ya saka hannunsa aljihu ya ciro 10k ya ba ni.

“Aa na gode”

A bakin gaskiya ta ba zan karba ba, domin ko na karba ban san miye zan yi da su ba a yanzu. Sai dai na lura hakan be masa dadi ba domin rufe ni yayi da fada a dole na karba na yi masa godiya.

“Tafi bangaren Hajiya ki ce na ce cikin yaran nan duk wanda yake nan ya sauke ki gida”

“Tohm”

Na mike tsaye na yi ma Mama sallama sannan na fice daga falon yana ta kallona. Bangaren Hajiyar na dawo na sanar mata abun da Alhaji ya fada sai mutumen dake tsaye a gabanta yayinda take zaune ya juyo ya kalleni. A nan ma wani mamakin ya kara kama ni, mutumen nan da ya taba yunkurin biya min kudin siyayyar da na yi a wani dare da muka fita tare da Hafiz.

“Kamar na sanki?”

Na bude baki kamar zan yi magana sai kuma na yi shiru, ban san me zan ce ba, ni dai ina da saurin gane mutane shiyasa na gane shi.

“Noor ce Yar wajen Anty Amarya ce, ita ce wadda mijinta ya rasu”

“Ai ban sani ba, Allah ya jikanshi da Rahama”

“Ameen, ku tafi tare sai ka sauke ta ka wuce, Noor bari ga Abdull zai fita yanzu sai sai ya wuce da ke, ki jira shi a waje”

“Okay”

Na juya na fito daga ciki, ban san wacece motarsa a cikin motocin gidan ba dan haka zauna a balcony har ya fito.

“Kika zauna a kasa?”

Bance komai na na mike tsaye na bi bayansa muka isa gurin wata sabuwar mota, sai da ya fara shiga sannan na bude na shiga front seat. Ba tare da yace min komai ba yayi reverse ya fice daga gidan.

“Ina ne unguwarku?”

A lokacin da na dago sai na ga idonsa akaina suke. Na fada masa na sake maida kaina kasa kamar ba ni ba. Na ji lokacin da wayarsa ta yi kara ya amsa.

“Hello Safeena...”

Sai kuma yayi shiru, yana sauraren abun da ake fada masa.

“Yanzu na fito gida, amman zan biya ta can, sai na zo miki da shi, shi kadai kike so ko da wani abun?”

Na yi shiru ina saurarensa kamar wata Munafuka kamin na ji ya ce.

“Okay sai na dawo”

Ya aje wayar ya dago zan kalleshi idona suka fada cikin nasa da sauri na dauke kaina ina jin sautin murmushinsa. Ban sake kallon gefen da yake ba har muka isa unguwar.

“Ka sauke ni a nan unguwar bata da kyau can ciki”

Na fada.

“Karki damu, amanarki aka ba ni sai na kai ki har gida”

Yadda ya fada haka ya aiwatar har kofar gidanmu ya isa da motarsa ya faka, ni kuma na bude na fito zan rufe kofar ya ce.

“Ba godiya”

Ban ce masa komai ba na rufe motar, na gode masa sai ka ce rokonsa na yi ya kawo ni. Sai da na shiga gida sannan na ji motarsa ta bar kofar gidan.






KAREEM POV.

Yana gama sallah asuba ya shiga kitchen hadawa yaransa breakfast. Domin Yusura bata musu komai tun da ta dawo gidan, Kullum shi zai hada musu breakfast ko kuma ya saka aika musu daga restaurant dinsa kamin su tashi break.

And now cooking is one of his favorite things, yana samun nishadi a girkin, musamman idan yaran suka farka suka same shi a kitchen suna hayani yana aikinsa har ya gama, ya karya tare da su wani sa'in kuma ya zuba musu na su, ya tafi da nasa a office ko kuma su su tafi da na su school shi kuma ya ci a gida. Idan ya fita sannan Yusura take saukowa ta gyara ko'ina ta dora na rana. Tun da ta dawo gidan be taba leka dakinta ba, be taba ce mata uffan ba, ita ma kuma bata bari sun hadu ba, da zarar ta ji motarsa ko ta san lokacin dawowarsa sai ta shige dakinta.

Yau ma sai da ya raka su har gurin bus sannan ya dawo ya zauna ya ci nasa breakfast. Bayan ya gama ya mike tsaye ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya fito yana rike da lab coat dinsa da wayarsa sai kamshi yake zuba. Yayi kyau sosai ramar da yayi ta kara masa kwarjini da haifa. Sai da ya fice daga falon sannan Yusura ta sauko a zatonta ya fice gaba daya, dinning ta nufa ta tsaya tana kallon kayan karyawar da ya shirya, biredin da ya gasa ta dauka taba tabe baki ta shinshina ta aje.

Sannan ta ja kujera ta zauna ta bude flask din ruwa zafi, a daidai lokacin Kareem ya turo kofar falon ya shigo domin daukar wallet dinsa da ya manta a dakinsa. Kallo daya yayi ma gurin da take zaune ya dauke kai ya haura sama ya dauko wallet dinsa ya sake fice. Yusura bata taba jin kunya irin ranar ba, bayan amincewa da aurensa da ta yi wannan ne abu da na biyu da take bakinciki a rayuwarta, ji ta yi kamar ta fasa komai na gidan dan bakinciki.

Tuki yake a hankali har ya isa asibitin, ya faka motarsa a gurin da aka rubuta Dr Kareem sannan ya fito ya dauki kayansa ya rufe motar ya shiga cikin Babbar asibiti ana miko masa gaisuwa yana amsawa. Office dinsa ya shiga ya fara duba takardun dake gurin sannan ya fita ya fara duba marar lafiyar da aka aje da ya kamata ya duba su.

After ya gama ya dawo ya zauna a office dinsa patient din dake shigowa suka fara shigowa yana dubata. Third person da ta shigo ita ce Safeena, tana sanye da dogon Hijabinta har kasa sai dai hakan be boye cikin dake jikinta, har ta zauna ita yake kallo. Sai da ta aje jakar dake hannunta sannan ya jingina baya ya kwanta jikin kujerar yana kallonta.

“Wai ke wace irin yarinya ce Safeena?”

“Ni din wata yarinya ce, mai wuyar warke ciwo, wata yarinya ce da ka koyawa soyayyarka kuma kake kokarin guduwa bayan ka yaudareta da farko”

“Gargadin da na yi miki, da kuma tazarar da na baki daga lokacin da muka yi haduwar karshe zuwa yau bata fahimtar dake, na rumgumi kaddarata, ke ma ki rumgumi taki?”

“Ka rumgume kaddara saboda Yusura tana sonka tana kyautata maka a yanzu? Ko kuma daman can karya ka yi min kace bata kula saboda kullum ka rika samun biyan bukatarka da ni? Ka yi breaking heart dina da farko yanzu kuma bayan na saba mu'alama da kai na saba da kwanciya a kirjinka na saba da soyayyar kake tunanin sake guduwa ka bar ni?”

Ya mike tsaye daga zaunen da yake ya nufi windows dinsa ya bata baya.

“Kana da kyau, Kareem kana da kudi amman duk wannan be tabbatar min da ina sonka ba sai da mu'amala ta hada mu, all this while na kyale ka ne saboda ina dauke da cikin nan”

“Me kika zo yi yanzu? Tashi ki fice daga office din nan”

“Baka da wannan damar ba saboda da kai na zo ba, saboda cikin nan ne, na dawo da awon cikin nan a nan ne, a nan zan yi ta zuwa har zuwa lokacin da zan haihu”

Ya dafa Window ya rike kansa.

“Namiji zan haifa suka ce, kuma ina alfahari da haka”

Kareem ya dauki lokaci a haka kamin wani tunanin ya zo masa sai ya juyo da sauri ya kalli cikin na ta sannan ya kalli fuskarta, sai ta yi masa murmushi.

“Fita ki bar office din nan”

Ya nuna mata kofar, zata sake magana da daka mata tsawa har sai da ta zabura.

“Fita ki bar office din nan na ce”

Ta mike tsaye da sauri ta dauki jakarta tana kallon yadda ya hade fuska kamar be taba ganinta ba, ta fice daga Office din. Dawowar yayi ya zauna kan kujerar ya dafe kansa ya runtse ido yana numfashi da karfi, ya girgiza kai kamin ya daga hannunsa ya buga a tebur din yana jin wani irin bakinciki marar misaltuwa...

It could be a joke maybe tana gwada shi ne, if not ai tana da hankali matukar ba wata manufa take da ita akansa ba ba zata taba sha'awar haihuwa da shi alhalin tana da aure ba, ta dauki dawainiyar cikin da ba na mijinta ba ta kai masa yayi komai, ba zata fara ba. Abun da zuciyarsa ta raya masa kenan har ya ji ya samu saussaucin cigaba da aikin da yake. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi ya tuna da ba shi da abokin hira ko shawara a yanzu domin Hafiz is no more balle ya fada masa hasashensa ko damuwarsa.Baba yana kallona ne kamar ni na kashe Hafiz saboda, Hafiz ya tafi be samu kyautatawa Baba kamar gyara masa gida ko kuma yi masa wata babbar kyauta da yake tsammani ba tun a bayan aurena.
Ni ma ban fahimci hakan ba sai a ranar da Hafiz ya cika sati daya da barin duniya, Mama ta kira waya tana kara kwantar min da hankali, bayan mun gama wayar ne Baba ya rufe ni da fada wai na ci amanarsa wata kila da na kyautata masa da yanzu Allah kadai ya san yadda rayuwa zata zame mana.

“Daman sai da zuciyata ta raya min ba zaman lafiya kike da yaron nan ba, saboda juya min baya da yayi ko lokacin da gobarar nan ta tashi be zo yayi min jaje ba, be ba ni komai ba, ashe ma ba zai dade duniyar ba, kina ta shuka masa rashin mutunci, in ba shi ba taya za su ce wai ba za ki masa wanka ba? Ta ina aka taba haka so suke su hana miki gadonsa kenan”

Ni dai bance komai ba, gaba daya duniyar bata min dadi, ni kaina ina dorawa kaina nauyin da ba zai gogu ba saboda hana mijina hakkinsa da na yi, ya tafi da abun a ransa kuma na daukarwa kaina zunubi.

“Wallahi zan iya kararsu akan haka, domin babu hujjar da tace ba za a baki gado ba, na bincike limin yace kina da hakkin wanka domin an riga da an daura muku aure, kuma sakin da yayi miki ai ba ki cika idda ba”

Sai a lokacin na kalleshi cikin wani irin rauni da damuwa na ce.

“Baba dan Allah ko da sun ce ba za su ba ni hakkin wanka ba, dan girman Allah dan Isar Annabi, Baba kar kace zaka yi kara ko fada ko kuma daukar wani mataki, dan Allah ka kyale su, idan ma ina da hakki Allah ya sani zai saka min”

“Toh haka za a zuba musu ido su ci su cinye hakkinki Noor? Idan aka karba ai ko wani abun a rage da shi, dubi yadda gidan nan yake fa, ko gyara aka yi ba a rage ba? Allah kadai ya san abun da bawan Allah nan ya bari”

“Ko ma dai miye bari Baba mai karewa ne, rayuwar ma ta kare balle kuma abun da rayuwarta ta aje, ni dai da zaka yarda da magana ta Baba da ka yi hakuri ka kyale komai dan Allah”

“Ai daman ke sakarya ce baki san komai ba, sai shashanshanci, ba dan kin nuna masa rashin tarbiya da rashin hankali ba yaushe zai sake ki? Allah ya wadarranki Noor, duk yadda nake ganin kamar zaki natsu ko ki yi hankali ba zaki taba yi ba, duk yadda bake ganin kamar sanadinki wata kila zan warke sai kin kunyartar da ni, ke dai har abada va yar arziki ba ce”

Ya rufe da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai kam na san ban yi dacen abubuwa da yawa ba a rayuwa ciki har da uba. Domin ko a labari ban taba jin uba makamancin nawa ba, mai tsananin kwadayi da son abun duniya.
Na sani sarai idan na kara wata maganar zai iya rufe ni da duka, a dole na yi shiru na ina ta sauraren masifarsa har yayi ya gama ya fice daga gidan. Haka na gagara tashi a gurin har Hana ta dawo daga makaranta ta same ni zaune a kofar dakin, ni ba kuka nake ba damuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login